MY ENEMY BOOK 2 by Asmeetah Writer
MY ENEMY BOOK 2 by Asmeetah Writer
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
STEP TWO
1 and 2
ƘASAR JIDDER✈️
Murmushi Roshan ya yi tareda faɗin "Uncle kayi haƙuri wallahi abubuwan ne suka
cakuɗe mana..."
Mai martaba yace "daman nasan abinda zaku ce kenam ai, toh gaskiya ku
gyara domin zumunci yanada kyau...."
Ɗan ɗago da kansa Roshan ya yi daga bisani yace "am sauran kwana biyar
yanzu, amma Ni kaɗai ne mai yin Auren banda twins..."
Mai martaba kallon yanda Uncle Deen yake yayi tareda faɗin "why?
Razhdeen!..."
Ɗagowa Uncle Deen yayi shima idonsa akan mai martaba ya ce "Uncle!..."
Mai martaba yace "naga tinda na fara magana baka ce komai ba, kai meye zai
hanaka yin Auren?..."
Kafin mai martaba ya iddasa maganarsa sai ji sukayi Hajiya Maamie ta tari
yawunsa da cewa "ya zaka tambaye shi alhalin ku kuka hanashi...."
Duk ɗagowa sukayi suna kallon ta cike da mamaki ko sallama batayi musu ba,
kuma da alamun laɓe tayi tana jin duk maganganunsu.
wani irin harara ta wurga masa cike da takaici take faɗin "ai ba buƙatar
yin sallama tinda ana shirin watsa mun ƙasa a ido,
fisabilillah mai martaba saboda rashin gaskiya irin taka mun gama tsaida
magana akan cewa ku haɗa Razhdeen da Ramlat in yaso ayi bikin rana ɗaya duk gaba
ɗaya, amma shine yanzu kake tambayarsa wai meye zai hanashi Aure? toh wa kuke
tunanin zai Aura kenam?...."
Mai martaba girgiza kai yayi sannan yace "Maamie kenam! shin kin
tsaya Kinga ƙarshen wasan ne?
ki tsaya kiga gudun ruwana mana, Nima abinda nake shirin yi kenam, nima so
nake a haɗa bikinsu gaba ɗaya..."
Hajiya Maamie ɗaga kafaɗa tayi tareda cewa "gwara kam in har anason
ganin farin ciki na, zanje na turo Ramlat tazo su gana da juna..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta.
Mai martaba sunkuyar da kai yayi ƙasa yana jinjina irin ƙarfin hali na
Maamie.
Razhdeen gaba ɗaya bai gama fahimtar abinda suke nufi ba, juyowa yayi ya
kalli Roshan, cikin sa'a kuwa shima Roshan Uncle Deen ɗin yake kallo, haka suke
kallon juna cikin rashin fahimta abinda ake nufi da haɗa Razhdeen da Ramlat,
Ganin basu fahimci ina aka dosa ba yasa duk suka maida kallonsu kan Mai
martaba wanda kansa har zuwa yanzu yake durƙushe,
Roshan ne ya buɗi baki yace "Uncle me yake faruwa ne kam? naga kana
cikin damuwa..."
Mai martaba ya ɗago a hankali yana binsu da kallo yace "shin Razhdeen
yanada wacce yake so?..."
ya tambayi Roshan ne saboda yana ganin shi zaifi bashi amsa akan lokaci,
Roshan yace "gaskiya Uncle banida masaniya akan haka amma ka tambaye shi
mana gashi nan, nidai a sanina dashi bai taɓa yin budurwa ba kuma har zuwa yanzu
babu wata..."
Kafin ya ƙarasa mai martaba ya dakatar dashi da cewa "ya isa haka Roshan,
kowa yasan halin Razhdeen ba kula mata yake ba,
Razhdeen abinda nake so dakai shine za'a haɗa bikinku gaba ɗaya ayi kai da
Roshan, tin ba yau ba na rigada na maka matar da zaka Aura tinda kai bazaka iya
zaɓo ba...."
ya ƙarasa maganar idonsa akan Razhdeen wanda shima mai martaba yake kallo
fuska a murtuƙe ba bu Annuri..
"Who is her?.."
yayi tambayar a taƙaice.
Mai martaba yace "ƙanwar matata Maamie wato Ramlat, tana zaune anan gurin
mu..."
girgiza kai Razhdeen yayi zaiyi magana saiga Ramlat ta shugo da sallama a
bakinta tana ɗauke da tray ɗin kulolin abinci, ta ajiye akan glass table dake
tsakiyar falon, ba jumawa kuwa saiga kuyange su uku sun shugo ko wacce tana ɗauke
da tray ɗin kayayyakin abinci aciki,
suna ajiye wa suka fice, Ramlat ce ta zauna a ƙasin carpet tana gaishesu,
Roshan ne kawai ya amsa shi kuwa Razhdeen ko kallon yanda take beyi ba, tasha
ƙwalliya sosai sai fidda ƙamshin turare take tana satar kallon Roshan,
ita har cikin zuciyarta tafi son Roshan saboda ya kasance mutum mai faram-
faram babu ruwansa kuma ko wanne acikin su da kalar tsarin kyan da ALLAH yayi masa,
babu wanda yafi wani kyau, sanin dai-dai sai ALLAH.
Mai martaba idonsa akan Razhdeen wanda kansa akan wayar hannunsa yanata
pressing ko ɗagowa baiyi ba,
Mai martaba yayi ƙarfin halin cewa "Razhdeen ganan Ramlat wacce ake son
haɗa ku, dan Allah ka dubeta da kyau kar ka watsa mana ƙasa a ido, Ni na zaɓa maka
ita, ban taɓa neman alfarma a waranka ba sai yau...."
Gira a haɗe Razhdeen ya ɗago cikin ɓacin rai yake kallon Mai
martaba murya ciki-ciki yace "Uncle alfarmar mai kake so nayi maka?..."
Mai martaba yace "akan Auran wannan yarinyar..." ya ƙarasa maganar yana
nuna Ramlat da yatsa, sannan ya kuma cewa
"Na rigada nayi magana da Abbanku kuma ya amince mun akan wannan batun, mun rigada
mun tsayar da maganar rana yata yau Insha ALLAHU za'a ɗaura muku Aure gaba ɗaya,
sannan itama Ramlat zata biku can Nigeria ta zauna har zuwa ranar bikin..."
Gaba ɗaya ran Razhdeen ya gama ɓaci har eyes ɗinsa sun kaɗa sunyi
jawur, cikin ɗaga murya yace "Umarni ake bani ko kuma Zaɓi?..."
shi kansa Mai martaba sai da ya ɗan tsorita ganin yanda yanayin
Razhdeen ya chanza lokaci ƙanƙani,
Roshan ne yayi saurin dafa kafaɗarsa yana ɗan bubbuga shi kaɗan alamar
rarrashi domin yasan halin ɗan uwan nashin muddin ransa yakai maƙura toh zai iya
yin rashin kunya a kowa ma, kuma gashi suna matuƙar girmama mai martaba,
Razhdeen jin anyi shuru ba'a bashi amsa ba ya kuma cewa "ina tambayarku
Umarni kuke bani ko kuma zaɓi?..."
shi kam mai martaba ido kawai yabi su dashi, shima har cikin zuciyarsa
bason haɗin nan yake ba, zaiyi ne saboda matarsa Maamie amma yasan Razhdeen in har
ya bijirewa abu baya taɓa jin ƙira.
kallon Ramlat yayi sannan yace "toh Kinga a gaban ki abinda ya faru, da
haka zaki zauna dashi?..."
Ramlat tana kuka tace "Abul wallahi Aunty Maamie ce take son haɗin nan Ni
Yaya Roshan nake so, daman nasan Uncle Deen bazai taɓa sona ba..."
Jinjina kai Mai martaba yayi sannan yace "Roshan kuma kinga da matar da
zai Aura..."
"Dan ALLAH Abul wallahi inason Yaya Roshan mezai hana ku Aura masa mata
biyu Ni da wacce yake son Aura, wallahi zan zauna dashi a haka..."
Shi kuwa Razhdeen niyarsa shine yabar ƙasar gaba ɗaya, daƙer Roshan yake
rarrashinsa yana so ya shawo kansa amma fur Razhdeen yaƙi,
sai cewa yake "Please inason komawa Nigeria daga nan zan wuce U.S,
saboda an raina mun wayo Ni za'ayi wa Auren dole? hakan ma wannan kucakar
yarinya marar class, a gabana Auntynta take wulaƙanta Uncle amma a haka zan Aure
ta? Impossible..."
Roshan riƙe hannayensa yayi yana bashi haƙuri game da cewa "My Man ka
kwantar da hankalinka, Insha ALLAHU wannan haɗin bazaiyu ba, saboda Nima kaina
yarinyar bata mun ba, sannan ga ɗabi'un Yayarta marasa kyau amma inaso komai ka
bishi a hankali, ka dubi darajar Uncle shima kamar mahaifi yake a wurin mu, Uncle
ba kamar Abbah bane yanada sauƙin kai, muje ka same shi muyi magana ta fahimta
sannan ka nuna masa cewa kanada wacce kake so kaima..."
Daƙer Razhdeen ya haƙura suka koma cikin masarautar, kai tsaye part ɗin
da aka tanadar musu suka wuce domin a halin yanzu Razhdeen baya buƙatar yin wata
magana ta fahimta...
