ME ZANYI DA ITA Complete-2
ME ZANYI DA ITA Complete-2
♡*
NAZEEFAH SABO
NASHE
FREE📚
08033748387
Da sanyin safiya ta fito daga rugar fulanin cikin wata bukka dake daga gefen rugar
sanye take da kayan fulani irin usul din fulanin nan fuskarta a cunkushe da
mabayyanin ‘bacin rai. Tana tafe tana kunkuni alamar ba dan son ranta ya fito ba.
A saman buzu ta tarar da kakanta Na gurin uba moddibo wanda ya kasance gawurtaccen
malami a garin nutsuwa tayi sosai don shi kad’ai take tsoro a garin , ta ra’be
gefensa ta tsuguna sai da ya kai aya sannan ya d’ago ya kalleta fuskarsa ba yabo ba
fallasa yake amsa gaisuwar da take masa “ Gashi inji innaji tace tana gaidaka “
moddibo ya girgiza kai had’e da jan’kwaryar yana girgiza kai “ ‘yar nema ai Na zata
yau ma kinyi halinnaki kin zubar dashi wallahi da yau ma sai na zaneki dan na lura
sam ke baki tausayin innarki idonki a tsakar ka yake d’auki ki kaiwa salame Ta
adana shi a ciki” mi’kewa tayi zuciyarta a tunzire kamar ta kai masa mari ita fa ta
tsaneshi bata ‘ki ya she’ka barzahu ba don ya takura mata baki kamar shantu ta
fad’a a zuciyarta zanyi maganinka aradu gobe. A tsakar turken tumaki ta tarar da
ita salame ta amsa gaisuwarta tana kar’bar’kwaryar nonon fuska a sake tace “ya
jikin innar taki?” “ ba sauki sai na Allah yo wannan uban ciki yayi mata turtsitsi
ta ina zata samu sau’ki Idan ba haifeshi tayi ba aradu duk ranar da Ta haife abin
da yake cikinta sai na jibgeshi “ salame ta zaro ido tana kallon shatu da take zaro
zance “ashe kuwa dai shatu da ake cewa baki da kai zancen ya kusa tabbata jaririn
zaki jibga?” Ta ta’be baki “ yo idan ban jibgehi ba ai aradu ban haifu ba a cikin
innaji ko sallah fa a zaune take yi gashi tun a ciki shegen karanbani garai yayi ta
kwarafniya jiya fa ina kallon cikin yana wutsilniya wallahi tana cin abinci kika ji
d’if tun kan yazo duniya ma ya nuna halinsa” salame ta girgiza kai tana
katse’kwaryar ta mi’ka mata daidai lokacin da modibbo ya shigo yana dogara sanda “
to uwar shashashanci kina nan kina zuba kamar ‘ya’yan kanya zo ki wuce ki kai mata
rubutun Allah ya raba lafiya” “ ameen “ ta furta murya can ‘kasa “ ai kai na gado
a kwakwazo duk gari an sani” mai kika ce “? A guje ta arce tana fad’in cewa nayi
Allah ya tashe mu lafiya salame kuwa girgiza kai tayi don ita taji abinda tace
sarai don dai shi ma kunnensa yana da matsala ne.
Tun a hanya take Allah-Allah taga d’aya daga cikin yarannan sai dai bata gansu ba
haka ta koma gida ranta a ‘bace da rashin cikar burinta.
Tana shiga innaji ta kar’bi rubutun had’e da nuna mata buta ta san nufin innaji
tunda lazimi take ta sunkuci butar ta fara alwalar. A nutse ta tada sallah duk da
rashin jinta innaji Ta tsaya sosai wajen bata ilimin addini don masaniyace sosai Na
boko ne dai sai taga dama take zuwa ko idan an tura ta ta shige gonakin jama’a
tayi’barna.
Suna idar da sallah innaji ta ri’ke hannunta murya a raunane tace “ shatu jikina
yana bani kamar rayuwata tazo gangara don haka ya zama dole yanzu Na sanar dake
labarina ko da nan gaba zaki bu’kaci haka a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido ga
mahaifinki tsawon wata biyar da tafiyarsa har yau ba amo ba labari daga tafiya
fatauci ina son ganinsa ban san ina ya tafi ba.” Hawayene ya ciko a idanun shatu
sam bata son taji innaji tayi mata zancen mutuwa ta lura kuma kwana biyu kullum
zancenta kenan. “ innaji don Allah ki daina min zancen mutuwa idan kika mutu an
higa uku “ baki shiga uku ba shatu Allah yana tare dake kuma kina da gata tunda
moddibo yana raye balle nasan mahaifinki komai dad’ewa Zai dawo ki share hawayenki
burina kawai ki nutsu “ fad’awa jikinta tayi “don Allah ki daina cewa zaki mutu ni
kece gatana “ innaji murmushi tayi tana kallon zallar yarinta a idon shatu da Ba
zata gaza shekara sha daya ba. “ To ki dinga addu’a Allah ya rabamu da cikinnan
lafiya naga aurenki shatu “. Da sauri ta furta ameen “
Har dare tana son jin labarin da innaji zata bata amma kuma tana tsoron zancen
mutuwa don haka tayi mu’kus.
Cikin dare ta kasa ha’kuri ta mi’ke zaune “Innaji baki bani labarin ba “ murmushi
innaji tayi don tasan shatu da son jin zance ta mi’ke zaune da ‘kyar ta jingina da
bango.
*********. **********
Asalina haifaffiyar garin liman katagum agarin bauchin yakubu sai dai mahaifiyata
yar asalin mambilace a jihar yola acan mahaifina ya ganota ya aura shi yasa zaki
ganmu da asalin kyau na fulanin usuli.
Mahaifina d’an bokone mu biyu iyayena suka haifa daga ni sai yaya ta dijama.
Kasancewar mahaifina lecturer hakan yasa ya dage akan harkar iliminmu. Muka taso
cikin tarbiyya da ‘kaunar juna ni da yayata mai tsananin kama dani ta girme ni da
shekara hud’u. Yayata tana gama secondary samari su kayi mata ca hakan yasa babanmu
yace dole ta fitar da miji duk da kasancewarsa d’an boko baya take ilimin addini
yana bashi ha’kkinsa sosai. A lokacin ina ss 1 yayata ta fitar da miji a kayi mata
aure da wani matashin mai kud’i ahmad manga inda suka tare cikin garin bauchi a
unguwar gwallaga.
Lokacin da na shiga ss2 a lokacin muka fara soyayya da wani ma aikacin makarantar
atbu inda gidanmu yake kasancwar a staff houses muke shara yake da gyaran compound
d’in gidanmu soyayyarsa ta d’ibeni don kyakykyawa ne sosai . Ba wanda ya sani a
gidanmu a ‘boye muke komai duk da bama keta iyakar ubangiji amma fa soyayya tayi
zurfi a tsakaninmu ta yarda tabbas a lokacin idan aka hanamu aure zamu iya rasa
rayuwarmu. Duk da bashi da ilimi haka nake son shi tunda yana da ilimin addini
bokon ma a hankali nake koya masa a ba ca da. Ina ss 3 tashin hankalin ya fara zuwa
don kuwa wani d’an abokin babanmu yace yana so na babanmu kuma yace ya bashi gashi
bababnmu irin masu kafiyar nan ne sam baya juyuwa mai juyashi dama babansa ne kuma
ya rasu. Hankalina ya tashi sosai nayi kuka kamar raina zai fita na gaya wa mamanmu
bana sonsa ta fad’awa baba yace ban isa ba bai haifi dan da zai ce yes yace no ba.
Haka mamanmu tayi ta rarrashina ita da yayata amma zuciyata Ta kasa ha’kura.
Hakan ya tunzira zuciyar Baba yace ya fasa barin sai na gama jarrabawar na ‘karasa
a gidan mijina aure zai yi min.
Aka fara shirin biki hankalinmu a tashe ni da miji wannan yasa ana gobe d’aurin
auren muka gudu ni da miji. Da sassafe muka wayi gari a wata ruga ya bani kayan
fulani na saka sai da muka zo gidan ya sanar dani gidansu ne nan ya shiryawa
mahaifinsa ‘karya akan cewa iyayena sun rasu a hanya kuma fulanin tashi ne hakan
yasa suka rungumeni a gidan bayan wata biyu aka d’aura mana aure da miji duk da
kullum zuciyata na bani shawarar na koma gida amma ina tsoron mahaifina. Shakararmu
goma da aure kafin Allah ya kawo cikinki. Har yau a garin nnan ba wanda yasan ina
da ‘yan uwa sai yanzu da nake gaya miki kina zuwa liman katagum kika tambayi gidan
sarkin fulani nan ne main house na familyn babanmu koda ta Allah zata kasance. Ya
fad’a hawaye na ziraro mata na tuno iyayenta.
Shatu ma hawayen take “yanzu innaji da gatanki muke ta yawo bama nan garin bama can
mune har nan niger 🇳🇪 ashe asalinmu yan nigeria 🇳🇬 ne “. Innaji ta dafa kanta tace
“kaddarar haihuwarki ne shatu da ta wannan cikin fatana idan kin sadu da dangina
kice su yafe min na mutu ina tsananin kewarsu “. Share hawayenta tayi tace “insha
Allah innaji ba zaki mutu ba da ‘kafarki zaki ga danginki “.
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-
2
Sumul suka farka innaji ranar ta d’an ji sau’ki, har yamma shatu na tare da ita Ta
kasa motsawa ko nan da can ranar kam jikinta a sanyaye yake duk tsiwar da masifat
ta zubar tana gefen innaji a zaune kan tabarmar karauni. Innajin Ta tsefe mata
kanta Ta wanke tas da kanwa da karkashi sai ‘kyalli gashin yake yasha man kwakwa
kasancewar shatu mai gashi na ban mamaki tamkar mutanen ‘kasar hindu don ma bata
son gyarashi da ‘kyar take barin innajin ta ta’ba mata kai shima sai tayi mata jan
ido.
Har aka gama tana kwance lamo ba mai magana tsakaninsu ita innaji tana karatun
suratu maryama ita kuwa shatu ta lula duniyar tunani gaba d’aya ta rasa sukuni.har
la’asar tayi kafin ta mi’ke tayi alwala ta kuma zubawa innajin ruwan alwala innaji
ta kar’ba tana murmushi “ Allah yayi miki albarka shatu yasa ki cimma duk burin da
nake miki fata a rayuwarki “. “Ameen “ shatu ta fad’a murya a sha’ke. Suna idarwa
innajin ta aiketa gidan modibbo kar’bo rubutu.
Duk tsokanar da yara suke mata a hanya ranar banza tayi dasu burinta taje ta dawo
ta iske innaji lafiya sumul, don haka take ta sauri kamar zata tashi sama.
Kamar an cillota haka ta afka tsakargidan da sauri ta saki ajiyar zuciya had’e da
cewa Alhamdulillah Allah innaji na d’auka kafin na dawo kin mutu” murmushi innaji
tayi kafin ta furta “mutuwa ai sai lokaci yayi ayshatu” da sauri ta dubeta jin
sunan da ta kira ta dashi innaji ta waro ido tace “lafiya “ ta hau girgiza kai “
ji nayi kin kira ni da sunan da baki Ta’ba kira na ba “ dariya kawai tayi tana shan
rubutun ta had’e da kallon shatu kallo mai nuna tsananin ‘kaunar da take mata.
Cikin dare innaji ta fara jin ciwon na’kuda tun tana daurewa har abin yaci
‘karfinta ta mi’ke da ‘kyar ta bud’e wata adaka ta zaro wasu hotuna da biro ta
rubuta address din family house d’insu ta nad’e a takarda ko bakomai bata san ya ta
Allah zata kasance ba.
Da ‘karfi ciwon yazo mata har bata san lokacin data fara tashin shatu ba a razane
shatu ta tashi saboda wani mummunan mafarki da take a wannan lokacin, ganin innaji
cikin wani mawuyacin hali bata san sanda ta zunduma ihu ba tana ru’kun’kumeta “
bana so innaaji bana son mafarkin da nayi ya tabbata “. Da kyar innaji ta’ka’kalo
wani murmushi tana mi’ka mata takarda “ ayshatu ban san ya ta Allah zata kasance ba
amma koma dai yayane bayan raina ki nemi dangi na idan mahaifana suna raye ki basu
wannan takardar da wannan hoton suna gani sun san ke jini nace Ayshatu idan babanki
ya dawo kice masa ya yafe ni Allah ya yanke ganawarmu “. Hawaye take yi sosai na
tsananin azabar na’kuda. Ayshatu kuwa ta zama kamar mutum mutumi ta rasa ma mai
zatayi abinka da’kan’kantar shekaru. Sai jijjiga innaji take ba bakin magana har
zuwa sanda taji innajin ta saki kalmar shahada jikinta gaba d’aya ya saki ji kake
d’if lamarin Alhakamu ya tabbata. Ita kuwa a nata tunanin barci innaji tayi bata
san mutuwa ba bata san ya ake mutuwa ba gashi ana fad’a musu zafin fitar rai a
yanda kuwa ake kwatantawa tabbas wannan ba mutuwa bace barcine ta ayyana hakan a
ranta, don haka hankalinta kwance ita ma ta kwanta a gefen innajin barci ya
kwasheta barcin da shine ya kaita har’karfe goma na safe.
Tana farkawa ta tashi a razane tana kallon hasken d’akin tare da tunanin me yasa
innaji yau bata tashesu sallahr asuba ba. dubanta ta kai inda innajin take da sauri
ta zare ido ganin idonta a kakkafe ya kalli sama ai bata san sanda ta hau jijjigata
ba jin bata motsi yasa ta runtuma waje a guje tana Kiran jama’a “kuzo ku duba min
innata tayi barcin zomo na tasheta ta’ki tashi “ ma’kota suka shiga gidan sai gani
tayi suna fitowa jiki a salu’be ga kallon tausayi suna mata . Kalmar da taji wata
ta fad’a ne Allah yaji’kanki maryamu halinki na gari ya biki yasa ta farka daga
tunanin da take na cewa innaji barci take.aiko zuba hannu aka ta ‘kwalla’kara sai
ganinta a kayi a zube ba numfashi.
Allahu akbar kabeeran Ubangiji kenan mai yin yarda yaso a lokacin da yaga dama
Allah yaji’kan iyayenmu.
A safiyar juma’ar misalin ‘karfe sha d’aya na safe aka sada innaji zuwa gidanta
na gaskiya hawaye sai zarya yake a fuskar abokan arziki kowa ya shaida innaji bata
da abokin rigima to ita maganar ma bata dameta ba balle har ta samu abokin rigima.
Shatu zube a cinyar gwaggoji sai mayar da ajiyar zuciya take da razana har sai da
moddibo ya sake mata rubutu aka bata. To haka dama rayuwa take.
A hankali shatu ta fara sabawa da rashin innaji kullum kuwa ma’kale da takarda da
hotunannan take kwana tayi al’kawarin sai ta sadu da dangin mahaifinta. Gidansu
gwaggoji ta koma ta daina wanka ta daina komai wai ita ta gama jin dad’in duniya
tunda innaji ta tafi ta barta. Yaran mutane kuwa a lokacin ta ‘kara takura musu
musammam masu uwa raye shatu bata da ‘kiba sam amma sai ‘karfi ta gallabi mutanen
garin tun ana d’aga mata’kafa saboda rashin uwa har tausayin ya kau aka fara kawo
‘kararta wajen gwaggoji. Gwaggoji bata da fad’a sam don haka shatu take’kara
sangarcewa kullum da rashin jin da zata rakito ta kai yanzu har manya shiga
shirginsu take musamman masu gonaki da suke kuka da ita.
Makaranta kuwa tuni tayi sallama da ita ta allo kawai take yi itama don moddibo
yana cin gidansu ne da batayi ba. Gashi yanzu shi bashi da cikakkiyar lafiya yau
fari gobe tsumma.
Da rasuwar innaji jikin moddibo ya ‘kara tsananta, hakan yasa shi fara had’a
komatsansa baya so ya mutu anan ya fito ya mutu cikin ahalinsa da suke garin yola.
Itama gwaggoji hankalinta yafi kwanciya su tafi musamman saboda shatu ko bakomai a
can dangi da yawa za’a samu mai tayasu kula da ita.
Safiyar wata asabar suka fito da ‘yan ‘kullin kayansu suka fara sallama da mutanen
garin da suka yi dandazo a ‘kofar gida, duk jikinsu yayi sanyi musamman yara da
suke kallon shatu Idanunsu fal ‘kwalla. Shatun ma kuka take ta kalli yaran tana
murmushi “kuyi min tsokanar’karshe don Allah ko bakomai zan dinga tuna ku.” Shiru
su kayi mata, murya na rawa ta fara binsu d’aya bayan d’aya tana cewa “ku fad’a
mujiya mai idonta a loko....” Ai kuwa yara suka fara har ita suna kuka kuka,
dariya- dariya a haka suka rakasu har inda mai amalanke yazo ya d’ebesu tana d’aga
musu hannu suna bin amalanke , rayuwa kenan ba mamaki shikkenan tayi sallama da
garin nijar. Amma ta’kudirce insha Allah zata dawo.
Kwanansu kusan biyu suna tafiya, kafin Allah ya kawo su garin yola nan suka hau
motar garinsu demsa, daga demsa suka shiga wata’kur’kura ta isar dasu cikin
‘kauyensu gwamba. Ai kuwa mutanen garin suna ganinsu suka shiga fitowa ana murnar
ganinsu.
Bayan sun shiga cikin gidan mai girman gaske ginin’kasa suka fara yiwa juna gaisuwa
anan suke jin labarin mutuwar muji mahaifin shatu. Ashe da ya taho hatsari yayi a
garin yola hakan yasa ya bada address din family house d’insu na nan kafin a kawo
shi kuma rai yayi halinsa. Su kuma basu san inda zasu samesu ba. hankalin shatu ya
tashi ta zube wajen har iskokanta suka ziyarceta, kowa a wajen ya tausaya mata
musamman da suka ji labarin rasuwar maryamu ma. Moddibo kuwa innalillahi wa inna
ilaihir raji’una yake ja kansa yana juyawa sai gani a kayi shima luuuuu ya kifa. Ai
ko ana d’ago shi aka ga rai yayi halinsa. Nan kuwa koke- koke ya ‘karu shatu kuwa
kuka take aljannun Na sake bugeta. Gwaggoji kuwa kasa magana tayi tana taajjabin
lamarin Ubangiji ashe haka mutuwa take lokaci d’aya taji mutuwar d’anta ‘kwaya
guda da rage bata dawo daga razanin ba shima mijin ya mutu, ai ji tayi ina ma ita
ma ubangiji ya d’au ranta.
Moddibo kam ya dace ya mutu ranar juma’a aka sadashi da gidansa Na gaskiya. Haka
rayuwa take Allah yasa mu cika da imani .
Gwaggoji daga ranar bata sake samun lafiya ba. sai dai a kwantar a tayar, hankalin
shatu ya matu’kar tashi duk ta sake firgai firgai ko wanka batayi, bata so ta rasa
gwaggoji a karo na hud’u Ta san idan ta rasa gwaggoji gatanta ya gama zubewa
warwas. Mutanen nan taga basu da zumunci ko a yanzu haka ita take yiwa gwaggojin
komai hatta da gyara jiki idan ta’bata. Iyakacinsu da su abinci shima ko
yaro’karami zai iya cinyeshi.
Ranar wata juma’a da yayi dai-dai da rasuwar malam sati takwas, suna kwance
gwaggoji na nishi sans-sama tace “ shatu ko bayan raina kada ki zauna ana tunda
kince maryamu ta gaya miki inda magaifiyarki take kiyi tafiyarki can, wadannan
mutanen kowa kansa ya sani, ga ‘yan ubanci da suka a kansu ba zasu ri’ke ki da
gaskiya ba , ina jin tsoron in mutu in barki anan don haka na dad’e da tanada miki
kud’in mota.” Ta fad’a tana lalube a cikin bujenta dubu goma cif ta ciro ta mi’ka
mata. “Ki’boye shatu ki adana su Allah yayiwa rayuwarki albarka ya kareki daga
sharrin dukkan abin ‘ki, baki da wani gata sai dangin mahaifiyarki saboda haka ki
tafi can ni na san lokaci na yayi, mutanennan mugaye ne duk ‘yan uba suke da malam
dalilin gallazawar da suke mana da saran ‘boye yasa muka gudu muka barsu yaranmu ta
dalilin azabarsu su uku muka rasa don haka kema ba zasu barki ba....” tari ne ya
fara sar’keta tuni ta fara aman jini, zuciyar shatu ta bushe Ta riga ta saba da
mutuwa ta san ita d’inma mutuwar zata yi.
A Jikinta kuwa gwaggoji ta saki kalmat shahada ta mutu, ko alamar hawaye babu a
idon shatu sai zuciyarta data ke wani tu’ku’kin ba’kin ciki. Ta ja mayafi ta rufe
mata fuska taja gefe tana jan wani numfashi mai huci ta tabbata yanzu bata da wani
gata........
Sai asuba ta sanar da mutanen gidan mutuwar gwaggoji. Ba tare da wani nuna jimami
ba su kayi jana’izarta aka kaita gidanta na gaskiya.
Bayan kwana bakwai rayuwa ta canjawa shatu zancen gwaggoji ya fara tabbata, ko
abinci basa bata sai tayi musu aikatau. Karshe suka ce zata fara fita tallan nono
bayan ga ‘ya’yansu mata basu d’ora musu ba.
Cikin dare taji jatau suna shawara da d’an uwansa wai su had’a ta aure da liti
yaron da kowa ya shaida d’an Ta’addane, ai kuwa shatu a daren ta mi’ke Ta hau shiri
tabbas lokacin barinta garin yayi a yau zata tafi dangin uwarta.
Cikin duhun daren ta fito sai dai kafin ta kai ga d’arewa’karamar katangar jatau ya
hasketa. Waye nan.......
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-
3
“Waye nan” jatau ya sake fad’a da sauri shatu ta juya tayi kamar zata shiga bayan
gida, murya can ‘kasa tace “nice zan zaga ne “ tsaki yayi ya shige yana bambamin
fad’an “iskancin banza da wofi kawai ki nemi frigita ni cikin tsohon dare zan yi
maganinki mai kama da ifritan aljannu” shatu dai bata ce komai ba tabi bayansa da
harara tana sakin ‘kananan tsaki “ aradu Allah zai kaimu lokacin da zanyi
maganinku “ yana shigewa sad’af- sad’af Ta shige bayan gidan ta kuma haure’karamar
katangar ta bar gidan a guje.
Shatu duk da kasancewarta yarinya da ba zata gaza shekara sha biyu tana da wayo da
kaifin basira, hakan yasa bata sha wuyar kai kanta tasha ba, ta hau motar da zata
kaita har cikin gari sannan aka saka ta a motar garin bauchi.
*************
Tafiyar awowi ce ta kaisu bauchi ko daga nan ta tambayi motar katagum, yaran tasha
yasa ta a motar da zata kaita tafawa balewa daga can ne zata samu motar katagum.
Suna isa kuwa kasancewar gidan babban gidane bata sha wuyar nemansa ba a kasadata
da family house din nasu. Duk inda ta wuce sai an bita da kallo kasancewar tayi
kama da mutanennan da ake kira bararoji, jikinta dukun-dukun hakanan kanta she
looks very dirty.
Sam bata damu da rufe gashin kanta ba haka take tafe wurjanjan da silifas wari da
wari a ‘kafarta.
Gidane babba irin ginin mutanen da , mai dauke da d’akuna birjik a kowacce shiyya,
kasancewar nan ne ainahin gidan sarauta na garin, yasha gyara sosai da paint kana
gani dai kasan ba wahala a tattare da ahalin gidan. Fili ne fetal ga manyan bishiyu
ko ta ina. Rashin sanin inda zata yasa ta nufar wasu yara da taga suna wasan’kwallo
a harabar gidan, ganinta a gurin yasa suka arce da gudu don su tabbas zatonsu
aljannahce. Tsaki shatu taja had’e da komawa can gefe da ‘kullin kayanta ta zauna.
Iface-Ifacen yaranne ya fito da ahalin gidan a rud’e suna duban yaran da suke
fad’in “Aljannah Aljannah “ shatu ta girgiza kai tana juyosu daga waje a zuciyarta
tace “ai kuwa sai kunci ‘kwal uwarku akan iyayenku zan huce a aljannar zan zo musu
kafin na bayyana kaina “ da sauri ta hargitse sumar kanta tsaf ta mi’ke ta hau zare
ido ta shagid’e hannu d’aya, Ta dumfari babbar shiyyar da taga yaran sun nufa.
Ba zato ba tsammani suka ganta a tsakiyar filin kan kace meye iyayen yara sunyi
hanyar neman tsira sai tsohuwa dada da aka bari jikinta yana’bari tana fad’in
innahu min sulaimanu kuyi min aikin gafara wallahi ba laifina “ shatu ta cusgune
fuska ta dumfari dada ai kafin kace mai dada ta saki gudawa da fitsari a wando
ganin tana shirin fad’uwa shatu ta tintsire da dariya “ ke tsohuwa dakata kada ki
sume min ni ba aljannah bace kamar yarda kuka d’auka mutum ce ni d’iyar maryama ‘ya
wajen d’anki Lamid’o “. Dada ta zaro ido tana kallonta kafin tace “ki rantse da
Allah “ shatu taja tsaki “ kwarankwatsa ni ba aljannah bace ko kinga kofato a
‘kafata “ sai sannan dada taja dogon numfashi tana zamewa a jikin bango zata zauna.
Shatu ta kalli gudawar tace tana toshe hanci. Sai sannan dada ta lura ta saka
salati da sauri ta rarrafa tashiga bayan gida shatu kuwa sai tuntsira dariya take.
Sai dada ta kimtsa ta dubeta bayan ta kaita rumfarta taje ta kira matan gidan “ to
duk ku fito ku ji min bayani wai wannan d’iyar maryama ce maryaman da tuni lamid’o
ya sallamata ga d’iyarta mai kama da jinnu ta bayyana “ shatu ta girgiza kai a
hankali ta furta “zaki bayanin wannan ma “.
Sai sannan kowa ya fito cikin tsananin ta’ajjibi ana kallon shatu wai wannan jinin
lamid’o ce yarinya kamar fulanin daji ita kuwa maryama mai yayi mata zafi ta za’bi
rayuwar daji akan rayuwarta cikin gata da mutuncinta “. ‘Daya daga cikin matan ta
fad’a shatu ta watsa mata wani kallo had’e da cewa “ yo haka ‘kaddarar Allah ta
za’ba mata kuma kada a sake a zagi uwata don kuwa bata raye aradu raine zai ‘baci “
Ta fad’a cikin karyayyiyar hausarta ta fulanin usli. Gaba d’aya suka zaro ido dada
ta saka kuka “yanzu’yar nan kika ce maryama ta mutu? Innalillahi yau ya lamid’o da
liman zasuji da wannan ba’kin labarin kullum zancen su na maryama ne “
Ta fad’a tana jan majina hawaye sha’be-sha’be, kafin ta share hawayenta tsaf ta
mayar da kallonta kan shatu tana mata kallon ‘kurilla “ wace shaida zaki bamu mu
yarda ke d’in jininmu ce d’iyar maryama daso?” Shatu ta mata wani kallon she’ke’ke
aradun Allah babu shaidar da zan baku sai na cika cikina tunda ku kam baku san zuru
ba kun san wahalar da na hya kafin nazo nan amma ba wanda yace min ga ko ruwa Na
hya “ dada tace “kwarai da gaskiyarki ke harira kawo mata abinci ke kuma furera ki
kira matar lamid’o kice ko mai suke su biyo jirgi daga habuja suzo hukuncin
ubangiji ya tabbata.”
Ana kawo mata abincin ta fara ci hannu baka hannu kwarya dad’in abincin har tsakar
kanta ga nama zu’ku-zuku wanda rabonta da cin nama tun sallahr layya ta bara idan
har bata manta ba. Taci tayi nak ta sha zo’bo sai sannan ta fara washe baki tana
dariya ta kalli dada “to ko ki yarda ko kada ki yarda ni d’in diyar maryama ce ga
hotunan da ta bani kafin rai yayi halinsa” ta fad’a tana zaro hotunan daga bujen da
yake jikinta. Wanda suka san maryama da wanda sai a hoto suka santa duk suka zaro
ido dada girgiza kai “ ba shakka hukumullahi la ajabun innalillahi wa inna
ilaihirrajiuna wato maryama daso sallama tayi damu “ hawaye shabe shabe dada ta
saki tana sake rushewa da kuka , sai kuma ta dubi shatu tana fyace majina “ ikon
Allah wato shi ubannaki bararo ne?” Shatu ta zaro ido “ kan bala’i inji uban wa?”
Ta fad’a tana cizon yatsa
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-4
ELEGANT ONLINE WRITERS****
Dada ta zuba mata idanun tsofaffinta , cikin gatse tace “inji ubanki muji da ya
sace mana’ya ya gudu da ita” shatu ta girgiza kai had’e da mi’kewa a katifa tayi
kwanciyarta. Ba a d’au dogon lokaci ba barci yayi awon gaba da ita. Dada ta bita da
harara “ wannan yarinyar daga gani ‘yar daru ce bari kakannin naki suzo ni za’a
barwa ke sai na koya miki hankali tukun, ke fure kira min su lamid’on kiji sun taho
“ furere ta amsa daya bayan d’aya suna ficewa daga d’akin. Koda furere ta kira
wayar taji shiru ta tabbatar sun taho kenan tunda ta san ba sajin kud’in jirgi
kullum a tafe suke.
Dada tana zaune tana lazimi ita kuwa shatu barci takeyi sosai abinta cikin
kwanciyar hankali.
Liman na dawowa dada ta sake bashi labari, cikin farin ciki yake kallon shatu da ba
abinda ta d’auko na uwarta da alama can dangin ubanta ta d’auko don ban ga kamanni
ba “ ya fada yana kallon dada, dada ta ta’be baki “ yo kaima dai ka fad’a yarinya
kamar bararo ko fulanin daji anyi magana tace inji ubanwa? Bari su su lamid’on suzo
sa tantance idan jininsu ce ko Ba tasu ba sa san yarda zasuyi da ita, ni wallahi
tulin sumar kanta ne ma da idanunta suke ban tsoro yarinya kamar d’iyar jinnu don
kyau “. Malami dariyar su ta manya kawai yayi gani n shatu ta mi’ke ba tare da
sanin dadar ba tana ta harararta “ yo ki fito kice min kawai baki yarda dani ba
mana Allah na tuba na me zan zauna ina muku’karya “
Sallamar su lamid’o ce yasa dada yin shiru bata tanka ta bata Allah ya sani tsoro
yarinyar ke bata “ maraba lale da iyayen maryama kuzo yau dai kuga jikarku d’iyar
maryama “ da sauri suka ‘karasa d’akin suna watsa idonsa akanta ta kuwa ‘kuri tana
kallonsu.maman maryama tace “dada kada kice min wannan jinin maryama ce?” Dada ta
ta’be baki “babu wai itace maryama ta haifo muku bararoji mai kama da ubanta. Ai
mama bata’karasa jin abinda zata ceba ta ‘karasa da sauri ta kamata ta rungume “
Alhamdulillah ashe zan sake ganin maryama?” Shatu ta zame jikinta “ ai kuwa ba zaki
sake ganin maryama idan dai ba yau kema zaki bita yarda ta tafi ba ashe kuna sonta
ku ka kasa bata burin ranta akan haka ta gudu ta bar gida ta bar gatanta ta
gwammace rayuwa cikin daji “. Lamid’o zama yayi yana kallon yarinyar mai cike da
tsiwa da surutu mama kuwa sake janta jikinta tayi “ mun dade muna neman inda zamu
ga maryama sai yau Allah ya nufa “ cewar lamido dada ta girgiza kai “ yau ai kaga
dalilin da yasa ba zaku ga maryama ba tana can ‘kungurmin dajin da ba wuta balle a
samu tv ta ina zata ji cigiyarta da ake ba’kin cikina d’aya ne Allah ya dauke
maryama ba tare da mun sake ganawa ba sai bararon ‘yarta da ta bar mana” dada ta
fad’a tana fashewa da kuka, mama ma zama tayi da’bas a kujera tana juya maganar
dada lamid’on kuwa salati kawai yake ja , yanzu maryama ta mutu maryaman da ya
dad’e yana nema ya nuna mata gata dama tuni ya yafe mata , mama kuka ta saka sosai
tana rungume shatu a cinyarta cikin tsananin’kaunarta sam bata damu da daud’ar da
take jikinta ba. Shatu taji zuciyarta ta karye da tausayin kakanninta mutuwar
innaji ta dawo mata sabuwa kar itama ta rungume mama tana sake sakin kuka mai ratsa
zuciya mama ta sake rungumeta tana shafa himilin gashinta.
Tsawon lokaci suna cikin jimami kafin lamid’o ya kalli shatu yace ya sunanki?”