INDO tana zaune kan sallaya da carbinta a hannu tana lazumi ta fara jin
kururuwar Maamie daga Falo sai balbala masifa take,
Dasauri INDO ta tashi a tsorace ta fice domin ganowa abinda ke faruwa,
tana fita Falo ta tarar da mai martaba zaune akan sofa ita kuma tana
tsaye a kansa baki ya gagara rufuwa, ga kuma Ramlat itama zaune a one seater ta
ɗora hannu akan goshi, gaba ɗaya ta tsani ganin Maamie tana masifa a mai martaba
wannan abun kunya,
a fusace Maamie ta kallo yanda take tsaye da zureren hijab ɗinta, ta ɗago
yatsa tana nuna ta dashi tace "ki maida hankalinki bada ke nake ba, ina ruwanki da
shiga shirgina, tin ba yau ba na gaya miki idan ina magana da mijina ki daina
shiga...."
Maamie cikin tsawa tace "toh babu ruwanki, idan kinji abinda ke faruwan
akwai abinda zakiyi ne?..."
INDO ta girgiza kai tareda cewa "a'ah kiyi haƙuri, naga bai dace ki
tsaya a kansa kina ɗaga masa murya bane..."
Kafin ta ƙarasa maganar Maamie ta malmalo wata ashar ta maka mata tareda
faɗin "kije kiji da wannan tsohon uban nakin da yake gab da mutuwa akan kujerar
mulki ya gagara sauƙa saboda kwaɗayin abun duniya..."
Mai martaba ne ya buɗi baki yana cewa "kibi duniya a sannu Maamie..."
Harara ta watsa masa tareda faɗin "Duniya kam gani a cikinta ta ishi kowa
ma bani kaɗai ba,
Kuma wallahi kusan yanda zakuyi ku Aura wa Razhdeen Ramlat tin kafin ajiyo
kan mu, kana maganar wai tace Roshan take so yooo banda na ga, mai Roshan yake da
shi, wanda ko rabin kamo ƙafar Razhdeen baiyi ba a arziƙi..."
Sai a yanzu Ramlat ta buɗi baki tace "nifah Maamie Yaya Roshan nake
so...."
Maamie a fusace ta miƙar da hannu tana danƙwalonta tareda faɗin "ke kin
ci ubanki, ina samar miki waran da zakiji daɗin rayuwa ki ƙwanta a dukiya ki tashi
a dukiya amma ke kina Kai kanki wurin wahala, mai za'ayi da kishiya banda dole,
ALLAH ya tsinewa wanda ya ƙirƙiri sunan kishiya babu daɗin ji,
Haka zamu ƙare rayuwar mu a zuwa kan kishiya?
lokacin da mai martaba zaiyi Auran farko mu biyu ya haɗa ya Aura lokaci guda
Ni da Maimuna wacce ba'a san duniyar da take ba yanzu, kafin daga baya ya ƙara
Auran wannan matsiyaciyar,
shine ke kikeso kema ayi miki irin nawa? kamar wasu marasa gata da farin
jini,
toh bazaiyu ba Razhdeen ɗin zaki Aura..."
Mai martaba hannu yasa ya dafe saitin zuciyarsa jin an ambaci sunan da
yake tada masa da hankali wato Maimunatu...
Ana cikin wannan halin saiga Razhdeen da Roshan sun shugo falon,
duk maganganun da Maamie tayi suna jinta,
Roshan ne yazo har gaban Maamie ya tsaya yana mata kallon ƙurilla daga
bisani ya cire glass ɗin kan dara-daran idanuwansa, ya soma magana cikin ɓacin rai
yake faɗin
"Alhamdulillah tinda ALLAH ya hore mun abinda zan rufawa kaina asiri,
dukiya inada su dai-dain gwargwado kuma fiye da yanda kike tunani, domin da za'a
haɗa kanki dana danginku gaba ɗaya bazaiyi kwatan yawan adadin dukiyarda nake da
shi ba, naji ɗan uwana Razhdeen ya fini yawan dukiya amma inaso ki sani cewa ko
a yanzu nace ya bani rabin dukiyarsa ba musu zai bani saboda mu ɗin gudan jini ne,
nashi nawa ne haka kuma nawa nashi ne,
Ƙanwarki kuma ki sanar mata cewa koni Roshan bazata samu shiga ba
balle my twins da ko ƴar aiki bazai ɗauketa ba balle a matsayin mata..."
Murmushi tayi tana yatsina fuska tace "Hmmm! Roshan kenam, Ni baka
isheni kallo ba, bata kai nake ba ka matsa ka bawa ɗan uwanka wuri mu magantu..."
Roshan ɗaga kafaɗarsa yayi tareda faɗin "okay fine! Idan kikayi dashi
tamkar kinyi dani ne..."
Maamie itama kallonsa take fuska a sake sai faman sakin murmushi take
tace "Razhdeen inaso muyi magana ta fahimtar juna, kaga yanzu mun zama ɗaya
Ramlat tamkar ƴar uwarka ce, kuma ka dubeta ita ɗin marainiya ce bamuda uwa babu
uba, dan ALLAH ka temaka ka Aureta ko zata samu farin ciki,
Ni zanyi iya ƙoƙarina naga ka Aureta tinda wannan matsolon Sarkin ya
kasa aiwatar da komai...."
Saida ta kammala zantuttukanta tass sannan tayi shuru tana son jin
amsar da zai bata, itadai addu'arta shine yace ya amince..."
Kafin ta ƙibta ido har ya kai hannu ya zabga mata wani irin gigitaccen
marin da bata san lokacin da ta dungura kan kujera tayi tsalle ta faɗa bayan
kujerar ba,
Maamie tana kwance a bayan kujera shuru bata ɗago ba har zuwa wannan
lokacin,
Mai martaba murya na kakkarwa yace "Razhdeen meka aikata haka? shin
bakada hankali ne? Matata ce fah? ka manta yanda nake a wurinka?..."
Cikin ɓacin rai Razhdeen yake kallonsa tareda faɗin "bana juran
ganin irin waɗannan dabbobin matan, saboda haka ne yasa bana zama inuwa ɗaya da
matar Abbanah saboda nasan wata rana zan iya illata ta, duk da yanzu naji labarin
basa tare, don haka itama wannan tabi a hankali kafin nabar ƙasar nan..."
yana kammalawa ya juya zai fita shima Roshan bin bayansa yayi zasu fice
a tare,
Juyowa Roshan yayi yana kallon Mai martaba cikin tausayawa yace "Uncle
akwai ɗauri a jikin ka Please ka nemi maganin karya asiri domin ba haka aka barka
ba, Uncle wanda na sani a baya bakai bane yanzu, duk zafin ran Abbanah baiyi ka ba
amma yau kaine nake gani haka mace tafi ƙarfinka? Amma zan tayaka da addu'a karka
damu...."
yana kammalawa shima ya fice, kai tsaye part ɗin su suka nufa...
Mai martaba girgiza kai yayi domin al'amarin yana shirin fin
ƙarfinsa,
kallon yanda INDO take yayi sannan yace "ki kai musu abinci basu ci komai ba
tinda suka zo, sannan ki lallamesu su ci karsu zauna da yunwa..."
yana tsaye yaji kukan Ramlat tana faɗin "Abul ta mutu kazo ka
duba ta bata motsi wayyo Allah nahhhh..."
tana kuka sai faman jijjigata take amma Maamie ko motsi babu, Saida mai
martaba ya zagayo bayan kujerar ya tarar da ita kwance ga fuska har ya kumbura,
a hankali ya furta cewa "kije ki ɗauko mun ruwan sanyi.."
Da gudu Ramlat ta miƙe taje frig ta ɗauko jug mai ruwan sanyi ta kawo,
ana watsa mata kuwa ta farfaɗo tana sauƙe numfashi sama-sama,
tareda faɗin "aina nake? ina ne Nam? gida nake son zuwa.."
Daƙer mai martaba ya ɗagota sannan ya wuce da ita bedroom ɗinta tana
sumbatu cikin rashin hankali domin ji take kanta yana juyawa bata san a yanda
hankalinta yake ba, da haka aka shige da ita ciki...
*A TANTANCE MUN*
*SHIN DA HAJIYA MAAMIE DA KUMA HAJIYA KILISHI WACCE TAFI WULAƘANCI????*
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
STEP TWO
sorry for the mistake a farkon step two nasa 51 to 52 maɗorin ƙarshen step
one neh, naga wasu suna mun complain akan anyi musu nisa sosai a step two, toh ba
haka bane farkon ne, but yanzu zamu cigaba akan page 3 and 4 na step two
*Chapter* 3 and 4
Mamie kamar wata zautacciya haka ta rikice bata san yanda kanta
yake ba,
lalume ta fara yi tareda faɗin "ina Ramlat? Ramlat kina ina bana gani
dai..."
Ramlat ce ta zauna gefenta a bakin gado ta riƙo hannayenta tana faɗin "Aunty
gani nan dai..."
Maamie tana kuka tana cewa "duba mun akwai fuska a jikina?.."
Ramlat tace "akwai fuska mana"
Maamie ta kuma cewa "ki duba da kyau shin ba'a rabe mun kaina da gangan
jikina ba? yanzu haka kina kallon fuskata? naga duhu nake gani sannan banji alamun
kai a jikina ba..."
Ramlat tace "haba Maamie ai duk ke kika jawo haka, gashi kema Uncle
Deen bai barki ba balle Ni,
shin har yanzu kina kan bakarki ne? gashi kinyi mun biyu babu shima Yaya
Roshan ɗin yana shirin kuɓuce mun..."
Maamie tace "kina nufin kice ba Razhdeen zaki Aura ba? toh wallahi
tallafi ko naman jikina yake yanke wa kullum saina sa ya Aureki dolensa..."
"Hmmm! kece a wahalai nidai zanbi tawa hanya yanda bazan jawo a illatani
ba...". a cewar Ramlat.
Maamie cewa tayi "au ina nema miki gidan daɗi ke kuma kina mai watsa mun
ƙasa a ido?..."
cikin ɓacin rai Ramlah tace "shikenam Aunty Maamie kiyi duk yanda
kika ga ya dace..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta,
Maamie cikin ɗaga murya tace "Ai kuwa zanyi abinda ya dace idan naje wurin
Boka matsagwal, wallahi sai Razhdeen yazo yana binki har da tsuguno..."
ta ƙarasa tana jan numfashi sama-sama ga fuska yanda ya kumbura suntum har
shatin photon hannunsa ake gani akan fuskar...
ƳAR AMANA tana zaune a yanda suka saba hallaruwa tana riƙe da jitar ta sai kaɗawa
take,
Dake duk mutanen wurin ba wanda baya jin daɗin sautin jitarta,
tana cikin wannan halin sai ga wata danƙararriyar mota baƙa ƙatuwa wasu matasa ne
su biyu suka fito suna rufe da fuskokinsu da baƙar hula suka yo kan Ƴar Amana dake
zaune,
duk waran babu wanda bai tsorita da ganinsu ba domin har da masu
riƙe da bindiga, ɗagowa tayi tana binsu da kallo kafin ta ankara har sun finciko
hannunta, sun ɗagata sama tana bubbugan bayansu haɗe da shure-shure amma ba bakin
yin ihun,
kafin kace mai tsofin wurin sun haɗe waran da kururuwan "wayyo ɓarayi
mun shiga uku, akawo mana ɗauki ƴan fashi...."
Nan danan suka ja motarsu a ɗari suka bar wurin,
daman sun juma suna target ɗinta tin barinta a hannunsu ogansu ya hura musu
wuta akan sai sun nemota sai yau Allah ya bada sa'ar kamata...
Cikin Daji aka nufa da ita already sun rufe mata fuska da baƙin ƙyalle..
🤏Baiwar ALLAH tin da Aunty Yolash tazo take faman gyarata irin
gyaran Amare duk da bata son Auren ko kaɗa, har ila yau fuskar Razhdeen ne yake
mata gizo, wani sa'in sai taji kamar ta fita taje ta nemo Razhdeen ta roƙe shi
akan ya Aureta,
kwata-kwata batada wani sukuni, ba wai bata son Roshan bane Ita dai
zuciyarta Razhdeen ya zaɓa mata kuma shi yafi dacewa da ita amma babu yanda ta
iya...
Minal kuma tana can gidan Razhdeen ita da Mohandas ita take
masa girki duk da bata iya sosai ba sai ya saka mata hannu, wani sa'in kuma shi
yake yi da kansa,
Soyayya iya soyayya suna shanta sun fahimci juna sosai domin har Mohandas ya
amince akan cewa bayan bikin Roshan shima zai musulunta sannan a ɗaura musu Aure a
ɓoye in har Abbah bai amince ba....
Maamie tace "naje wurin Boka ya bani turaren bita zaizai kuma ba makawa
asirin nan saiya kamashi domin Boka bai taɓa yin rashin nasara ba..."
Ramlat tsayawa tayi tana kallonta cike da mamaki take girgiza kai
sannan tace "wai Aunty Maamie bazaki daina zuwa wurin bokan nan ba koh? meye
amfanin haka? toh Ni gaskiya ki daina sakoni a lissafin waɗanda boka zaiyi musu
aiki...."
ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki...
Maamie ta ƙafeta da kallo tareda riƙe haɓarta tace "iyyeeee! Lallai yarinyar nan
kema na kusa nayi aiki akanki indai zakina bijire mun wallahi, kuma dole sai kinyi
aikinda Boka yace kiyi aikin banza kawai, wawiya arziƙi na biyoki kina guduwa masa
tsabar shirme irin nakin,
dallah malama tashi ki shashshafa turaren ki kai musu abincin breakfast tin
kafin wancan matsiyaciyar ta kai musu uwar shishshigi..."
"Toh naji..."
A cewar Ramlat wacce take ƙoƙarin tashi, tayi duk abinda Maamie tasa ta wato
turaren nan haka yake tashi yana bada zazzaƙar ƙamshi, haka suka fice a tare kai
tsaye kitchen suka nufa, suka tarar an kammala girki an saka musu a kuloli na
musamman,
Ɗaukar kayan girki tayi ta nufi Falo tana shirin ficewa, saiga INDO
daga upstairs tin kafin ta ƙarasa sauƙowa tace "Ramlat ina zaki da kulolin
abinci?..."
Maamie wacce take zaune a kujerar Falo ta ɗora ɗaya akan ɗaya
sai wani irin kallo take watsawa INDO, baki a murguɗe tace "yanda kika aiketa uwar
shishshigi, kina so a baki ki kaiwa dangi ne? don naga akwai tamowa a jikinsu..."
Maamie sake baki tayi tana mata kallon mamaki, tasa hannu a saitin haɓarta
tana faɗin "iyyeeee! Lallai matar nan, yanzu har kina da bakin da zaki gaya mun
magana? Ahh lallai wuyanki ya isa yanka, tabbas saina ƙara miƙewa tsaye a kanki
ƴar banza..."
INDO kallonta kawai take cikin rashin fahimtar abinda take nufi,
Abinda Maamie take nufi shine akwai sihirinda tayi mata kuma yana shirin
karyewa dole sai ta sake zuwa gurin bokan ta...
Ramlat ganin bazata iya tsaya sauraronsu ba yasa tayi saurin ficewa
zata nufi masauƙin su Razhdeen.....
hakan na nufin tsafin baiyi aiki ba tinda so ake yaji ƙamshi shi
kuma wari yaji, an samu matsala kenam...
Haka ta shige Falo tana kuka, kai tsaye bedroom ɗin Maamie ta
wuce ganin bata tarar da ita a falon ba,
Maamie tana ganinta a cikin wannan halin tayi saurin dafe ƙirjinta
tareda faɗin "na shiga uku kar dai kice an samu matsala..."
tana kuka tace "naga korata yayi cikin fushi, Ni Maamie nace miki mu rabu
da Uncle Deen ɗin nan babu wani tsafin da zai kama shi...."
kafin ta rufe baki Maamie tayi saurin katseta da cewa "yi mun shuru
dallah! ai wannan tsoron nakin ne zai jawo mana matsala, zakiyi abu amma bazaki
sake jiki kiyi ba ƴar Banza kawai..."
Ramlat tace "toh Maamie ya zanyi, yanzun meye mafita? gashi gobe
asubanci zasu yi su koma Nigeria..."
Maamie tace "wa? ai ƙafarki ƙafarsu dake zasu tafi kuma dole Abbansa nasan
saiya tilasta shi akan ya Aureki tinda yana jin maganar mahaifinsa..."
Maamie tace "eh mana, kuma da daddare inaso kije ki kusance shi da
waɗannan ƙananun kayanki nan masu bayyanar da surar jiki, amma ki tabbatar Roshan
baya ɗakin..."
Zaro ido Ramlat tayi tareda dafa ƙirjinta tace "nashiga uku Maamie
wallahi kasheni zaiyi, ke baki san halin Uncle Deen ba koh?..."
Maamie a fusace tace "Dan buro ubansa idan yafi ƙarfin kowa ai baifi
ƙarfin makircin mace da surar jikinta ba..."
Maamie ta kuma cewa "kiyi duk abinda nace, kai inta kama kiyi tsindir
a gabansa..."
Haɗiyar yawu Ramlat tayi tareda cewa "tam! I'll try my best..."
Roshan yace "ya shiga bathroom yanzu ina tunanin wanka yake yi..."
Mai martaba yace "Roshan yanzu Abbanku yake cemun tareda Minal ku ka
taho, ina kuka barta?..."
Saida ƙirjin Roshan ya buga jin asirinsa ya tonu, baiyi tunanin Abbah zai
sanar wa Uncle ba,
Mai martaba kallon ƙurilla yake masa yace "ina jinka banason rashin
gaskiya fah..."
Suna fita Ramlat tayi saurin shugowa daman ta daɗe tana tsaye
tana jiran fitarsu,
tsayawa tayi tana kalle-kalle a ɗakin kamar wani baƙonta, tana sanye da
Black net shirt wanda bai rufe mata cibiya ba, duk ana kallon surar jikinta ba
tareda tasa ko breziyya ba,
sai wani ɗan gajeren wando wanda ya tsaya a iya cinyarta,
Ga daman tanada dirin jiki...
Saida tayi kusan minti talatin tana tsaye kafin Uncle Deen ya
fito daga cikin bathroom ɗaure da white towel a kunkuminsa,
Ganinsa yasa ta zaro ido waje ta ƙame a wurin ganin yanda tsarin surar
jikinsa yake, ga gargasa a kwance luf-luf kamar gashin jarirai, yanda kasan ba
mutum ba domin Ni kaina bazan iya tsara muku yanda surar jikin Razhdeen yake ba,
Ga farin fata mai ɗauke ido har wani shining yake, tsayi kuwa ba'a magana
domin idan ya jeru da Ramlat zata zamana a iya kunkuminsa zata tsaya, bugu da ƙari
ma ga ƙira mai kyau haɗi da murɗaɗɗen jiki, ƙirjinsa kuwa sai ya haɗe mata biyu
zuwa uku aciki tsabar faɗi kamar tray..
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
STEP TWO
5 and 6
"Roshan ka daina mun ƙin-ƙinda ka fito fili ka sanar mun abinda ke faruwa, kunyi
wa Abbanku ƙaryar cewa kun taho da Minal Ni kuma ban ganku da ita ba, shin ina
kuka barota?...."
Roshan yana sunkuye da kai ƙasi tinda Mai martaba ya fara magana
bai ɗago ba,
Saida mai martaba ya sake ƙiran sunansa ganin ya tafi dogon tunani...
Girgiza kai Roshan yayi tareda faɗin "Uncle ana bikin ƙawarta ne shine ta
tsaya a wurin kuma itace babbar ƙawar Amarya..."