Murya a dashe tace “ shatu “ lamid’o ya jinjina kai “ to ya akayi kika gane nan
kika zo ina so naji labarinki da garin da kuka zauna da labarin rayuwar maryama a
garin....... shatu ta gyara zama daidai lokacin da wani daddad’an’kamshi ya ziryaci
hancinta tana d’aga ido ta hango mai sallamar da sauri ta mi’ke tana wara ido tana
fad’in “innaji “ mama ta kama hannunta “ zauna aysha ba mamanki bace yayarta ce da
take bi ana ce mata mammah “ mammah da take tsaye ta waro ido tace “ mama kada kice
min y’ar maryama ce ina maryaman ina ‘yar uwata alhamdulillah yau burina ya cika “.
Mama hawaye ya ziraro mata don Ta san za’ayi haka Ta sani sarai deejah bata da buri
irin taga maryama kullum zancenta kenan. Shigowar samarin yaran deejan yayi daidai
da lokacin da mama tace “ Addu’a ‘yar uwarki take bu’kata yanzu Allah yayi mata
rasuwa wannan y’arta ce Aysha da ta bari “. Gani su kayi mammah kawai ta zube
numfashinta na ‘kokarin d’aukewa da sauri y’ay’anta su kayi kanta suna jijjigata
had’e da kiran sunanta amma shiru. Dada ce ta d’ebo ruwa ta watsa mata sai kuwa ta
kawo ajiyar zuciya “mama don Allah kice min wasa kike ko mafarki nake ba maryama ta
bace ta mutu “ Lamid’o ya mi’kar da ita zaune Kafin yace “ Allahn da ya fi mu son
maryama ya amsheta addua tafi bu’kata yanzu sai kuma d’iyarta da ya bar mana mu
dinga kallo muna jin dad’i Alhamdulillah da wannan hikima ta ubangjji “. Da sauri
mammah taja shatu jikinta ba tare da ‘kyankyaminta ta rungumta tana bata sumba a
gefen kumatu cikin nuna mata tsananin ‘kauna take share mata hawaye tana kallonta
with so much caring , saurayin d’anta da yake gefe imran ya hau ‘bata fuska cikin
tsananin mamakin mammahn da bata’kyankyamin wannan yarinyar da Daud’a ta samu wajen
zama a jikinta. Zuciyarsa har tashi ta fara yi saboda mutum ne shi mai
tsananin’kyankyami da tsafta har da ta siyarwa. Runtse idonsa yayi kawai ba ya ma
son sake kallon wannan kwamacalar. Ya bud’e kujerarsa wata karama da ya shigo da
ita daga motarsa ya zauna. Sai a lokacin dada ta kula dashi duk da’kamshinsa ya
sanar da duk ahalin gidan zuwansa’kamshin turarensa na amouage interlude 53 ya
karad’e gidan sanye yake cikin black jeans da white long sleeve shirt ta Ralph
lauren polo ya gyara glass dinsa da yayiwa idonsa kyau ba’a ganin ‘kwayar idonsa
gashin kansa a kwance luf, murya a dashe yake gaida lamid’o da dada. Dada cikin
mamakin halinsa na ko da yaushe tace” jakadan turawa yaushe ka bayyana a ‘kasar.”
Cije lips dinsa yayi bai bata amsa ba sai ammar kaninsa ne yace “ yau kwanansa biyu
“ dada ta kyabe fuska “ ai dama shi ba zaka ganshi ba Sai a dangin uwarsa saboda
sun fimu farcen susa ammar kaine namu Allah yayi maka albarka yo wannan dama fuska
kamar hadarin kaji wake maraba dashi ga shegen tsurfar tsaftar tsiya da ‘kakale
aikin banza ko mu har a gaya mana tsafta “ . Ammar dariya kawai yake shi kuwa imran
ya’kare tsuke fuska shi yasa sam baya son zuwa gurin tsohuwar nan mai shegiyar
maganar tsiya. Lamid’o ya gyara murya kafin ya dubi Aysha “ ina jinki ayshatu bamu
labarin “ ai kuwa ta sake gyara zama ta jingina kanta a jikin mommah ganinta take
kamar innaji wallahi. Mommahn ta kara janta jikinta duk da warin da bakinta da
jikinta yake bata’kayamaceta ba tana sauraran yarda take basu labari tiryan-tiryan.
Kafin ta gama bada labarin gaba d’aya gurin kowa kuka yake har ammar banda imran da
ya d’auke kai gaba d’aya haushin yarinyar yake ji ga shegen surutu kamar kanya ba
mamaki ma ‘karya take ba jininsu bace idan banda haka mai ya had’a su da bararoji.
Yanzu haka had’a baki a kayi da ita tazo ta cucesu mutanen duniya da basu da
gaskiya musamman su d’in da an sansu a gari . “ ya kamata ku bincika kafin ku
tabbatar da gaskiyarta “ hakan kawai yace yaja baki yayi shiru kamar bashi yayi
magana. Momma ta d’ago a fusace zata yi magana lamid’o ya d’aga mata hannu ita kuwa
shatu wata harara ta zuba masa da ya sashi ware ido yana kallonta cikin mamakin
rainin da ta nuna masa sai kuma yayi Kwafa. Dada ta gyara zama “ yo saboda Allah ai
gaskiya bature ya fad’a nima fa mamaki nakeyi ace wannan bararojin jininmu ce to ka
fad’a ace ina ka fito don dai mune masu kalan dangi sai kuma mu had’a jini da
bararo “ mommah idan ranta yayi dubu ya ‘baci ta kalli dadan kafin taja’kafar shatu
ta nunawa dadar “ duk wanda ya san yar uwata maryama ya san wannan copyn kafarta ne
da hannunta dada ki daina daka ta imran da shegen halinsa dinnan na bin kwakwkwafi
a ina yasan maryama balle ya tantance jininta maryama da ta bar gida yana shekara
guda duk’kaunar da maryama ta nuna maka ban mance da ita ba.” Imran ya ta’be baki
kawai ita kuwa shatu zaro hotuna tayi ta mikawa mommah da takardar da innaji ta
bata tace ta basu. Mommah na gani ta mikawa lamid’o “ Baba kalla kaga wallahi
rubutun maryama ne wannan tabbas “ lamid’o ya kar’ba ya kuma shaida tabbas rubutun
d’iyarsa ne.
Sun ci sun sha akayiwa maryama addua sannan su lamid’o mazauna abuja suka fara
haramar tafiya. Mama tace shatu tayi wanka ta canja kaya kafin su wuce shatu ta
had’e rai sam bata san zancen wanka. Mommah ce tace” haba mama na zata zaki bar min
ita mu koma kano tare musamman ganin bani da y’a mace ashe maryama ce zata haifa
min” mama ta girgiza kai imran yana zaune a gefe yana adduar kada Allah yasa mama
ta amine banda rigimar mommah ya zata kai musu bararo gida......😂😂😂😂 To fa!
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-5....
Momma ta sake gyara murya cikin kwantar da kai ta furta “ Don Allah mama ki bar min
ita kinga ke kina da wasu y’an matan ga hafsa ga nahnah ni kuwa Allah bai bani
haihuwar d’iya mace haihuwar ma daga ‘ya’ya biyun ba saketa nayi ba.” Mama ta
girgiza kai “ Gaskiyar magana addarsu ba zan iya ba su wadancan da kike magana ina
na gansu kun kwashe kun kai can uwa duniyar turkey karatu, yanzu kuwa ita zan dinga
gani kamar maryama da na rasa “. Dada taja tsaki “ kaji min wani zancen shirme Idan
da wanda ya dace ya ri’ke wannan ‘ya ai dijama ce yo fisabilillahi tana da wata
uwar ne bayan ita a duniya ai itace take da iko da yarinyar nan ba ke ba daga kawai
kin haifi uwarta, don haka na zartar da hukunci dijama ki tafi da ita ke kad’ai
zaki iya da wannan bararojin mai ido a tsakar ka ko samarinki sa ladabtar da ita
musamman wancan miskilin kafi mahaukaci ban haushi da idanunsa kad’ai sun isa
hukunta ‘yar banza idan ta’kamarta ido ai gidan ta tarar.” Wani kallo shatu ta
watsa mata a zuciyarta tace “ sai nayi maganin wannan tsohuwar kafin ta sheka
barzahu “. Liman da lamid’o murmushi kawai suke ganin yarda mama ta had’a rai
alamar sam hukuncin dada baiyi mata ba sai dai ba yarda za tayi da ita. Momma kuwa
sai murmushi take tana sake jan shatu a jikinta. Daga gefe kuwa imran ne yake ta
watso mata harara kamar ya sha’keta ta mutu tabbas banda an kusa bikinsa zai bar
‘kasar da amaryarsa ‘yar abuja zubin london inji dada da barin’kasar zaiyi kafin a
sake ganinsa kuwa sai an yara. Ya kalli agogo yana mi’kewa “Momma ya kamata muyi
haramar komawa saboda akwai abinda dada ya sani a company ban kai ga hattamawa ba
kuma kinga mota muka biyo “ Duk wannan dogon zancen yayi shine saboda baya so dada
tace kwana za suyi yamma tayi. Dada ta zabga masa harara da ficificin idonta na
tsoffi “ Ma’karyacin banza Ka dai ce ba zaka iya kwana anan ba saboda shegen
gwalangwasonka kada kayi ubanka’karya salihin bawa dashi ko da yake shima ya zama
d’an banza watansa nawa bai zo ya dubani ba ko don bani na haifo wanda ya haifi
ubansa ba amma ko bakomai ai ubannasa aminin lamid’o ne, shikkenan dai Allah raka
taki gona ban kuma ce Ka gaya masa ba bare kasa ya daina min aiken wata da ya saba
ko bakomai ai d’an albarka ne tsiyarsa ta rashin zuriya ta bishi sahura dai taga
takaici da jikanta baya son ziyara”. Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya ba har
shatu idan Ka d’auke imran da ya sake kicin-kicin da fuska ya d’aureta tamau ya
mayar da kud’in da yayi niyyar bawa mutanenta da ita kanta aljihu, yasa kai ya fice
bayan yayiwa liman da lamid’o sallama. Dadah ta gyad’a kai “jarababbe umma ta gaida
aisa gayyar na ayya ke dai dijama kin haifi ala’ka’kai.” Murmushi kawai tayi ta
mi’ke tana ri’ke da hannun shatu ta furta “Allah dai ya shirya mana zuri’a bari mu
wuce kada dare yayi don ma mugun gudu yake a motar “. “ wani irin gudu ki gaya masa
ya tafi a hankali bana son shashanci “ lamid’o ya fada yana kallon babbar d’iyar
tasa cike da kulawa ya san sosai take jin zafin rad’ad’in mutuwar nan “ kuma ki
cire damuwa a ranki kada kije kiyi tunani har ciwonki ya tashi maryama addua take
bu’kata yanzu, ita ta dace ko bakomai tayi mutuwar shahada tsakaninmu da ita addu’a
dafatan muma mu cika da imani “ lamid’o ya sake fad’a yana kallon’yar tasa ba tare
da dubi da hararar da dada take watsa masa ba “ Ba shakka zamani wato lamid’o a
gabana kake lallashin ‘yarka ta fari kai Allah da ya tsinewa nasara da ya kawo
boka har tayi sanadin rusa al’adarmu da dane ko inuwa d’aya ba zaka had’a da dan
fari ba balle har zance ya shiga tsakaninku tur da wannan wayewa, ko da yake har
gwara kai ba gani ba na tsaya ina magana da kai da iyayenan zasu dawo da sunyi tur
da haihuwata kai ku tashi ku tafi kada wanda ya sake dawo min nan balle ku sake
sakani rashin kunya wai da bakina nake kiran sunan lamid’o waliyazubillah duk da
dai na uku ne kai amma wa ya san na farko da na biyun Allah na tuba tun kan ayi
suna suka mutu ai dai kai ne dai na farkon....” gaba d’aya gurin dariya ake suka
fice suna mata sallama Momma tace “ Danger number one “
Ta mudubin motar ya hango fitowarsu da sauri ya waro sexy eyes ganin da yarinyar
aka fito mai hakan yake nufi wai wannan’yar dajin motarsa zata shiga kai ina
impossible ai da sake.
Ya fito daga motar daidai lokacin’karasowarsu mommah tace “bud’e motar mana imran,
yamma fa tayi “ ya ‘bata fuska sosai “ Momma yamma fa tayi kuma gaskiya gudu zanyi
sosai why not ku kwana anan idan yaso gobe nayi muku booking flight ku taho.”
Momma ta watsa masa wani kallo ta san sarai nufinsa Aysha ce baya son ta shiga
motar bai kuwa isa ba zata nuna masa ita ta haifeshi “ sannu ubana to yau d’in za
mu tafi idan yaso’karewar gudu ka mayar da motar taka jirgi bud’e mana malam “
fuska a d’aure tamau tayi maganar tana mamakin halayen imran da sam bata san inda
ya kwaso su ba. Jiki a salu’be ya bud’e motar had’e da mi’kawa Ammar key d’in “
kuje I will manage ko a hotel ne by morning insha Allah zan bi flight na taho and
make sure kuna zuwa ka kira car wash su d’au motar nan every thing na cikinta ya
zama clean.” Ammar ya kar’bi key had’e da bud’e driver seat momma ta waro ido tace
“ yana ina shi “ Ammar yaja numfashi don yasan fad’an momma shi kuma yana son d’an
uwansa baya son’bacin ransa “ Momma zai zo ya tuna akwai yana da abinda zaiyi a
bauchi “. Gani yayi kawai momman ta fita ware ido tayi tana kallon imran jingine
jikin bishiyar’kofar gidan kallo da take masa ne yasa shi rusinar da idanunsa baya
jurewa sun saba tun suna yara da idon take hukunta su, hanya kawai ta
nuna masa ta shige. Ransa a ‘bace ya bita tabbas ya san dai kafin ya isa gida wani
ciwon sai ya kamashi.
Shima Ammar d’in kallo d’aya tayi masa ya fito ya koma d’aya seat d’in zuciyarsa
fal da tausayin d’an uwansa don ya san kam yau sai ta Allah.
A salu’be ya tada motar bayan yayi adduar tafiya الحمدلله الذي سخر لنا... zuwa Karshe ya
kuma ware a .c don ya kore masa warin jikinta da dum da motar tayi har da su fess
turaruka. Momma tana kallonsa tana’bata rai cikin’kyamar banzar d’abi’arsa. Shatu
kuwa kwafa tayi don sarai ta san ma’anarsa ta hakan wato kyamarta ma yake yi ai
kuwa za tayi maganinsa kafin ta bar motar, ba mamaki ma bayan fitsari har kashi sai
tayi a motar....😂😂.
Wani irin gudu yake shararawa duk a tsorace suke a motar ganin yarda yake mommah
kuwa ta’ki magana sai addu’a da take a zuciyarta. Shatu kwance take luf a cinyar
mommah wani barci ne yake fusgarta, cikin hukuncin ubangiji kuwa cikinta ya fara
murd’awa ta daddage ta saki wata tusa da ta d’umame motar gaba d’aya Allah ne ya
kiyaye saura’kiris ya saki sitiyarin motar yaja wani wawan burki, ammar ya
dinga’kok’arin’kinshe dariyar da ke cikinsa amma ina sai da ta bayyana a guje ya
fice tuni ya fara kwara amai, Ammar ya fito masa da ruwa yana aikin jera masa
sannu. Momma kuwa duk da tausayinsa ya shigeta haka ta gintse. Shatu sai dariya
take yi tana’karawa momma tace “ wallahi shatu idan ya kamaki ba ruwana “ “ yo
mommah ba k’yamata yake ba saura gudawa ma “ Mommah ta waro ido “ kada ki fara
shatu idan ba so kike ya kashemu a titi ba kina ganin wawan burkin da ya sha Ba don
Allah ya kiyaye Ba kowa a bayanmu ba da tuni mun mutu.” Shatu ta zaro ido “ momma
mutuwa kuma a yanzun da zan fara jin dad’in rayuwa aradu ma ki daina wagga zance yo
tunda nake ban ta’ba tunanin zan shiga wannan abin ba ban Ta’ ba ganinsa ba sai yau
amalanke muke shiga garinmu da zanzo nan kuwa motar kayan miya Na shigo aradu dana
shiga nan na zata aljannah nake “ mommah ta girgiza kai “To kada ki sake abinda zai
zubar damu a titi motoci su take mu mutu.” Ta d’aga kai. Ya huta sosai kafin yace “
Ammar jeka Kai bud’e glasses d’in motar ventilation ya shiga ka fesa air freshners
tabbas Ba mamaki mommah ta d’auko ajalina “ Ammar ya d’an shafa bayansa “ bros ba
zaka mutu ba just because of her sai kwananka ya ‘kare Ka dinga daurewa pls mommah
bata jin dad’i the way she looked at you ka dinga controlling temper Dinka” hannu
ya d’aga masa “ jeka kayi abinda nace maka kawai ni Na san abinda zanyi muna zuwa
gida I will pack everything nawa na tare “ Ammar ya zaro ido “ saura fa 4 months
bikin ya zaka tare yanzu “ Imran tsaki yayi idan ban tare ba so kake na mutu ko?”
Ammar ya juya yana’kunshe dariyarsa ya gama duk abinda ya sashi sannan ya dawo yana
kallon yarda yake mayar da numfashi alamar ya galabaita a aman “ Bros mu tafi kada
dare yayi “ mikewa kawai yayi ya mi’ka masa key d’in “ muje kayi driving I can’t do
it “
Ta mudubin motar yake watsa mata harara ta saki baki sai barci take har da munshari
ya sauke duk glasses d’in iska Na shiga motar a zuciyarsa yace “ Gwara a tafi haka
“ momma dake kallonsa ta ta’be baki “ zan baka mamaki imran kada Ka shiga
hankalinka “.
FREE📚
08033748387
-6
Ammar cikin nutsuwa yake driving har suka isa cikin garin kano’karfe 8:00 dai-dai,
shatu lokacin har fitsari ta janga’ba a kujerar ba tare da sanin mommah ba.
A unguwar railway su kayi parking bakin wani tangamemen gida gari guda, da tafkeken
gate, gani tayi kawai gate din ya zuge ba tare da tasan wanda ya zugeshi
ba.Automatic gate ne. Ammar yayi packing a packing space. Momma ta bud’e ‘kofar
had’e da jan hannun shatu a hankali ta waro ido ganin gurin da lema murya ‘kasa-
k’asa tace “ shatu fitsari kika yi?” Shatu ta d’an ta’be baki “ To mommah fitsarin
ne ai ya matseni kuma ina cewa zanyi zai fara masifa “. Momma tayi saurin rufe mata
baki don kada imran da ya fice da sauri yaji “Muje kafin ya ankare “ da sauri shatu
ta fita daga motar ammar yayi dariya yana tunanin yarda za’ayi da cakwakiyar’yar
mommah da yayansa, yasan dai kwarai za’a buga show.
Suna shiga tangamemen falon kamshi ya doki hancin shatu ga sanyin A.c ta lumshe ido
had’e da runtse ido tana bud’ewa tabbas dai da a mafarki taga wannan gidan to
tabbas zata ce aljanna tayi mafarki da ita. Momma ta ri’ke mata hannunta ta
kaita’kofar wani sashe suna shiga ta kaita wani d’aki kusa da nata “ daga yau ga
d’akin Ayshata muje in nuna miki komai a toilet kiyi wanka ko da yake wannan
wankan na yau yafi ‘karfinki da kaina zan miki da nace ma in kaiki saloon to bana
so su fara ganin wannan daud’ar kannaki jira ni anan am coming.” Da sauri ta fita
daga d’akin shatu ta sake ware ido tana kallon gadon yanzu wannan d’akina ne gado
na da sauri tayi tsalle a gadon tana tintsira dariya “ ahe dai ina da gata muke
zaune can a dajin Allah aradu innaji ta kwari kanta cabd’i”
Shigowar mommah yasa tayi shiru momma ta shige toilet ta zube kayan da yake
hannunta duk mayukan wanke kaine da combs dama toilet din akwai dryer. Shatu ta
fara’bata rai sam bata son a ta’ba mata kai da dai mommah zata gane da ta kyaleta.
Momma ta zare du’kun’kunennan mayafin nata ta zaunar da ita bakin jaucuzi ta fara
kunce tufkekken gashin kanta mommah tayi mamakin ganin tumulin gashin ta ji’kashi
ta saka shampoo ta barshi for a minutes sannan ta fara had’a ruwan da zata dirje
daud’ar Jikinta.
Sosai ta wanke kan sai sheki yake wajen wanka ne shatu Ta fara’boye-‘boyen jiki
mommah Ta harareta “ zaki tsaya ko sai na ‘bata miki rai ke da ko irgar dangi baki
fara ba to koma kin fara ni ba uwarki bace “. Shatu Ta d’an sunkiyar da kai mommah
Ta saki murmushi “ Ashe kina da kunya.” Tas shatu Ta fito duk da dai sai a hankali
zata baje amma ko bakomai anfi baya.
Fitowarta ne yasa momma ta tsaya domin ba kayan da zata bata tasa tsaki tayi tace
“zauna nan ina zuwa bari na aika ammar ya siyo miki ready made kafin da safe mu
shiga kasuwa “.
Tana fitowa babban falo ba taga ammar ba sai imran da yake zaune yayi wanka da fara
jallabiya tas a jikinta mai gajeran hannu a jikinsa yayi kyau sosai kana ganinsa
kaga mutum mai mutu’kar tsafta. Sai baza’kamshin turare yake yunwa ce take cinsa ya
aika ammar yayi musu take away don baiga alamar masu aikin sunyi girki ba, may be
basu zata zasu dawo ba.” ina Ammar?” Momma Ta fad’a tana tsatstsare sa da ido ,
Imran murya can’kasa yace “ Na aike shi eatery samo abinci.” “ sai ka tashi kai na
aikeka samowa Aysha kayan sawa ba tazo da kaya ba “ ta fad’a tana juyawa ba tare da
Ta lura da waro idon da yayi ba yana ji kamar ya rusa ihu ganin zata shige yace “
kud’in fa?” Ba tare da Ta juyo ba tace “ ka siya da naka “ dunkule hannu yayi ya
daki d’aya cikin d’aya kamar ya tashi sama kuma ya juya da sauri ya fice daga cikin
gida.
Da yaje ma rasa mai zai d’auka yayi ya d’auko mata riga da wando Na maza kawai
bayan ya kintata tsahonta yaga ba zata zarta hakan ba. yunwa yake ji sosai amma
mommah Ta sashi zuwa siyawa wannan bararojin kaya.
A falo ya ajiye kayan ya nunawa Ammar “ mikawa mommah “ ya zauna a dinning ya fara
cin abincin” mintuna kad’an mommah da ‘yarta suka fito Ta saka riga da wando duk da
Na maza ne sai sukayi mata kyau, mommah Ta gyara mata kai an tsaga an raba biyu,
jelar gashin Ta sauka har dantsen hannunta gashi mai yawa masha Allah sai ‘kamshi
take kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai ya cigaba da cin abincinsa momma taja
kujera tace “zauna “ Ta zauna tana hararar naman da yake ci tsoronta Allah kada ya
cinye naman hakan yasa ta shiga tunanin yarda zata koreshi daga wajen ta kuwa
daddage ta saki attishawa sai kuwa ga majina ta biyo hancinta da sauri ya furzo
abincin dake bakinsa ya mi’ke da sauri ya bar wajen. Zuciyarsa na tunzirashi yayi
mata dan banzan duka kawai. Ita kuwa dariya Ta fara babbakawa “ Nagode Allah yo
mommah da fa cinye naman zaiyi kaf da banyi haka ba “ mommah duk da dariyar da take
cinta ta gintse tace “ baki kyauta ba kings yanzu kin hanashi cin abincin Ba kyau
kada ki sake Ammar bishi da abincin d’aki”. Ammar ya mi’ke yana murmushi sosai
yarinyar take burgeshi shi kam sam bata damuwa sha’aninta take zubawa.
Yana dawo da abincin mommah Ta kalleshi “ baya ci ne?” Ammar a sanyaye ya d’aga kai
yaja kunnen shatu dake zaune “ if you try it again Allah sai Na zaneki mommah kija
mata kunne “. Narai narai tayi da idonta “ To ni ina ruwa na kawai atishawace fa
tazo ya zanyi da ita to “ “ Excusing kanki za kiyi ki fita kiyi haka ake yi wai ke
baki da manner ne?” Kuka Ta saka “ Ni ka daina min wannan maganar ban iyata ba idan
bakwa san zama na kuma kawai kuce na tafi. Ya bud’e baki zai yi magana mommah tace
“ Ammar ya isa ai da gaskiyarta to ya zatayi da atishawa fisabilillahi ni fa kada
wanda ya ‘kara takura mata duk wanda Ba zai iya zama ba shi ya bar gidan. Ammar ya
bud’e ido “Mommah......” “kada kace komai “ ita kuwa shatu plates d’in imran taja
ta fara cin naman cewa takeyi “ Yo ai yayiwa kansa ni kuwa gaba Ta kaini......”
Ammar murmushi yayi ya wuce yana furta “ Allah ya shirya “.
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-7
Momma murmushi Ta sake saki ganin yarda shatu take cin abincin hannu baka hannu
kwarya “ ci a hankali Aysha ba inda abincin nan zaije gashi nan ma idan baki ‘koshi
ba ki ‘kara saki jikinki nan d’in gidanku ne kamar yarda kowa yake ji gidan ubansa
ne.” Ammar’kunshe dariyarsa yayi ganin yarda momma ta hau da yawa yasa ya koma
falon ya kunna t.v . Ai kuwa shatu a zabure ta mi’ke ta isa wajen tana sid’e
hannunta “ Ikon Allah yau gani ga irin akwatin kallon d’an gidan mai gari da aka
kaiwa amaryrsa da ya auro a niamey, aradu wannan tayi gomanta.” Sai kuma ta fara
zabura tana tsalle ganin yarda mutane ke rawa a cikin t.v d’in ta ‘karasa tana
shafawa Ammar mai zaiyi idan ba dariya ba. Momma da take gefe ta dafe kai anya
shatu zata gyaru ta dawo kan saiti kamar yarda take son ta ta lura’kauyancine kawai
a kanta zuciyar momma ta shiga tunani. Sai kuma ta mi’ke ganin yarda ammar yake
tuntsira dariya tana zuwa ta figi hannunta “ wuce muje shashasha kina zaune yana ta
tuntsira miki dariya ga sabon kamu ya samu wallahi Ammar ka kiyayeni ina lura da
take-takenka ta wancan ce ta fito fili shi kyamarta take kai kuwa mahaukaciya ka
d’auketa to ahir ka kiyayeni “Ammar ya guntse bakinsa “ Allah ya baki ha’kuri momma
amma fa wallahi dole Na samu comedy a gidan ji fa yarda take acting wallahi
illiteracy d’inta yayi yawa za’a sha fama “ “ ubanka ne zai sha famar ko ni? Ina
ruwanku da ita to duk zaku ci ubanku da ni kuke zancen ashe ta imran ce ta fito
fili “ Ta sake kwafa suka shige part d’inta hannunta ri’ke dana shatu.
Suna shiga d’aki shatu ciki ya kad’a to an ci abinda ciki bai saba ci ba da sauri
Ta kalli mommah tana yamutsa fuska. Momma Ta dubeta had’e da dafa kanta “ Me ya
faru ki daina fushi ki rabu da su zan yi maganinsu ai da ni suke zancen” Shatu Ta
fara matse-matse “ Ni fa mommah ba zancensu ya dameni ba yo ni ina ruwa na ai
gaskiya Ammar ya fad’a. “ “ Au ni na damu kenan to meye ya dameki kike had’e-had’en
fuska” “ Kahi nake ji “ Momma Ta zaro ido to “ kashin kike ji kike tsaye anan, anan
zakiyi min kashin?” Da sauri taja hannunta wuce muje na nuna miki inda zakiyi don
ba mamaki ma baki san toilet sit d’in birni ba” da sauri shatu ta bita ji take
kamar Ta saki kashin suna shiga ta hau duba inda momma ta nuna mata shatu ta waro
ido “ A wannan abin fari ‘kal dahi zanyi kahin “. Momma tsaki tayi kafin ta furta “
idan ba kiyi anan ba a bakina zaki yi ?“. Ta sake le’kawa “ Ruwa ne fa a ciki aradu
ba zan zauna ba inje ruwa ya zu’keni ya tafi dani “ Momma Ta dafe kai tana kallon
shatun cikin takaici “ kada fa ki sake kiyi min kashi a wando ki hau ba wani ruwa
da zai tafi dake duk gidan da zaki a garinnan yawancin irin wannan d’inne sai dai
idan kin daina kashin” “ To zan hau amma ki tsaya ni” “ In tsaya ki ki cika min
ciki da warin kashi to ba dani ba ki hau in kin gama wannan zaki ciro kina danna
nan ruwa zai zo kiyi tsarki shi kuma kashin ba barinsa zakiyi ba ki danna nan ruwa
zai tafi dashi kin jini ai da kyau?” Shatu Ta d’aga tana d’ofana akan seat toilet
din ta zauna. Momma ta saki ajiyar zuciya Ta ja mata ‘kofa ta fita zuwa nata
d’akin a gaijye take tubus banda soyayyarta da maryama ba abinda zai kaita d’aukar
shatu musamman ita da mijinta da suka tsarawa kansu rayuwar turai basa son hayaniya
sam shi yasa sam basu damu da haihuwa ba sai gashi ta d’auko shatu wanda Ta san sai
tayi bore kafin mijinta ya amince da zaman shatu a gidan. D’akinta ta shiga wanka
kawai take bu’kata da nutsuwa.
Shatu anyi abin kai bayan ta gama tayi tsarkin ta mi’ke sannan ta danna inda akace
zata kore kashin idan ta gama ai ko sai tayi tsalle ta koma can gefe tana kallon
ruwan abin kuma sai ya bata dariya ta sake dannawa haka tayi- tayi kafin ta gaji ta
fito a zuciyarta take fad’in “ wato hi kahin ma wani matsayi ne dashi na musamman a
Gidannan cabd’i Allah ya kyauta “. Ganin momma bata d’akin Yasa ta fita tana
bilayin nemanta . Ganin bata ganta ba a d’imauce Ta fara’kwala mata kira duk gidan
yana amsa kuwwar muryarta.
Da sauri d’aukacin mutanen gidan har su Imran suka fito tunanin ko ba lafiya ba,
abinka da ba’a saba hayaniya a gidan ba, dai- dai lokacin mai gidan shima ya bud’e
‘kofar part d’insa ya fito don bai dad’e da dawowa ba yaji tashin muryarta. Da
kallo ya bisu ganin sunyi cirko-cirko suna kallonta. Had’e fuska tayi tana binsu Da
kallo “ To wai lafiya naga kun saka ni tsakiya sai wani kallo na kuke.” Imran tsaki
yayi ya juya ya shige part d’insu da ya san ma itace ba zai fito ba to barcin
gajiya ya fara fisgarsa ya jiyo hayaniyarta kai mommah ta d’ebo musu damuwa.Ammar
da ya lura da Dahdansu yayi saurin cewa “ welcome dahdah “ girgiza masa kai yayi
fuska a had’e yace “ who is she?” Ammar ya mayar da kallonsa kan shatu da take
fad’in “ Wannan sa ido da yawa yake uwa ta fa na kira baku ba” Ammar yayi saurin
katseta “ ke are you mad kin san da wa kike magana “ “ kai ka san mai kace inace
mad d’in d’an garinku sai kayi tayi min yaren birni so nawa zance maka bana so “ Ta
fad’a tana ta’be baki . Cikin tsawa Babannasa yace “Ammar am asking you who is she
I said?” Mommah ce Ta fito daga’bangarenta turus tayi ganin taron jama’ar gidan Ta
mayar da idonta kan dahda “ Ai ban san ka shigo ba ina wanka.” Fuska a had’e yace “
Yayi kyau kai kuma amsa min tambayata wace shashashace wannan?” Mommah ta had’e
fuska “ diyar tawa ce shashasha to ko baka santa ba ai bai kamata daga ganin ba’ko
ka kira shi da shashasha ba er maryam ce sister ta wani abu ne?” Wani kallo ya bita
dashi sai kuma ya hau step d’in da zai kaishi ‘bangarensa.” Almasifatu shi kuma
wannan d’in waye da naga duk kun firgita da ganinsa “. Momma ta waro ido Allah ya
taimaka ya shige bai ji ta ba Ammar ya watsa mata wani kallo “ ke ubannamu kike
kira Almasifatu?” Cikin ‘ki’k’kifta ido tace “ Aradu ban san ubanka bane yo ai da
ba zan kira shi da haka ba.” “ zagi na kika yi kenan ?” Cikin kufula Ammar ya
fad’a. Momma Ta dafe kanta had’e da jan hannunsa “ Bafa zagin ka tayi ba Ammar sai
kunyi ha’kuri da ita kafin ta goge” Ammar ya kad’a kai “ki daina bin bayanta fa
mommah cewa fa tayi ubannaka?” “ To kayi hakuri mana haba su a garinsu ai ba zagi
bane hakan “. Shigewa part d’insu kawai yayi yana nanata kalmar AlMASIFATU. Momma
ranta had’e tace “ Maza wuce d’akinki kada Na sake ganin’kafarki a waje sai da safe
nan gidan bama hayaniya mai gidan duka yake “ sum sum ta wuce . Momma Ta dubi masu
aikinta biyu da suke kwana su kansu a ‘boye suke saboda mai gidan ya sha fad’a mata
baya san shirgi, ‘ya’yansa kad’ai sun isheshi “ ku kuma mai kuke yi anan? Yawon
d’aukar news ko?” Da sauri suka fice ita kuma Ta shige ciki sam bata san yau zai
dawo ba ba abinda Ta tanadar masa. Kitchen d’in da yake part d’insa Ta shiga saboda
tsantsaninsa komansa anan yake ita take masa komai bai yarda kowa yayi masa ba. don
haka ma yayi kitchen a part d’insa saboda kar ma wata rana tayi gigin saka masu
aiki yi masa wani abin. To ashe dai imran a can ya gado tsafta.