Jinjina kai Mai martaba yayi yace "duk alamun rashin gaskiya sun
bayyana akan fuskarka Roshan, babu gaskiya acikin lamarinka amma ban sanka da
wannan halin ba, Roshan baka ƙarya meyasa yanzu?..."
Gaba ɗaya gumi duk ya wanke masa fuska kamar wanda ya fito daga
cikin rijiya,
wani irin yawu ya haɗiya wanda ya tokare masa maƙogaro,
tsoronsa idan har Abbah yasan cewa Minal tana tare da Marshall toh kashinsa ya
bushe, motsi yake da lips ɗinsa a hankali ya furta cewa
"Uncle ka sanar wa Abbah cewa bada Minal muka zo ba?..."
wani irin sauƙe nannauyar numfashi Roshan yayi yana faɗin "thank
God,
sannan yace Uncle zan sanar maka duk halin da ake ciki..."
Nan Roshan ya sanarwa mai martaba halin da ake ciki na Minal da kuma
Mohandas..
Dogon numfashi mai martaba yaja sannan yace "TOH banda abinka Roshan meye
zaka iya a wannan lamarin? kadai san halin Mahaifinku idan yace baya son abu TOH
kuwa duk duniyan nan bamai sashi yayi, sannan kuma shi Mohandas so kake ya
bijirewa iyayensa kenam akan mace?..."
Roshan idonsa akan mai martaba yace "Uncle ina tausaya musu ne, wallahi
suna son junansu kuma shima Mohandas ya amince akan zai musulunta, nasan idan ya
karɓi musulunci Abbah bazai hanashi Auren Minal ba..."
Murmushi Mai martaba yayi yace "yaro yaro ne, Roshan har yanzu da ƙuruciya
akanka, kana nufin kace Abbah zai bawa Mohandas Auren Minal ba tareda iyayensa
suna so ba? ko kuma Abbah zai ɗauki yarinya ya bashi ba tareda iyayensa sun sani
ba?
TOH bari kaji shi Aure ya wuce yanda kake tunani, ina mai sanar maka cewa
Mahaifinku bazai taɓa yadda da wannan al'amarin ba sai dai idan har iyayen Yaron
suma sun Aminta nan ne za'ayi abu cikin lumana..."
Roshan Dafe goshinsa yayi yana hura iskar bakinsa tareda jinjina
maganganun mai martaba,
Ɗagowa yayi yana faɗin "yanzu ya zamuyi Uncle?..."
Roshan yace "Uncle inason jin daga bakinka duk yanda kace hakan za'ayi..."
Mai martaba yace "sai dai a samu iyayensa ayi magana cikin hankali idan
su bazasu musulunta ba to subar yaronsu ya musulunta inyaso sai a Aura masa
yarinyar..."
Roshan jinjina kai yayi sannan yace "tabbb! Uncle ai gwara tawa
shawarar zai iya yuwa, amma nasan iyayen Mohandas yanda suke riƙe da ƙarfin
Addininsu bazasu taɓa yadda ba wallahi...."
Mai martaba ne ya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa tana ringing,
Dubawa yayi yaga number Abbah ne, Saida ya kalli Roshan tukun yace
"shine..."
Zaro ido Roshan yayi ya haɗe hannayensa biyu alamar roƙo kar Mai
martaba ya gayawa Abbah halinda ake ciki,
Mai martaba ne yasa wayar a speaker yanda Roshan zaiji duk tattaunawar
da zasuyi...
Mai martaba ne yayi sallama tareda faɗin "na gaida mazan pama..."
Abbah yace "yadai muna cikin waya ka katse ƙiran?..."
Mai martaba yace "wallahi naɗanji hayaniya ne shine naje dubowa meke
faruwa..."
Abbah yace "okay! yakamata yaran nan su dawo gida yau saboda hidimar
bikin da za'ayi yau sauran kwana huɗu..."
Mai martaba yace "yau kuma? sai dai gobe su taso da sassafe, saboda har da
matan gidan gaba ɗaya zasu tafo..."
Mai martaba yace "a'a Ni sai ana gobe ɗaurin Aure zan taho,
Amma Roshan shi kaɗai za'a Aurar ne? mezai hana a haɗa da Razhdeen?..."
Abbah yace "kabar zancen Razhdeen shi da bai tsayar da kowa ba, ai
baza'a Aura masa babu ba..."
Mai martaba yace "hakane amma maizai hana a haɗa shi da Ramlat ƙanwar Matata
Maamie naga tana sonsa sosai..."
Abbah ne yace "shi ɗin yana sonta ne? In har yana sonta sai a haɗa
Auren gaba ɗaya, idan kuma Razhdeen baya ra'ayinta TOH gwara Abar maganar nan
saboda banason damuwa, kasan halin Razhdeen nima haƙuri nake dashi, kuma ba kowace
mace ce zata iya zama dashi ba in har ba sonta yake ba, domin ita zata sha wahala
Ni kuma hakan ne banaso..."
Mai martaba dogon numfashi yaja tareda faɗin "toh maganar gaskiya dai
Hajiya Maamie ce take son haɗin nan amma shi Razhdeen baya so domin jiya ma Saida
suka samu matsala har Saida Razhdeen ya mareta a take ta sume a wurin..."
Mai martaba yace "a'ah ita kanta Uwar yarinyar, kasan Razhdeen bashida
haƙuri kuma baya son raini ita kuma Maamie rashin kunya da wulaƙanci..."
Abbah yace "kana nufin kace matarka Razhdeen yasa hannu ya mara?..."
Mai martaba yace "No bawai na gaya maka saboda ranka ya ɓaci bane i
just tell you that haɗin Auren bazai yu bane tinda ba son yarinyar yake ba..."
Abbah numfashi ya sauƙe yana faɗin "ba abun mamaki bane domin
Razhdeen zai Aikata, shiyasa banason tura shi baƙunta wani wuri amma zanyi maganin
shi, Please King kayi haƙuri Razhdeen Sam bai kyauta ba..."
Mai martaba yace "wallahi ko a jikina Yaya, kadai san zaman haƙuri kawai nake
da ita, ta zamo mun ƙarfen ƙafa..."
Abbah yace "kayi haƙuri idan kuka zo gaba ɗaya za'a san yanda za'ayi..."
Mai martaba yace "inda zai musulunta sai kawai a Aura mata shi..."
Abbah ya kuma cewa "Da nayi tunanin nan amma yanzu na sauya ra'ayina koda ya
musulunta ma ƴata bazata Auri jininsu ba, yanda ta fito a cikin Musulunci haka
jininta zai cigaba da gudana a cikin Musulunci, banason jikokina su kasance sunada
family christoci..."
Abbah yace "kaje ka same shi kace ya taho Nigeria yanzu yanzu inason
ganinsa..."
Kafin Abbah ya katse ya kuma cewa "inaso zanyi video call da Minal kaje
ka same ta yanzun nan..."
Roshan tashi yayi ya fara tafiya da haka yabar falon mai martaba ya
fice kai tsaye ɗakinsu ya nufa yana zuwa ya buɗe ƙofa ya shige,
samun Razhdeen yayi yana zaune a bakin gado ya shirya tsab cikin ƙananun kaya
ga yanda ƙamshin turare yake tashi,
Roshan yana zuwa ya juyar da wayar saitin fuskar Razhdeen,
wani irin kallo ya watsawa Roshan ganin yanda ya saita masa fuskar waya
a tunaninsa photo zaiyi masa ne, sai ji yayi daga cikin wayan ance "Minal nace ka
haɗani da ita ba wannan mai kama da mutuwa ba fuska ba annuri...."
Razhdeen idonsa akan wayar ta ciki yake kallon Abbansu, shima Abbah
kallonsa yake, daga bisani Abbah yace "kai kuma Razhdeen inaso yanzu ka dawo gida
banason dogon zance..."
A hankali yake jan ƙafa zai fice daga ɗakin kwatsam yaji Abbah yana
faɗin "dakata! dakata mun!! Ɗaga mun wayar sama saitin fanka naga abu yana lilo
kamar mutum..."
Shima Roshan ɗaga kansa sama yayi domin tabbatar da abinda Abbah ke
magana akai,
Zaro ido yayi baki a sake ganin Ramlat a ɗaure saman fanka kanta na
kallon ƙasi, sawaye kuma a ɗaure da fanka,
Saida ya nannaɗeta da zanin gado kafin ya ɗaureta sannan ya janye ta
sama, iya fuskarta ne a waje, bayan ya gama mata dakun sakwara, ba ƙaramin duka
yayi mata ba ganan hancinta yanda yake ɗigo da jini,
Dasauri Roshan ya sauƙar da kansa ƙasi yana maida kallonsa kan
Razhdeen sai yanzu ya lura da dorinar da yayi kaca-kaca a ɗakin,
Shi kuwa Roshan ya kama kunkumi kansa a sama yanda yake ta kallon Ramlat
yana tunanin ta yanda akayi Razhdeen ya ɗaureta haka, kuma alamun a sume take
domin ko motsi bata yi kodai mutuwa,
haka yake ta wannan tunanin,
Roshan sauƙe numfashi yayi yana faɗin "yanzu ta ina zan fara?..."
Saiga Maamie ta shugo baki a washe ta ɗauka cewa sun gama fahimtar
juna ne data jita tayi shuru a ɗakin,
ta shugo tana faɗin "tana inane? ha'a kodai itace a lulluɓe saman
gado, ahhhh Masha Allah tinda bacci take bari na barku karna takura muku Koh....."
Maamie tana ɗagawa ta wani sau ƙara tana dafe da ƙirjinta, ƙafafunta har
wani rawa suke, lokaci guda gumi har ya wanke mata fuska...."
Sai ga mai martaba shima ya shugo jin ihun MAAMIE yana faɗin "lafiya
kuwa meke faruwa?..."
Maamie tana kuka tace "wani irin tambaya ne wannan kana ganin sun kashe mun
ƙanwaaaa...." nan ta fashe da matsanancin kuka harda majina,
Maamie tace "kafin ka gama tambayarka Ni a Ciro mun gawar ta tinda sun
kasheta mungwaye kawai azzalumai macuta, Allah ya isana tsakanina daku wallahi...."
Mai martaba ne ya rirriƙeta yana faɗin "meye haka kike dukansa shi ba
ƙaramin yaro ba, ko ce miki akayi shi yayi mata haka? TOH gashi can kije ki same
shi ki dake shi..."
Girgiza kai mai martaba yayi yana faɗin "kaga Roshan kayi haƙuri dan
ALLAH, yanzu ya za'ayi mu Ciro ta..."
Roshan ya kalli Razhdeen sannan yace "my man ka temaka ka Ciro ta..."
Mai martaba yace "a'a! ALLAH ya huci zuciyarka Major General Razhdeen Allah
ya kiyaye hanya ya tsare rayuwarka..."
Mai martaba tsayawa yayi ya rasa yanda zai yi duk sun tafi sun barshi,
Saida yasa aka ƙira ma'aikatan mazan gidan kafin suka zo suka Cirota daƙer....
*POSTING DAYS*
*SUNDAY*
*TUESDAY*
*THURSDAY*
*FRIDAY*
*SANNAN A DAGE DA COMMENTS DOMIN SHI ZAISA A RINƘA YAWAN MUKU POSTING....*
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
STEP TWO
7 to 8
Baiwar ALLAH kuma tana can cikin ɗakinta a kwance saman katafaren
gadonta kamar mai yin Bacci, sai dai ba baccin take ba, amma idonta a lumshe suke,
Ga wata ƙatuwar waya ƙiran iPhone 15S, ƙira ake tayi ba ƙaƙƙautawa daga
wannan ƙiran ya yanke sai wani ƙiran ya sake shugowa anyi ƙiran yafi sau 15 a
lokaci guda kuma duk mutum ɗaya ne mai wannan ƙiran,
Baiwar ALLAH tana ji amma taƙi ɗaukar ƙiran domin ta rigada tasan cewar
Roshan ne mai wannan damun,
wani ƙiran ne ya sake shugowa Once takai ƙwayar eyes ɗinta kan
screen ɗin wayar ganin ROSH a rubuce kan screen yasa taja dogon tsuka tareda tashi
zaune tana hararar wayar cikin ɓacin rai ta soma magana tana faɗin
"Mttssww! aikin banza wai dan saboda kai ka sayi wayar shine zaka takura Ni? I hate
dis nonsense wallahi, banason mutum mai nacin tsiya, takurawarka ne yasa nake ƙara
tsanarka wallahi Roshan....."
a fizge tasa hannu ta ɗauki wayar ganin bazai daina ƙiran ba,
ɗaukar ƙiran tayi ta kara a kunne tayi shuru tana hararar gefe, magana
yake ta cikin wayar yana ambaton sunanta "Ammata! Hello Ammata!! Assalamu alaikum
bakya jina ne? Ammata nah Dan ALLAH kiyi magana mana...."
ɗan tsuka tayi acan ƙasin harshenta tace "wai dan ALLAH meyasa kake
son takura mun ne? ko dan saboda kai ka ban wayar shine zaka rinƙa takura mun, Ni
gaskiya bana son irin haka..."
ta ƙarisa maganar tareda tura ɗan lips ɗinta kamar wacce take
gabansa,
Ƴar tinny ce tayo kan Razhdeen tare da faɗawa saman cinyarsa tana faɗin
"Ankui Deen wai yauce Mommy nah jata dawo ne?..."
hankalinsa ne ya karkato kan Ƴar tinny murya ciki-ciki yace "Mamana
kiyi haƙuri zata dawo coming soon kinji Koh..."
tace "Ni a dawo mun da ita, kullum idan nace Abbah ya dawo da ita sai yace
zai dake Ni ...". kamar zata fashe da kuka ta ƙarasa maganar cikin lankwasa
murya...
Baiwar ALLAH hawaye ne kawai yake faman gangaro mata, abu biyu ne
suka tada mata da hankali na farko bata son Auren nan sannan kuma taji an ambaci
sunan Ƴar Amana, sai kawai taji zuciyarta na bugun uku-uku, maganar zuci ta
shiga yi tana faɗin "yanzu a wani hali kike ciki Ƴar uwata, shin kin mutu ne ko
kina raye? a cikin haske kike ko a cikin duhu? wayyo Allah Ƴar Amana ina
kewarki...."
bata san lokacin da kuka ya kuɓuto mata ba, kuka take na gaske kanta
na kallon ƙasi...
Aunty Yolash tana cikin jawabi taji ƙarar kukan Baiwar ALLAH nan
ta dakata da maganar tana kallonta,
Shima Abbah hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, murya a harharɗe yake faɗin
"lafiya kuwa Dota? meya sameki kike kukan? shin bakya son Auren ne? ki gaya mun dan
ALLAH yanzu a dakatar..."
kowa ya kasa kunne yana son jin abinda Baiwar ALLAH zata ce,
Aunty Yolash ce itama ta tashi ta nufi wurin da take zaune ta zauna
tare da rungimarta tace "Dota kiyi haƙuri ki sanar mana abinda yake ranki, Bama
son muyi miki dole domin ke ɗin Amana ce a gare mu, shin bakya son Auren ne?..."
Rukky tana kwance kan cinyar Pinky domin ba lafiya ne gareta ba tana
fama da zazzaɓi, murya na kakkarwa alamar jin sanyi tace "Aunty daman fah idan
Amarya anayi mata nasiha kuka take, kowace Amarya ma hakane..."
Aunty Yolash tace "a'ah muna son jin daga bakinta ne domin bamu san
abinda ke ranta ba, kar mu toye mata hakki..."
Pinky ɗan tsuka taja tare da kawar da fuska gefe daman ita sam bata ƙaunar Auren
nan domin a duniyar nan babu mace data fi tsana kamar Baiwar ALLAH, a cewar ta ita
tayi sanadiyar rabasu da mahaifiyarsu..."
Baiwar ALLAH tace "babu komai kawai lokaci guda naji kukan ban san meyasa
ba...."
Aunty Yolash tace "Ayyah sorry Dota saboda zaki kasance cikin Amarci ne
shiyasa, kuma son samu ace iyayenki suma suga ranar Auren ki...."
kafin Aunty Yolash ta ƙarasa maganar taji Baiwar ALLAH ta ƙara fashewa
da wani sabon kukan,
rungumarta tayi tana rarrashinta daƙyar ta iya dakatar da kukan..."
Saida Abbah yayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki, ya rarrasheta
kafin nan zuciyarta tayi sanyi,
Saida suka kammala tattaunawarsu tsab akan batun Auren kafin nan Abbah
ya dawo kan Razhdeen,
ya kalle shi sannan yace Razhdeen!.."
Uncle Deen kallon Abbah yayi jin ya ambaci sunansa, shi gaba ɗaya
hankalinsa akan Ƴar Amana yake, tunaninta kawai yake sai fuskarta yana masa
gizo...
Aunty Yolash kawar da kai gefe tayi tana dariya ciki-ciki domin
Razhdeen ba ƙaramin dariya ya bata ba,
daɗinta dashi baya ɓoye maitarsa, koda mutum bazaiji daɗi ba to dole saiya
gaya masa abinda ke ransa, baya tsoro kuma baya fargaban abinda zaije ya dawo..."
Abbah yace "TOH shi Roshan daka ɗauki hukunci akansa fa? shi da ya
gama fahimtar halinka kuma yake kiyaye ɓacin ranka..."
Razhdeen kallon Abbah yayi sannan yace "why tin lokacin baku
tambayeni laifin da yayi mun ba sai yanzu? Dad you known banason yawan magana
sosai, my headache..."
haɗe gira yayi tare da faɗin "okay let me go and sleep before..."
ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin miƙewa.
Abbah yayi saurin dakatar dashi yana faɗin "Noooo ka saurara kaji kalar
tattaunawar da zamuyi mana..."
zama yayi ya kasa kunne yana sauraron Abbah,
Baiwar ALLAH haka kawai sai satar kallon Razhdeen take tayi...
Abbah ya cigaba da cewa "naji mai martaba ya fara mun wata magana ne dangane da
ƙanwar matarsa Maamie, akan cewa za'a haɗa Auren ka dana Roshan itace wacce zaka
Aura..."
Dasauri Razhdeen ya ɗago yana kallon Abbah fuska a murtuƙe babu
alamun Annuri a fuskar,
Aunty Yolash itama da sauri ta furta "whattttt!..."
Yaran gidan kuwa gaba ɗaya haɗa baki sukayi wurin cewa "Ramlatttt!..."
Baiwar ALLAH kuwa kanta ne yayi wani irin sarawa da ƙarfin gaske kamar
wanda aka doka mata Gatari, dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi tana dafe dashi....
Aunty Yolash tace "wai Yaya kana nufin kace Ramlah ƙanwar MAAMIE?
Impossible wallahi, kaima kasan cewa Hajia Maamie ta shure Hajia Kilishi matarka
wulaƙanci da rashin mutunci Koh? shin baka san cewa Hajia Maamie ita take iko da
mai martaba ba koh? toh idan baka saniba yau zan sanar maka, duk abinda hajia
Maamie tace ayi a masarautar nan shi akeyi idan tace bata son abu TOH kuwa mai
martaba bai iya yayi ba, itace hakima mai mulkar masarautar...."
Abbah yace "ehh king ya sanar mun amma nace ya bari sai sunzo zamu
tattauna akan batun tinda duk zasu zo Auren nan, amma ita yarinyar batada matsala
ai koh?..."