Sai da ta d’ora abincin sannan ta’karasa bed room d’insa . A zaune ta ganshi da
news paper a hannunsa sallamar ma ciki-ciki ya amsa ba tare da ya d’ago ba “
Yalla’bai barka da dawowa ina ta magana kayi shiru wai me ya faru ne?” Ya d’ago
fuska a cusgune “ Da izinin wa kika d’auko bagidajiyat yarinyar can to bari kiji in
gaya miki I can’t tolerate this nonsense maza-maza gobe ki mayar da ita inda kika
d’aukota ai kin san sarai bana son hayaniya yaran ‘yan uwana ma ban yarda na ri’ke
ba balle wannan yaran da bata da respect don haka ki mayar da ita, saboda bana son
haihuwa da yawa Na ‘ki ‘kara aure so ba wani abu da zai sani ri’keta...........”
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-8
Momma tagumi ta zuba tana kallon dahda “ Amma ka bari kaji er waye kafin ka fara
fad’ar ba zaka ri’keta ba, er fa maryama ce maryama jinina da muka taso tare
maryaman da na sha mama na bar mata, duk ba ma wannan ba bata raye wa kake so ya
rike mata er ta wa take dashi idan bani ba.” Jikin dahda ne yayi sanyi “ maryama ta
mutu?” Ya fad’a cikin taushin murya ba kamar yarda ya d’au zafi ba, innalillahi wa
inna ilaihirrajiuna, momma ta ja ajiyar zuciya kafin tace “ maryama ta mutu nima
d’azu kira ya ruskeni daga katagum muka tafi a can muka samu ita wannan er tazo ita
kuma take sanar damu mahaifiyrta ta mutu.” Allah ya gafarta mata Allah yasa ta huta
amma ina mahaifinta?” Momma gyara zama cikin kasa da murya tace” shima Allah yayi
masa rasuwa “ Tausayin shatu sosai ya kama Alhaji, ya
Hau girgiza kai yana jaddada lamarin girman ubangiji “ Allah ya gafarta musu Allah
kuma ya bamu ikon sauke nauyin ri’kon maraya “. Farin ciki ya ratsa zuciyar mommah
sai sannan hankalinta ya kwanta da har ya amsa zai ri’keta “ Nagode dear bari na
kawo maka abincin” .
Ta fara zuba masa abincin ya dubeta “ kiyi ‘ko’kari sosai akan yarinyar nan ki
koya mata tsafta uwa uba tarbiyya don sosai na lura bata da manner, insha Allah
nima I will try my best naga na kula da lamarinta don kamar nauyinta ne Allah ya
d’ora mana.” Insha Allah mommah kawai take fad’a zuciyarta cike da farin ciki a
take a wajen ya tura mata kud’i a account ya umarceta da kashegari aje ayiwa shatu
siyayya. Godiya ta sake masa ta mi’ke don fita shirin barci.
******** kwananta biyar da zuwa gidan amma har ta fara murjewa, jikinta yayi kyau
masha Allah duk da haskenta bai fito gaba d’aya ba . Duk wani abin da bata sani ba
mommah ta koyar da ita yarda za tayi amfani dashi a gidan.Ta fara kuma ‘ko’karin
ganin ta daina rashin kunya duk da har zuwa lokacin da yarinta a tattare da ita.
Abubuwa da dama bata iya cinsu har a lokacin da zarar taci sai tayi aman su saboda
rashin sabo sai dai son cin nama shan madara da milo kuwa har dana maza da kauri
sosai take damawa ta shanye.Ammar tuni ya fara sakin jikinsa da ita kasancewar
yanzu duk ta d’an zubar da rashin kunyar an samo mata malami da zai dinga koyar da
ita.Imran ne baya shiga shirginta .
Yauma da wuri ta tashi, tayi saurin yin wanka da brush don kar mommah tayi mata
fad’a gashi ne dai bata taje shi ba bata son gyaransa sam bata’ki kuma mommahn Ta
aske shi ba kamar yarda tace.
Ganin su mommah tayi suna ta aiki a gidan ta fara tunanin ko mai zai faru ake ta
wannan aikin Ta kuma lura zuciyar momma sam ba dad’i don komai a sanyaye take
yinsa. Momma ta dubeta tana amsa gaisuwar da take mata cikin nutsuwa” yauwa my baby
kin yi wanka maza kije kiyi break fast kizo d’aki ina son ganinki “. Amsawa tayi da
sauri tana isa kan dinning , Tayi turus ganin imran a dinning d’in yana break
idanunsa ya zuba mata, da sauri ta dur’kusa tana gaisheshi imran ya had’e fuska. “
ke bar nan wajen before I slap you “ kallon ‘kasa-‘kasa tayi masa “ To ba yunwa
nake ji ba zaka ce na bar nan.” Harara ya watsa mata sai kuma ya cigaba da abinda
yake kafin bakinsa ya furta “ Dirty Girl “ zama tayi ba tare da san abinda yace “
kin san mai nace miki?”kamar doluwa ta hau girgiza kai “ ‘kazama nace miki
Alhamdulillah na kusa barin gidan sai kuci’kazantarku ku kad’ai “. Ba tayi masa
magana illa kallon plate d’insa da tayi yana shirin kai tsokar nama ta miyar
turmeric baki ta saki murmushi kafin tace “ Ga kanan’kazami kana cin miya kamar
gudawa.....” Ai da sauri ya furzar da naman bakinsa yayi wajen sink shatu ta
tuntsire da dariya a hankali ta furta “ ba’kin mugu in dai ina gidannan ka daina ci
ka ‘koshi “ sosai ya kuskure bakinsa ya bita da wani kallo kafin ya wuce shatu ta
ja plate taci abinci tayi nak “ Allah gaba ta kaini ba gashima har nayi’kiba ba
gobe ma ka sake ce min’kazama Allah mhmmn sai kuma ta girgiza kai.”
Da kyar take nishi sai kuma ta tuna kiran da momma take mata da sauri ta shige
sashen mommah a zaune ta ganta ta rakfa tagumi idonta har ja yayi. Jikinta a
sanyaye ta ‘karasa ta zauna daf da ita “ Momma mai ya sameki?” Momma ta shafa kanta
“ bakomai shatu anjima za’ayi ba’ki babar mai gidan nan zata zo don Allah don’t
make any thing da za’a tafi dake a baki bana son kiyi rashin kunya ko wani abu
kinji ki daina yawan fitowa kiyi tasa catoon a d’akin ki.” Shatu ta d’aga kai “
Tana da fad’a ne Mommah?” Shatu tace tana kallon ta , mommah ta girgiza kai “ Ba
fad’a kad’ai ba zata iya sa daga ni har ke mai gidan nan ya koremu “ “ cabd’i muje
ina duk wannan naman mu barhi “ Momma tayi tsaki “ ke kike ta nama Aysha Idan nama
ne duk mai sau’ki ne gidanmu ma akwai ina son mijina bana son ta raba ni dashi “
“ Au to hi dahdan sai ya rabu dake “ momma ta d’aka mata duka “ sau nawa na hanaki
cewa hi da he a maganarki ? Ba abinda zaki fahimta yanzu sai nan gaba zaki san and
wacece hajja tashi kije Na gaya miki ba ruwanki da kowa, kuma ki dinga dur’kusawa
har ‘kasa kina gaisuwa kin ji?” Shatu ta girgiza kai kawai daidai lokacin da suka
ji dirin motoci a harabar gidan.
Da sauri mommah ta mi’ke cikin rawar jiki ta fice, shatu ta bita da kallo kafin ta
fita taga wacece wannan da mommah bata son’bacin ranta. Babban falon ta fita duk
mutanen gidan suna zaune gefe d’aya mommah ce dur’kushe tana gaida hajja murya a
cunkushe hajjan take amsawa tana yatsine fuska. Ganin yarda su imran suka gurfana
suna gaisheta yasa ita ma shatu ta’karasa ta dur’kusa tana gaishe su. Hajja ta zuba
mata manyan idonta “ ita kuma wannan daga ina? Sabuwar mai aiki kuka yi da har kuma
ta sake ta za’ke take shiga cikin ahalin gida, Ba shakka to mi’ke daga nan kafin Na
kai miki mangari.” Shatu ta d’ago ido zata aikata halinnata sai kuma suka had’a ido
da mommah sum sum ta mi’ke ta shige “ ina magana an min banza ga a tsohuwar banza
ko nace wacece wannan deejah?” Murya can ‘kasa mommah tace “ d’iyar maryama
ce’kanwata to ta rasu shine na d’aukota “. “ shine aka ajiyeta ba tare da izini na
ba ko? Ni da gidan d’ana ga a baitil mali an samu wacece ma maryama a zuri’arku?”
Momma ta sake sunkuyar da kai “ ‘kanwata data bar gida da dadewa “. Hajja salati
tasa “ kice min’kanwarki da ta tafi karuwanci shine kika d’auko shegiyar’yarta kika
cud’anya cikin tsaftatacciyar zuri’ata, zuriar da aka Haifa ta sunnar manzon Allah
to kuwa ba zai yiwu ba kai imran kira min ubanka a waya.” Gaba d’aya suja juya jin
takun tafiyar dahda murya a cunkushe ya shigo, shatu da take ra’be a ‘kofa ta shige
d’aki wai yau ita ake kira da shegiya ai kuwa tayi al’kawarin sai ta sa matar nan
kuka.
Dahda ya dur’kusa a gefenta. Fuskarsa yana d’an sakin murmushi yace “ Hajja ashe
kin shigo ? Barka da zuwa ta amsa tana girgiza’kafa “ kai ka bawa shegiya lasisin
zama a gidanka ?” Cikin rashin fahimtar zancennata yace “ wacece shegiya?” Kwafa
tayi “ baka santa ba kenan d’iyar gantalalliyar’kanwarta maryam da ta bar gida
saboda ubanta ya za’ba mata miji ta gwammace ta tafi yawan dadiro.” “ Hajja wanda
ya mutu fa ya mutu mai yasa zaki dinga’bata mata gawa ba kuma yawon dadiro ta tafi
aure tayi ta haifi er ta don haka wannan zancen don Allah ki daina fad’arsa “. Dada
ya fad’a fuskarsa a had’e. Hajja ta sake tsuke fuska “ Ba shakka ubana to ai sai ka
bari sai na zama sokuwar uwa sannan in dinga bari kana fad’a ina fad’a shashasha
kawai wanda mace ta riga ta gama dashi shi yasa wannan karan da shiri na nazo kaga
can to matarka ce ni na bada sadaki aka auro maka ita tunda na bika na bika ka’ki
amincewa da auren shi yasa ni na auro maka ita kuma wallahi kace baka amince ba sai
dai ka sake wata uwar.” Mommah wani fad’uwar gaba ne ya sameta ganin wacce aka nuna
aka ce kishiyarta ce y’ar’kanwar hajjance uwa d’aya uba d’aya da ta dad’e tana
zawarci kuma y’arta imran zai aura sannan ace itace kishiyarta tabbas akwai ‘kura.
Dahda cikin ‘bacin rai yake kallon ta tana zaune fuskarta sai murumushi take tana
rausayar da kai.
Dahda mi’kewa yayi kawai yayi hanyar fita. Hajja ta sake tunzira “ Ba shakka
sallamamme ai ban gama magana ba kake shirin fita wannan yarinyar na bada awa
ashirin da hud’u t bar gidannan ‘bangaren da nake sauka anan amarya zata tare yanzu
ne na san kayi aure da ka auri’yar dangi, Auren imran kuma na saka rana na da wata
biyu, ba’kin ciki ya kasheki dijah dama ai na gaya miki ina tafe ga dai abin
takaici kishiyarki kuma surukar d’anki sai ki had’iyi zuciya ki mutu, ku matan
yanzu baku da buri irin ku mallakewa mutum d’a . Momma mi’kewa kawai tayi
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-9
Tana shiga d’akinta hawaye ya fara zubo mata, Tunani take sosai a zuciyarta so take
ta hango laifin da takewa dangin mijinta suka tsaneta har haka, mai tayi musu?
Shine abinda take tunani a zuciyarta, har ga Allah bata nufin kowa da sharri
rayuwarta take free ba tare da kowa a ranta ba amma sun bi sun tsaneta.
A gefen gadon ta zauna, shatu data gefe jikinta yayi sanyi ganin mommah na hawaye,
taji duk duniya ta tsani waccan Almasifatun tsohuwar a hankali ta zauna jikin
mommah itama ta saki nata kukayi. Momma dafa kanta kawai tayi alamar rarrashi.
Daidai lokacin Ammar da Imran suka shigo d’akin jikinsu a sanyaye suka zauna kan
cushion chair d’in da take gefe fuskarsu sam ba walwala musamman ammar, sam baya
son abinda zai saka mahaifiyarsa a ‘bacin rai. Ammar yayi’kasa da muryarsa “ Momma
kiyi hakuri komai lokacine, kuma wata rana sai labari.” Girgiza kai tayi “ Na kai
ma’kura Ammar iya ha’kurin da zan iya kenan kun san iya lokacin da nake’kunsar
ba’kin cikin hajja tun ranar da na kwana d’aya a gidannan duk a dalilin mahaifinku
bai auri za’binta ba, kuma ba kowa bace za’bin nata sai wannan matar da sai da ta
san yarda tayi yanzu ta auro masa ita, to lamarin ya isa zan tattara in tafi amma
ba zan zauna ba’kin ciki ya kashe ni ba just like bani da iyaye, gidan ubanku ne ku
zauna, bare shi gashi nan zasu aura masa wacce suke so, tun yaushe nake jan
kunmensa ya rabu da yarinyarnan ya’ki, saboda kawai kyanta da kwalliyarsa yana
rud’arta to yaje ya aureta amma ka san Allah ba hannuna a cikin lamarin aurenka,
wanda dama don a gasa min ba’kin ciki aka’kir’kiresa.”
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta mi’ke ta shiga had’a kayanta, Ammar ya ri’ke akwatin
“ please mommah kada kiyi abinda baki ta’ba yi ba da yarintarki balle da girmanki
please ki rabu dasu,ko mu kad’ai zamu iya share miki hawaye, kuma wallahi at this
point sunyi na’karshe, kaima yaya Imran don Allah kayi hakuri ka kyale musu’yarsu
ko don kwanciyar hankalin Mommah “ wani kallo Imran ya zuba masa “ meye laifin
shaheeda da zan rabu da ita, ko kana tunanin a bayansu take? To kullum maganar ta
tana jin haushin abinda suke wa mommah.” Wani kallo momma ta wurga masa sai kuma
tayi kwafa “ mhmn ba dai shaheeda bace Imran ka aureta ban hanaka ba, tunda lokacin
da na hanakan ai baka ji ba, sai dai bahaushe yace wanda bai ji bari ba.... kai
kuma Ammar kada ka sake masa magana idan ta nice ma barin gidan zanyi ba sai na
zauna zanga kayan takaici ba .” Imran shiru yayi yana sake zabgawa Ammar harara sai
kuma yayi kwafa ya fice. Mommah tabi bayansa da kallo tana masa addu’ar shiriya a
zuciyarta ji take kamar ta rusa kuka gaba d’aya sun cusawa Imran soyayyar shaheeda
ta ‘karfi da yaji da yaudara da komai. “ ka rabu dashi Ammar tsakaninka dashi
Addu’a ya riga yayi nisa a soyayyar shaheeda ba zai ta’ba ganin aibunta ba.” Ammar
ji yayi ransa ya sake’baci idan dai da shine ko da gold aka’kera shahida sai ya
ha’kura aurenta balle shi dai ban da kyan fuska bai ga mai ya gani tare da shahidan
ba tana tafiya kamar sillan kara,sai iyayi da kwainane. Shatu dai tana gefe tana
kallon ikon Allah, takaicin Imran kuwa ya gama cikata. Har so take taga wacece
wannan da ya fi sonta akan’bacin ran mahaifiyarsa. Ammar ya cigaba da bawa mommah
ha’kuri ganin ta’ki ha’kura yasa ya fita wajen bayan ya danna kiran hajiya mama
mahaifiyar mommah a cikin wayarsa. Basu san me yace ba sun ga dai ya dawo da sauri
ya mi’kawa mommahn wayar, ya wurga masa harara don ta san’kara ya kai ta wajen
hajiya maman. Tana sallama hajiya mama ta shiga fad’a tuni mommah ta sa kuka ta
fara bata labari. Hajiya mama cikin zafi ta katseta “ kishiya saboda kishiya zaki
bar gidanki akan ki aka fara kishiya?da girman ki da komai kike neman zubar da
mutuncin ki to ahir ki kiyayeni kina shirin auren da’kanne da ‘ya’ya, nan gaba su
kuma idan sunyi wa zai musu fad’a? To ki saurareni da kyau ki mayar da akwatinnan
kafin ma su gani su ji dad’i gobe insha Allah’kannenki sun zo hutu daga turkey zasu
zo kanon suyi miki hutu hisham ma dama yana ta son zuwa wajen mutuminsa Ammar. Ina
shatu?” Momma ta mi’kawa shatu wayar “ maza ki masa hajia mama ce “. Shatu ta
kar’bi wayar cikin rashin sabo ta fara gaisheta “ lafiya lau shatu ya ba’kunta?
Gobe zaki ga aunties d’inki suna ta son ganinki.” Murmushi shatu kawai tayi saboda
ba ‘yan hayaniyar a kanta. Hajiya mama ta sake cewa “ Ba dai matsala dai ko?” Shatu
ta girgiza kai “ Bakomai mama” To masha Allah sai kin ga sa’ko “ hajiya mama ta
fad’a tana kshe wayar. A hankali shatu ta mi’ka wa Ammar waya, ganin yarda jikinta
yayi sanyi yasa Ammar ya shiga janta da wasa” shatun mommah’kalau kuwa yau na ganki
jiki ya mutu? Ko don ki had’u da Babarki a masifa “ harararsa shatu tayi “ Ai
wallahi ba tsoronta naji ba, don dai kawai mommah ta hana ne amma wallahi da tuni
ta d’ebi kashinta a hannu yo Allah na tuba wannan ‘karamar alhakin, ka san Allah
da ‘kauyenmu ne yau sai na saka yara sun mata kid’an Atire.” Ammar mai zaiyi banda
dariya mommah kuwa bud’e ido tayi tana kallon shatu yarda take yi da baki “ To
shatu ba ‘kauyenku bane kuma anan idan kayi wa wanda ya girme ka rashin kunya
kulleka ake a gidan yara don haka be careful.” Ammar ya fad’a fuskarsa d’auke da
alamar tsoratarwa. Shatu ta kya’be baki “ Ai in dai ba kayi a fili ba sai mutum
yayi ta bayan fage yarda za ‘a gane ba.” Ammar girgiza kai kawai yayi yace “Allah
ya shiryeki shatu.” “ Tashi maza kije kiyi sallah Ayshata ai Na san kina jin
maganata ba zaki jawo min abin fad’a ba “.murmushi tayi tana mi’kewa dad’in yabon
da momma tayi mata da sauri ta shige toilet ta bar momma da ta zuba tagumi tunani
yyi mata katutu.
Dahda da daddare da kansa ya shigo d’akin mommah ganin ko nemansa ba tayi ba. A
zaune ya sameta kan sallaya da alama lazimi takeyi, jikinsa a sanyaye yake dubanta
yana son matarsa shi kad’ai kuma ya san irin son da yake mata, ba don komai ba sai
don yarda bata tsallake umarninsa kuma iya iyawarta take kyautata masa ba ta son
‘bacin ransa sam.
Tana ganinsa ta d’an d’auke kai idanunta yana kawo hawaye. A gefenta ya zauna had’e
da ri’ko hannunta tayi’ko’karin zamewa ya matse hannun murya a ‘kasa yace”Deejah
yau mantawa aka yi da abincinka?” Wani kallo tayi masa kafin hawayen idonta su
zubo. Hawayen ya dinga bi da ido “ kukan na menene?” Murya can’kasa tace “
abincinka yana wajen amaryarka” fuska ya sake tamkewa kafin yace “ wace irin magana
ce wannan? Kema kin san sarai ba da amincewata aka yi aurennan ba, to me yasa zaki
damu kanki yarda ta shigo haka zata koma, bani da tsarin ajiye mata biyu a gidana,
ba ra’ayina bane tashi muje ki bani abinci kada ki sake’bata min rai” Ya jata ya
mi’kar tsaye suka fita. Hanyar part d’insa direct suka nufa. Dai-Dai lokacin
hafsa’yar hajjan ta ganosu itace auta a d’akinsu da sauri taje ta sanar da hajjan.
Hajja kuwa tayi saurin fitowa fad’i take muje ba dani za’a yi wannan iskancin ba
muje da kaina in kai masa amaryar in kuma nuna masa ni Na haifeshi ba shi ya
haifeni ba...
A bakin ‘kofar part d’in nasa ta tsaya tana buga ‘kofar da ‘karfi kamar zata
‘balle ‘kofar. Dahda ransa a ‘bace ya bud’e ‘kofar, murya a sar’ke yace “Hajja
lafiya?” Kallon sama da ‘kasa ta jefa masa “ sannu isashshe har kana da bakin
tambayata lafiya to ita lafiyar tana gidan ubanka wuce muje ka taho da amaryarka
ita ta cancanta ta kwana a d’akinnan sai an mata kwananta uku rus da bazawara ta
bata, kuma ban amince da ko bakin’kofar nan naga sillan’kafafunta ba wuce muje ka
taho da matarka.” Mommah da take cikin parlourn tana jiyo duk abinda yake wakana ta
mi’ke zaune zauciyrta na tafarfasa ta fice daga palrlourn.
Shatu dake zaune a main parlour tana jiyo duk abinda yake wakana tayi al’kawarin
yau tsohuwar nan ba zata kwana da lafiya ba. Ta shige d’akinta tana’kissama irin
abinda za tayi mata. Da sauri ta shiga tanadin kayan duk da zata yi amfani dasu.
Cikin dare ta nufi d’akin da aka sauke hajja, a hankali ta murd’a’kofar Ta shiga,
Hajja ta tarar ta saki baki tana barci taci sa’a kuwa hajjan ita kad’aice a d’akin
tabbas shirinta zai tafi yarda take so, Ta sake kallon shigar da tayi a
mudubi’kusumbi tayi sosai a bayanta ga gashinta da ta saka ya rufe mata fuska gaba
d’aya sai wani farin hjibin momma da ta sin’kife jikinta dashi, ba’a ganin fuskrta
Sam, Ta dur’kushe sosai kamar wada tana lan’kwashe ‘kafarta kamar a shanye take.
Tsaye tayi gefen gadon hajjan kafin tasa sandar hannunta ta zunguri ‘kafar Hajjan
“ Ke tashi ajalinki yau yazo tsohuwar banza mai takurawa jama’a....... A razane
Hajja ta rusa wani ihu fad’i take “ ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba innahu
ala raja’ihi la’kadir......
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-10
Sosai Hajja ta sake razana ganin shatu tana nufota, fad’i take “ Don Allah kada ku
cutar dani ku fad’i mai kuke so nayi? Ni baiwar Allah ce ba ruwa na da kowa a
duniya.” Shatu ta ‘kya’kyata wata mahaukaciyar dariya “ so muke kada ki sake cutar
da hadizatu idan kuma kin’ki zaki ga sakamakon taurin kai kina ji?.” Da sauri hajja
ta d’aga kai “ Na bi Allah na biku insha Allah ba zan sake komai ba” shatu ta sake
kecewa da dariya bayan jin abinda tace cikin daka tsawa tace “ To rufe idonki kuma
kada ki sake ki bud’e sai nayi nisa da tashi sama.” Da sauri hajja ta rintse idonta
gam, shatu da sauri ta fice daga d’akin ta shige d’akinta. Ai cikin azama hajja
tana bud’e idonta tayi saurin mi’kewa ta fice daga d’akin jikinta har makyarkyata
yake, A tsakiyar falon ta tsaya ta dinga kwalawa mutanen gidan kira. Yarda muryar
tata ta karad’e gidanne yasa d’aukacin mutanen gidan fitowa, suka tarar da ita a
dur’kushe hankali tashe suke dubanta. Dahda ne yayi’karfin halin cewa “lafiya
hajja?” Hajja ta zuba masa wani irin kallo “ ina kuwa lafiya ko da yake yanzu ba
zan yi magana ba sai da safe kai ni falonka a can zan kwana kuma kana zaune daga
gefe na Yau gamo nayi da aljannu a gidannan.” Dariya ce taso kama Ammar ganin yarda
ta ha’ki’kiance take’buya a bayan dahda. Momma kuwa baki ta ta’be ta juya ta koma
ciki bayan tayi wa amaryar mijinta kallo d’aya. Ita kuwa amaryar bin bayan mijinta
tayi tana tsinewa hajja a zuciyrta yarda zata’bata mata daren amarci duk da tanadin
da ta shirya masa ga turarukan tsubbace tsubbace da ta ambula a jikinta banda wanda
ta turara sai da ta kusa samo kan mai gidan sannan wannan tsohuwar zata rusa mata
shirinta.
‘Karfe bakwai nayi Hajja ta fito babban falon gidan bayan ta tasa ‘keyar dahda a
gaba “ Muje ka had’o min kaf kan ahalin gidannan ina da magana dasu “ cikin tausasa
murya yace” Hajja da kin bari gari ya ‘kara wayewa ....” “ Na’ki Na bari garin ya
waye ahmadu nace na’ki Na bari manga uba na, saboda ba kai kayi gamo da abinda Na
gani ba ko.” Tayi saurin tare shi da sababin fad’a. Shiru kawai yayi yabi bayanta
zuciyarsa fal ‘bacin rai don dai uwa uwa ce da ba wanda ya isa yazo gidansa ya
aikata masa haka.
A tsaye suka tarar da momma tana sake gyara cushions d’in main parlour d’in tas ta
gyara gidan sai’kamshin turaren wuta gidan yake. Dahda ya bita da kallo ganin yarda
tayi kyau sosai cikin wani pink lace duk da fuskarta ba fara’a amma dai bata fasa
gaisheshi ba, sannan ta’karasa gefen hajja da take zaune saman kujera ‘kafa d’aya
kan d’aya tana girgiza jiki fuska cike da masifa, muryar mommah a cunkushe itama
tace “ Hajja barka da safiya an tashi lafiya?” Sai da Ta ‘kare mata kallo sama da
‘kasa cikin masifa tace “ ‘kalau sumul na tashi duk da ba haka kika so ba, cikin
kiyayewar ubangiji na tashi lafiya, saboda kin san tsaye nake akan ‘kafafuna wajen
ibada, wai ke deejah har tsubbun taki ta kai ki fara turawa mutum aljannu ? Saboda
Na saka d’ana yayi aure, to albishirinki wannan auren mutu ka raba kuma idan kin
tashi yau da daddare ki turo min sarkin rauhanai ma ba aljannu ba , Aljannun naki
mai suka isa suyi min sunzo sun baki labarin yarda Na fatattakesu da ayar Allah.”
Shatu da sauri ta juya Ta shige kitchen saboda dariyar da Ta ciyota. Hajja Ta
cigaba “ kuma ni da gidan d’ana ba inda zani zama daram.” Mommah shiru tayi tana
al’ajabin hajja yau kuma gingimemen sharrin da za tayi mata kenan lallai tsanarta
da hajja ta girmama. Hajja ta juya gun Dahda “ kai kuma manga kana tsaye baka
tambayeni ba’asi ba, yo ai dai kace hajja mai ya faru kike wannan fad’a da safiya
haka tunda kai haka Allah yayi ka kamar d’an fari, to ko Mahmud da yake d’an farin
baya abin da kake. Wato kana ji cikin dare matarka tayi min turen jinnu wai suna
gargad’i na na rabu da hadizatu kaji fa wai dijah yanzu har tayi shaharar turo min
Jinny?” Dahda ya girgiza kai saboda ‘bacin rai ma kasa magana yayi ya zuba mata ido
kawai. Ammar ne cikin d’aure fuska yace “ ko dai mafarki kika yi hajja ina mommah
taga aljannun da zata turo miki? Mu tunda muke gidannan ba wasu aljannu.” Girgiza
kai hajja tayi sai kuma tace “ Ba shakka, ‘karya nayi maka kenan? To manga ubanka
da yake zaune shine ma’karyaci ba ni ba. Ra’ayal aini yarda nake ganinka haka naga
aljannu ina tofa musu addu’a suna ihu da tumami suna fad’in deejah ce ta aiko su,
haka Na ‘konesu ‘kurmus ba mamaki idan kuka je d’akin ma kuka ga haya’kin da
tokarsu, yo ni za’a kawowa zancen banza aljannun me Allah na tuba”. Ba wanda ya
sake mata magana haka ta mi’ke ta koma d’akinta tana sake bambamin tijara. Shatu da
take la’be a bayan ‘kofar kitchen ta girgiza kai had’e da yin ‘kwafa ta juya ta
shige d’akinta .
‘Karfe biyu daidai ba’kin Abuja suka sauka. ‘Kannen mommah ne hisham da hafsa sai
nahnah. Kyawawa dasu farare tas kamar su innaji da mommah. Shatu tana zaune tana
lesson driver ya dawo daga’daukosu d’aya bayan d’aya suke bin ta da kallo ita ma
tana kallonsu, Hisham ne ya bud’e mata alamar ta taho ya dube ta kafin yace If I
guessed It right you’re shatu ?na canka shatu ce ko?” Da sauri ta d’aga kai hisham
da su nahna suka rungumeta da ihu cikin tsananin farin ciki suna murnar ganinta
hakanne Yasa Ammar da mommah da imran saurin fitowa suna murnar ganinsu ,
kasancewar sun dad’e basu zo hutu ba nahna da hafsa suna turkey, shi kuwa hisham
mate d’in Ammar ne tare suka gama makaranta a egypt, Imran ne yayi oxford
university england. Murna da hayaniyar da suke ce a main parlour ta fito da mutanen
gidan har Hajja da ta fito tana dogara sandarta da yake tana da ‘kiba ciwon’kafa ya
sata a gaba.
‘Daya bayan’daya take hurga musu kallo tana amsa gaisuwarsu a gatsine “ Ba shakka
dijah kin ci gida kin mallake manga kin mallake dukiyarsa ga ‘yan uwanki ma sun zo
sun taru a gida, kai Allah wadaran naka ya lalace su kuma wad’annan gand’an-gand’an
‘yan matan daga ina?” Nahna fuska a d’aure za tayi magana mommah ta girgiza mata
kai “ Don’t say any word here ku shiga part d’ina am coming.” Kasancewar akwai
tarbiyya hakan yasa basu shiga ba suka ja hannun shatu su kayi gaba su imran ma
suka bi bayansu. Mommah ba tace da hajja komai ba ta mi’ke zata wuce. Cikin masifa
Hajja tace “ la shakka ga ‘yar iska wato kin bawa banza ajiyata nayi tayi ko? To
kinyi da gyatumarki mai kama da sadakar yallar nan kuma da ni kike zancen yau yau
zasu juya su koma, kuma kaf jakunkunansu sai nazo Na caje don yanzu haka wani
tsubbun suka kawo miki an ji anyi miki kishiya azo a koreta ko? Kuma idan zasu tafi
ki tattara har bararojinnan su tafi da ita shaid’anun banza kawai.” Momma wani abu
Ta had’iya kawai ta juya ta shige part d’inta zuciyarta na tafarfasa, itama fa
mutum ce ba dutse ba dole zuciyarta zata dinga zafi da irin cin kashin da hajja
take mata amma ya zata yi dole ta girmamata tunda d’anta take aure. Sai da Ta share
hawayen fuskarta sannan ta’ka’kalo fara’ar dole ta bud’e’kofar falonta.
A zazzaune ta samesu tuni sun watsar da lamarin hajja sun saka shatu a tsakiya, sai
fito mata da tsarabar kayayyaki suke wanda suka siyo mata a turkey da wanda
kakanninta suka bata, sai nuna mata tsananin soyayya suke, hakan yasa fara’ar
fuskar shatu ta kasa ‘boyuwa kowa nuna mata ‘kauna yake ashe ba zata yi maraiciba
bayan mutuwar innaji, ashe yanzu ne zata fara fuskantar farin ciki a rayuwa. Ta
lura kowa sonta yake idan ka d'auke Imran da yake gefe yana harararta ‘kasa-‘kasa.
Hisham ya dubi Mommah kafin yace “ Hope dai by now an yi mata register a school ?“
Momma ta girgiza kai “ so muke brain d’inta ya da’n bud’e before taking her to
school insha Allah” Imran ya ta’be baki cikin takaici yace “ Allah wahala kawai
kuke wannan yarinyar she will never be socialized kamar yarda kuke so , rayuwar
daji fa tayi ai sai a slow kawai dama kun daina wahalar da kud’inku kawai don
wasting time dinku zaku yi ji fa wasu tarkace a hannunta “ ya fad’a yana nuna
hannunnata, gaba d’aya gurin shiru kawai su kayi zuciyarsu kowa da mamakin imran.
Hisham ne ya katse shirun yana dafa Imran yace “ Amma son banyi expecting hakan
daga wajenka ko bakomai she is your bloody sister da nake fatan mu nuna mata
soyayya mu kuma bata jin dad’in da ta rasa.” Tsaki yayi Hasfa ganin yarda mommah ta
damu sai ta sako wasa cikin zancen “ Rabu dashi Yaya hisham bayan ma bai san yarda
rana zata fad’i ba “ da sauri ya zaro ido “ wa? God forbid wallahi insha Allah rana
a gabas zata fad’i ko don ba kiga babban kamun da nayi ba classy baby ga good
hygiene ga kyau ga ladabi.” Tsakin da mommah ta zabga ne yasa yin shiru duk gurin
kuma aka saka dariya ban da shatu da imran ya riga ya ‘bata mata rai. Mi’kewa tayi
zata shige ciki taji Nahna tana cewa “ Mhmn Allah ya kaimu lokacin da zaka zo
kana’yar murya “ ya mi’ke yana fad’in “ ai ko a ‘kafa aka d’aura min wallahi sai na
cire na yar “ Mommah kwafa tayi tana nuna musu dinning “ Hisham close the chapter
kuyi taking shower ku ci abinci duk da dai tafiyar dad’i kuka yi tafiya a jirgi”
Nahna tace “ Yo wa zai zo kano from Abuja a mota.”
Da yammacin ranar kuwa ‘yan matan mommahn gaba d’aya suke a kitchen suna tayata
d’ora sanwar dare, shatu na gefen Nahna tana tayata had’a salad. Ta dubi antynnata
kafin tace “ Anty Nahna ku nawa ne’yan uwan innaji?” Nahna murmushi tayi tana dafa
gashin kan shatu data gyara mata shi ya sauka har tsakiyar gadon bayanta. “ Mu
biyar ne Mommah ce babba sai adda maryamu sai hamma hisham sai ni sai kuma hafsa
shekara d’aya ne tsakaninmu da hafsa. Mu kad’ai ne a gidanmu babanmu bai kara aure
ba shi yasa sam ba abinda yake d’aga mana hankali bamu da yawan da za’a samu
sa’bani a cikinmu muna son junanmu kamar mu had’iye kanmu, shi yasa sam ba muyi
Farin ciki da auren da ammar zaiyi ba, mun so ya auri jininmu ta yarda zamu sake
tashi tsintsiya mad’aurinki d’aya, amma hakan bai yiwuba kana tasa Allah na tasa
amma Allah’s plan is better than ours right?”murmushi shatu tayi ‘kaunar dangin
innajinta yana sake ratsa ta musamman ganin yarda suke nan nan da ita. Sai kuma ta
kama hannun nahna race “me kika fad’a daga ‘Karshennan ina so in iya irin maganar
nan” Nahna ta sake sakin murmushi kasancewarta ma’abociyar murmushi, tana jan
hancin shatu tace “ kin san turanci?” Shatu Ta d’aga kai “ Na sani innarmu idan
tana koya min karatu tana yawan ce min sai na iya abcd sannan zan iya turanci “
Nahna tace “ To wannan maganar da nayi shine turanci kice kin iya abcd?” Shatu
cikin dariya tace “ kai na iya fa har’karshe kuma har rubutu na iya da karatun
hausa Na abcd kuma na iya su boy girl, man da woman kai har su cup fa na iya.” Da
sauri hafsa da mommah suka juyo nahna kuwa murmushi tayi kice “ yarinyar tawa kanta
na ja ba zama kiyi wuyar shiga school ba.” Momma farin ciki ya cikata “ai kuwa gobe
za’a miki register a school ko primary 4 su kaiki shekara nawa kika ji innajinki na
fad’ar shekarunki?” Shiru tayi tana lissafi sai tace “ haka dai da zata mutu ina
shekara sha uku “. Hafsa tace nawa kenan a karatun book?” Wani kallo tayi mata tace
“ kai mhmn thirteen d’inne ban sani ba aradu har dubu munje da innaji tace min
thousand sunansa “ gaba d’aya suka hau tafa mata. Momma cikin farin ciki ta jata ta
rungumeta tace “lalle maryama tayi ‘ko’kari am so proud of her .”
Shigowar amaryar dahda ce ya dakatar dasu daga hirar da suke, ko magana bata yi
musu ba ta bud’e fridge tana wani gatsine sai kuma Ta d’aga waya murya cikin kissa
take fad’in “ Am coming dear naje samo maka drink d’in da kace ne.” Tana fad’a tana
kallon mommah da take murmushi ‘kasa-‘kasa, “0key dear yanzu zan dawo kada ka damu
zan maka abinda yafi kis.......” wani kallo mommah tayi mata da yasa ta gintse
abinda tayi niyyar fad’a ta juya har ta kai ‘kofa momma tace “ kice masa har ya
dawo daga kadunan da ya tafine? Kuma yaushe ya fara shan drinks na general
kitchen..” wata kunya ce ta kama amarya ta juya da sauri ta fice, gaba d’aya suka
saka dariya a kitchen d’in mommah tace “ kaji min shashasha right now fa na gama
receiving call d’in and he told me yana kaduna amma kaji makira “. Suka sake
she’kewa da dariya. Nahnah tayi tsaki “ Ni ba’kin cikina d’aya mommah da kuka
amincewa imran ya auri ‘yarta ba kiyi masa jan ido ba, don sun ga d’anki ya taso da
nasibi ga arziki ta ko ina ‘karuwar masa yake, kuma sun lura da matsanancin son da
yake miki shi yasa fa suka shiga jikinsa idan ban da haka ina imran ina wannan
yarinyar tana tafiya kamar bulala, ji fa ranar da muka had’u da ita a mall wallahi
nunawa tayi bata son mu ba.” cikin takaici momma ta girgiza kai “ ki rabu da imran
taurin kai gareshi kamar mutanen farko sau nawa na nuna masa bana so sau nawa na
hanashi, amma ya’ki jin zancena amma lokacine zan nuna masa bashi da wayo daga shi
har dangin ubannasa, muje dai zuwa a kuma juri zuwa rafi....”
Ita kuwa amarya tana fita d’akin hajja ta shiga ta zauna ta gaya mata’karya da
gaskiya hajja ta hau kai ta zauna. “ kika ce sun zageki zainabu?” Amarya Ta d’aga
kai hajja ta kuwa mi’ke zaune “ Ai kuwa tunda suka zageki ba ke suka zaga ba ni
suka so zaga aka fake dake, to kuwa ba zai yiwu ba uwarki ni na sha mama na bar
mata ban ga d’an abu ta kazar uban da zai zagar mana mahaifiya na ‘kyaleshi ba ke
ko da kuwa sadakar yallar uwarsu ce muje madafar “ Amarya farin ciki fal ranta ta
mi’ke ta bi hajja kitchen.
Tsaye hajja tayi ri’ke da ‘kugu tana musu kallon sama da ‘kasa “ Eeh lallai kuwa ba
shakka na ta’kar’kare na d’au cikin manga, Na sha ba’kar wuya a haihuwarsa ashe dai
ku na haifawa, an shigo cikin daula a dafa wannan a sauke wannan,A samu na banza
aci ai nak, bama wannan ba uban me zainabu tayi muku kuka zageta? Ko kuwa sa’kon
zagin kuka bata taje ta isar min hamsha’kai ?” Shatu ta zaro ido tana kallon amarya
murya ‘kasa-‘kasa tace “ Allah ya shirya babba da ‘karya cab” gaba d’aya kitchen
d’in ba wanda bai ji maganarta ba har hajja. Amarya ta zaro ido “ ke don ubanki ni
nake miki ‘karya ko hajja?” Shatu Ta sake gyara zama tace “ duk wanda yayi ‘karyar
ai addu’a nayi “ a sukwane ba suyi auneba suka ga ta zuba wa shatu mari hannu
bibbiyu a zafafe hafsa ta janye ta tana mata wani banzan kallo “ kada ki sake ki
sake dukanta me tayi miki? “ momma ta nuna musu hanyar ‘kofa “ ku fita “ ta’kofar
baya suka fice sannan ta kalli hajja “ kiyi ha’kuri ba wanda ya zageta amma tunda
ta fad’a miki kin yarda Allah ya baki ha’kuri” daga haka Ta fice bayan ta watsa wa
amarya kallon banza.
Hajja bata shiga d’aki ba anan main parlour ta dinga zazzaga tijara zagi ta uwa ta
uba ta dinga aikawa su mommah bayan amarya ta zauna ta sake fonfata wai har taji
sanda suke cewa so suke ta mutu su sake mallake manga gaba d’aya har dukiyrsa hakan
yasa ta sake sauke kwandon tijara zagi ta uwa ta uba. Ran shatu ya’baci musamman
ganin yarda su nahna suka fara had’a kaya wai tafiya zasuyi da sassafe zasu bi
flight d’in safe su tafi, haka ma hajiya mama tace bata son tashin hankali su taho
kawai. Shatu kuwa ta’kudirce a ranta tsohuwa hajja ba zata kwana lafiya ba sai Ta
gwammace kid’a da karatu.
Cikin dare shatu ta mi’ke daga gefen nahna da suka kwana tare a d’akinta, sad’af-
sad’af ta fice. Murd’a ‘kofar hajja tayi a hankali ta shige ta mayar da ‘kofar ta
rufe, dubanta ta kai kan hajja da ta saki baki tana barci tayi, har da yawun barci
ta saki dariyar mugunta bayan ta kashe fitilar d’akin da fanka har da a.c . ‘Dif
d’akin ya ba’kunci duhu ga windows dama duk a rufe, shatu ta shige ‘kar’kashin
gadon hajja a hankali, kasancewar ba auki ne da ita ba zuruf ta shige . Muryarta ta
kumbura ta fara fad’in “ke tsohuwa ke tsohuwar banza tashi maza ajalinki yazo....”
Hajja da taji maganar daga sama a razane ta farka taji d’akin d’uf misalin dai
duhun kabari da ake fad’a . “Kada ki sake kiyi mana ihu ba dai kince kin ‘konamu
ba zuwa mu kayi ki ‘kara ‘konamu mun ja kunnenki ba kiji ba to yau a tsakiyar
dajin aljannu zaki kwana kafin gari ya waye mu zu’ke jininki.......” Hajja jikinta
‘bari kawai yake murya a razane take fad’in “ Hajja kwananki ya’kare idan ban da
shegiyar ‘karyata dama mai ya kaini cewa nayi fad’a da aljannu......😂😂🤣🤣🤣
Kai yau nayi typing da yawa so that ina jiran in ga ruwan comments.
FREE📚
08033748387
-12
Shatu tayi saurin matse dariyar da take son kamata, ta sake jijjiga ‘kasan gadon ,
cikin murya mai amo sosai tace “ Baki ga komai ba tsohuwa sai kin bud’e ido kin
ganki a gaban sarkin aljannu yana bada umarnin a shanye jininki a yar da gawarki a
daji namun daji su cinye ba dai ba kya jin magana ba mun ce ki fita daga harkar
hadizatu kin ‘ki hahhhhhahhhha yau zamu sha jini ku ‘karaso maza ku d’auketa kada
ku sauketa sai a dajin sarki ‘kuraizu hahhhhhahhha.” Ta sake tuntsirewa da
shegiyar dariya hajja kuwa tuni ta sume tun bayan da Ta ‘kwallara wata ‘kara da
duk gidan ya amsa bayan taji an jijjiga gadon da ‘karfi. Imran ne ya fara fitowa
kafin su mommah suma su fito kowa yana Duban d’akin hajja inda ‘karar take fitowa.
Imran baiyi wata wata ba ya bud’e d’akin da sauri ya ‘karasa gun hajja da ya gani
a san’kame akan gado, ya fara jijjigata sai dai ba alamar numfashi a tare da ita,
idanunsa ne ya sauka akan tsinkakken abin hannun shatu da sauri ya zaro ido bayan
ya d’au abin hannun yana dudduba inda zai ganota, bai ga alama ba ya zira abin
hannun a aljihunsa. Momma kuwa da sauri ta ‘karaso tana dubata a gigice take sosai
hakan yasa murya na rawa take cewa “ Imran kira doctor she is unconscious “ Imran
ya mi’ke yayi saurin shiga toilet nan ma bai ga shatu ba, ruwa ya d’ebo ya zubawa
hajja a jikinta ,da sauri ta kawo ajiyar zuciya ihu take tana fad’in kada ku tafi
dani bijahil kudrati na daina shiga sabgar dijama innalillahi.” Kowa d’akin tsit
yayi yana kallonta, Imran ya kamata “ Tashi Hajja ba wani aljannu da izinin
ubangiji koma akwai zan binciko su” Hajja ta mi’ke jikinta sai ‘bari yake fad’i
take “muje d’akinka imran tunda manga baya nan a can zan kwana ni da d’akinnan har
abada anan matattarar aljannun gidannan suke.” Ammar da yake gefe ya tuntsire da
dariya sannan yace “ Hajja rannan fa cewa kika yi kunyi fad’a dasu har kin ‘konasu
to yau me yasa kika kasa.” Shiru tayi tana dube-dube “ kai Ammar ka iya bakinka
yanzu d’akin nan taf yake da jinnu kafin kaima su dawo kanka muje lmrana” jikinta
rawa yake sosai Imran ya fita da ita daga d’akin.
‘Dakin mommah ya nufa da ita da sauri taja tunga ta tsaya “ ina zaka kaini Imran?”
Fuska a had’e yace d’akin mommah mana wani abu ne?” Hajja taja baya kafin tace
“ma’ana so kake naje d’akin su samu nayi su dagargazani d’akinka zaka kaini dama
manga na nan ne sai ba kwana a d’akinsa gobe kuwa jirgin asuba zan bi zuwa garinmu
ba zan sake kwana a gidan manga baseries kuyi min bukin na tikitin jirgi.” Ammar
yace “kice ba zaki zo bikin bros ba?” Kallonsa tayi sai kuma tayi ‘kwafa ta dam’ki
hannun Imran “muje d’akinnaka” Imran ya’bata fuska Kafin yace “ Ni fa hajja ba’a
shigar min d’aki ni kad’ai nake amfani dashi for goodness sake ya zanyi dake idan
kin so shiga toilet ki dai canja shawara idan ba zaki shiga d’akin mommah ba sai
dai a kaiki d’akin amarya” “To kaini can d’in ita ‘yar banza ma ko fitowa ba tayi
ba duk wannan budirin da ake.” Shi dai baiyi magana ba ya jata ya kaita part d’in
amarya . Yace “sai ki buga mata ni zan tafi na kwanta” ya juya da sauri ta
cakumoshi ganin labulai na motsi, tsaki yayi sai kuma ya hau dukan’kofar amarya
tana fitowa ya bar hajja yayi saurin fita so yake yaje ya rutsa yarinyar can.
Ko da ya shiga d’akin ganinta yayi kwance akan gadon hajja tana ta tuntsira dariya,
ko kad’an bata damu ba da taga ‘kofar d’akin a rufe da key bata da hanyar fita ta
san kuma dole goben asirinta zai tonu. Tsit tayi bayan ganinsa a tsaye kamar wanda
aka turo fuskarsa a had’e kamar hadarin kaji. Gadon ya’karasa ya janyo jelar
gashinta sai gashi ta mi’ke tsaye tsam, fuskarta babu alamar tsoro ko kad’an. Ji
yayi kamar ya mammaketa ya ja bakinta ya murd’e duk da taji zafi bata nuna masa ba
sai ma ‘bata fuska da tayi “kece aljannar da ke tsorata Hajja kenan to yau
asirinki ya tonu kuma sai na gayawa kowa abinda kika aikata har dahda so kike ki
kashe masa uwa kenan?” Turo baki tayi tana masa kallon ‘kasa-‘kasa, ba tare da tayi
magana ba, ya sake janta ta durgo daga kan gadon sai gata a gabansa, kallon mamaki
yake mata ganin yarda sam ba tsoro ko kad’an a tare da ita ya rasa irin yarinyar
nan ko dai da gaske tana da ala’ka da jinnu tunda ance rayuwar daji tayi. “Wato ke
baki tsorata ma da laifin da kikayi ba, ji yarda kike kallona da idanu kamar na
mayu d’auke idonki a kaina before i nock your head, yau a toilet za kiyi spending
darenki wuce Muje.” Ta’be baki tayi an gaya masa tana tsoron kwana a toilet ne
balle wannan toilet d’in nasu na ‘yan gayu ita tsoronta d’aya kada ya gayawa
wannan Almasifatun Babannasu da ko idonsa bata son gani razana ta suke. Ya turata
toilet d’in har zai kashe fitila da yake switch d’in a waje yake sai ya fasa ya
rufe toilet d’in da key ya fice daga bed room yana mamakin taurin zuciyar shatu.
Da asubar fari yazo ya bud’eta ba don komaiba sai don baya son ya shafawa mommah
black paint dole zai bar hajjan a zuwan jinnun gaske ne. Tana barci a kwamin wanka
ya sameta hankalinta kwance. Tsayawa yayi yana kallon al’ajabi yarda take barci
peacefully a cikin toilet idan shine ai an kasheshi baya jin zai kwana da lafiya.
Ya daddage ya d’aka mata duka, ta d’anyi saurin bud’e idonta tana ganin shine ta
saki murmushin mugunta don tayi targeting sai ta rama wallahi nan kwana kusa kuwa.
Ta zuro’kafafunta ta fita. Shi kuma yabi bayanta. Sai da yaga ta shiga d’akinsu
sannan yaja ‘kofar part d’in hajja ya fice masallachi.
Ana idar da sallahr asuba Hajja ta fito main parlour ta zauna, ko tunanin d’aukan
kayan ta bata yi ba. Imran yana shigowa daga masallachi yayi arba da ita dariya
taso ‘kwace masa sai dai da yake ba ma’abocin dariyar bane sai ya gimtse “ wai
meye haka hajja tafiya ba shiri” ya fad’a yana jingina da bango. “ mi’kewa hajja
tayi tana gyara sandarta kafin ta sake gyara glass d’in idonta ta kafeshi da ido
kafin tace “ko ubanka manga bai isa yace sai na sake kwana a gidannanba aljannu na
neman kassarani maza-maza muje ka kaini tashar jirgi.”Ransa a ‘bace ya juya sai
kuma yace”ai dai kya yi sallama da mutanen gidan.” Ya shige sashen mommah Hajja
tayi saurin bin bayansa “muje ka wani bar ni anan nifa tsoron gidannan nake ji”
shatu da take la’be a window ta tuntsire da dariya da sauri hajja ta dam’ki hannun
sa “kaji ko wallahi har yau suna gidannan ko baka ji abinda naji ba” hararar shatu
yayi tayi saurin sakin labilan. Nahna da take zaune tana azkar ta kalli shatu “ ke
lafiyarki kuwa?” Shatu taso bata da labari sai kuma ta gintse tace “zo kiga
tsohuwar nan anty nahna zo kiga yarda take rawar d’ari duk tabi ta ma’kal’kale yah
Imran” Nanah tace “Allah ya shiryeki shatu ko dai ke kike tsorata ta?” Da sauri
shatu ta girgiza kai. Suna kallo su mommah suka rakata su kayi mata sallama.
Kashegari kuwa budurwar Imran ce ta bayyana a gidan tazo hutu a cewarsu wajen
uwarta daga abuja fara ‘kal da ita har yellow take sai dai a tsaye take tsam kamar
sanda shatu da take jikin window inda ta saba la’be, tana ta kallon yarda Imran
yake rawar ‘kafa da budurwarsa ta kuwa ta’kar’kare tace “Muciya da zani” kasancewar
parlourn ba hayaniya ba wanda bai ji furucinta ba sai da maganar ta fito tayi
saurin toshe bakinta tana kallon Imran da suka yi four eyes da ita ransa a matu’kar
‘bace.....”
FREE📚
08033748387
-13
Da sauri shatu ta ruga part d’in mommah, shima Imran yayi saurin mara mata baya,
yau kam ba mai hanashi cin kwal uban shatu, a bayan mommah ya ganta tana ta dariya
‘kasa-Kasa, kamar mayunwacin zaki haka ya bita zai cafkota, mommah tayi saurin
ri’keta tana furta “kai lafiya uban mai tayi maka?” Cikin ‘bacin rai yace mommah
please ki rabu dani in jibgi yarinyar nan, habibteey fa take tsokana wai muciya da
zani” dariya ce taso kufcewa mommah tayi saurin rufe baki wanda hakan ya sake
‘kular da Imran yayi kukan kura ya kamota mari lafiyayye ya sauke mata. Da sauri
mommah ta janye ta ranta a matu’kar ‘bace “ wai meye haka ne Imran kasheta zaka yi
akan wata habibty to wai ma da tace mata muciya da zani sunanta ne? Ko kuwa an
canja mata suna ne ta koma muciya ina ce dai ba sunan mutum bane muciya?” Ransa a
‘bace yake sake kallon mommah kafin yayi ‘kwafa wallahi da ita take kuma zaki gane
baki da wayo” Mommah ta’kunshe dariyarta ita da nahna da shigowarta kenan tace “a’a
Imran kaso kanka sai dai kuma idan tsarguwa kayi ni ban ga abin damuwa ba indai ba
habibteeyn taka tayi kama da muciyar da zani bace” Hafsa da Nahna suka tuntsire da
dariya. Tsaki Imran yayi ya juya ya fice zuciyarsa cike da sake tsanar shatu.
Bai ganta ba a parlourn hakan ya nuna masa ta shiga sashen mahaifiyarta don haka
direct d’akinsa ya nufa yana danna waya nemanta yake, sai dai sai rejecting calls
dinsa take.
Ita kuwa tana can zaune fuska a tur’bune tana kallon mahaifiyarta “amma anty wannan
yarinyar wacece? A gaban mutane fa ta disgani wai muciya da zani yanzu idan tasa
Imran ya ankare da halittata fa ya fasa aurena” zainabu ta girgiza kai “bai isa ba
bashi da wannan right d’in baby don na riga Na d’inke zuciyarsa a jikin taki tsaf
ba zai ta’ba kallon wata mace bayan ke ba da sunan so” murmushi ta saki “wallahi na
yarda da lamarinki anty gashi nan ma yanzu sai kirana yake tun d’azun na tabbata ya
kasa sukuni ne”zainabu ta girgiza kai “ba zaki gane irin yarda na tsani Dijah bane
saboda ita fa manga ya’ki aurena har an saka rana ta da yana had’uwa da ita yace ya
fasa aurena bayan na tabbata ba yin kansa bane tsubbun su na fulani ne ya kamashi”
Shaheeda ta girgiza kai “kullum fa anty sai kin bani labarinnan ko hadda ne yaci
ace by now nayi haddarsa ni yanzu damuwata ayi a saka ranar nan na kama shi a
hannuna ina son Imran to the extent.” Zainab ta dafa ta “shaheedah na sani na san
kina son Imran amma fa bana so ki sashi sosai a zuciyarki don bana son lokacin da
aikina zai kammala ki kawo min cikas bance kada ki so shiba a’a nafi so ma ki so
shi sosai ko bakomai ba ko don dukiyarsa yaci a soshi, duk da kema na san don hakan
kike sonsa da bashi da ko sisi ko shine aljannu don kyau ba zaki aureshi ba,aurenki
da Imran ba fashi don nima shine burina, sai dai ina da wata manufa mai ‘karfi akan
haka kuma kada ki sake ki bijire min a lokacin da bu’kata ta tazo” shaheeda
murmushi tayi kafin ta janye jikinta ta mi’ke tsaye ta furta “Allah ya nuna mana
lokacin bari inje in gaishe da inlaw ta kada tace bani da kunya.” Zainabu ta had’e
a rai a zuciyarta tana tunanin lokacin da zata cimma burinta da ya jima a
zuciyarta.
Murya can ‘kasa tayi sallama a ‘kofar parlourn idanunta akan shatu tana jin
tsanarta a ranta. Momma ta amsa mata sallamar fuskarta ba yabo ba fallasa su kuwa
su nahna ba wanda ma ya kalleta. Sum-sun har ‘kasa ta dur’kusa ta gaida mommah.
Amsa mata mommah tayi fuskarta fal fara’a tace “Ya gida ya mutanene gidannaku?”
Kanta a ‘kasa tace “lafiya lau” hafsa ta bita da wani kallo a zuciyarta tace
munafuka. Shatu kuwa ‘kara ‘kare mata kallo take tana son ganin wani aibu a
fuskarta sai dai bata gani d’in ba fuskarta ba yabo ba fallasa tana da kyau dai-dai
nata sai dai daga ganin goshinta kasan bata da gashi tsam ta mi’ke “mommah bari na
kawo mata ruwa” momma ta gyad’a kai “kin kyauta kuwa mah girl hakan yayi”
Shigowar Imran yayi daidai da kawo mata ruwan da tayi. Yana ganinta yayi saurin
had’e rai. Ita kuwa shatu bata ma san yana yi ba ta isa gabanta ta ajiye mata ruwan
ta kuma ‘ki yarda ta kalleta ta hau zuba ruwan, da azama Imran ya ri’ke hannunta.
“Kwashe ruwan nan ki tashi daga nan kafin nayi ball dake wa yace miki ita
‘kazamace da zata sha ruwanki.” Kallonsa shatu tayi kallon da bata ta’ba yi masa
sai taji zuciyarta ta buga bata ta’ba ganin zahirin kyansa ba sai yau da suka yi so
close dashi, taushin hannunsa a cikin nata yasa ta zubawa hannayensu ido. Kamar a
mintsineshi da sauri ya janye hannunsa, itama shatu hakan ya fargar da ita ta janye
idonta da sauri ta mi’ke jikinta a sanyaye tayi hanyar d’akinta. Mommah kuwa ranta
ne ya’baci tunaninta haushi shatu taji daji saboda furucin da Imran yayi a
Kanta.mi’kewa tayi ita ma ta bi bayan shatunta. A kwance ta ganta akan gadon. Ta
zauna a bakin gadon taja ‘kafarta “ Tashi shatun mommah tashi maza kije ku tafi da
nahna za tayi miki shopping d’in school.” Da sauri ta mi’ke tana murmushi “mommah
yaushe zan fara zuwa?” Mommah tana murmushi tana duban shatu ta lura shatu sam bata
da ri’ko shi yasa kullum take cikin walwala ko tunani da wuya ka kama ta tanayi
always zuciyarta fresh take as babies hearts. Tana kallonta ta fice da d’an
saurinta. Ko da suka fita parlourn tuni suka tarar Imran ya fice da gimbiyar tasa.
Da sassafe shatu tayi shirin school ta fito kenan ta tarar da masu aiki a kitchen
hannunsu duk hand gloves da alama uban ‘kyankyamin su ke yiwa girki. Da fara’a ta
shiga tana kallon Daniel tace “ shugaban yan girki abincin waye wannan?”cikin
gwarancin hausarsa yace “Babyn mommah kayi kyau wow!” Harara ta zuba masa “tambayar
da nayi maka kenan?” Daniel yana dariya ta shagala da kallonta yace abincin oga
Imran ne” murmushi ta saki tana dubansa ta juya ta shiga store cikin abinda bai fi
second biyar ta fito a guje “daniel zo ka fita da ‘bera” daniel ya zaro ido “‘bera
kace mai kyau you mean rat?” Tsaki taja “kayi sauri ka tsaya kana surutu sai ya
shige wani wajen” yana shiga ta rufo ‘kofar da key “idan ka cireshi ka gaya min
sai na bud’e.” Ta bud’e peppe soup ta tara yawu a bakinta ta tottofa ta mayar ta
rufe tana dariya, sannan ta ciro wata leda a jakarta ta tsiyaya ruwan cikin shayin
dariya take sosai “yau zamu ga ‘karsheb tsafta zaka sha yawuna ka sha kuma ruwan
hammata ta.” Da sauri ta bud’e daniel jin Imran na’kwala masa kira.” Kaga ‘Beran?”
Ta wurga masa tambayar bayan ta lura yana kallonta “ban ganta ba” ficewa tayi tana
cewa “ta gudu kenan bagware wai ban gan taba sai kace ‘beran macece?”
Not edited.....
Tun da ta ganshi a parlourn hakan yasa ta zama don taga ko zaici abincin,shi kuwa
yana dinning a zaune ya had’a tea ba tare da ya dubeta ba da alama sauri yake don
haka da azama ya d’aga cup d’in tea d’in ya kur’ba ya kuma bud’e bowl d’in peppe
soup d’in ta zuba a plate ya kai baki yana kur’ba dad’in peppe soup d’in ya ratsa
har kwanyarsa ya lumshe ido yana sake zu’ka. Dariyar da shatu ta saka ce yasa shi
saurin bud’e idonsa sai kuma ya had’e ransa yana dubanta tana ta she’ka dariya har
da tuntsirawa,jikinsa ne ya bashi tabbas akwai dalilin dariyar tata don haka da
sauri ya ture plate yace”ke zo nan” tana ‘kunshe baki ta fara shirin guduwa
“wallahi kika d’aga ‘kafa daga wajennan ko da one step ne zaki ga abinda zan miki
zo nan nace.” Hantar cikinta ne ya d’uri ruwa har ta juya zata wuce ba tare da taje
d’in ba taji ya dam’keta ta baya gashinta yaja taji zafi sosai don haka ta runtse
ido.”Don Allah ka sakar min gashi akwai zafi fa to wai mai ma nayi maka?” Tayi
maganar cikin muryar shagwaba bai mata magana ba ya jata zuwa part d’insu a parlour
ya wurgata saman kujera”gaya min uban me kike wa dariya ko na baki wahala nan dai
ba mai cetonki balle kice wallahi idan baki gaya min ba ko school d’in da kike
zumud’in zuwa ba inda zaki”Jin yace ba zata school ba ne hankalinta ya tashi duk
d’okinta da takeyi zai ruguza mata shiri ta fara rawar baki”kada ki sake kiyi min
‘karya ina da abinda zan saka a jikinki in gano gaskiya don fad’a min gaskiya kafin
na gano da gaskiya.” Ya fad’a cikin’kara tsare gira. Hakan ne ya sake razana ta
tayi saurin cewa “idan na gaya maka gaskiyar zaka barni in wuce school?” “Fad’i ina
jinki” ya fad’a yana tsareta da ido. Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “Don Allah
kayi ha’kuri a cikin peppe soup ne na zuba yawu na a tea kuma na zuba maka ruwan
hamma.....” da sauri taga yayi toilet yana kakarin amai hakan yasa ta suri school
bag d’inta tayi waje a guje. Ya dad’e yana amai kamar ya amayar da kayan cikinsa
‘karshe ya fito har wani jiri yake ji kamar ya kifa haka ya kwanta akan gado yana
maida numfashi har ga Allah yarinyar nan ta cuceshi cuta bata wasa ji yake kamar ya
fito da kayan cikinsa ya sauyasu ha’koransa kuwa da harshensa ya dirje su yafi sau
nawa har rad’ad’i suke masa zazzafi mai zafi ya kamashi haka ya ‘kudunduna a gado
duk da yana da important issue haka ya ha’kura da fitar.
A school an kar’beta ko da suka gwadata suka ga gwara kawai su kaita primary five
tunda tana da sharp brain idan yaso a gida a samar mata lesson teacher.