Aunty Yolash tace "hakane amma kuma tana ɗaukar zugar Yayarta Hajia Maamie,
nipah gaskiya Yaya bazaiyu a rinƙa tara mana mata marasa tarbiyya a gida ba, Hajia
Kilishi ma ya muka ƙare da ita kuma du a ƙara kawo mana wata, itama Hajia Maamie
za'a ɗau hukunci akanta ai....."
murguɗa baki pinky tayi tana gunaguni tace "Uwata bata gidan ma
amma baza'a barta tasha iska ba..."
Aunty Yolash tace "ita data sha iska kuwa har abada domin ko mutuwa
tayi dole a faɗi halayarta na Arziƙi ko akasin haka,
ke nifa ba abokiyar yinki bane, Uwarki ce sa'ar yina domin ko Auntynki
Minal bata isheni kallo ba tinda a gabana duk aka haife ku..."
ƙara wurga mata harara Pinky tayi tare da murguɗa baki tace "to kiyi
dani ɗin mana..."
Abbah har numfashinsa ne yake shirin ɗagewa tsabar ɓacin rai dake
yanada hawan jini, Aunty Yolash ce ta tashi tana rirriƙe shi tare da bashi haƙuri
tana rarrashinsa,
Pinky tana kwance ba abinda take sai kuka, ji nayi an ɗagota da hannu
ɗaya ana janta suka nufi hanyar bakin ƙofa za'a fita da ita, idanuwanta ta buɗe
tana ƙoƙarin ganin wanda yake shirin fita da ita, naga Razhdeen ne fuska ba annuri,
daga nan ta saddaƙar cewa yau ranar mutuwarta ne, Ihu ta fara kurmawa tana ƙiran
sunan Mommy, "wayyo Allah nah Mommy kizo ki temake Ni zasu kashe Ni, Mommy nah
wayyo, Dan ALLAH Uncle Deen kayi haƙuri ka ƙyaleni, wallahi bazan ƙara baaa...."
Abbah kuwa cewa yake "kaje ka hukuntata tinda itama halin uwarta
gareta, ba'a gidan nan za'a mun wannan iskanci ba..."
*ƳAR AMANA*
wani makeken ɗaki ne wanda yake zagaye da wantalelen carpet babu kujera ko ɗaya a
ɗakin, fili ne kawai, ga wasu ƴan mata guda 50 duk suna zazzaune a filin ɗakin sun
jeru hannayensu a ɗaure ta baya, ƙafafu ma a ɗaure, kana ganin kasan sato su akayi,
aciki kuwa harda ƴar Amana itama anyi mata ɗaurin da akayi wa sauran...
ɗakin duhu ƙirin baka iya ganin abinda ke ciki dake ƙofar a ƙarƙame
yake, sai wani ɗan ƙaramin window wanda iska zai rinƙa shiga kaɗan-kaɗan, wannan
lokacin kuwa window ma an rufe babu mashigar iska, duk matan nan babu wacce bata
rigirta ba, numfashi sama-sama haka suke shaƙa, wata a ciki kuwa har ta mutu tana
zaune kai a durƙushe wuya ya rigada ya karye, amma babu wanda yasan ta mutu...
suna cikin wannan halin suka ji motsin mutum yana ƙoƙarin buɗe ƙofa, a
hanzarce duk suka ɗaɗɗago suna bin bakin ƙofar da kallo duk da duhu ne wurin basa
iya ganin ƙofar ma,
wani irin farin ciki ne ya bayyano musu domin suna muradin shaƙar
iskar waje...
sai ga wasu mazan suma sun shugo, haka aka rinƙa fita dasu waje, duk
aka jejjera su a waje, ga wurin kurmin daji ne babu mutane a dajin sai su, anan
suke aikata miyagun ayyukan su, kuma anan suke ƙirƙiran ƙwayoyin maye, anan ake
sato ƴan mata a kawo su, wasu a fitar dasu ƙasar waje aje a sayar dasu, wasu kuma
yankasu ake acire wasu abubuwa ajikin mace ta hanyar nan suke samun maƙudan kuɗaɗe,
suna zazzaune ga wasu manya-manyan zabga-zabgan maza suna tsaye a
kansu, saiga wata ƙatuwar motar baƙa ƙirin har wani sheƙi take, mai taya ta
bayan mota, baka iya ganin wanda yake cikin motar, can ba jumawa sai ga wanda yake
cikin motar ya buɗe murfin motar a hankali ya fara sauƙar da ƙafarsa ta hagun daga
baya ya fito gaba ɗaya,
wani mutumi ne ɗan dattijo dashi, yana sanye da baƙin glass ga gemu
ya ɗan sauƙo, mutumin baƙi ne yana sanye da manyan kaya water fruit, zuwa yayi
ya tsaya a gaban ƴan matan yana wani irin lanƙwasa yana binsu da kallo ɗaya bayan
ɗaya, cikin dirarren murya yace "wayyo ga ƴan mata zuƙa-zuƙa amma dole na ganku
na ƙyale ku saboda banida abun more rayuwa kashhhhhh!!!..."
Yarinyar data rabani da dukiyata inda zan ganta a yau wallahi
babu abinda zaisa na yankata a yau..." ya ƙarasa maganar yana bugar ƙafarsa da
ƙasa tsabar takaici....
wani daga cikin yaransa ne yace "Ogah ɗaya daga cikinsu ta sheƙa pah..."
saiji sukayi yace "kai ina yarinyar dana ce ku nemo mun ita a duk inda take
a doron ƙasa ?...."
yayi maganar a ɗaya daga cikin yaransa, wani ne yazo yanda Ƴar Amana
take zaune yasa hannu ya janyo ta har gaban Yallaɓai...
Ƴar Amana tin lokacin data gashi taji gabanta yanata faman yankewa
domin tasan mutumin asalin mungune bashida imani,
Yallaɓai kallon ƴar Amana yayi tare da tintsirewa da wata mahaukaciyar
dariya harda tafa hannayensa, yana faɗin "shegiyar yarinya ashe tana wurin tana
jin ina cikiyarta tayi luƙusss,..."
ya durƙusa a gabanta tareda kamo sumar gashinta ya kuma cewa "yau gaki a
fadata, nine Sarkin wannan yankin, a wancan lokacin nasa an kamo ki a gidan marayu
kin kuɓuce kin gudu, TOH yau kam babu ƙafar guduwa idan kuma kikace zaki ƙara tsere
mun wallahi tallahi saina yanke miki ƙafafu Kinga kuwa ke kurmiya sannan gurguwa,
shin ina ƴar Uwarki Baiwar ALLAH? tana ina? Hhhhh naji cewar tana gidan General
koh? akwai tsaro sosai a gidan shiyasa banyi gigin zuwa yanda take ba, ke da ita
kunyi bankwana har abada daga nan sai ƙiyamar da ba dawowa...."
Ƴar Amana sunkuyar da kai tayi ƙasi ko ɗagowa tayi ta kalleshi bata
yi ba...
hannu yasa ya ƙara ɗago ta kanta suna kallon juna yace "munafuka ko
irin hawayen nan bata yi, ke wai jaruma ko? to yau zan nuna miki tsoro a cikin
idanuwanki..."
ya miƙe tare da ja da baya yana faɗin "duk ku Aske musu sumar kansu
domin waɗannan babu wacce za'a sayar da ita da ranta, idan aka musu yankan rago
zasu fi Albarka, yau za'a yanka mutum biyu gobe ma mutum biyu da haka har su ƙare,
kullum mutum bibbiyu, da zarar sun ƙare sai a ƙara sato wasu ƴan matan kuma du,
bamason talauci ya wanzu mana, indai akan kuɗi ne zamuyi abinda yafi haka..."
Wata ma tana kuka tace "Ni marainiya ce a wurin Kakata nake zaune iyayena sunyi
hatsarin mota duk sun rasu, ina kan hanyar dawowa da islamiyya saiga baƙar mota ta
tsaya a gabana suka ɗauke Ni ....."
Duk Yallaɓai yasa aka Aske musu gashin kansu anyi musu tanƙwal,
kayuwa sai sheƙi suke,
Sai a wannan lokacin Ƴar Amana ta fara tsiyayar da hawaye ganin
yanda akasa Aska ana yanke mata zara-zaran sumar gashin kanta, ganin yanda sumar
gashinta yake zubowa ƙasi yasa ta yanki jiki ta faɗi sumammiya, duk da haka ba'a
dena ba saida aka yanke gashin gaba ɗaya kayin yayi tal kamar madubi...
Ko wacce haka akayi mata domin daman in zasuyi yanka sai anyi wa mutum
Aski,
Sannan aka zo duk wacce take wurin Saida aka manna mata wani kalanda mai
danko ajikin kalandar an rubuta ranar da za'a yanka ka da lokaci,
Ita Ƴar Amana an manna mata ranar Jumma'at ranar 15 ga watan August next
week kenam da misalin ƙarfe 7 na safe itada wacce tace ita kaɗai iyayenta suka
haifa...