Da ta dawo kuwa samu tayi duk gidan suna part d’insu Imran wai bashi da lafiya
ta’be baki tayi ta samu abinci kawai ta fara ci ita ina ruwanta da ciwonsa mutum
sai shegiyar tsaftar tsiya har da wani amai da ciwo. Taci ta ‘koshi sannan tayi
wanka ta zira da wando tana fitowa ta tarar da mommah ta shigo. Mommah ta bud’e
mata hannu tana welcoming d’inta tare da furta”oyoyo autar mommah ya school d’in”
ta d’aga kai “
Ba laifi mommah amma fa sai an jawa ‘yan class d’in kunne bana son rashin kunya don
naji suna ce min wai ra’kumi a cikin ‘yan tsaki to yau dai nayi musu na ba’kunta
gobe kuwa wallahi na jaki zasu ci” Mommah murmushi tayi ta dafa ta “ba’a fad’a a
makaranta baby na kada ki kula kowa kin ji’yar albarka kiyi karatunki kawai ki koma
gida shine abinda ya kaiki kinji?” Murmushi tayi ta d’aga kai shigowar nahna ce
yasa mommah ta tuna ruwan tea zata dafawa Imran kuma ya ro’keta don Allah da kansa
zata kawo masa don yanzu tsoron ta’ba komai na gidan yake da zai iya ma da kansa
zai shiga kitchen d’in ya dafa to jiri yake ji saboda tun safe ba abinda ya shiga
cikinsa.Momma ta girgiza kai “kinga kuwa nahna shaf na manta abinda nazo yi bari in
tashi” Nahna tana dariya tace “ya kuwa ce da kanki yakeso ki dafa masa kuma kina
juyewa in kawo masa ni ban san me ya sameshi ba” mommah tace “mhmn rabu da Imran
haka yake idan yana cuta sangarta ce dashi zan ga yarda matarsa zata yi da
‘kyan’kyaminsa wallahi abin yana damuna sai kace wani mai cutar tsafta.” Da kanta
ta dafa tea d’in ta bawa Nahna ta kai masa.
Yana ganinta ya mi’ke zaune da kyar yana ri’ke kansa ya jingina da bangon gadon a
hankali ya motsa bakinsa muryarsa ta fito “please mommah ce ta dafa kuma kina tsaye
a wajen? Ibilishiyar yarinyar nan kuma bata wajen ko?” Nahna ta girgiza kai tana
dariya ta tabbatar masa mommah ce ta dafa da kanta. Ta zuba ta mi’ka masa yana
sipping a hankali. Lokacin shaheeda ta murd’a ‘kofa ta shigo kallo d’aya tayiwa
nahna ta d’auke kai hannunta d’auke da cooler ta nufi gefen gadon ta zauna cike da
kwainane sai zabga ‘kamshi take ta zauna a gefensa tana jan yatsun ‘kafarsa “am
sorry Habibi ya jikin?” Nahna ta kai idonta kan hannun sai kuma ta ta’be bakinta da
sauri ta fice tana mamakin rashin kunya irinta ‘yan matan yanzu sam basa iya tsare
mutuncin kansu shi yasa ko auren aka yi mazan basa ganin mutunci su.shaheeda ta
sake kallonsa tana murmushi “ Habibi in zuba maka abincin?” Da sauri ya girgiza
kai, ta kuwa had’e rai a hankali tace “kai habibi I cooked it with my own hand fa
please kaci kaji?” Cikin muryar shagwa’ba take gaya masa hakan ya sake narkar da
zuciyarsa yana jifanta da wani kallo ya matsu ya matsu sosai ya auri shaheeda shi
kad’ai irin son ta da yake dan’kare a zuciyarsa yana jiran lokacin da Zai amayar
dashi.ta zuba a plate ta zauna tana bashi a hankali cikin sigar jan hankali.
Mommah ce ta tilasta shatu sai taje dubashi, ta mi’ke tana zun’bura baki a
zuciyarta take tunanin ita mommah bata san itace silar ciwon bane ta tabbata yanzu
idan taje sai ya huce haushin abinda tayi masa. Hafsa ce cikin fad’a tace “Ba zaki
tashi kije ba sai na ‘bata miki rai baki san d’an uwanki bane shi duk duniya baki
da kamarsa fa shi da Ammar.” Mi’kewa tayi ta fita niyyarta idan ta fita ta la’be ta
dawo tace taje, sai dai a rashin sa’arta Nahna ta mi’ke tace “Bari muje na san
halinta yanzu ta ‘buya tace taje.” Ta tura ‘kofar bed room d’in a hankali bayan ta
shiga parlourn hakan yasa Nahna saurin juyawa ta koma. Ita kuwa shatu mummunan gamo
tayi shaheeda ce a gefen Imran tana ta shafa masa fuska wai tausa take masa ta
shige jikinsa sosai kamar me. Da sauri shatu ta runtse ido tayi saurin juyawa shi
kuwa Imran motsin da yaji ne yasa shi saurin mi’kewa sai yaga fitar shatu da sauri
ya janye jikinsa yana wa shaheeda wani irin kallo “sau nawa zan gaya miki bana son
irin wad’annan abubuwan bafa wayewa bace yanzu kinsa yarinya ‘karama ta gammu a
haku me kikeso tace mai kike so tayi zargi a zuciyarta?” Shaheeda marairaice masa
fuska tayi “Haba habibi meye a cikin hakan kawai fa tausa ne amma tunda baka so
insha Allah na daina Allah ya kaimu lokacin da zaka zama halal d’ina in nuna maka
pure love da ba surki amma waccen yarinyar mai take zuwa yi har bed room d’inka?”
Runtse ido yayi yana tunanin lamarin yarinyar baya ko son ganin fuskarta tsoronta
lamarinsa yake bashi don haka dole ya samarwa kansa lafiya ya fita sabgarta kafin
tayi abinda zai kaishi lahira burinsa ma lokacin bikinsa yayi ya tattara ya bar
gidan ba sai ta ganshi bama balle ta hukunta shi da ‘kazantarta.
A ranar Dahda ya dawo amarya aka shiga giringid’ishin kama miji mommah dai ko
gurinsa bata jeba balle taga abinda zai ‘bata mata rai, sai da ya gaji da kansa ya
shiga part d’inta tana zaune da kwalliyarta ta tsadaddiyar atamfa ta kashe d’auri
parlorn nan sai ‘kamshin turaren wuta yake yi. Murmushi ya sakar mata “uwargida ran
gida barka da hutawa ni nazo gaisheki tunda ba’a nemansa” murmushin ta saki itama
bayan ta gama saurararsa tace “hakan da kayi shine abinda ya kamata ka bi
cikakkiyar sunnar manzon Allah ya hanya?” “Alhamdulillah” ya furta yana sauke
nauyayyiyar ajiyar zuciya ya tabbata da itace da girki da tuni ta kai masa ruwan
wanka ta kuma taimaka masa da tausa da lafiyayyen girkinta tana zuba masa tana
murmushi ba dole dijah ta sace zuciyarsa shi kad’ai ya san wacece dijah ya kuma
tabbatar ba zai samu kofa kwafinta bane balle wacce ta kaita. “Na biya wajen hajja
wai me ya faru ne ta tabbatar min da aljannu a cikin gidannan wai ba zata sake zuwa
ba” yana murmushi ya fad’a mommah ma dariyar tayi tace”Ba mamaki da aljannun a
d’akin da take sauka amma mu dai bamu ta’ba gani ba” “Ni na sani na san rigimar
hajja ce yanzu ba ma wannanba ta rigime min sai anyi bikin Imran nan da wata d’aya
da Rabi” mommah ta saki murmushi kafin tace “Masha Allah Allah ya nuna mana me yayi
saura ai ya gama gininsa Allah yasa albarka yasa abokiyar arzikinsa ce yana d’akima
ba lafiya” Dahda ya mi’ke “ai naje na duba shi ina shigowa zainabu ta fad’a min
Allah ya bashi lafiya yace min stress ne yayi masa yawa Imran ne akwai son kud’i
baya son hutawa” mommah tana dariya tace “kyan d’a ya gaji ubansa”
FREE📚
08033748387
-15
*****
Tun daga lokacin Imran ya tattara shatu ya watsar a gefe baya shiga shirginta sam
ko a waje ya ganta baya zama idan kuwa yana waje tazo da sauri yake barin wajen.
Hakan da yake yi kuma sosai ya fara damun zuciyar shatu bata so ba sam bata so ya
daina shiga lamarinta ba haka kawai take son ta dinga ganinsa tana jin muryarsa da
kuma kyakykyawan murmushinsa, hakan yasa ko da yaushe take zama a main parlour
kawai don yas shigo ta ganshi taji’kamshinsa ta kuma ga kyakykyawan takunsa da yake
yi tamkar a cikin izza bata san daliliba haka kawai IMRAN AHMAD MANGA yake burgeta.
Ba wai soyayya take nufi ba tunda har a lokacin bata san so ba kawai dai burgeta
yake tsaftarsa kallonsa tafiyarsa maganarsa komai Imran manga yayi burge shatu yake
sosai har cikin zuciyarta ba mamaki hakan yana da ala’ka da zamowarsa d’an uwanta
kuma jininta wanda duk duniya bata da na biyunsu. Ganin ya daina shiga shirginta
itama ta tattarshi ta watsar ta kama Ammar abinta da uncle d’inta Hisham da kullum
suke tare indai suna gidan.
Tuni ta mayar da hankalinta akan karatunta both islamic da boko bata wasa burinta
ta zama mai ilimi ta kuma iya english kamar yarda taga su Anty hafsa suna yarawa
abin yana burgeta yana sata nishad’i, hakan yasa take damun mommah da zancen ita
kuma mommah ta dafa kanta tace “sha kuruminki shatun mommah zaki iya turanci da ko
bature england sai ya sara miki” hakan da mommah take fad’a shi yake ‘kara mata
ho’b’basa taji tana so tana kuma zakwad’i da karsashin son zamowa baturiya mai yara
english ba gargada ko tuntu’ben harshe. Sosai take dagewa lamarin har tsoro yake
bawa mommah ganin yarda ta mayar da karatu abokinta ko da yaushe zaka sameta da
littafi na islamiyya da na boko. Tsoron mommah d’aya kada karatu ya sa ‘kwalwarta
ta’buwa don haka sau tari take ‘kwace littafin ta saka mata kallo ko tace tayi
barci ko na rabin sa’a ne kwanyarta ta samu hutu.
Tuni su hafsa suka tattara suka koma Abuja saboda yawan damunsu da hajiya mama take
da yawa akan hutun ya isa, kullum fad’a take tana ‘karawa “ Ba hauka bane abin ku
tattaro komatsanku ku dawo nima ina bu’katarku idan bikin yazo kwa koma tunda dai
bata da wasu sha’ki’kan da suka wuce ku” hakan yasa dole suka tafi zuciyarsu cike
da tausayin mommah ganin yarda kishiya da dangin miji suka sakata gaba. Koda suka
gayawa hajiya maa murmushi kawai tayi kafin tace “haka rayuwar ta gada ba yarda
bawa zai zauna ‘kalau bai jarrabeka ba idan kaga Allah baya jarrabarka ma ka
binciki kanka balle d’iya mace a gidan miji taya kuke zaton zata samu aljanna a
‘bagas ai dole ne a jarrabeta ko ta’bangaren kishiya uwar miji ko dangin miji,
‘ya’yansa ko d’ungurungum mijin ma gaba d’aya babu wata mace da zata ce salin Alin
tana rayuwarta ‘kalau tsakanin bawa da ubangiji godiya kawai a duk yanayin da ya
tsinci kansa don haka ta godewa Allah tunda mijinta na sonta saura kuma ta barwa
Allah ta sha mamakin hukuncinsa ai hukumullahi la ajabun.”
********
Wata d’aya ya rage biki a kuma lokacin ne ‘kannen Ahmad manga mata masu ji da kansu
suka iso gidan d’an uwansu da set d’in akwatinan lefe za’a wuce dasu dangin uban
shaheeda da suke Abuja.
Mamaki ne ya hana momma magana da suka samu a sashenta suka ce taje taga lefen da
Imran ya had’a. Baki sake take kallonsu kafin ta furta “shi Imran d’inne ya had’a
lefe ba tare da sanina ba saboda bai mayar dani uwa ba ko mai?” Tsaki hameedah tayi
tana tauna chewingum sai kuma ta tintsiro d’ankwalinta gaban goshi tana watsawa
momman kallon raini tace “yo da ke har wata tsiya kike d’aukan kanki d’a dai kin
haifa amma baki isa kice zaki juya shi ba wannan kam sai yarda muka ga dama kin dai
juya ubansa mun’kyale ki yanzu kam the table
Don haka muka saka dole ya auri shaheeda mu juya shi son ranmu kema ki d’and’ani
rad’ad’in da mu kaji da kike juya yaya manga ki taso kiga lefe idan kinga zaki iya
idan kuma ba haka ba kya gani a jikin surikarki kuma ‘yar kishiyarki shaheedah.”
Ran mommah ne ya ‘baci har ta gagara ‘ko’karta furta ko kalma d’aya ce ga hameedah
yarinya ‘yar cikinta da take tsaye take mata fitsara. Suma duka sauran ba wanda bai
furta albarkacin bakinsa ba sannan suka juya suka tafi suna dariya da shewa burinsu
ya cika sun ‘batawa mommah baiwar Allah zuciya. Tsahon lokaci tana zaune a wajen ta
kasa mi’kewa tufka take a ranta kawai da warwara tabbas idan ba’a yi wasa ta bari a
kayi aurennan zasu ci galaba a kanta za kuma suyi duk abinda suka ga dama hawan
jini suke neman cusa mata da ciwon zuciya,ita bata ga abinda tayi musu a zahirance
da bad’inance kawai dai ‘kiyayya ce suke mata su kansu da basu san asalinta ba
balle tushenta. Ya zama dole tayiwa tufkar hanci lefe dai ba zata je ta gani ba
kuma Imran zai zo ya sameta zata nuna masa ita d’in nan dai itace wacce ta haifeshi
ta d’au cikinsa wata tara ta kuma shayar dashi nononta na tsawon watanni sha
takwas.
Tsawon lokaci mommah na zaune a parlournta ranta a matu’kar ‘bace ta gaji ta gaji
da tozartawa da wulakancin dangin miji, mafita kawai take nema tun daga
parlournnata tana jiyo su tana jiyo ba’ka’ken maganganu da suke jefo mata masu kama
da gugar zana hakan ya ‘kara hassala zuciyarta taji kuma zata iya komai don
‘kwatowa kanta ‘yancinta ciki kuwa har da samowa Imran aure ko da a cikin d’iyoyin
friends d’inta zata nuna musu tana da iko da d’anta kuma ba wata shegiya da zata yi
mata tin’kaho da d’anta alhali sanda tayi na’kudarsa ko wacce cikinsu tana can
shanye da baki tana barci.lokaci yayi da zata farka daga barcin da take ta amshe
matsayinta na uwar d’a mai cikakken iko akansa fiye da kowa a duniya.
“Please mommah na mai ya faru ne naga fuskarki ba walwala? Kuma su anty fannah
sunce kije kiga lefe kin ‘ki why mommah?” Kallonsa tayi kallon cikin ido kallone da
tun suna yara suka san tana yi musu idan sunyi mata babban laifi. Da sauri ya
rusinar da idonsa baya jurewa wannan kallon baya son sa yana razana shi ya kuma san
duk sa’in da mommah tayi shi ranta ya kai ‘kololuwa a ‘baci “ please mommah am
sorry duk da ban san laifina ba” “ sorry for what Imran? You are sorry because ka
wula’kanta ni ka nunawa duniya bani da amfani a wajenka ka nunawa duniya dani da
babu ni you can make decisions about anything aurenka Imran ace sai dai ace nazo
naga lefe? Ana yar min da magana baka neman albarkata baka damu da farincikina ba
ko da yaushe sai ‘bacin raina nagode kaje ka yi aurenka kaje mutanen da kake
tunanin zasu baka farin ciki su baka fiye da wanda ni zan baka Allah ya sanya
albarka a aurennaka but put this in your mind bani ba ‘yan uwana a bikinka ba zamu
zauna muga ‘baci rai ba.” Daga haka ta mi’ke ta shige d’aki jikin Imran ne yayi
sanyi ji yake kamar yace ya fasa baya son ‘bacin ran mahifiyarsa bai san me yasa
zuciyarsa ta kasa ha’kura da shaheedah ba, tsawon lokaci yana zaune kafin shatu ta
fito tana ‘yar wa’karta ta “uwa tana da girma mahaifiya tai mini komai” da sauri ya
kalleta gani yake kamar da shi take da shi d’in kuwa shatu take amma ya kasa
ta’buka komai yana juya kalaman wa’kar shatu a zuciyarsa.
Ko da ta fita bata zame ko ina ba sai wajen mai gadi, da murmushi y tareta don yana
son shatu musamman yarda take girmamashi ga kyauta akai akai “uwata ta kaina ya aka
yi?” Ya fad’a yana mata murumushi shatu tayi ‘kasa da muryarta “Baba taimako zaka
yi mi please amma bana son kowa ya sani” ya girgiza kai “ shatu danger yau kuma wa
ya takaloki?” Dariya tayi kafin murya can ‘kasa tace “wasu ‘kadangarun bariki zanyi
magani ga dubu biyu ‘kai’kayi zaka siyo min don Allah” Baba ya ware ido “Aa fa
shatu’kai’kayi kuma mai zaki yi dashi?” Ta had’e rai idan ba zaka taimakeni ba
shikkenan bara na tafi” ganin tayi fushi yasa yace “zo uwata zan taimakeki ai ba
zan’ki mai taimakona ba” ta mi’ka masa kud’in tana dariya.
FREE📚
08033748387
-16
ELEGANT ONLINE WRITERS.....
Baba murmushi ya saki “ko waye ya shiga gonar uwata? Ko ma dai waye ya jawowa kansa
yau” Baba mai gadi ya furta a hankali yana jinjina girman al’amarin shatun.
Tun yamma ta dinga zagaye gidan har ta tabbatar da windown ko wane d’aki sannan
hankalinta ya kwanta taje ta ‘boye ‘kai’kayinta a ma’ajiyar da ta tabbatar babu mai
ganinsa,sannan ta cigaba da harkokinta tamkar babu komai a zuciyarta.
Tana general kitchen ita da masu aikin gidan amaryar Imran ta shigo sai wani iyayi
take da rawar ‘kafa.shatu ta zabgawa harara kafin ta bud’e fridge tana duban masu
aiki “Imran yace kuyi masa abinci ne?” Ta tambayesu cikin kallon raini. Saratu ta
girgiza kai “ai dama bamu muke masa abinci ba daniel ne kuma tun wancan satin ma ya
dakatar da daniel ko ruwan tea zai sha naga a kitchen d’in mommah yake dafawa da
kansa.” Kallon one by one tayi musu tana yatsine fuska “Ba dole ba,ba dole ya daina
cin abincin gidannan ba gida duk an tara gayyar ‘kazamai dama zuwa nayi inyi
warning d’inku kada wacce ta sake yi masa abinci ni da kaina zan dinga yiwa mijina
abinci bana son ya dinga cin na kowani ‘kazami.” Shatu tsayawa tayi tana kallonta
sai kuma ta tuntsire da dariya ta kalli saratu tace “saratu bani aron muciyarku
akwai abinda zan gwada da ita” ta fad’a tana yiwa shaheedah kallon sama da ‘kasa
ita bata ga abinda Imran ya gani a jikin wannan ba ‘kafafu kamar sillan kara.
Shaheedah ranta yayi ‘kololuwar ‘baci da sauri ta cafko shatu ta fara wanketa da
mari shatu ta daka tsalle ta rama sannan ta shiga ‘kar’kashinta ta tad’eta ta fad’i
hakan yasa shaheedah ‘kwalla ‘kara ina shatu bata saurara mata ba ta hau kanta ta
shiga lugude a ruwan cikinta. Masu aiki suna gefe sai dariya suke sun ‘ki rabawa
saratu a zuciyarta fad’i take dai-dai kenan shegiya mai girman kan tsiya. Ihun
shaheedah ne ya karad’e gidan hakan yasa duk mutanen gidan suka yiyo general
kitchen d’in ban da mommah da take wanka. Da sauri su kayi kan shatu suka fara
jibgarta tun tana ihu har muryarta ta dashe gefen bakinta da goshinta ya kumbura
suntum. Ihun shatu ne ya fito da momma daga toilet riga kawai ta zira ta fito a
guje dai-dai lokacin Imran ya dawo kenan shima ya juyo ihun yayi yo cikin gidan da
sauri yabi bayan mommah. Momma ta tarar dasu har a lokacin dukanta suke sun mata
jina-jina su saratu sai ihu suke suna fad’in zasu kasheta. Da sauri momma tayi
kukan kura ta ‘kwaceta bayan ta dubesu ranta a ‘bace tace “mai tayi muku? Mai tayi
muku zaku yi mata wannan hukuncin?””an daketa d’in ko zaki rama mata ne ita har ta
isa ta doki shaheedah ta kwana lafiya wacece ita a gidan?”muryar tsagera hameedah
ce mai wannan tsaurin idon tana fad’a tana yiwa mommahn wani banzan kallo. Imran
kansa sai da yayi mamaki Ammar kuwa da ya shigo yanzu yaji furucin hameedah akan
mahaifiyarsa bai san sanda ya waska mata mari ba. baki bud’e kowa yake kallonsa
babbarsu falmata tace “kana hauka ne Ammar ‘kanwar ubanka ka Mara?” Ita dinma wani
kallon banza yayi mata yace “‘kanwar ubana tafi uwata ne?nawa hameedan take ina ce
shakara biyu ta bani shekara nawa tawa uwar ta bata da zata gaya mata magana?” Yana
fad’in haka yaja hannun shatu da mommah suka fice daga kitchen d’in bayan yayiwa
Imran kallon banza,yana tsaye ana zagin mahaifiyarsa ya kasa d’aukan mataki.
A bakin gado ya zaunar da mommah idanunta kawai yana zubar da hawaye, hakan ya
‘kara tunzira zuciyarsa ya mi’ke a zuciye zai fita mommah tayi saurin ri’ke
hannunsa tana girgiza kai tace “kada kaje Ammar hakan ma da kayi nagode maka ko
bakomai yau na san na haihu ka ‘kwatar min ‘yancina Allah yayi maka albarka d’auki
shatu ka kaita clinic ayi mata dressing ciwukannan.” Kallonsa ya mayar kan shatun
dai-dai lokacin da Imran ya turo ‘kofar ya shigo, murya can ‘kasa yayi sallama,
Ammar jan hannun shatu kawai yayi suka fita sam baya son ma ganin d’an uwannasa
gani yake kamar an canja musu shi Imran mai zuciya Imran mai tsananin son mommah
mai gudun ‘bacin ranta, yau shine ya zama haka a gabansa ake cin mutuncin uwarsa ya
kasa magana ya kasa kata’bus.Yana kallo suka fice ya bisu da kallo da ajiyar
zuciya, sannan ya samu gefen mommah ya zauna, kansa ya d’ora a kafad’arsa wasu
‘kwalla da bai san na menene ba suna ‘ko’karin zubo masa, ya kama hannun mommah
murya can ‘kasa furucin “Am sorry mommah” ya fito daga bakinsa, bata kalleshi ba
illa d’auke kai da tayi “kiyi ha’kuri ita ma yarinyar bata kyauta ba na tambayi
masu aiki sun gaya min duk yarda aka yi ita ta kwatantata da muciya saboda raini
ita kuma tayi saurin hannu ta mareta bata san wannan yarinyar ba ‘kyaleta za tayi
ba, ko ta’kyaleta a lokacin sai ta nemo abinda zata rama gaba kad’an please momma
kiyi ha’kuri amma kiyi mata fad’a” wani kallo mommah tayi masa sannan ta zare
hannunta “wacece yarinyar sunanta ne baka sani ba ko kuwa canja mata suna kayi
Imran anya kuwa jininka ce fa ita,duk duniya ku ya kamata ku nuna mata gata tunda
bata da wasu sha’ki’kan y’an uwa kazo kana ce min wani bata kyauta ba, rashin
kyautawar mai tayi? ‘Dirka-d’irkan mata su zauna suyi mata jina-jina sannan ace
wani bata kyauta ba to ba ha’kura nayi ba wallahi wannan karan sunyi da y’ar halak
ni kad’ai kuma Na san abinda zan musu tashi ka bani wuri mai kayan haushi kawai ka
zo ka cika ni da wani zancen banza da wofi zanyi maganinku ne gaba d’aya daga kai
har dangin ubannaka sai na shayar daku mamaki.” Imran zuba mata ido kawai yayi ya
ma kasa magana sam ba ya son hayaniya d’abi’ar dahda tsaf ya d’auko shi yasa yaji
har kansa ya fara ciwo. Jan pillow yayi kawai ya kwanta a gadon mommahn ya ri’ke
kansa da yake d’an sara masa.
Mommah ta dubeshi kawai tayi tsaki ta mi’ke ta bar masa bedroom d’in tana cigaba da
‘kananan maganganunta.
Koda dahda ya dawo duk da girkinta ne ranar ko ‘keyarta bai gani ba, tana part
d’inta ta tasa shatu a gaba tana lalla’bata ta sha peppe soup ko kad’an ne kafin
tayi barci. Amma shatu fir ta’ki yau zuciyarta a hassale take da ‘bacin rai sun
riga sun kai zuciyarta ‘kololuwa a ‘bacin rai duk ‘ko’karin mommah da Ammar haka
suka gaji suka ‘kyaleta suka zuba mata ido sai ajiyar zuciya take saukewa tana hura
hanci.
Gefe d’aya kuwa amaryar dahda zainab ta saka shi a gaba tana gaya masa ‘karya da
gaskiya a gaban y’an uwansa ta tattara lefin gaba d’aya ta d’orashi kan baiwar
Allah mommah, Dahda kawai jinsu yake yana girgiza kai ya san abinda matarsa zata yi
ya san wanda kuma ko da kuskure ba zata aikata ba.Da ya gaji da ji mi’kewa yayi ya
shige part d’insa ransa a ‘bace shi yasa ko da wasa baya son danginsa su
ziyarceshi. Sai da yayi wanka sannan ya fara jera kiran mommah a waya amma ta’ki
picking,gaba d’aya jinsa yake kamar maraya ta riga ta’bata shi ta sangarta shi baya
iya ta’buka komai ba tare da taimakonta shi wannan auren matsala babba Hajja ta
gangamo masa sam a tsarinsa bashi da niyyar ‘kara aure. Ganin ta’ki picking calls
d’insa hakan ya sashi mi’kewa ya dangana ga part d’inta.
A zaune ya sameta kan sallaya ta d’ora kanta a saman gado tana jan carbi fuskarta
da alamar ‘bacin rai sosai. A hankali ya taka wajenta ya zauna a gefen gadon,
motsinsa ne ya sata saurin d’ago da kai su kayi four eyes lallausan murmushi ya
sakar mata yana dafa kanta yace “Haba Dija na me ya faru? Yau ko ‘yar sannu da
zuwan ma babu.” Still fuskarta a d’aure ta mi’ke ta fara nad’e sallay sai kuma
hawaye sharr ya biyo fuskarta ta dur’kushe a gabansa ta kife fuskarta a cinyarsa ta
saki kuka, kuka mai cin rai da tunda yake bai ta’ba ganin dijansa nayi ba.
hankalinsa ne ya tashi da sauri ya dafa kanta sannan ya mi’ke tsaye ya d’agata
rungume ta yayi sosai yana fad’in “yi shiru ki gaya min menene me suka yi miki?” A
hankali yake fad’a mata cikin cool voice. Dijah kukan take sosai kafin ya fara
wiping tears d’inta a cikin wani salo na matu’kar soyayya da son cooling zuciyarta.
Shi kad’ai yasan yarda kukan dijan yake d’aga masa hankali “Don Allah Dija kiyi
shiru ki fad’a min wai menene? Bana son kanki yayi ciwo please.” Ganin damuwa
‘karara a fuskarsa ya sa ta tsagaita kukan nata ta fara bashi labari, tana gamawa
ta d’ora da fad’in “don haka dahda na gaji a wannan karan dole ne a san abin yi ko
Imran ya fasa auren can da aka ‘kir’kireshi don a wula’kanta ni ko kuma ya had’a da
za’bina ko kuma wallahi na bar gidannan don ba zan zauna ba’kin ciki ya kamani ba
zuciya ta ta buga Allah ne kad’ai yarda nake jin ciwo a zuciyata kullum matsalata
dangin miji sun saka kayi aure ka auri ‘yar uwarsu ban ce komai ba ko bakomai hajja
tana da iko da kai to nima a barni nayi iko da nawa d’an idan kuma ba haka ba na
bar maka gidan ka zauna da duk wacce suke so ka aura,amma dole wannan karan nima
Imran yabi umarnina a matsayina na uwarsa da ta kawosho duniya.” ‘Kuri manga yayi
mata da ido ganin yarda take masifa wai dijan sa ce haka dijan sa mai ha’kuri mai
sanyin hali ita masifar danginsa yasa ta juye ta koma masa mai fad’a, sam bai ga
lefinta ba ya tabbata an kaita ma’kura dama ance shi mai ha’kuri bai iya fushi ba a
duk sanda aka ‘kureshi dole yayi mata abinda take so ko don ya faranta mata
zuciyarta ta sauka daga fushin da take idan ba haka ba yana tsoron yana tsoron
ranar da zata fara mayar da martani ga hajja, ya san tabbas abin ba zai yi kyau
ba.Hannunta ya kama yana matsawa a hankali,murya ‘kasa-‘kasa yace “It’s enough ‘yan
mata na dijan manga gaya min mai kike so ayi?” Murmushi ta saki zuciyarta na rage
zafin da take mata, ta haka manga yake samo lagonta a duk sanda tayi fushi shi yasa
basa dogon fad’a suke shiryawa. Ta gyara zamanta a jikinsa tana masa kallon cikin
ido “in dai manga na yana son ganin farin cikina to ya amince da ‘kudirina ta haka
zaka’kwato min ‘yancina a wajen ‘yan uwanka so nake ka aurawa Imran shatu ya
had’asu su biyu ta haka kawai zan nuna musu power ta nima na dasa musu ba’kin cikin
da suka dasa min ba dai shatu bace ba sa so to ita zata zama kishiyar d’iyar tasu
‘yar so.” Kallonta yake cikin nazarin anya tana cikin sense d’inta idan ban da haka
wacce shatun? Wannan ‘yar ‘kwailar bayan haka ta san ko sama da ‘kasa zata had’e
Imran ba zai kar’bi shatu matsayin mata ba amma bari ya tambayeta wacce shatun take
nufi? “Wai wacce shatun kike nufi dijah?” Ya fad’a yana sake ‘kure ta da kallo,
dariya ta saki tace”au muna da wata shatun ne bayan ta gidan nan shatu na nake nufi
shatu da suka yiwa duka saboda ta ta’ba d’iyar gold to ita nake nufi” girgiza kai
manga yayi shima yana murmushin yace “amma dai wasa kike ko? Idan ban da haka
wannan yarinyar da bata wuce 14 ba za’a yiwa aure banda haka ma kin san halin
d’anki ba yarda za’ayi ya amince da wannan batun.” Momma ta marairaice fuska tana
kwanciya a kafad’arsa tace “please dahda don’t say No kai kad’ai ne last hope d’ina
kaga dai da kayi aure ban ce maka komai nayi ha’kuri duk da zuciyata na hurting
sosai kullum a haka nake kwana amma na san dole ne kabi umarnin hajja indai kana
son ganin daidai please ka cika min burina don Allah ka amince.” Tausayinta ne ya
kamashi ya fara shafa bayanta amma shifa yana tsoron lamarinnan ya san halin Imran
da ba’kar zuciya ban da haka ma yarinyar is too young “
Dijah ba fa wai na’ki bane ‘kan’kantar shatu nake dubawa bana son ayi abin da za’a
tauye mata ha’k’ki matsayinta na marainiya kada mu cuceta ta yama zata iya kishi da
shaheedah apart from that ma ta ya kike zaton Imran zai amince da auran shatu?”
Murya can ‘kasa tace “shi yasa bana so ka fad’a masa ya zama sirri tsakanina da kai
so nake sai dai suji an d’aura da shatu kawai ko bakomai nima power ta ta uwa ta
fito Ba kuma tarewa za tayi ba har sai ta gama school, shi kuma Imran ka barni
dashi na san ta yarda zan ‘bullo masa shekaru kuwa ba abin ji bane duk da ba tarewa
za tayi ba mutanen da ma a shekarunta tuni sun jima a d’aki. Ni dai abinda nake so
da kai kawai ya sirri tsakanina da kai nima anan ko ‘yan uwana ba zan gayawa ba
insha Allah sai dai suji” d’aga mata kai yayi “zan cika miki burinki dija na ko don
ki cigaba da kasance min sanyin idaniya ta yanzu tashi muje ki bani abinci I have
gists for you” ya fad’a yana kashe mata ido d’aya. Shi yasa kullum manga yake narka
mata da zuciyarta take kuma kishinsa don ya san salo salo na kama zuciyar mace.
To fa masu karatu ya zata kaya ne kun amince ayi auren ko a barshi tabbas dai akwai
rigima kwantacciya.😂Imran mijin shatu ko ya zata kasance? Ku biyo ni next month
insha Allah na tafi hutu typing wahala
[8/30, 9:26 PM] +234 706 428 6235: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-17
Cikin daren kamar an mintsineta ta mi’ke duk da jikinta da yake ciwo hakan ba zai
hanata aiwatar da ‘kudirinta ba a karo na barkatai ta sake kaiwa dogon mudubinnata
ziyara,shatu ta sake ‘karewa ciwuwwukan da suka ji mata kallo cikin matsanancin
‘bacin rai ta girgiza kai muryarta a dashe tace wallahi ba zaku kwana lafiya ba
ayau yarda kuka saka ni ‘bacin rai sai na hanawa idanunku barci. Ta isa inda ta
ajiye ‘kullin ‘kai’kayinta tana murmushi “yau akwai rawar asosa casss a gidannan”
sai kuma ta tuntsire da dariya murya a ciki tace “mu zuba ni daku shege ka fasa” ko
takalmi bata saka ba don kada mommah taji takunta ta fice daga part d’in mommahn
cikin sand’a.
Duk windows d’in bedrooms d’insu ta dinga zugewa a hankali tana hura musu sai kuma
aka ci sa’a duka gadajennasu a jikin windows suke sai da ta taka abu sannan
tsawonta ya kai.tana gama hura musu tayi saurin juyawa ta shige general parlour
karaf suka ci karo da Imran zai shiga sashensa bayan ya gama aiyukan da zaiyi a
system d’insa a parlourn,da sauri ya kai dubansa kanta har zaiyi magana sai kuma ya
ta’be baki ya shige part d’insu, shi yanzu tsoronta yake ji sosai ba ya son ya
fad’a tarkonta. Shatu tayi murmushi kawai ta shige part d’in mommah tana jira a
fara rawar asosa.
Tana zaune kuwa a gefen gadonta ta fara jiyo iface-iface a general parlour ihu
sosai Ta jiyo hakan ya sata fitowa daga d’akinta sai taga mommah ma da dahda sun
fito daga d’akin mommah. Momma da sauri tace “koma ciki shatu ke da baki da lafiya
bari muje muga menene” bata so hakan ba amma hakan ta zauna kan kujera.bayan dahda
ya kalleta yayi mata alamar t zauna.
A parlour suka samesu gaba d’aya sai ihu suke har da masu ludaya da
Cokula suna sosawa. Shaheeda kuwa daga ita sai guntuwar vest sai ihu take tana
kiran Imran ya taimaka mata shi kuwa yana tsaye yana mamakin mai ya samesu tabbas
ya tabbata shatu ce tayi musu ramuwar gayya saura ‘kiris ya saki dariya a karo na
farko da lamarin yarinyar ya daina bashi haushi sai dariya, yarinya sai shed’ananci
kamar zuriar shaid’anu.Dahda da mommah fad’i suke “subhanallahi mai ya faru?”
‘Kannen dahda sai cewa suke ya taimaka musu jikinsu kuwa yayi rud’u-rud’u salati
dahda yasa yace suje su suturce jikinsu su tafi asibiti.amma ina lamarin ya girmama
har da masu birgima a ‘kasa. Ammar ne yace “Dahda anya ba aljannnun gidan nan bane
suma suka shafesu kmar yarda suka yiwa hajja” dahda ya girgiza kai ba mamaki ammar
yanzu dai kira doctornmu ya dubasu” shi dai Imran yana daga gefe sai murmushi yake
yana hango kuma shatu data la’be bayan ‘kofa tana zabga dariya kamar yace ga babbar
aljannahr can sai dai yaja bakinsa yayi shiru kada ya jawowa kansa daga ruwan
hammata ta bashi ruwan tsarki.
Kafin doctor yazo haukane kawai ba suyi ba sai da Ammar ya shigo ya sanar dasu
shigowar doctor sannan Imran ya kalli shaheeda ransa a ‘bace yace “Go and cover
your body ko kunya baki ji” wani kallo ta watsa masa kafin tayi magana doctor ya
shigo da sauri Imran ya dafa kansa ya jata ya turata d’aki yana tsaki. Ko da ta
shiga d’aki hijab kawai ta zira ta sake fitowa a guje. Doctor ya gama dubasu sannan
ya fito da allura ya fara yi musu don dama dahda yayi masa bayanin ciwon. Sai kusan
‘karfe 4:00 na dare sannan abin ya lafa musu amma fa sunji jiki duk jiknnan yayi
luhu-luhu balle idonsu.basu koma d’akunansu ba don suna tunanin tabbas aljannun ne
tun da a d’akin da hajja take sauka suka sauka yau kam sun gasgata zancen hajja.
Jin shigowar su mommah yasa shatu shiga d’aki da sauri tana tuntsira dariya. Amma
mamakinta d’aya me yasa Imran bai tona mata asiri ba karo na biyu kenan yana kamata
da irin wannan.shi kansa Imran tunda ya shiga d’aki yake smilling shi kad’ai ya
lura yarinyar nan comedian ce ta bugawa a news.
Da safe ma basu koma d’akin ba a sashen amarya suka koma zama suna sake la’antar
mommah don a cewarsu aljannu take turo musu ai kuwa indai sune su zuba su da ita
gida dai baza su barshi ba sai sun kai kwanakin da suka ‘kayyadewa kansu tunda a
goben zasu tafi abuja kai lefe. Hameedah tana sake girgiza ‘kafa ranta a matu’kar
‘bace tace “wallahi wannan matar muka ‘kyaleta nan gaba raba mu za tayi da yaya
manga gaba d’aya dole mu tashi tsaye a kanta mu har a gaya mana malamai mu da
Muku jinin barebari.” Falmata ma cewa tayi”wallahi kuwa naga alama kuma lefe tayiwa
kanta tunda hajja tace mu kai kada ma mu nemi danginta wallahi kaiwa zamuyi ke kuma
shaheedah sai kin dage sosai duk abinda muka kawo miki kada kiyi wasa dashi munyi
al’kawarin sai mun dasa mata ninkin ‘bacin ran da ta sakawa manga sai mu zuba mu
gani tana ji tana gani Imran sai dai ta hange shi daga ness” gaba d’aya suka saka
shewa har da amarya zainab. Fanna na gyara zama tace mai yafi wannan takaici ace
d’anka yana auren ‘yar kishiyarka kuma zainab ke kin samu d’a daga sama kamar yarda
uwarta ta samu manga daga sama suke juya mana shi son ransu.” Dariya suka ‘kara yi.
Ko da ta gama shirin school tana fitowa general parlour ta gansu murmushi ta saki
ta fara wa’kar ado gwanja ta casss. A harzu’ke suke kallonta,Hameedah ta mi’ke da
sauri tana jifanta da wani irin kallo “ke don uwraki da wa kike?” Shatu rausayar da
kai tayi gefe kafin tace “kawai don ina wa’kata sai ki zageni” fitowar Imran da
Ammar kenan sunyi shirin fita su ka ji hameedah tana wallahi sai na sake jibgarki
kamar yarda nayi miki jiya shegiya mai idon aljannu.” Imran waro ido yayi yana
kallon hameedah mamaki fal ransa lalle bata san sharrin yarinyar nan ba bata san
itace gayyar aljannun da suke wajigasu ba, har shatu ta karkace zata yi rashin
kunya Ammar ransa a ‘bace ya jata “wuce ki tafi school tun d’azu driver na jiranki
kin tsaya jan magana.” Baki ta zun’buro irin na shagwa’ba “Yaya Ammar uwata fa ta
zaga.” Harara ya zuba mata “kin wuce ko sai na mangareki tayi ta zaginki ma yana
tsiro ne? Oya maza-maza wuce school kafin na sameki a wajen” sum sum ta wuce har
taje ‘kofa ta juyo da ‘karfi tace “an fad’a d’in a sosa cass a sosa iya da razor.”
Imran bai san sanda murmushi ya ku’buce masa Ammar kuwa darawa yayi sosai yace “kai
shatu danger” hameedah kuwa ‘kwafa tayi tana zabgawa Ammar harara.
Kashegari kuwa suka isa abuja dangin baban shaheeda suka kai lefe ba tare da dangin
mommah ko d’aya ba duk da kuwa suna cikin abujar. Haka suka dawo da sha tara ta
arziki duk da suma ba lefen wasa suka kai ba lefene na gaske na gani a fad’a na
kuma d’orawa a instagram,a yayata a duniya. Biki kuwa aka saka shi sati uku cif don
suma dangin uban shaheedahn a shirye suke tsaf kuma masu farcen susa ne tabbas kuwa
za’ayi biki na kece raini. Bayan sun dawo kano da kwana d’aya suka wuce maiduguri
hannayensa dam’ke da sha tara ta arziki. Mommah ba tace musu Komai ba duk da ta
tambayi Hajiya mama kuma ta tabbatar mata ba a gaya musu kai lefen ta basu ha’kuri.
Hajiya mama ta girgiza kai a cikin wayar tace”Lala lala dijah ke zan bawa ha’kuri
kiyi ha’kuri da jarrabawar da Allah yayi miki ta fitinannun dangi miji kina zaune
ubangiji zaiyi miki sakayya suma fa mata ne kuma sun haifi mata ki zuba musu ido
yanzu ubangiji ai tun a duniya yake sakayya ba kayi ba ma anyi maka ina ga kayi
kiyi ha’kuri kullum shine abinda zan iya ce miki.” Hawaye ya zubowa mommah sai dai
ba ta nunawa hajiya mama kuka take ba tayi godiya ta kashe wayar a zuciyarta tace
“akwai ranar ‘kin dillaci ranar da zata cusa musu nasu ‘bacin ran dole ne su girbi
abinda suka shuka d’a dai nata ne kuma ba zata bari su juya shi kamar yarda suke
muradi ba.
*****************
A hankali awanni suka yi ta shigewa suna zama kwanaki daga kwanaki kuwa,har
satittikan biki suka zo gidan a hargitse yake kowa sai shiri yake ana ji da lamarin
bikin to ba dole ba ta kowane side jikan farko kuma d’an gaban goshi ake yiwa
Aure,tun ana saura sati biki dahda yasa shaheedah dole ta koma gidan babanta duk da
ba haka suka so ba uwarta taso ta tsaya ta cigaba da banka mata mallakin mallaka
sai dai dole ta tafi. Hajja ma ana saura satin tazo ta tare a part d’in dahda daga
gefe a babban parlournsa akwai wani bedroom and toilet anan ta baje danginta kuma
suna d’aki mai Aljannu.
Mutanen katagum ma sun hallara ciki kuwa har da Dada tsohuwa mai ran ‘karfe. Tuni
mommah ta fara gyara d’iyarta tsaf fatarta ta goge a spa haka nan an yi mata saloon
gashin nnan an jawo shi tsahonsa har da na Mamaki.
Suna dawowa daga spa a gajiye suka tarar Hajiya mama tazo ita ma da ‘yan uwanta na
yola ga Hafsa da Nahna da sauri shatu ta rungume uncle Hisham shi kuwa duk da
nauyin da tayi masa haka ya shiga wulwulata yana fad’in a cafe a cafe ‘yar gidan
mommah mai mommah ke baki ne kika yi wani fresh har glowing kike?” Kayan dad’i” ta
furta tana murmushi har hushiryarta ta fito. Still Ammar yayi yana kallonta har
bakinsa ya gaza shiru yace “mommah ‘karin gashi kika kaita aka yi mata da wankin
fata?” Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya ba Hafsa tace “Ammar ko dai kana ciki
ne a d’aura gobe da kai kawai.” Girgiza kai yayi “Ina ni ina rigimar shatu ni
‘kabilar ibira ma zan aura sun fi iya kula da miji” shatu ma harara ta zabga masa
Allah ya kiyaye ma in aureka kayi fari da yawa ni nafi son irin Yaya Imran wanda
baya magana sosai kai kuwa surutu kamar parrot.” Dariya sosai parlorn duka suka
ganin Imran yana tahowa yana ware ido alamar yaji zancenta sarai. Tamke fuskarsa
yayi ya zuba kallonsa akan shatu da tayi saurin jan gyale ta rufe fuskarta alamar
kunya tsaki “kada ma ki saka rai da samun irina ke ai irinki Ammar d’in ne ya dace
dake sai kuje ku haifi parrots d’in”Dada tsohuwa ta ta’be baki “Yo Allah na tuba
kada dai inga mutum yazo yana ‘yar murya kana ganin yarinya zankad’aziyya wanke
hannu ka ta’ba da mai matarka ta ka tafi ta to ku ku zama shaida ko nan gaba kada
Imran yazo yace a bashi balarabiyar nan.” Tsaki yaja yana mi’kewa “MAI ZAN YI DA
ITA? Ni kuwa God forbid gayyar ‘kazanta da surutun tsiya Ina da mata ta ‘yar gayu
ta bugawa a jarida.” Ran shatu ne ya ‘baci tun da take bata ta’ba jin haushin
kalamansa ba sai yau hawaye ya fara bin fuskarta.
[8/30, 9:26 PM] +234 706 428 6235: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
FREE📚
08033748387
-18
Sosai take hawayen saboda kalaman Imran sun ‘bata mata rai. Momma ta jata jikinta
da sauri tana jifan Imran d’in da harara “fice min daga nan tunda burinka ya cika
ka saka shatu kuka yo itama su’butar baki Tayi idan banda haka mai za tayi da kai a
haife ka haifeta tunda ka ninka shekarunta.” Ficewa yayi ba tare da yace komai ba
Allah ya tsari gatari da saran shuka” ya raya a zuciyarsa.
Ana gobe kamu masu tafiya abuja suka dinga dandazon tafiya dangin mommah dai ba
suje ba a cewarsu bikin namiji suke zo ba ruwansu da dangin mace sun san ma kun
sunje wula’kanci zasu sha,gida ya d’ad’e ba kowa daga mommah sai danginta suke Ta
tsara yarda bikinsu zai kasance.Juma’a ne d’aurin aure don haka ranar asabar za
suyi dinner lahadi suyi bud’ar kai ango ma alhamis d’in zasu wuce da abokansa da
suka zo daga wurare da dama wasu ma ba ‘yan ‘kasar nan bane.
Don haka yau part d’insu na samarin gidan a cike yake sosai don ma babban parlour
ne sai bedrooms guda hud’u a ciki don gidan dahda ba dai girma ba gari guda ne.
Tana zaune a gefen dada tsohuwa tana shan dariyar labarin da dadan take bata na
Imran da yake yaro yana tsoron saniya ita kuwa sai dariya take su antynta nahna
suna zaune suna cire mata jan lallen da akayi mata na salatip ba ‘karamin kyau yayi
ba ya haskaka kyakykyawar ‘kafarta ta.tana mi’kewa mommah Ta shigo parlourn tana
dubanta daga ita sai wata riga da tsayinta yaje mata gwiwa sai skinny black pant
ajikinta gashinta kuwa an tufke mata shi guda biyu ya sauka har fin gefen
Kafad’unta duk da ba kwalliya tayi ba tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu”maza
jeki ki kira wo min yayanku Imran” mommah tace tana zama a kujera had’e da ri’ke
kai alamar a gajiye take sosai. Ba tare da jin komai ba shatu ta fice tana jin dada
na ‘kwala mata kira amma tayi shiru dada tayi tsaki “kaji y’ar banzan yarinya a
haka zata fita kai ba kallabi ke kuma dijah kina kallonta ta fara fa ‘kirgar dangi
ita ko ta ido bata dashi ne? ‘yar nan” mommah murmushi kawai tayi “To dada nawa
shatun take?” Dada ta girgiza kai “nawa take? Wannan d’irkekiyar budurwar ake kira
nawa take yarinya ta fara ‘kirgamu yanzu haka ma ta fara al’ada” mommah ta girgiza
kai “Bata fara ba wallahi dada ai da ta fara nima ba zan bari ta dinga zama haka ba
na san shari’a ta hau kanta” “zancen banza shari’a kuma ta yaushe tunda ga abubuwa
nan sun fara bayyana” ita dai mommah shiru tayi tana jin dada na ta masifa.
Ko da ya koma zancen dai Ali ya ya tayar masa tsaki yayi “ku dai Allah ya shiryeku
duk ‘yan matan garinnan ku rasa ta kulawa sai wannan ‘kwailar” Abdul tsaki yayi “Ai
wallahi Imran kayi ba’kar dabara ya za’a yi da wannan a gidanmu inje neman auran
wata ba zaka zauna ka jira wannan d’in ka kiwatata kaje kana auren wata
‘kemasashshiya zubin turawa ga zubin larabawa haba Alhaji wallahi ka cuci kanka.”
Imran ya masa wani duban banza”God forbid Allah ya kiyaye kai ka sanni ka san waye
ni kuma ka san burina na auren matured wacce ta san ciwon kanta kuma mace mai
tsafta ba kuma na san mace mai tsananin kyau saboda bana son ko wani rubbish ya
dinga kai idonsa kan matata so wannan bata cikin layin matan da nake so mace mai
kyau ai hatsarice.” Gaba d’aya ta’be baki suka yi suna kallonsa su basu ta’ba jin
mutum ma mai irin ra’ayinsa ba.Ali yace “Allah ya raba mu da auren mummuna mun fi
son kyakykyawa ta shiga taro.”Imran tsaki yayi “Allah ya kyauta sai ku shirya
kar’bar ciwon hawan jini don ba abinda ‘kananan yara zasu saka muku idan ba su saka
muku hawan jini ba.”
Ranar Alhamis da daddare su hajja suka dawo saboda ranar juma’a ne d’aurin aure
kuma sun fi son su kar’bi amarya da kansu. Ko kallon arziki ba wanda yayiwa su
mommah da suke zaune a general parlour suna tayi musu sannu da zuwa, a ciki suke
amsawa Hajja zube a parlour ana Ta d’aga kai ‘kafa d’aya kan d’aya tana ‘karewa
Hajiya mama kallon banza ita dole sai dai Ta nuna gidan d’anta ne. Hajiya mama da
yake bata iya fad’a ba ta mi’ke tana kallon mommah da dada tace “Dada muje daga
ciki ku barsu su huta.”Dada ta girgiza kai “oh oh babu inda zani anan zan zauna ina
kallon mai shige da fice to ina dalili zaki turani can ciki ban san mai duniya take
ciki ba wanda yaga ba zai iya zama ba shi dai ya tafi amma dada kam zama
daram”Hajiya mama ba tayi magana ba tayi shigewarta d’aki.dama su nahna basa nan
sun tafi kar’bar d’inki tana ji hameedah na shewa tana cewa “Oh Hajja aure dai ya
d’auru Allah yaso ba’a ruguza shi da surkullen fulani ba” Hajja ta masa “Da wallahi
kuwa” Mommah tana jinsu ta shige kitchen ranta a ‘bace tasa masu aiki suka kai musu
abinci daga haka Ta shige part d’inta wajen Hajiya mama tana dialling call d’in
dahda.
Da daddare kuwa ta sake jaddadawa dahda burinta Na son d’aura auren gaba d’aya a
gobe “ka d’aura a can abujan kawai dangin Ubanta ba matsala bane daga baya ta kaini
har garin nayi musu bayani duk da dai basu damu da ita ba da sun damu da ita ai da
sun biyo sahu.”Dahda yayi murmushi yana jan hannunta “Your wish is my command Dija
na I do as you said.” Murmushi tayi tana had’a goshinsu waje d’aya.
Dandazon mutanene suka halarci d’aurin auren a babban masallacin Na garin Abuja,
duk inda ka juya jama’a ce Imran fuskarsa d’auke da fara’a at last dai zai mallaki
burin ransa shaheedah da ya dad’e yana mafarki a matsayin matarsa matured mai
tsafta kuma ‘yar gayu kuma ‘yar ‘kwalisa kamar yarda yake son matarsa ta kasance.
Suna zaune shida abokansa suka ji an fara shelar za’a d’aura auren ayi shiri
jama’a. Ai kuwa cikin yardar Allah aka samu ba’kuncin shiru mai shela bayan mintuna
kad’an ya shela cewar an d’aura auren Imran da Haleemah shaheeda akan kud’in
miliyan d’aya lakadan ba ajalan ba Alhamdulillah Imran ya fad’a a zuciyarsa Finally
angon shaheedah inji abokansa sai kuma suka ji an sake d’aura auren Imran da Aysha
mujittafa....... gaba d’aya abokansa suka waro ido suna kallonsa shi d’in ma
kallonsu yake....
FREE📚
08033748387
-19
Ina mi’ka d’umbin godiyata ga masu karatun littafinnan nagode ‘kwarai da gaske da
soyayyar da kuka nuna min da littafin me zan yi da ita?burina dama saka nishad’i a
zuciyarku. Ina alfahari daku I Really appreciated wallahi, da zan iya da na mayar
dashi 2pages kamar yarda kuka bu’kata, to hakan ba zai yiwuba ina da scheduled da
yawa so am sorry kuyi ha’kuri dani a hakan har muje inda zamu. Nagode sosai.
**********************************
Aliyu ne ya dafa Imran yana dariya “Amma lallai guy d’in nan ka raina mana hankali
yanzu dama mutum biyu zaka aura baka gaya mana ba” Abdul ya girgiza kai yana
murmushi yace “wonderful ni bama wannan ba how comes kai da baka son hayaniya ka
auri mata biyu ina cika bakin da kake mana na cewa mace d’aya ta isheka?” Yana
jinsu duk suna surutunsu ya kasa furta komai zallar tunani da zuciyarsa ta tafi,sai
zufa yake tunani yake wacece ita wacece ma wata Aysha da aka d’aura masa aure bai
sani ba, tabbas ashe kuwa tayi shirin zama bazawara don sam bai ga dalilin da zai
sa ya amince da mace har biyu ba. Koma waye ya bawa dahda wannan gurguwar shawarar.
Tsawon lokaci zuciyarsa ta kasa hasasho masa shatu ce yarinyar gaba d’aya zuciyarsa
ma bata hasasho masa shatu ba tunani yake a cikin ‘ya’yan abokan dahda da suka
mayance masa cewa suna sonsa aka d’auki d’aya aka bashi. Bai cewa abokansa komai ba
duk da surutan da suke masa, burinsa yaga dahda ko Ammar amma ba d’aya da ya
gani,hakan yasa dole suka shiga motocinsu suka tafi masauki.Imran dai ya zama
tamkar mutum mutumi.
Amarya shaheedah kuwa a bakin yayyenta maza da suka dawo dga d’aurin aure ta samu
labari.shaheed da ya shigo a rud’e ne ya dafa ta murya can ‘kasa yace “How comes
shaheedah duk cika bakin da kike yi ba zaki zauna da kishiya ba sai gashi ko tarewa
ba kiyi ba angonki ya auri wata zai had’a ta dake.” Shaheedah da bata d’au zancen
serious ba ta zabga masa harara “God forbid don Allah shaheed ka daina wannan wasan
bana son sa as per as am alive ko kallon ‘yan mata ba zan bar habibi yayi ba balle
kishiya over my death body” shaheed murmushi yayi kafin khalil ‘kaninta yace “ai
kuwa kin makaro don kuwa mata biyu aka d’aurawa aure da habibinnaki ke da wata
Aysha.” Da sauri shaheedah ta mi’ke tana kallonsu “please don Allah kuce min wasa
kuke?what a nonsense?” Khalil da shaheed suka sake tabbatar mata haka nan sauran
mutane da suka je d’aurin aurenma suka tabbatar mata,dalilin da yasa ta yanke jiki
ta fad’i, tuni nmufashinta ya d’auke,hakan yasa da sauri aka rufu akanta ana
‘ko’karin ceto ranta.
‘Yan kano kuwa tuni labari ya riski zainab ta hanyar mutane masu sanar da ita
fad’uwar shaheedan da dalilin fad’uwarta ta.cikin tsananin mamaki take cewa “mata
biyu a haba dai ba kuji da kyau ba idan kuwa hakan ya tabbata tabbas duk wacce tayi
‘ko’karin zama kishiyar shaheedah tayi shirin riskar ba’kin cikin da zai zama
ajalinta wallahi.” Da sauri ta mi’ke ta nufi General parlour inda Hajja take.tun
kafin ta furta komai hajja ta tabbatar da ba lafiya ba don yanayinta ya nuna
‘karara. Da sauri Hajja ta mi’ke da niyyar ta jata su samu sirri don ganin dada a
zaune da itama ta kasa ta tsare, amma ina zainab tuni ta furta abin da ya ri’ke
mata ma’kogaro “Hajja da gaske ne? Da gaske ne Imran mata biyu aka aura masa da
wata wai Aysha wacece ita?” Gaba d’aya gurin zaro ido su kayi, musamman Hajja da
maganar tayi mata dirar mikiya, da sauri ta girgiza kai “wannan ba gaskiya bane ba
yarda za’ayi manga ya zartar da wannan hukuncin bai gaya min ba sharri ne da surutu
irin na d’an Adam” zainab ta girgiza kai “Hajja babu fa batun sharri a wannan
zancen it’s true naji a bakunan da ba zasu min ‘karya ba kuma sun halarci d’aurin
auren ga shaheedah canma ance ta sume daga kin zancen.” Hajja ta ja ta zauna ja’bar
a kujera “To wacece yarinyar aka ce miki idan kuwa zancennan ya tabbata tabbas
manga zai ga ‘bacin raina kuma Imran dole ya saketa koma wacece zancen banza zancen
wofi kenan, ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa.” Mommah dake zaune
murmushi kawai take zubawa ta tabbata yau gidannan akwai show idan har suka san
wacece amaryar.tana kallonsu suka shige d’aki bayan hameedah ta tunatar dasu zancen
a sirri ya kamata ayi shi.Mommah ta ta’be baki a zuciyarta tace “oho dai burina ya
gama cika.”
Kowa burinsa Dahda ya dawo yaji ya gaskiyar lamarin yake.ko su Hajiya Mama mommah
bata gayawaba ta ja bakinta tayi shiru tana jiran kowa yaji labarin kamar dirar
mikiya tunda ta lura har yanzu basu san da shatunta aka d’aura aure ba.
Shi kuwa Imran yana can asibiti ya tasa shaheedah gaba da kallo da take ta kuka
bayan farkowarta,ta kuma tabbatar da lamarin gaskiya ne.sai ga Imran ya ‘bige da
jinya madadin hotunan d’aurin aure da suka ci burin aiwatarwa,irin dai wanda ake
yayi a social media d’innan.
Kukan take sosai da har ya ‘karawa Imran zazzafan ciwon kai,ya kama kannasa ya
ri’ke tun yana rarrashin ta da yi mata rantsuwar ta kwantar da hankalinta koma
wacece idan ya tabbatar da auren sakinta zai yi kuma da gaske yake.amma ina
shaheeda bata ji shi ba,hakan yasa kawai ya kama hannunta yana murzawa alamar
rarrashi idanunsa a lumshe. Haushi ma lamarin ya bawa abokansa yanda take kuka
kamar a kanta aka fara kishiya.Tsawon lokaci sannan aka sallamesu bayan ta gama
shan drip.ana komawa gida Abbanta yace ta bari ta warware a kaita. Suna ke’bewa da
Imran tace yace kawai a kaita please Imran anty na nake son gani kawai ko zuciyata
tayi sanyi.” Tausayinta yasa Imran gayawa wata ‘kanwar babanta cewar a kaita kawai
ta ‘karasa warwarewa a gidanta.
Haka kuwa aka yi babu ‘bata lokaci aka tafi airport dama sun yi booking
jirgi.amarya dai ta tafi fuska ‘kozai-‘kozai fuska ko kwalliya babu duk da burin da
aka ci na budiri a wannan ranar.
Ana kaita ko ta kan mommah da danginta ba abi ba duk da tunasarwar da dangin ubanta
suke musu amma Hajja ‘kememe ta’ki yarda tace “ku shige da ita d’akinta mai aka yi
aka yi wata dijah balle danginta wa ya san surkullen da suka yiwa manga ya d’aura
masa aure da wata yarinyar.ku kaita gurin uwarta ni ina nan ina jiran shigowar
manga tunda ya’ki d’aga waya ta.”hakan yasa ba wanda ya sake bi ta kan uwar miji
duk da al’ada ta shar’anta a bata damarta a kai mata matar d’anta. Hakan sam bai
damu mommah ba tunda burinta ya cika.
Shi kuwa ango Imran yana cikin d’akinsa zuciyarsa sai suya ta keyi shi mamakinsa
d’aya dama ana yiwa namiji auren dole? Yana jiyo abokansa suna ta dariyar
shegantkarsu.
SHIGOWAR DAHDA**************
Yana dawowa ya tarar Hajja da jama’arta baje a parlourn,gefe d’aya ga Dada da tata
jama’ar,zancen dai ya san ake hakan yasa bai san lokacin da murmushi ya ku’buce
masa ba ya san sarai za’a rina,Dijah ta jawo masa rigima yau,da bai san yarda
zaiyi solving d’inta ba. ya dur’kusa ya gaida su Dada sannan ya ‘karasa gefen hajja
ya zauna, Da kyar take amsa gaisuwar da yake mata tana gama amsa gaisuwar ta d’ora
da “meye gaskiyar labarin da naji game da aure biyu da akace an d’aurawa
Imrana,wacece yarinyar da har ni ban isa kayi shawara dani ba?” Manga waigawa Yayi
yaga Dijah bata wajen don haka ya ciro wayarsa ya kira ta yana kallon hararar da
Hajja take masa ya cigaba da kiran Imran shima a waya,so yake su hallara duk ayi
komai a gabansu. Tsawon mintuna mommah ta shigo da su Hajiya mama, sai ga Imran
shima ya shigo jikinsa a sanyaye, ya zauna a gefen mommah, haka nan zainab da su
shaheedah su hameedah suma duk suka bayyana.
Sannan manga ya gyara zama ya fara da “kamar yarda kuka saka Imran da shaheedah
soyayya har suka amince da junansu suka ‘kaunar junansu haka ita ma Dijah
mahaifiyarsa ta bu’kaci son a had’a Auren Imran da shatu yarinyar wajenta.........
Idanu waje kowa yake kallonsa cikin tsananin mamaki.Imran kuwa zama yayi kamar
statue yayi masa ‘kuri da ido kawai yana tunani shatu shi aka aura ma Shatu,shatun
dai da ya sani ‘kazama shi kuwa mai zai yi da ita a yanzu ba sai anjima ba zai
saketa wallahi yaushe zai iya wannan abin kunyar mai zai cewa mutanen da yake
cikawa baki yana fad’in mai zai yi da ita? Ita kuwa shaheeda tuni ta zube a jikin
hameedah ta ma kasa kuka sai sakin ajiyar zuciya take.
Imran murya na rawa ya fara ro’kon Dahda “please dahda wallahi bana sonta ko kad’an
kada kuyi min haka zaku sa min attack wallahi don Allah ka amince Na sake ta.”
“Wallahi Imran ka sake Na saki shatu sai dai ka sake uwa don wallahi sai na zare ka
daga cikin ‘ya’yana Na gaya maka kada ma ka fara attempting zancen saki idan kuwa
haka ta faru zan nuna wa kowa bad side d’ina wallahi an kaini ‘karshe” sosai kuwa
yake kallonta saboda yarda take maganar da gaske take daga ‘kasan zuciyarta take
fitowa, ranta a ‘bace idanunta kuwa yayi jajir.
Sai ji su kayi Hajja ta saki dariya muryarta a sama tace “Ai kuwa ba ki isa ba
dijah ni kuma zan nuna miki nice uwar manga ko ki amince ya sake ta ko kuma ni na
saka manga ya sake ki.......
FREE📚
08033748387
-20
“Babu wanda aurensa zai mutu saboda son zuciyarki,ashe abinda kike aikatawa kenan a
gidan d’anki Hindatu duk abinda kike ciki labari yana zuwar min,kamar na san hakan
zata faru nace a kawo ni nan d’in kafin na wuce gida na, gaskiya Hindatu kin bani
mamaki kuma sam ba jinin y’ar uwata ce a jikinkiba ita d’in macece mai kara mai
mutunci mai yakana da alkunya idan Banda ma zamani mai ya kawoki gidan d’anki
saboda abin kunya kuma kizo ki saka matarsa a gaba da rashin mutunci saboda siyawa
kai raini,to bakin ki ya mutu anan wajen,aure dai ya d’auru kuma ba mai warwareshi
manga ya sanar dani komai,don mai ita ba zata yi iko da d’anta ba alhali kema da
naki d’an kike iko babu wacce zaka saki a cikinsu duka matanka ne kuma ban amince
da saki ba zancen banza zancen wofi wa yace maka ana sakin mace haka kawai,to kada
in sake jin makamancin wannan zancen, duk abinda kuke ina zaune ina jinku dama don
inga kamun ludayin kowa shi yasa nayi bakam a waje na zauna, to hindatu naji duk
tijararki.”sai a sannan dattijon arzikin yaja ajiyar numfashi ransa a matu’kar
‘bace yana kallon hindatu (Hajja yau dai munji sunan hajja na gaskiya a bakin
kawunta kawu sa’idu)Hajja tana shakkarsa sosai don duk dangi yanzu shine babba
shine kuma mai fad’a aji, gashi dama mafad’aci ne ba’a kuma isa yace ga abinda
za’ayi ba a canja ba, kaifi d’aya ne kuma wargi yake dai-dai ‘kugun ko wani ja’iri.