Domin akowace rana za'a yanka mutum biyu ne,
Idan aka yanka abubuwan da ake buƙata sune kamar Nonuwa, ƙwayar idanun,
harshe, sai kuma farjin mace,
Duk suna zaune aka kamo waɗanda aka manna musu cewa yau za'a yanka su,
duk matan ihu suka fara yi suna kururuwa ganin an janye wasu ƴan uwansu guda biyu,
shigar dasu akayi cikin wani ɗaki a ɗan gefe da dajin, shi kuwa
Yallaɓai zama yayi domin shine ogansu shine maisa ayi,
hango Ƴar Amana yayi tana kwance har zuwa yanzu bata farfaɗo ba,
murmushin mugunta yayi tare da kawar da fuskarsa gefe,
Can wasu ɗan lokuta sai ga masu yanka sun fito hannayensu riƙe da wuƙaƙe
duk jini, ɗaya yana riƙe da ƙaton faranti yanda aka ɗoɗɗora kayan amfanin ƴa mace,
har dana wacce ta mutu a ɗakin
zuwa sukayi suka ajiye a gaban Yallaɓai wanda fuskar yake murtuƙe babu
kyan gani, Ciro wayarsa yayi ya danna ƙiran wani daga ƙasar waje yana faɗin
"Hello David akwai kayayyakin mata uku sun hallaru, zaku iya turo mun da kuɗin ta
Acc, a yau zan tura yarana biyu su kai muku, kuma gobe ma haka daga yau har kullum,
daman mata hamsin ne kafin a nemo wasu..."
Yallaɓai yace "mun gama magana ai! mace ɗaya a 20millions take kaga kuwa
mata uku 60millions kenam..."
other side "ok don't worry we'll send you right now, but we need the
things Early morning..."
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
STEP TWO
9 to 10
Washe gari ranar Thursday manya-manyan baƙi ne suke ta sauƙa a gidan General, dake
ranar Friday ne ɗaurin Aure,
Roshan da mai martaba tare da iyalansa gaba ɗaya duk sun iso, ƴan uwan
mahaifiyarsu Razhdeen da Roshan kusan su Ashirin duk sun zo daga Saudiyya, ga
family su Abbah wasu daga ƙasar Egyph wasu kuma London wasu daga Ethiopia banda
waɗanda suka zo daga garuruwa Kano, Bauchi, Kaduna, pataskum jahar Yobe dadai
sauran garuruwa,
Gidan General baƙi ne tam a gidan, tsabar girman gidan an raina yawan
mutanen da sukazo domin gidan duk ya cinye su dan ma wasu da yawa basu zo ba,
Razhdeen ganin yanda ake ta baƙi yasa ya koma can gidansa
yanda Mohandas yake, ita kuma Minal Roshan ne yabi ta gidan ya ɗauketa suka dawo
gida,
Baiwar ALLAH gaba ɗaya a takure take ganin yanda ake ta zuwa ganin
Amarya, tin daga yau aketa faman shishshiryata dake yau da daddare akwai dinner
hall da za'a taru ayi,
Roshan tin dawowarsa yake ɗaukin ganin fuskar Baiwar ALLAH amma ya kasa
ganinta, taƙi fitowa daga room ɗinta, ga kuma yanda mata suke shiga cikin ɗakin,
babu halin ya shiga ciki,
ya ƙirata a waya sau ba adadi amma taƙi yin picking balle ta ɗan fito ya
ganta..
Daƙer ya samu ganin Ummy dake itama rawar kanta ya ƙaru sai gigiwa aketa
yi anata shiri kamar wanda zasu fita ƙasar waje,
a waya ya sanar mata cewa tazo swimming pool ta same shi,
tayi mamakin jin haka sosai ganin yanda aketa shirin tafiya hall amma shi
yana gida, amsa ɗaya ta bashi cewa gata nan zuwa...
zuwa tayi ta same shi a swimming pool yana zaune akan kujerar wajen ya
kifar da kansa akan table,
Dafa kafaɗarsa tayi tare da faɗin "Yaya Roshan lafiya kuwa, meya faru dakai?..."
Ummy tace "Yaya Roshan haka zaka cigaba da haƙuri da ita har a ɗaura
Auren domin yanzu kowa ma haƙuri yake da ita, bawai kai ɗaya ba, koda jiya ma
Saida Abbah da Aunty Yolash suka tambayeta matsalarta kodai bata son Auren ne tace
a'a, amma nafi tunanin ko tunanin iyayenta take shiyasa kasan baza taji daɗi ba
ace ana Aurenta amma dangin mahaifinta ko mahaifiyarta babu wanda ya halarci wurin,
babu ƴan uwanta ko ɗaya kaga dole zata shiga damuwa matuƙa, ina tunanin wannan ne
matsalarta gaskiya...."
Ummy tace "Hmmmmmmmmmm TOH yanzu zaka iya tashi kaje ka shirya?..."
Yace "TOH yanzun ba yanda za'ayi na ganta ko sau ɗaya ne? kinsan
tinda na iso ban ganta ba nayi missing ɗinta over..."
yamutsa fuska Ummy tayi tare da faɗin "ku haɗu a wurin dinner, kasan dai
yanzu Aunty Dota bazata iya ratsa mutane tazo nan ba koh?..."
Yace "okay shikenam mu haɗu a can..."
Abbah yana huci yace "duk wanda ya bani shawarar na dawo dake wallahi
tallahi ba masoyina bane, babban maƙiyi nane kuma Ni da shi zumunci ya yanke har
abada saboda haka ki tashi kibar mun gida yanzun nan, ƴaƴanki koda ke ko babu ke
zasu rayu cikin aminci, kuma ki dube su dakyau babu abinda ya ragu a jikinsu da
bakya nan, saima girman jiki da suka ƙara, ina mai miki albishir da cewa a gobe
ranar Jumma'at za'a haɗa Auren Roshan da Aurena a ɗaura, an bani ƙanwar Matata
marigayiya Fatima akan na Aura, kuma Alhamdulillah ɗabi'unsu ɗaya da tarbiyyar su
da duk wasu nau'ikan zamantakewar Aure, sunanta Ummu Salamah Amintacciyar yarinya
daga Saudi Arabia,
Kilishi ki tashi kibar mun gida yanzun nan tin kafin nasa
karnukana su korar mun ke...."
Jiri ta fara ji jin chief zaiyi Aure, nan ta ƙara fashewa da kuka ta
buɗi baki zatayi magana yayi saurin daka mata wani irin gigitaccen tsawa har saida
sauran mutanen wurin suka firgita, a gigice ta miƙe tsaye ta nufi bakin ƙofa tana
kuka, anan ta tarar da Ummy tana tsaye bata ƙarasa shugowa ba duk ta wanke
kwalliyar fuskarta da hawaye, tsayawa tayi Hajiya Kilishi a gaban Ummy ta kamo
hannayenta biyu tana ƙiran sunanta ciki-ciki tace "Ummy ki gafarce Ni..."
Daga nan tayi wucewarta...
Abbah shima juyawa yayi ya haura saman upstairs rai a ɓace, kab mutanen wurin
babu wanda yaji daɗin abinda ya faru amma masu faɗin madalla su sukafi yawa domin
da yawan su babu wanda yake jin daɗin zama da Hajiya Kilishi saboda ta kasance mace
marar son mutane, Aunty Yolash ɗan tsaki taja tareda wurga ƙwayar idonta kan
Hajiya Maamie wacce itama tana wurin tace "waɗanda za'a kora ai sunada yawa, ina
mai martaba shima yazo yahau kan layi, domin baza'a mayar mana da ɗan uwa bita zai-
zai ba...."
Hajiya Maamie dogon tsuka taja tana hararar Aunty Yolash da sauran ƴan
uwansu tace "Ni kuwa an mutu dani wallahi, babu yanda aka iya dani, mutu karaba
takalmin kaza Ni da mai martaba, dole a ganni a barni domin na zamo ciwon ido..."
Aunty Yolash tace "yooo wa kika ajiye balle ki zauna dashi har
ƙarshen rayuwa? To dai kina gani wacce ta ajiye har ƴaƴa biyar ma ta fita balle ke
ko ɓatan wata baki taɓa yi ba...."
Aunty Yolash tace "Uhmmm! Kin yanda nayi Aure yanzu ke kuma ki samu ciki a
wata ɗaya zuwa biyu?..."
Aunty Yolash a ruɗe ta dafa ƙirji tare da faɗin "buro ubanaaa?! kika
ce buro ubanaaa?!! buro ubanaaa kika ceee?!!!..."
Nan danan idon Aunty Yolash ne ya kaɗa yayi jawur domin tin tana
cikin mahaifiyarta ta rasa mahaifinta memakon a bishi da addu'a sai kuma zagi,
ai bata san lokacin da tayi sufa ta cabko wuyan Hajiya Maamie ba,
Hajiya Maamie ta tsorata sosai da ganin yanayin Aunty Yolash,
mutanen wurin ne suka rirriƙe Aunty Yolash domin ba ƙaramin shaƙa tayi mata ba,
duk yawan mutanen falon babu wanda ya iya ɓanɓaran Aunty Yolash daga jikin Hajiya
Maamie,
Abbah jin hayaniya yayi yawa ne yasa shi sauƙowa dasauri, shima daƙer ya
iya fizgar Aunty Yolash ganin bazata saurari abinda zai faɗa ba,
Cikin faɗa yake magana tare da faɗin "wannan wani irin hauka ne? babu
dama a barku ku kaɗai sai an samu matsala?..."
ya kalli Aunty Yolash yace "ke meyasa bakida haƙuri ne? to ku same Ni
acan falo ɗina yanzun nan..."
yana kaiwa nan yayi ficewarsa,
Aunty Yolash harara ta wurgawa Hajiya Maamie itama tayi gaba, Hajiya
Maamie itama bayanta tabi, a falo duk suka tarar da Chief yana zaune akan tsararren
Soparsa kai a sunkuye yanata karkaɗa ƙafafu, duk zama sukayi a ƙasin carpet
domin falon Chief indai ba manya-manyan baƙinsa bane ba'a zama masa akan sopa,
Chief ɗaukar waya yayi ya ƙira wata dattijuwa a can falonsu wacce tana
wajen akayi komai, can sai gata ta shugo da sallama a bakinta, amsa mata yayi tare
da nuna mata saman kujera ta zauna, zama tayi tare da faɗin "to gani naga an ƙira
Ni..."