Parlourn shiru yayi kowa yana jin kawu yana ta fad’a Hajja zuciyarta sai tafasa
take, tabbas kawu ya kawo mata cikas kuma sai taci uban manga da yaje ya sanar
dashi. Kawu yayi fad’ansa son ransa sannan ya kalli Imran “Na jiyo gareka ko gaba
naji magana makamancin ta rabuwa da za’bin uwarka sai naci mutuncinka,wa ya gaya
maka ana jayayya da maganar uwa? Kada in sake jin haka ba and mamaki abinda ta
hango kai baka hangoshi ba.” Haka ya gama fad’ansa ya kuma ce gobe ana gama biki
Hajja ta had’a karonta ta tafi kada kuma ya sake ganin ‘kafarta a gidan d’anta ba
da wani muhimmin daliliba.
Shatu kuwa tana can d’aki bata san budirin da ake ba, tana kwance saman bed d’in
mommah da wayar mommah a hannunta tana buga game. Har sai da anty nahna ta shigo
murmushi fal fuskarta ta dafa shatun “Amaryar Imran.” Shatu ta mi’ke zaune
hankalinta na kan game tace “mai tayi amaryar tasa? Nahna tsaki tayi tace “akwai
wata amaryar bayan ke.” Sam bata d’au zancen serious ba don ko a mafarki bata ta’ba
sawa zuciyarta Imran ba balle har tayi tunanin zama amaryarsa tsokana ce dai irin
ta Anty Nahna ina ita ina Imran da ko inuwa guda basa had’awa. Shigowar mommah da
fad’a da mitar Hajiya mama ne yasa su kayi shiru da zancen fad’a take tana ‘karawa
“Haba addarsu ai wallahi kin yi wauta ta ina aka ta’ba wasa da aure anyi magana
kince wai nuna musu iko za kiyi to ikon me ki jefa yara cikin matsala, yaushe shatu
ta isa aure fisabilillahi nawa shatun take? Ai shirme dai kinyi shi wallahi kuma
ina jiye miki fad’an Babanku kin saka yrinya a matsala ke baki fita daga ciki ba
kin jefa y’arki a ciki wannan dangin mijinnaki da ba kirki bane dasu.” Shatu dai
mi’kewa tayi daga kwancen da take tana kallonsu d’aya bayan d’aya wai mai take ji
ne? Ita dai shatu aka d’aurawa aure da Imran da take ji duk duniya ba wanda ya
kaishi tsanar ta ina ita ina Imran d’an gayu mai ji da kansa? Muryar Dada ce ta
dawo da shatu duniyar su mommah tana jin Dada ta fara masifa “Ah to ni ban ga
laifin dijah ba ai maganin shege d’an banza yanzu Na san ashe Dijah jini na ta
d’auko, ba naki ba solo’biyo da abinda kika sani sai ha’kuri,yo akan me? Wani
shegen yayi mata na’kudar d’an sun d’auki wata ‘kanjamammiyar mata sun bashi, bayan
a haka an zauna ana yi mata isa da iko da fankamar banza sai kace a kansu aka fara
arziki ko da yake ba’ko a arziki shi yake nuna shi wani ne. Yanzu kuwa da tayi musu
haka ai sa san annabi ya faku, to ina dalili idan ban da tsiya ma ace ‘yar
kishiyarka d’anka zai aura ban ta’ba ganin wannan iskancin ba sai a dangin mijin
dijah.ai gasu can dai wancan jarababben kawunnasu ya kashe bakin tsanya yayi min
dai-dai wallahi.” Hajiya mama shiru kawai tayi tana jin fad’an Dada.ita kuwa shatu
tayi zugum ba tare da ta san mai ‘kwa’kwalwarta zata tuna ba.wai ita shatu ‘yar
‘karamar nan aka yiwa aure? Lura da haka da mommah tayi yasa ta isa bakin gadon ta
kamata,rungumeta tayi a jikinta tana shafa bayanta “kwantar da hankalinki daughter
na ba yanzu zaki tare ba sai kin girma kin gama karatu sannan zaki tare kin ga ko
ai da dad’ewa.” Sai sannan shatu ta saki ajiyar zuciya tana dariya ta rungume
mommah. Gaba d’aya d’akin murmushi su kayi banda Dada da ta ‘bata fuska cikin
masifa tace “zancen wofi kenan kaji shashancin banza shikkenan ita kuma sai ta
‘kare a gantale a titi to ba zai yiwuba yanzun zata tare mu da akayi mana aure
yaushe muka kaita yarinya ta fara ‘kirgar dangi sannan ace wani sai ta girma yo
girma na me? Kin san da hakan kika d’aura mata aure, to ban amince ba a sada ta da
d’akin mijin ta cikin mutunci da kima wallahi kafin ayi abin kunya yayi mata ciki a
gadonki.” Gaba d’aya d’akin kunya ce ta kama su wannan sakin baki na Dada, murya
can ‘kasa mommah tace “To shikkenan zata tare amma ai sai an gama shirya mata
abinda za’a kaita d’aki dashi ko?” Dada ta mi’ke tana fad’in “To shine zance amma
kya ajiye budurwa zangangan a gaba kice wani sai ta girma,girmo nace ba girma ba.”
ficewa tayi tana ‘kananun mita. Hajiya mama fuska ba walwala tace “Ba dai maganar
Dada zaki bi ba na tariya ban amince da wannan shashancin ba ki bari ta girma ta
san ciwon kanta tukunna.” Mommah d’aga mata kai tayi kafin tace “ko d’aya Na dai
amsa mata ne don mu huta da mita kafin ta tara mana gayyar jama’a ba wani tarewa da
zata yi sai ta gama makaranta tsaf tukun.” Hafsa tace “wannan shine dai-dai wallahi
Addarmu gwara ma da kika yi maganin mutanen can haba ikon yayi yawa.”haka dai aka
yi ta tattauna zancen har Ammar da Hisham suka shigo hundred percent sun goyi bayan
mommah.
Shi kuwa ango yana can zuciyarsa tamkar ta fashe bak’in ciki ya gama cika shi.yana
ji abokansa suna ta tambayarsa wacece Amaryarsa ta biyu amma ya kasa basu amsa,sun
lura ransa a matu’kar ‘bace yake don haka suka kyaleshi suna cigaba da shirin
dinner shi kuwa ko kallonsu bai yi ba balle ya nuna alamar shirin.
A can ‘bangaren Amarya an sha ba’kin gumurzu kafin ta ha’kura ta saduda bayan
mahaifiyarta ta tabbatar mata ko za tayi yawo tsirara sai ta raba auren Imran da
wannan mai kama da bararojin.hakan yasa ta share hawayenta ta fara shirin dinner
don mai kwalliya Nashe glam wato khadija Nashe tazo za tayi mata, kafin a fara kuwa
tace bari ta je ta ga angon.
Cikin part d’insu ta shiga duk da abokansa da suke zaune dam’kar a parlourn bai
hana ta kutsa kai ba, ba tare da wani shakka ba tace musu “sannunku” Gaba d’aya
suka amsa ta dubi Ali da shi suka fi d’an sabawa tace Imran fa?nuna mata cikin
bedroom yayi yana sakin murmushi a zuciyarsa yake tunanin ko mai Imran zai yi da
wannan ai shi cetonsa aka yi da aka bashi wata duk da waccen d’in ma basu san
wacece ba. Suna kallo ta shige uwar d’aka ba tare da shakka ko kunya ba Amarya ta
kawo kanta kenan sabon salo abdul ya fad’a yana dariyar sha’kiyanci.
Tana shiga ta tarar dashi kwance a rigingine saman carpet idonsa a lumshe da alama
dai ba barci yake ba,zama tayi a gefensa tana jan yatsun hannunsa, a hankali ya
bud’e idonsa yana ganinta ya d’an saki murmushi tare da mi’kewa zaune ya jawo ta
yayi mata kyakykyawar runguma ita ma ‘kan’kameshi tayi kawai ta saki kuka kasa ce
mata komai yayi shima yana sakin ajiyar zuciyar suka lula wata duniyar ranar da
yake jira ga shi ta zo masa a baibai ranar da shaheedah zata zama mallakinsa. Sun
dad’e a wani yanayi na romancing juna kafin ta janye jikinta a hankali bata shirya
kar’barsa a wannan lokacin ba kamar yarda antyn ta ta ja mata kunne sai komai ya
kammala sannan zata amince dashi akwai aikin da tasa malaminta yayi mata.wani kallo
yayi mata “why shaheedah?” Murmushi ta sakar masa “ka tashi kayi shirin dinner mu
tafi wani dalili can ba zai ruguza mana farin cikin da muka dad’e muna arranging
ba,an dai riga an gama cutar mu kuma wallahi bana jin zan iya zaman kishi da
kowacce mace akan ka don haka kayi shirin rabuwa da ita wallahi ta kowani hali ma”
murmushi ya sakar mata yana shafa kumatunta “ki sha kuruminki my lovely wife ni na
san abinda nake shirya mana bana son ki ‘kara d’aga hankalinki aure dai an d’aura
amma ba wanda zai saka ni dole nayi acecpting d’inta as a wife kallon arziki ma ba
yi mata zanyi ba.”
Murmushi ta saki murna fal ran ta tace “yauwa tnx so much dearie ai ko cewa aka yi
ta tare ka amince sai ta zame mana house girl ko?” ‘Daga kai yayi yana shafa kanta
murya can ‘kasa tace “Amma don Allah kada tace dinner yau bana son ganinta wallahi
raina ‘baci yake.” “Tohm shikkenan ba zata ba zan san yarda zan yi da ita yanzu
jeki a fara shirya min ke ki fito kamar ‘yar tsana.” Tana dariya ta mi’ke Ta fice
daga d’akin. Gaba d’aya suka zuba mata ido barin Ammar da Hisham da basu san tana
ciki ba. ko kallonsu ba tayi ba ta fice da Sauri.
Ali ya kalli Ammar yana dariya “kun ga abin mamaki ko? Amaren yanzu basu da ta ido
they are shameless yanzu fa ita ta kawo kanta wajen mijin ko da yake dama ya fi son
irinsu matured in ji shi da fad’a” gaba d’aya suka tuntsire da dariya. Ammar yace
“Da kun ga wacce aka aura masa da kun san ba ‘karamin gata aka yi masa ba.” Ali
yace “yauwa wa aka aura masa please?” Hisham yace “shatu ce fa.” Gaba d’aya suka
zaro ido Ali ya tuntsire da dariya “wai wannan yarinyar mai kama da larabawa ita ce
yake tuejewar baya so?cab ni fa nan har ina cewa ina ciki to ai shi ba ‘karamin
gata aka yi masa ba.” fitowar Imran daga d’aki ce yasa su kayi tsit suna kallonsa
fuskarsa a tamke kamar tunda aka halicceshi bai ta’ba dariya ba. harararsu yayi ya
fice daga d’akin yana jin suna tuntsira masa dariya.
Mutane ne ‘yan biki a zaune a parlourn haushi ya kama shi hakan yasa yace saratu
mai aiki ta kira masa shatu, ta amsa tana ‘kunshe dariyar da take cin ta don duk
sun san labarin, ta shige a d’akin mommah ta samu shatu tana dariya tace “shatun
momma kizo in ji Babban yaya.” Sak shatu tayi tana kallon jama’ar d’akin..
FREE📚
08033748387
-21
Tsaf shatu ta fito tayi masifar kyau cikin makeup d’in da dressing d’in da aka yi
mata pink lace ne da touches d’in maroum a jiki hakn yasa aka saka mata head maroum
dinkin ya zaunu daram a jikinta duk da dai ‘kwailace inji Imran amma fa
Komai yaji don tafi waccen matar tasa muciya da zani 😂. Tafiyar da za tayi ma sai
da Nahna ta koya mata sai zabga’kamshin turare take. Suka fita da su Hafsa don
mommah da Hajiya mama dama ba zuwa za suyi ba. Ta windown bedroom d’insa ya
hangosu, don haka da sauri ya ajiye babbar rigarsa da hularsa a saman gado ya fice
da key d’in mota a hannunsa. A tsaye ya tarar dasu murmushin dole yayi yana duban
Hafsa don ya san Nahna bala’i ce da wayonta sarai ba zata yarda da rainin
hankalinsa ba. “small mom mu d’anyi magana ma na” bin sa tayi tana murmushi ganin
yarda yake kallon shatu ita tunaninta mamakin kyan da tayi yake. “Waye zai kaiku
ne?” Ya fad’a yana kallon Hafsa “wallahi Ammar muke jira wai ya tafi shiryawa”
“okey ita wannan ku bani aronta zan kawo ta da kaina” Hafsa ta kalleshi “mhmn mhnn
faof Big son kada ka jefa ni a trouble don Na sanka trouble maker ne”. Dariya yayi
sosai “nothing will happen insha Allah kada kiji komai wannan jaririyar ma kawai
dai kin sanni da kishi apart from that ma yanzu duka responsibility d’inta yana
kaina tunda an shafa ko ba haka ba?” Hafsa ta ta’be baki “ni dai da ka barta” zuwa
yayi yaja hannun shatu yana murmushi “muje ke” shatu tayi ‘ko’karin janye hannunta
ta kasa ya matse shi gam ya kuma yi mamakin jin wani irin taushi a hannun kamar
audiga. “Alhamdulillah” ya furta bayan ya shiga part d’insa ya tarar gayyar
abokansa sun fita, turjewa shatu ta fara yi ya jata da sauri har suna had’e jikinsu
ya tura ta bedroom dinsa jin ana bud’e bedroom d’in Ammar.suna shiga ya tura ta
saman kujera yana murmushi “ba dai nace ba zaki ba ance sai kin je yanzu ai sai
naga ta yarda zaki.” Turo baki tayi alamar zata yi shagwa’bar da ta saba, ya matsa
kusa daf da daf da ita yana mata kallon cikin ido “wallahi kika fara min kuka anan
sai kin gane kurenki ba dai ba kya jin magana ba? Sai in ga mai fita dake ai har da
wani zuwa ayi miki shafe-shafe kayan haushi kawai in dai don ni kika yi to ba kiyi
kyau ba look at your mouth kamar gidan tsutsa.” Shiru tayi masa zuciyarta Na ‘kuna
yanzu duk wannan kwalliyar a banza aka yi kenan? Nocking d’in da ake ne Yasa shi
saurin zira rigarsa don ya san shaheedah ce ya gyara hula yana fesa turare Ta
mudubi yake yi mata dariyar mugunta ganin yarda ta ‘bata fuska ‘kiris take jira ta
fashe amma taurin kai ba zai bari tayi kuka ba. Tana kallo ya bud’e bedroom d’in ya
zare key d’in da sauri ya fita ya kulle ya rufe ta baya da key yana murmushin
mugunta. Shaheedah da take tsaye ta zata ita yakewa murmushin ganin kyan da ta
zuba.
Tayi kyau sosai cikin black dressing ya kama hannunta suka fita.to su shatu za’ayi
dinner a d’aki kenan,yana fita shatu tasa kuka ta tuge d’an kwalin da sar’kar kuka
take sosai kamar me gashi tana ta buga ‘kofa amma ba wanda ya jita hakan yasa ta
zauna gefen gado,ga mararta ta fara ciwo ta kuma san period ne tunda tun last month
dama ta fara,Allah yasa dama da pant d’inta da pad a jaka don mommah ta gaya mata
in dai ta ga date d’inta yazo to ta dinga fita da shirinta,tana ji mararta na ta
motsi ta zuba tagumi kawai.
Gurin dinner ya had’u an cika kamar me kowa yayi kyau an ci kuma an sha ana ta
spray d’in kud’i, Hafsa da Nahna kuwa sai neman shatu suke ba ita ba labarinta,
haka yasa hafsa taje kusa da Imran tana tambayarsa,murmushi yayi yace tace fa ba
zata iya zuwa ba bata jin dad’i tana d’aki na.” Hafsa bata kawo komai ba ta juya
jikinta a sanyaye tana tantamar zancen Imran a zuciyarta.
Ita kuwa shatu tana can ri’ke da mara ba tayi aune ba ta fara bleeding tana mi’kewq
taga tayi masa staining bed sheet waro ido tayi a hankali tace “Na shiga uku” sai
kuma ta ‘kyal’kyale da dariya “Allah ya ‘kara ni nace ya kulleni kuma wallahi ba
zan wanke ba” kuma sosai yayi staining. Ta shiga toilet ta zame pant da under skirt
d’inta ta yar a wajen sannan ta wanke jikinta a toilet seat d’in shima ko flurshing
ba tayi ba ta gyara jikinta tsaf Ta fito tana dariyar mugunta.”Alhamdulillah nagode
maka period da kazo yanzu.”
Ta koma saman bed d’in tayi kwanciyar ta daga d’ayan side d’in ‘kamshin turarensa
da sanyin a.c ya gauraye ta lumshe ido barci tuni ya fara fisgarta.
Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shiga d’akin da suka sauka tayi shirin
FREE📚
08033748387
-22
Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shige masaukinta tayi shirin barci ta
kwanta sannan Ta samu Hajiya mama da zancen tariyar shatu kamar yarda su kawu
sa’idu suka bu’kata “Hajiya mama kin ji bu’katar da suka zo da ita na son shatu ta
tare nan da one week.” Hajiya mama da sauri ta kalleta “wani irin zance ne wannan
ina ce dake mu kayi zancen nan kika tabbatar min baki saka nan da sahekara biyar ma
zata tare ba,su waye suka zo da wannan batun nifa bana son mutane su ga muna
tauyewa yarinyar nan ha’kkinta a fara zaton don marainiyace don haka ni ban amince
ba na tabbata kuma Babanku ma ba zai amince ba.” mommah tayi ‘kasa da kai tace
“wallahi Hajiya mama nima yanzu na fiki da na sanin aurennan ji nake kamar na
warwareshi ban da kawu sa’idu ne ma yazo da maganar da tuni na gama solving d’in
problem d’in to shi mutum ne kaifi d’aya da baya canja magana, shi ya gayawa Dahda
yace a gaya min a bisa umarninsa yarinya ta tare ko nan da one week ne ba na son
yaga kamar na nuna masa bai isa da yarinyar ba.” Hajiya mama ta girgiza kai kafin
taja ajiyar numfashi tace “Tir’kashi ana wata ga wata yanzu shatu mai zata je ta
aiwatar a gidan auren shekara sha hud’u da watanni ai an daina yayin wannan
auren,wallahi dama da kinyi shawara dani tun a farkon fari ma ba za’a yi wannan
auren ba yanzu mai gari ya waya? Kin san dai babu dalilin da zamu bad’awa wannan
dattijon arzikin ‘kasa a ido dole mu amince da abinda yace tunda dai kina gani
ranar shi yazo ya siya miki ‘yanci a gidannan dole mu amince Allah yasa haka shi
yafi zama alheri a gareta,ikon Allah kenan idan banda haka ga iyayenta nan su hafsa
ko maganar aurar dasu ba’a fara ba sai ita jaririya a kansu to Allah ne kad’ai ya
san lamarin da ya ‘boye a bayan hakan sai mu bita da fatan alheri,amma ko nan gaba
idan zaki aiwatar da abu ki dinga neman shawara don aikin mai shawara baya ‘baci
kuma ko bakomai ba za’a zo ana dana sani ba Allah ya shige musu gaba yasa ace gwara
da aka yi.” Murya can ‘kasa mommah tace “ameen ai insha Allahu ma zan ja kunnensa
kada ya sake ya d’ora mata nauyin auratayya har zuwa san da za ta gama ko da
secondary ne” murmushi mama tayi a zuciyarta tace “kayya ban da yaran zamani duk da
dai aure ne aka yi shi ba da son junansu ba.” momma ta gyara zama tace”kuma da dada
zan had’a ta su tare har zuwa san da
Zamu ga kamun ludayin zamannasu,Sannan ga babansu ua bada ten million yace a siya
mata kayan d’aki suna cikin account d’ina.” “Kash ai da bai wahalar da kansa ba
addarsu,kuma tabbas Na san Babanku fad’a zaiyi amma shikkenan kiyi masa godiya ai
hannun ba zai ‘ki dad’i ba mu ma za muyi namu ‘ko’karin don Babanku yace kallon
shatu yake kamar maryam gatan da maryam ba ta samu ba shi zai mayar kan shatu, zan
kira shi nima da safe nayi masa godiya gobe sai ku fara shiga kasuwa da ‘yan uwanki
ku siya mata kaya Na gani Na fad’a kayan da ko gidan waye za’a kai ba’a ji kunya ba
zan wa Babanku waya anjima kad’an shima ya bada abin da zai bayar.” Momma tayi
godiya ta mi’ke ta tafi wajen dahda don shima bai je dinner ba yace ba zai iya
wannan rashin kunyar ta ‘ya’yan zamani ba. Hajiya mama kuwa d’an kwanciya tayi da
niyyar cikin dare za ta tashi tayi nafiloli Ta sake ro’ka musu zaman lafiya da
zuri’a d’ayyiba don ita macece mai ibada kuma kullum addu’arta akan zuri’arta take.
Sai ‘karfe d’ayan dare dinner ta tashi duk da ango ya gaji amma kasancewar amarya
tana ta girgizar rawa yasa dole ba’a tashi ba.rawa ce ta rashin kunya take ta yinta
kamar yarda amaren zamani suke yi abin har mamaki ya dinga bawa jama’a musamman
ango da abokansa. Da ya gaji ne ma ya mi’ke ransa a ‘bace ya fisgi Hannunta suka
fice daga hall d’in dinnerr.zuciyarsa a cunkunshe da ba’kin ciki kasancewarsa mutum
mai kishi, bai san ba abinda mutane suke kallo a jikinta ba.
Tun a mota kuwa ya dire mata kwandon masifa kamar zaici babu. Ita dai tayi shiru
don ta san ta ‘bata masa rai. Yana packing kuma kallonta bai yi ba ya bud’e motar
ya fita.jikinta a salu’be ita ma ta fito daga motar tana kallo ya shige part d’insu
ta san ko ta bishi ba zai saurareta ba don haka ta wuce cikin gida da niyyar ta
kira shi a waya ta bashi ha’kuri,tunda dai ta lura har lokacin aikin su bai
kammalu ba.
Shi kuwa sauri kawai yake ya isa part d’insu ya fitar da shatu kafin friends d’inss
suzo su same ta. Yana bud’e d’akin mamaki ya kamashi ganinta tana barcinta
peacefully ya zata zai zo ya sameta tana kuka. Gashinta a baje a saman pillow. Ya
tsaya yana kallonta kafin ya daddage ya d’aka mata duka. Da sauri ta tashi da
addu’ar farkawa daga barci a bakinta kamar yarda mommah ta koya mata. Ta tsaya tana
kallonsa ranta a ‘bace. Tsaki yayi “da halla mi’ke ki fice Min a d’aki kafin wani
yazo ya ganki kin wani baje min a bed kina barci salon ki saka min virus,saura kuma
Idan kin shiga ki gayawa mommah ni na hanaki zuwa wallahi sai na miki rashin
mutunci dama tana tambayrki kice barci ne ya kwasheki kuma kanki Na ciwo shi yasa
ba kije ba.” ta’be baki tayi kafin tayi magana ya ja hannunta cikin mita yake cewa
“wuce muje na lura so kike sarakan maganar nan su ganki anan to ta Allah ba
taki.....” sak yayi yana kallon abokansa da suke zaune a parlourn idanunsu a kansa
a zuciyarsa yayi tsaki yace mayu kawai ya juya d’akinsa ya rufe gam da key. Dariya
suka tuntsire da ita Ali da Abdul suka bi bayansa don tsokana sai dai suna zuwa
suka tarar ya rufe bedroom d’in gam.Ali ya tuntsire da dariya “Bar magulmaci dama
wa zai ce baya son wannan zu’ke’kiyar da gaba ma ba’a son kyan da za tayi ba.
Shi kuwa Imran dama ya san idan ya bar ‘kofa a bud’e yaga ta kansa don haka ya
rufe. ‘Ko’karin cire kayan sa yake yana cire babbar rigar zai d’aura akan gado
idonsa yayi masa kyakykyawan gamo da sauri ya ware ido yana kallon stain d’in da
yake gadon sa da d’an ‘karfi yace “what?”lallai ma yarinyar nan ta gama raina ni
‘bata gurin nan tayi haka Allah yaso wani bai shigo ya gani ba, balle a zata
disvirgining d’inta yayi.ya dafa kan sa zuciyarsa na tashi “wallahi yau shatu kin
gama dani ina zan kai wannan kayan ‘kazantar ko masu aiki na bawa fassarar da zasu
yi min kenan kai ya Allah wace irin yarinya ce wannan?” Tsaki ya sake ja ya fara
‘ko’karin yaye dubet d’in da bed cover d’in ya d’aga can dole yaje toilet ko idonsa
ne ya rufe ya wanke ga shi bashi da hand gloves.iya gurin ya kama yana runtse
idonsa, bud’e toilet d’in ke da wuya ya sake yin wani gamon da sauri yayi cilli da
bed sheet d’in cikin sink amai na taso masa wannan wace irin ‘kazama ce yanzu kuma
ita aka aura masa? Wallahi ba zai iya wannan ‘kazantar ba, idonsa a runtse yay
flurshing toilet d’in yana yi yana ja
Mata Allah ya isa kamar wani ya sa shi. Ya saka harpic, yana sakin ajiyar zuciya a
zatonsa ya gama amma ina juyawar sa ke da wuya ya ga undies d’inta zube a ‘kasa da
sauri ya ja baya,kamar ba zai yi ba sai kuma yayi tsaki ba dolena nayi ba duk wanda
na kira kamar na tarawa kaina jama’a ne kowa kuma da fassarar da zai yi
masa.idanunsa a runtse shima undies d’in ya d’auke shi ya saka a toilet bin kafin
da safe ya kira ta wallahi sai ta wanke masa toilet tsaf duk dama gobe zai bar
gidan sai ta ci kanta ita kad’ai, da kyar ya wanke bed sheet d’in kawai don baya
son yin wani cikin friends d’insa by mistake ya shiga ya gani wallahi da shima
barin sa zai yi ta zo ta wanke to yana gudun ‘bacin rana kada ayi zaton wani abu
yayi da ita shi kuwa Allah kada ya nuna masa wannan ranar da wani ido zai kalli
jama’a bayan tarin cika bakin da yayi akan cewa MAI ZAI YI DA ITA. Yana gama
wankewa ya cilla shi cikin washing machine sai sannan zuciyarsa ta dinga tashi ai
kuwa ba ji ba gani ya dinga kwara amai sai da ya gama aman yayi brush yana gamawa
ya fice da sauri murya a cunkushe yace wallahi ban yafe ba banza ‘kazama.😂 ya gyara
gadonsa tsaf ya bad’e bedroom da turaren wuta da room freshner. Sannan ya fice
parlour baya tunanin zai iya wanka a toilet d’in wallahi dole key ya d’auka a daren
gwara yaje gidansa yayi wanka. Yana had’e rai ya fito, ai kuwa suna ganinsa Ali da
shegantaka ya taso”wai ya aka yi ne yalla’bai mai amarya tazo yi part d’inka ko dai
har ka fara sonta ne?”harara ya zabga masa “matseni in gaya maka” Abdul yace “ai
abin bai kai na matsewa ba in dai wannan ne ai baya ‘buya abinda zamu gani ‘kunshe
a mahaifarta muzo mu sha suna.” “Mtsww God forbid wallahi sai kace irin ku ai ni
tunda nace muku ba abinda zanyi da yarinyar nan to kuwa zaku sha mamaki ba ku san
waye Imran ba.” Dariya su kayi sosai suna kallo ya fice Ali yace “mhmn a dai juri
zuwa rafi yalla’bai wata rana tulun zai fashe” Abdul ta tuntsire da dariya yace
“d’an iska ranar mayar da martani ba.” Yana jin su murmushi kawai yayi ko don
tanadin iskanci da suka yi masa ai ba zai kusanci yarinyar nan ba haka zai saketa
wallahi da zarar shirinsa ya kammala. (To kowane shiri ne wannan mhmmn wani abin
sai d’an gidan manga)
Ita kuwa tana bedroom d’inta bayan tayi wanka Night gown a jikinta da cup d’in tea
a hannunta tana sipping a hankali so take ciwon marar da yake d’an damunta ya lafa
mata. Hafsa ta shigo d’akin idanunta a kanta ta zauna a gefen gadon “wai ina kika
shiga ne? Ban ganki wajen dinner ba?” Hafsa ta fad’a tana shafa kanta.
Murmushi shatu ta saki a karo na farko taji tana son rufa masa asiri saboda sam
bata son haushinsa da mommah take ji tace “wallahi period pain ya hanani fita d’azu
fa kamar na mutu dole kuwa nayi kwanciyata side d’in su Ya Imran.” Hafsa ta girgiza
kai “ashe da gaske yake wallahi na zata ‘karya yake har na had’a shi da mommah sai
kije ki wanke sa a wajen mommah don wallahi ta kunnu da yawa cewa take zai zo ya
sameta don ma Hajiya mama tana hanata tace ba huruminta bane da tuni ta kira shi ta
sulle shi sai kije ki wankeshi.” Shatu ta mi’ke ta tafi wajen mommah. Tsaf ta wanke
shi kuwa mommah ta jata jikinta “oh am sorry daughter to da kika yi zamanki a can
hope ba abinda yayi miki kuma kin sha magani?” Daga kai tayi tana kwanciya a cinyar
mommah da take feeling d’inta kamar Innaji she really love mommahnta to the extent.
Da safe Dahda ya shiga wajen hajja gaishe ta da kyar take amsa gaisuwar. Sister’s
d’insa ma duk suka gaisheshi anan yake sanar da Hajja tariyar shatu ita ma kamar
yarda kawu sa’idu ya tsara sati mai zuwa Hajja ta ta’be baki”To ni yanzu ina ruwa
na nayi magana kaje ka yayata ni a bakin duniya ai ba abinda zance maka manga aje
Allah yayi albarka gobe-gobe ma zamu tattara komatsanmu muyi gaba ba kuma zamu sake
dawowa ba kamar yarda ka bu’kata kuma ina son ka jini da kyau dama ka samu fili ka
siya ka fara yi min gini anan kano duk san da na tashi zuwa na dinga zuwa can na
sauka na san mallakina ne. Shashasha ana yi maka gata baka san gata ake maka ba duk
an mallakeka da
Surkullen fulani.” Murya can ‘kasa Dahda yake amsa mata “Insha Allah Hajja za’a
Gina,amma tafiyar da kun bari wani satin idan shatun ta tare.” Hameedah mai son
ganin ‘kwaf ta gaban Hajiya ta saka baki “eeh Hajiya mu bar shi wani satin idan ta
tare sai mu tafi cab amma za’a ga ‘kwailar amarya ai ni na zata ba yanzu zata
tareba. Dahda ya zabga mata harara don sam basa shiri da hameedah baya son
halayenta gaba d’aya.ya mi’ke yana yiwa Hajiya godiya bayan ya ajiye mata ma’kudan
kud’i da niyyar yi mata toshiyar baki. Bakin Hajja kam yana mutuwa tsaf saboda
kud’i.nan ta shiga jera masa albarka. Yana fita hameedah ta shige part din zainab
ta bata labarin tariyar. Hankalin zainab ya tashi don basu kawo tariyar nan kusa ba
sun zata sai ‘yar su ta riga ta mallake gida tukunna sai ga sabon labari ya bayyana
a zuciyarta tace ashe kuwa sai na tashi tsaye kafin kwa’bata tayi ruwa.
Tsaf yayi wankansa ya shirya cikin shigarsa ta musamma farin filtex d’insa da hula
damanga takalmi bartozzi ya d’ora agogon rolex d’insa a damtsen hannunsa kana
ganinsa kamar ka sureshi ka sace. Sai zabga ‘kamshin turarensa da yake mix yake
different colours ‘kamshinsa daban yake.
Direct part d’in mommah ya nufa cikin tafiyar izza kamar Kuma ‘kasaita kamar yarda
ya saba yi kullum. So yake yaje ya dam’ki ‘yar gidan mommah ta wanke masa toilet
duk da yasa an wanke amma sai ya wahalar da ita.
Cak tayi da tea cup a hannunta tana ‘kare masa kallo cikin shigar doguwar rigar ta
ta shadda as usual yanzu ma kanta ba d’ankwali. Sarai yaji idonta a kansa yayi mata
banza yana dur’kushe a gefe yana gaida su dada da Hajiya mama da momma. Dada ta
dubi shatu tsaki tayi “kiji min ‘yar banzar yarinya ba zaki gaida mijinnaki ba.” Da
sauri yace “ta bar gaisuwarta jeki bedrroom d’ina da toilet ki gyara min” ya fad’a
yana tsareta da ido tsaki momma tayi “akan me duk ina house helpers d’in gidan da
sai ita zata gyara maka don wani sabon iyayi gidan ma da yau zaka barshi.” Dada ta
zabura tace “Auzubillahi kuji min mata tana neman jawo mana masifa da ranar nan
ruguzu ta fad’o mana aikin mijinnata ne ba za tayi ba to kuma idan bu’katar ta yake
fa ba iya sharar za tayi ba tashi ki fice kafin na kai miki mangara a’a wallahi ba
ruwana idan rashin kunya zaki saka ta dinga yi masa ba kuwa zanje zaman d’akin nan
ba ki hana a raya sunnahr muhammaduna rasulillahi d’an Abdullahi. Kai tashi ka bi
matarka kaji.” Mommah gaba d’aya ran ta ya ‘baci har ya mi’ke a zafafe tabi bayansa
suna zuwa corridor tace “kai ji mana kuma wallahi ko hannu ka ri’ke mata ban
Yafe ba.” Tana fad’a ta juya Imran shi dariya ma ta bashi ya juya kawai a zuciyarsa
yace “kin san kina tsoron hakan kika yi mata aure kash ina ma bana gudun ayi min
dariya da ayau zan mayar miki da shalelen taki cikakkiyar mace.”
FREE📚
08033748387
-23
Suna shiga bed room d’in ya ja ‘kofa ya rufe, fuska a d’aure yake kallonta,ya
tsareta da ido sosai kafin yace,”sakonki na jiya ya isar min, wai ke ki nuna min
kin cika mace ko?har kin fara period, amma ban san ke wawuya bace sai yanzu,wa yace
miki mace tana bari ma a gane tana period? Baki san abin kunya bane hakan?” Turo
baki tayi kawai tana kallonsa,sai kuma a lokacin wata shahararriyar kunyarsa ta
kamata,ta ji sam bata kyauta ba yanzu shikkenan ya gane mata sirrin ta? Sirrin da
mommah tayi ta jan kunnenta akan kada ta bari a gani, da sauri ta runtse idonta.
Tsaki ya ja “Dama kafin na dawo ki tabbata kin fitar da ‘kazantarki daga toilet
d’in ki kuma wanke min bin d’ina,and then lastly ki tabbatar kin wanke anything
dake toilet d’in ya dawo kamar sabo, wawuyan yarinya kawai.” Ya fad’a yana kai mata
ran’kwashi, daga haka ya fice ya kuma kulleta da key ta baya.
Sai sannan shatu ta bud’e idonta, tana sakin ajiyar zuciya, a hankali tace “Wai ni
Shatu mai na aikata mutuminnan yanzu zai sake min kallon ‘kazama.” Tsaki ta ja ta
shige toilet d’in, very neat ta samu toilet d’in,amma haka nan ta ‘kara wankeshi.
Momma jin shirun yayi yawa, da sauri ta danna kiransa a waya don hankalinta sam ya
gaza kwanciya. Tsawon lokaci wayar tana ringing shi kuwa yana kallo yana driving
ya’ki receiving call d’in sai murmushi yake, ya san mai take yiwa bata san ko
bindiga aka saka masa ba zai iya aikata abinda take tunani ba.
Ji yayi text message ya shigo, ya bud’e yana murmushi had’e da ware ido kamar yarda
hakan ya zame masa jiki. “Wallahi ka aikatawa yarinyar nan wani abin sai ka sani.”
Dariya yayi sosai har da dukan sitiyari. A zuciyarsa yace “Ai kuwa yanzu wasan zai
fara Mommah.”
********************************
Cikin kuka da tashin hankali take kallon mahaifiyrta, “Yanzu Anty duk burin da naci
ya tafi a banza kenan? Yarinyar nan tarewa za tayi? Kuma ana nufin itama Imran
mallakinta ne kamar yarda yake mallakina? Tana da right da komai a kansa, zata
had’a jiki dashi? Komai da zaiyi min zai mata?” Cikin tashin hankali ta sake rintse
ido. “Na shiga uku Anty pls kiyi wani abu mana, wallahi ji nake kamar zuciyata zata
buga.” Tsaki Zainab tayi kafin tace “Ke bana son shashancin banza ki tsaya ki
saurari abinda zan ce miki,ko jiya munyi waya da shuwa ta tabbatar min da ta koma
gurin mutuminnan abinda ya sake ce mata kenan dole ki san yarda kika yi kika bashi
maganinnan yaci a nama, a kuma ranar da yaci ake so lallai ya had’a shimfid’a da
ita, yace min wallahi da zarar anyi haka kashegari zai sake ta kuma ba zai sake
waiwayarta ba.” Kukan ta sake saki “Ni fa anty a sake wata shawarar wallahi ba zan
amince ya shafi jikinta ba,balle har su had’a shimfid’a Imran nawa ne ni kad’ai.”
Tsaki Anty tayi ta mi’ke a zuciye tace “Sai ki shirya zama da ita din-din-din a
matsayin kishiya,ni dai abinda naga zan iya yi kenan shashasha ko meye abin damuwa?
abin rana d’aya lokaci d’aya, kuma wallahi kika sa nayi asarar kud’ina ranki ne
idan yayi dubu zai ‘baci,kin san nawa na kashe? Ban da tafiya cikin jeji da shuwa
ta kwana tana yi a garinsu, to kije kiyi yarda kike so, ki bari suyi surkullensu na
fulani su su mallakeshi,kin san dai yarinyar nan ta fiki komai da komai.” Runtse
idonta shaheeda tayi murya na rawa tace “zan gwada Anty Allah ya bani iko.” Antyn
ta dafa ta yauwa “ko ke fa idan kika yi hakan shine zaki samu kansa,ki ci karanki
babu babbaka.” Shaheedah ta saki ajiyar zuciya tana dafa hannun mamanta tace “Amma
Anty ta yaya zai amince ya kusanceta bayan kin san ba son auren yake ba.” Anty tayi
murmushi “Yaro-Yaro ne ai ba yanzu zakiyi ba sai lokacin da muka so ta bar gidan,a
lokacin dama kin tsara tafiya Abuja sai ki bashi a nama yaci,to kafin ki tafi ki
tabbatar kin bashi desire tablet a cikin tea da safe mai ‘karfin gaske,idan ya
bu’kace ki kice period kike ko kuma kafin maganin ya fara aiki kiyi sauri ki tafi
shikkenan fa fa’kat, burinmu na farko zai cika.” Dariya shaheedah tayi ta rungume
Antyn ta cikin tsananin farin ciki,hankalinta kam yanzu hundred percent ya kwanta.
Da yamma kafin a kai amarya Momma ta kira Imran, ba ‘bata lokaci yazo, tana
kallonsa su biyu a
Parlourn tace “Nasiha zan maka Imran a matsayina na mahaifiyarka duk runtsi duk
wuya ka kula da iyalinka,amana ce ubangiji ya dan’ka maka a hannunka, kayi adalci a
tsakaninsu Imran kada kaga ita wannan yarinya ce ka cuceta ko ka zalunceta,zata
tare nan da kwana shidda....” da sauri Imran ya zaro ido yace “kwana shidda Mommah
ai naga tayi ‘karama.” Mommah tsaki tayi”Ni kaina ba’a son raina hakan zata faru ba
ba yarda zanyi ne, sai dai ina son in ja kunnenka hakan ba yana nufin na baka
lasisin kula ta bane, wallahi ban amince ba kada wata mu’amala ta had’aku,
Ka bar ta tayi karatunta please Imran.”
Ransa a ‘bace ya saki ajiyar zuciya yana tunanin mai zai kaishi kusantarta ko shi
ya kawo maita duniya, gaskiya bai ji dad’in lamarin tariyar nan ba, har hakan ya
gaza ‘boyuwa a
Fuskarsa,sai dai bai ce komai ba ya mi’ke ya tafi bayan ya zaro key d’in part d’in
shatu na gidansa ya mi’kawa mommah kamar yarda ta bu’kata.
Tunda ya koma bedroom d’insa ya zubawa kayan da abokansa suka had’a masa na komawa
gidansa kallo,idan ka ganshi zaka yi zaton kayan yake kallo,Sai dai tuni zuciyarsa
ta tafi tunanin neman mafitar yarda zaiyi da auren Shatu, tunani iri-iri ya
shigeshi wata zuciyar tace kawai ya saketa ya gudu da matarsa su bar ‘kasar, a duk
shawarwarin wannan ce tafi tsaya masa.
Tsaf Amarya Shaheedah ta fito a cikin shigar laffaya sai zabga ‘kamshi take kai
kace anyi ‘barin turare a jikinta,sanye take cikin pink d’in laffaya, ta dai rufe
kanta amma idonta ko alamar kuka babu,
Burinta a yau ya cika na auran Imran, kamar yarda ta dad’e tana mafarki,yau dai ga
ta a matsayin matarsa,don haka take jin kamar taje ta kai kanta ganin su masu
kaiwar basa sauri sun tsaya sai zagaye suke da ita wajen ‘yan uwa.
Gida yayi kyau ya sha kayan alfarma na gani a fad’a,sai zabga ‘kamshi yake. Amarya
tun daga haraba take sakin murmushi cikin laffaya.
Kowa ya yaba sannan masu kawota suka tattara suka tafi, ‘yan mata zuciyarsu cike da
burin samun irin gidan ko makwafinsa.
Ango dai tunda abokansa suka fara siyan baki yake sakin tsaki,burinsa suyi su
tattara su tafi,tunda ya dad’e yana jiran wannan ranar a matsayinsa na kamilin
saurayi.
*************
Tsaf tayi shirin makarantar ta ta fito, tana isa parlour taji ‘kamshin turarensa a
parlourn, tayi mamakin ganinsa a yau d’in don rabonsa da zuwa gidan kwana hudu
kenan cif tun bayan da amaryarsa ta tare. Yayi kyau sosai cikin black blue d’in
yard d’inkinsa na kullum ne a jikinsa,gajeriyar riga mai gajeren hannu kan sa ba
hula, hakan kuma sai yayi masa kyau. Har zata wuce da sauri Dada ta ‘kwalo mata
kira “zo nan ‘yar nema baki ga mijin ki bane?” Bakin ta ta turo murya a cunkushe
tace “Dada na makara fa.” Tsaki Dada ta ja cikin masifa tace “Allah dai wadaran
naka ya lalace uwarki ce ta d’aure miki wani abu can, an ce wani sai kin yi
tsinanniyar boko matar da za’a kai d’akin miji jibi ace tana yawo a gantale don
wauta ko ‘yan magungunan gyara na daka ban ga ana baki ba,balle aje ga batun gyaran
jiki,sai anje an cuce shi an kai masa ke salam kamar kazar da ba maggi ba
gishiri,ko da yake ina ruwa na ke da uwarki ku zaku yi da na sani,ki wuce ki koma
ciki yau ba zuwa wata makarnta idan kika tare idan ya zama dole kya je.” ‘Kwalla ce
ta kawo idon ta,murya a cunkushe tace “Test ce fa dani zaki ce wani ba zan je
school ba.”Mommah ran ta a ‘bace tace “Dada ki bar ta taje idan yaso goben sai ta
ha’kura insha Allah ai kema dai zaki so ace ‘yar jikar ki ta zama likita.” Dada ta
gyara zama cikin masifa tace”To kuwa idan har zata je makarantar nan sai dai wannan
‘katon banzan ya kaita ba Ammaru ba da kullum za’a dinga tashin sa da sassafe kai
ta makaranta don an gan shi salihin bawa.” Ko kallon in da Dada take bai yi ba,ya
mi’ke yana yiwa Shatu kallon sama da ‘kasa a
Zuciyarsa yace “Ai dama Ammar d’in aka aura wa ita.” “Ki nemi mai kai ki school ba
abinda nazo yi ba kenan.” Cikin ‘bacin rai Mommah tace “Wuce kije ya kai ki idan
yaso ya zubar da ke a titi,saboda ka ga na kyale ka? Kwanan ka nawa rabon ka da
gidannan sai kace a kanka aka fara aure to kai zaka kai ta daga yau kuma kai zaka
cigaba da kaita, wuce ku tafi Shatu kada kiyi late ai ha’kkin ta akan ka yake.”
Dada tace “‘kwarai kuwa.” A ran sa yace yau zaku ga ha’k’ki wallahi sai nayi mata
abinda ba zata sake shiga mota ta ba.
Tafiya suka yi sosai kafin su isa d’an ‘karamin building d’in mai tsananin kyau a
ido,ginin kuma bungalow ne,gurin sam ba hayaniya. Da sauri Shatu ta kalleshi murya
a cunkushe da tayi al’kawarin ba zata yi magana ba tunda taga ba hanyar makaranta
yayi ba, ta san wata muguntar ya shirya mata saboda ance ya kaita makaranta.”please
Yaya Imran ka mayar dani gida idan ma ba zaka kai ni school d’in ba.” Ko kallon
inda take bai yi ba, ya zare seat belt d’insa yace “wuce muje malam ba dai sunce
ha’k’kinki yana kai na ba,to yau zan sauke babban ha’k’kin kafin ‘kananan su biyo
baya.”
Jikin Shatu ne ya d’au rawa don tun tana ‘kauyensu ta san menene aure tunda da
friends d’inta da yawa da aka yiwa Aure. Ta kalleshi da sauri ta ga ya had’e rai,
tuni idonta ya kawo ‘kwalla ta san matan. ‘Kauyensu suna bata labarin wahalar da
suke sha har ruwan zafi ake saka su.”Don Allah Ya Imran kayi ha’kur.” Ba tare da ya
kalleta ba yace “fita muje malama you are wasting my time,ai kin girma zaki iya
d’aukan nauyin auratayya zaki kuma iya d’aukan duk wani abu da matan aure suke iya
d’auka,tunda Babar ki ta aurar dake,ko baki san aure ba?” Da sauri ta girgiza kai
“Ban sani ba Yaya Imran.” “To me yasa kika tsorata har da kuka? Kada kiyi min
‘karya fad’a min gaskiya kin san aure ne?wallahi kika yi min ‘karya kika bari na
gane ‘karya kike min a yau zamu goge raini tsakanin ni dake don ba zan bar mana
wajenan ba sai na mayar dake cikakkiyar mace mai amsa sunan matar aure,gaya min
nace.” Da sauri ta fara wasa da hannunta jikin ta yayi sanyi sosai kamar ba Shatu
Danger ba, ta sunkuyar da kai sosai hawaye sai zirara yake.
Shi kuwa dariya ce take son kama shi ganin tun ba aje ko ina ba ta razana alamar ta
san duk abinda ake a aure,ya matse dariyar kafin yace “oya tell me ina jin ki mai
ake a Aure?” “Iskanci” shatu ta fad’a murya na rawa sai kuma ta fashe da kuka “Don
Allah kada kayi min kaji Yaya Imran wallahi Dijen gidan maigari tace da mijin ta
yayi mata shine ta samu ciki.”
Still idon ta a ‘kasa take magana ta ma kasa kallonsa.shi kuwa dariya ce kawai take
cin sa amma ya kasa yi,sai murmushi yake yana kallon yarda duk ta gigice. “Kin san
meye iskancin Kenan?” Da sauri ta girgiza kai “Ban sani ba wallahi amma dai tace
min cire kaya....” “yi min shiru fita muje ashe ma kin san komai yau kuwa zaki san
menene iskanci,shashasha kuma Idan baka da aure idan kayi shine ake ce masa iskanci
idan kuwa kana da aure raya sunna ake ce masa,Fita muje nace.” Ganin ba alamar wasa
a fuskar sa yasa ta fita ‘kafarta na rawa al’amarin ya gigita ta sai kace ba Shatun
Mommah danger ba. ‘kafar ta ta kasa d’aukanta a zafafe yace “ko sai nazo mun fara
daga nan.” Da sauri tabi bayansa hankalinta a tashe,ta san yau kashin ta ya gama
Yawo.”
Yana knocking Gate man ya bud’e gidan da sauri yana kai masa gaisuwa.gidansa ne da
ya gina yake saukar guest d’insa turawa idan sun zo harkar business Nigeria. Ya
tsaru iya tsaruwa yanayinsa tsarin turawa. Yayi kyau sosai parlor ne guda d’aya
babba sai kitchen da toilet a parlourn sai 2 bedrooms.
Raku’bewa tayi a one seater tana chewing hand finger d’inta a tsorace take sosai
tana kallo ya shiga bedroom ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando da sauri
ta runtse idon ta ganin ya nufo ta ta mi’ke a guje tayi hanyar bedroom.murmushi
yayi yace “shikkenan kin hutar dani kin
Kai kan ki.” Tana shiga ta rufo ‘kofar sai dai abin takaici babu key a Jiki. Tana
kallo ya shigo fuskarsa a had’e, ta dinga ja da baya tana ro'konsa "please Ya
Imran!" "wuce toilet kiyi brush sosai malama." ta bud'e toilet d'in shima abin
takaici babu key a jiki. Shatu ta zaro ido a hankali tace "Na shiga uku." Idanunta
duk sun firgice, tana ji ya turo ‘kofar ya shigo idanun sa a kanta “Ba zaki yi
sauri ba?” “Ni fa nayi brush d’ina a gida.” “Na sani ai wannan na musamman ne ba na
son naje kissing d’inki naji bakinki ba daidai ba.” Ai da sauri ta zube a ‘kasa
hawaye sha’be-sha’be.”Don daraja da girman iyayenkaw Ya Imran kayi ha’kuri.” “Idan
na ha’kura za kiyi min abinda nake so?” Da sauri ta d’aga kai,murmushi yayi “okey
taso ki fito mu d’aura al’kawari.” Da sauri ta mi’ke ta fito tana sakin ajiyar
zuciya, sai kuma ta kalleshi tayi saurin d’auke kai “please amma ka fara mayar da
kayan ka tukun.” Yayi mata wani kallo “Meye a jikin nawa? Ko naked kika ganni?” Da
sauri ta girgiza kai “To kina feelinga sha’awa ta ne? In d’auke miki ita yanzun
nan?” Da sauri nan ma ta girgiza kai ba tare da ta san menene ma sha’awar ba.
Ya ta’be baki “Oya zauna maza na fad’a miki sharad’ina.” Ta kuwa zauna ta ra’be a
gefe kamar ace kyat ta gudu.”Zan kyale ki idan kin amince da sharad’ina,kije gida
ki sawa Mommah rigima kice mata ba kya son auren idan kuma ta ‘ki kice mata ba kya
son ki tare yanzu,kiyi ta kuka idan ba haka ba wallahi kika bari aka kawo ki gida
na sai kin gaya wa aya za’kin ta zuwa zan miki abinda ake yiwa masu aure,kina ji na
ko?” Ta d’aga kai da sauri. “Yauwa idan kika yi haka kin zama good girl kuma zaki
yi karatu sosai,idan kuwa kika ‘ki ana kai ki zan miki ciki ki haihu kuma ba karatu
kina jina?” Da sauri ta d’aga kai, yayi tsaki “Ba kai zaki d’aga min ba kice na
amince da sharad’inka Ya Imran.” Da sauri tace “Na amince da sharad’inka Ya Imran.”
Ya gyad’a kai yana mi’kewa had’e fad’in “Good Girl.”
‘Daya bedroom d’in ya shige yayi kwanciyrsa, don ba zai mayar da ita yanzu ba sai
ya kad’a ‘yan hanjin Mommah tukunna. Murmushi yayi a zuciyarsa yana tunanin halin
da Mommah zata shiga.
Mommah lokacin d’auko ta yana yi ta tura driver, sai dai me? Driver ya kira ta yace
ai ance shatu ba ta zo makaranta ba.Mommah bata san san da ta zauna da’bas a kujera
‘kirjin ta yana bugu bata so ace hasashenta ya zama gaskiya ace Imran yaje ya
aikatawa Shatu wani abun da kan ta ba zai iya d’auka ba. wayarsa ta dinga
kira,kusan missed call biyar kafin ya d’aga murya a dashe tamkar yana cikin wani
hali yace “Hello Mommah.” Bata san san da ta ‘kunduma zagi ba.”Gidan uban wa ka kai
ta?” Dariya ta so kubce masa yace “Ba ko ina fa Mommah gamu nan muna tare.” Mommah
ta saki salati “kuna tare a gidan uban wa?” “Haba Mommah ki kwantar da hankalinki
ni fa mijinta ne ku da kanku ku ka fad’a to me ye na........” a zafafe ta katseshi
“Wallahi Imran ka jini da kyau idan ka sake ka bud’ewa yarinyar nan sirrin da yake
cikin aure zaka gamu dani nawa Shatun take?” Cikin dakiya yace “Amma ku kayi mata
aure Mommah ku fa kuka ce duk hakkinta a wuya na yake..” “Uban ka nace Imran, kaci
uban ka ka dawo min da yarinyar nan yanzunnan wallahi ko ranka ya ‘baci.” Ta kashe
wayar tana jan salati “Na shige su nima wa ya aike ni?”
FREE📚
08033748387
-24
Elegant Online Writers..
*_Masu son Littafin MIJIN MALAMA suyi following Acct ɗin nan a Arewabooks👇🏾_*
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
Bai Tashi mayar da ita gida ba sai da yaga 3:00pm sharp, lokacin yunwa ta ci ta
cinyeta. Ranta duk ya gama ɓaci da wannan mulkin mallakar, ta na kallo ya fito
fuskar shi fresh da alama wanka ya yi ya fito. Ita ɗin ma watsa mata kallo ya yi
“Tashi Malama kije kiyi wanka ban son ƙazanta, ba za ki shigar min mota ba sai kin
yi wanka tun safe har 3:00pm” Marairaice fuska ta yi, idanunta yana shirin kawo
ƙwalla ta ce “Don Allah Ya Imran ka bari idan naje gida zan yi” Ya girgiza kai ya
ce “Ba zan iya ba kusan 7 hours rabonki da wanka, sannnan ki shigar min mota? yi
sauri I have something to do kina wasting time ɗina” Miƙewa ta yi bisa tilas ta
shige cikin ɗakin don yin wankan.
Suna parking ya watso mata kallo “kada ki manta da alƙawarinmu, idan kuma kin ƙi ki
shirya karɓar haƙƙin ki na aure,don in dai na gan ki a gidana na san kin zaɓi zama
cikakkiyar House wife” Ta ɗaga kan ta kawai,ta fice daga motar cikin azama. Imran
ya bita da murmushin mugunta, ko ba komai ya san yau ya kaɗar da hanjin Mommah.
Tana shiga gida ta tarar da su Hajja a main parlour na gidan, bisa tilas ta durƙusa
ta gaishesu, ko ba komai dole ne ta bi umarnin Mommah, sai dai ko kallo bata ishe
su ba, har da masu harara da zabga tsaki, tana ji Hameedah tace “shegiya mai siffar
jinnu” Girgiza kai tayi a zuciyarta tace zamu haɗu wallahi kafin ki tafi.
Ba kowa a parlourn Mommah, hakan yasa tayi saurin shigewa bedroom ɗinta, sai dai
tuni Mommah taji motsin ƙofarta hakan yasa ta fito da sauri har tana yi kamar zata
faɗi
A bakin Gado ta tarar da shatu tana zaune ta zabga uban tagumi,idanunta ya ɗan kaɗa
alamar yunwa da barci ne a cikinsu,sai dai ita Mommah tuni tayi wa hakan wata
fassarar ta daban.
Da sauri ta dafa ta tana zama a gefenta tace “Shatu hope ba abinda yayi miki? Ko ya
miki wani abin?” Girgiza kai tayi hawaye na zuba a idon ta, ta rungume
Mommah,hankalin Mommah idan yayi dubu ya tashi,ta
dinga salati tana tafa hannu “Tashi mu gani muje toilet.” Shatu ta riƙe hannunta
tana girgiza kai “Mommah ba komai ni dai don Allah bana son auren yanzu bana son na
tare please Mommah.” Kuka take sosai hankalin Mommah ya tashi,saboda bata tabua
ganin Shatu a wannan halin ba.
Babu wani gyaran jiki da aka yi mata,duk da Dada tana ta maganar gyaran jikin,
Mommah kuwa tace ba yanzu ba tunda yanzu ba zaman Aure za taje yi ba. Ita kuwa Dada
da kanta ta bawa mai gadi kud’i yaje kasuwa ya siyo mata kayan magunguna tace suna
tarewa zata fara banka mata.
Masifa take tana ‘karawa “Ni ban ga dalilin wannan tsiya ba ace wai Auren da aka yi
ba yanzu miji zai tare da matarsa ba, to ba dani za’a yi wannan shirmen ba.”
Imran gani yayi kawai ana ta shiga da kaya na gani na fad’a, bugun turkey,
‘bangaren Amarya ya fara d’aukan harami kamar a ‘kasashen ‘ketare. Ransa ya gama
‘baci ya tabbatar shatu bata ji jan kunnen da yayi mata ba kenan. ‘Karshe don
takaici ficewa yayi ya bar gidan zuciyarsa a hassale, musammman ganin yarda
shaheedah ta hassala,sai kuka take masa.
Kashegarin Ranar Mommah ta shirya walima gagaruma, a kuma ranar aka yi kamun Amarya
Shatu. An ci an sha an kuma yi wa’azi sannan Mommah tasa aka yi saukar Al’kur’ani,
da niyyar Allah ya basu zaman lafiya ya sanya albarka a auren. Ango dai ko gidan
bai zo ba.
Mutane da dama walimar ta burgesu, har suka gaza shiru suke fad’an dama haka aka
dawo ake yi a kowane aure, aka rage bidi’a ko don samun albarka a Aure.
Tsirarun mutane ne suke fad’ar haka, yayinda majority abin bai burgesu ba, musamman
dangin Dahda da suke ta’be baki suke fad’in Iyayi ne da son a sani, ta kuma nunawa
mutane wai ita mai tsoron Allah ce. Bata ce komai ba duk da zancen yaje har
kunnenta tace “Allah ne kad’ai ya san zuciyar bayin sa.” Don haka sam surutun
jama’a baya damunta.
Rabuwar Mommah da Shatu, abu ne da girgiza zuciyarka in dai kana wajen, Shatu kuka
take kamar ranta zai fita, musamman idan ta tuna al’kawarin Imran na aikata mata
irin abinda aka yi wa ‘yar gidan maigari matu’kar bata saka Mommah ta janye auren
ba,haka ne yake sake tunzura zuciyar Shatu take kuka kamar zata mutu.
Mommah ma kukan take, tana ji kamar ta saka Imran ya saki Shatu tausayinta yana
sake tsirga mata.Ta rungumeta sosai a jikinta, tana rad’a mata kalamai masu dad’i,
wanda duk uwa ta gari ya kamata ta gayawa d’iyarta,yayin sallamar Aure. Tabbas
rabuwa da gida abu ne mai ciwo Shatu,sai dai fatan dacewa a gidan Aure.
Haka tana ji tana gani aka raba ta da jikin Mommah, su Anty Nahna suka jata
jikinsu.
Kamar yarda ake a al’adance dole sai an kai ka wajen dangin miji, itama Shatu haka
aka dangana ta da na ta dangin mijin. Sai dai ba wanda yayi musu kar’ba ta mutunci
musamman Hajja da tace ba zata kar’bi amana ba,haka nan cikin yaranta bata amince
wani ya kar’ba ba. Ta ‘kara da cewa “Ai ita ‘yar gata ce sai a mi’ka ta gurin uwar
mijinta kuma uwar ri’konta mai zai dame ta?” Ba wanda ya tanka su kamar yarda
Hajiya Mama ta ro’kesu, kada suyi abinda za’a tafi dasu a baki.
——————————————-
Gefe guda kuwa Imran yana can zaune a part d’insa, yana kallon Shaheeda da tabi ta
nad’e masa a jiki,tana kukan shagwa’ba, zuciyarsa har ta fara tunzira da rashin
ha’kurinta.
A zafafe ya janye jikinsa cikin kaurara murya yace “Wai Shaheedah ya kike so nayi
ne? For Goodness sake, nace miki nima ba a son raina aka yi aurennan ba, ba kuma a
son raina ta tare ba, ki barni mana kiga hukuncin da zan d’auka.” Cikin Muryar kuka
tace “To kada ka kula ta please!” Tsaki yaja yana zabga mata harara “In kula ta
ince mata me? Wannan yarinyar ‘karama kada ki sa wa zuciyarki ma banzan tunanin
nan, ki barni na san yarda zan ‘bullowa lamarin.” Shaheedah ta shafa gemunsa tana
murmushi, Hankalinta kam yanzu ya kwanta.
Duk bugun da dangin amarya su kayi, a ‘bangaren uwargida ba’a bud’e ba, hakan yasa
aka sadata da nata ‘bangaren ko bakomai dai sun fita ha’k’kinta.
Masha Allah Aljannar Duniya. Haka kowa yake cewa idan ya shiga part d’in Shatun
Mommah, yayi matu’kar kyau iya kyau. parlour ‘karami daga farko da bedroom d’aya da
suka ji turkish furniture, sai kuma ka shiga wani Babban parlourn shima mai d’auke
da Royal furnitures complete set da dinning set duka iri d’aya Golden and Milk
colour,curtains d’in parlourn da kujerun irin d’aya. Ga manyan turkish carpets
malale a kowacce kusurwa. Bedroom d’in irin kayan parlourn ne da alama haka suka zo
a set. Sai kitchen shima Babba ne sosai da store a cikinsa,komai na kitchen d’in
black and white ne, hatta tiles da wall tiles da cabinet d’in. Kai su Mommah sun yi
‘ko’kari sai dai muce Allah ya ‘kara zumunci.
Yarda ‘kasa yake haka sama yake sai dai shi sama bed roon uku ne da kuma terrace a
saman gidan, saman ma ya sha turkish furnitures da Royal furnitures, adon Blue and
Golden, d’ayan parlourn kuma Black and white.
Ko makaho ya shafa ya san part d’in Shatu yafi na Shaheedah komai da komai, babu ma
had’i.
Duk ‘yan kai amarya suka watsa ya rage daga Dada ‘yar zaman d’aki sai Shatu. Babu
abinda ya dameta tana zaune tana ‘karewa d’akin kallo, wani farin ciki yana ratsa
ta, a zuciyarta tana tunanin wai ita dai Shatu, Shatun ‘kauye Shatu mai idon mujiya
ta ‘kauyensu itace Allah yayi wa Gam da katar da alheri haka, kuka d’aya take na
rabuwa da Mommah da kuma tunanin kada Imran yayi mata irin abinda aka yiwa ‘yar
gidan mai gari da ba abinda zai dameta.
Dada tun tana mitar rashin shigowar ango har ta gaji ta fara gyangyad’i, ita kuwa
Shatu ba abinda ya dameta ya shekara ma bai shigo ba matsalarsa ce. Ta shige
had’ad’d’en toilet d’in ta tayi wanka tayi brush, sannan ta fito tayi shirin barci
dama tayi sallahr ta. Ta you kwanta a gefen da Dada take kwance a gadon.
Cikin barci taji Dada ta d’aka mata duka “Ke tashi lusarar banza la’ilahailallahu
mai zan gani haka? Don ubanki ina mijinna ki kika zo nan kika baje kina barci, ko
kazar baki je kin kar’bo ba Muhammaurrasulillahi.
Shatu dai ranta a ‘bace take kallon Dada tace “Don Allah ki ‘kyaleni nayi barci
na.” “Wallahi kuwa ba dai anan ba, ba zaki saka mu kwana mala’iku suna tsine mana
ba, maza tashi muje shi kuma inji dalilinsa na ‘kin zuwa siyan baki,ko kuma kazar
yaka mana ba’kin cikin muci?” Shatu ta mi’ke tana zira Hijabinta. Murya a cunkushe
tace “Ni fa Ina da test kuma Mommah tace kada na sake na shiga d’akinsa.” Dada ta
zuba mata dundu “Mommo nace ba Mommah ba ka ji min ja’irar yarinya, ita Mommahn
zata ceceki a kabari ne idan ana jibgarki? Wuce muje.”
Dole ta bita suka fita babban parlourn da zai sada su da ‘bangarensa kamar yarda
Anty Hafsa ta nuna mata.
Da hannu ta nunawa Dada ‘kofar murya na rawa tace “Ga ‘kofar nan sai ki buga ya
baki kazar muje mu kwanta.” Dada kuwa ta hau bugu.
Cikin barci yaji bugun yayi yawa da kyar ya janye Shaheedah da take barci
peacefully, ba tare da tunanin satar kwana su kayi ba. Ya fito yana kallon Agogo
‘karfe 2:45pm. Ya ware ido yana tunanin waye da tsohon daren nan?
Yana bud’ewa idanunsa ya sauka a kanta ita da Dada. Fuska a d’aure yace “Lafiya?”