Chief yace "toh inaso ki gaya mun gaskiyar abinda ya haɗasu kar kiga cewa kinada
alaƙa da Yolash kawai tsakanin ki da Allah zaki sanar mun...."
Aunty Yolash tana hawaye tace "Amma Yaya itama tamun gorin Aure fah..."
Chief yace "Aure ai ke kika hana kanki, Allah ya baki damammaki da dama amma kin
ƙi amfani dashi, nawa ne mazajen Aure suka zo nemanki amma duk kin ƙisu, kuma dan
anyi miki gori sai kiji haushi?
Ai gorin haihuwa yafi na Aure ciwo, har yanzu damarki bai wuce ba, akwai
waɗanda suke zuwa neman Aurenki, aciki akwai Governor Kaduna da Governor Bauchi ga
Alhaji Tafidan Bauchi ga manya-manyan shuwagabannin nan Abuja da dai sauransu idan
kuma kince a'ah TOH saiki cigaba da toshe kunnuwanki da jin duk wasu ƙananun
maganganu akan ki,
Ku tashi ku ban wuri...."
Aunty Yolash tana shiga babban falonsu kai tsaye room ɗinta ta wuce
ta danna sakata,
Mutanen da suke falo babu yawa duk sun kutsa kai ɗakin da Amarya take
itama Baiwar ALLAH ta kulle kanta a cikin Bathroom taƙi buɗewa, sunyi da ita akan
ta buɗe amma taƙi, gashi har lokacin dinner yayi, sauran yaran gidan ma ko wacce
tana ɗakinta cikin damuwa ganin yanda Abbah ya wulakanta Mommynsu kuma sannan sunji
labarin shima zaiyi Aure,
Angwaye sun jira har sun gaji basu ga ko mutum ɗaya ba acikin
matan gidan balle suga idon Amarya,
Da haka har lokaci ya ƙure aka bantsar da hidimar Dinner, amma ba ƙaramin
takaici suka shaƙa ba kaf Abokanan Ango da shi kanshi Angon,
Daman Aunty Yolash ce kawai zata iya tsawatar wa Baiwar ALLAH akan ta
buɗe TOH itama ga a halin da take ciki itama ta kulle kan natan, Ummy ma wacce
itace Yakamata ta rarrasheta itama ta zama uwar ɗaki....
Razhdeen shi da Mohandas layin mabarata suka nufa da isar su tsayar da motar
sukayi a dai-dain layin suna baza idanu ko zasu hango Ƴar Amana, a wannan lokacin
ma sun yi rashin Sa'a basu ganta ba, ɗan tsuka Razhdeen yaja tare da jan mota zai
bar wurin Mohandas yayi saurin dakatar dashi tare da faɗin "wait Major! Bayan
barin ka Nigeria nasha zuwa nan duba yarinyar nan amma bata nan, banyi tunanin
sauƙa daga motar zuwa tambayarsu ita ba amma a wannan lokacin dole zamu je mu
tambayesu ita, ina tunanin rashin zamanta anan ba lafiya ba..."
Mohandas yace "let me go and check her, stay inside the car..."
yana kaiwa nan ya fice kai tsaye wurin tsofin ya nufa, shi kuwa Razhdeen
yana daga ciki yana kallon wurin da take yawan zama...
Mohandas tsugunawa yayi a gaban tsohuwar da Ƴar Amana take suka gaisa
sannan yake tambayarta labarin Ƴar Amana,
Nan tsohuwa ta fashe da kuka tana faɗin "Allah sarki kurmiyar Allah,
Amanar Allah sun ɗauke ta..."
Mohandas cike da mamaki ya furta cewa "daman kurmiya ce?..."
Tsohuwa tace "ey kurmiya ce, ɓarayi ne suka sace ta..."
Juyawa yayi da gudu ya nufi motarsu, buɗewa yayi ya shiga yana jan
numfashi ido a zazzare,
Razhdeen ganinsa ba ƙaramin tsorita yayi ba ganin halinda ya kasance, tsoronsa kar
wani mummunan abu ya faru da ita..
Razhdeen cikin go slow ya juyo yana ƙarewa Mohandas kallo ido a zazzare,
Jin bai gamsu da maganar Mohandas ba yasa ya buɗe murfin motar ya fice, kai
tsaye wurin tsofaffin ya nufa yana zuwa ya tsaya yana binsu da kallo, a tsawace ya
fara magana yana faɗin "Who kidnap her?,
tell me please who come and kidnap my sarah?..."
Duk tsaya kallonsa suke domin babu wacce tasan mai yake faɗi domin da turanci
yake maganar,
tsohuwar ƴar Amana ce tace "kayi haƙuri yaro Bama jin Yaren nan..."
Anan duk suka sanar masa duk yanda akayi da cewar suma basu ga
fuskarsu ba domin baƙar hula ce akan su...."
tsohuwar ta miƙa masa jitar Ƴar Amana...
Razhdeen kamar zai dungura haka ya nufi motar yana shiga ya finciki motar a ɗari
suka bar wurin,
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*11_ TŌ _12*
Misalin ƙarfe uku na dare, agogo ne yake harbawa a hankali ƙit-ƙitt-ƙittt a yayin
da Razhdeen yake kwance saman katafaren gadonsa, yana rufe da mayafi sai iya fuskar
sa ne a waje yana kallon ceilling, kashe hasken ɗakin yayi sai ɗan hasken lamp da
ya bari mai launin green,
A daren yau Razhdeen bai samu yin bacci ba sakamakon abin da yasa a ran
sa, ɓatar Ƴar Amana ba ƙaramin girgiza shi yayi ba domin a halin yanzu bai san a
wani hali take ciki ba, gashi an bayyanar masa cewa zuwa akayi har wurin da take
aka ɗauke ta, duk yanda akayi sun haɗa mata tarko ne,
Tunani ne barkatai acikin kwakwalwar sa, mafita yake nema yanda zai
samu yarinyar nan domin a halin yanzu ita ce raunin sa!...
Duk mutanen ɗakin ne suka juyo suna kallon su, wata daga ciki ne ta
ce "toh ikon Allah duk meya kawo wannan maganar?..."
Ramlat ta kalleta sama da ƙasa sannan ta ce "bakin da Allah ya tsaga baya rasa ta
cewa, don haka abin da ke raina na faɗa..."
wacce tayi maganar ce ta kuma cewa "Amma ai bai kamata kiyi irin
wannan maganar a cikin mutane ba..."
Ramlat ta ce "Oh ashe dai a cikin mutane nake, ai Ni kuwa na ɗauka
dabbobi ne..."
Duk shuru suka yi saboda ba mai iya tanka mata, tsoron Ramlat ake
saboda Hajiya Maamie domin ba ƙaramar masifaffiyar mata ba ne, yanzu sai ta iya
hargutsa taron bikin,
Ummy uwar masu gida wacce jugowarta cikin ɗakin kenam, kalmar da
Ramlat ta furta ne ya daki dodon kunnenta, ai kuwa nan itama ta buɗi baki ta ce
"dabbobin suna da yawa ai amma sai dai wacce take agolanci tafi dabbobin
dabbanci..."
Ramlat miƙe wa tayi tsaye tana bin Ummy da kallo cike da mamaki ta ce
"Ummy Ni kike ƙira da Agola?..."
Ummy ta ce "to ƙarya akayi miki ne? ko gidan Uncle mai martaba da kike
zaune a gidan Ubanki ne shi? kin samu matsayi ne albarkacin zaman da kike a gidan
sarauta amma in ba haka ba kin isa ki buɗe baki kiyi wani maganar banza ne anan,
duk mutanen da kike gani acikin gidan nan duk jini ɗaya ne babu bare sai ke,
Yayarki ce matar mai martaba ita kuwa ba haihuwa take ba hakan yasa ta jawo ki
gidan sarauta kizo ki ci arziƙi babu a house..."
Ramlat ita kaɗai tasan takaicin da take shaƙa a yanzu buɗar baki
tayi ta ce "au gorin haihuwa zakiyi wa Aunty nah? eh naji bata haihuwa amma ai ta
kama kanta tana zaune a gidan mijinta, wata uwar kuma zubar da ƴaƴanta tayi take
bin yawon hotel..."
Ramlat tana kammala fitar da abinda ke ranta tayi saurin barin room
ɗin domin tasan uwar Ummy ce take yawon hotel,
wani abu mai kama da kibiya ne ya soki saitin zuciyar Ummy tsabar takaici
da baƙin cikin har an fara mata gori akan mahaifiyarta,
Da sauri ta juya zata bi bayan Ramlat taji an riƙo ta juyawa tayi taga Baiwar
ALLAH ce take ta faman girgiza mata kai alamar karta biye mata,
Ummy tsabar takaici bata san lokacin da ta rausa uban ihu ba tare da
durƙusa gwiwowinta ƙasi, duk mutanen ɗakin ne suka rufu kanta suna bata haƙuri
akan abinda ya faru, Ummy kuwa kuka take ko sauraron su bata yi domin abun da
ciwo ta sanadiyar haka yasa Mahaifiyarta tabar gidan Mahaifinsu,
Jin Ihun ya jawo hankulan wasu daga cikin mutanen gidan, Aunty Yolash
ce first ɗin shugowa dake tana kusa da ɗakin sai ga Rukky da Pinky wacce ba'a daɗe
da fito da ita daga ɗakin duhu ba,
Ummy tambayarta ake meya faru da ita amma babu bakin magana sai waɗanda
akayi a gabansu ne suka faɗi duk abin da ya faru, sam babu wanda yaji daɗin abinda
ya faru a cikinsu,
Baiwar ALLAH dake tsaye ta kama kai tayi shuru sakamakon wani irin Jiri
da hajijiyar da take ji, kanta ne yake mata wani irin matsanancin ciwo, ko kaɗan
bata son hayaniya a halin da take ciki yanzu domin ba isasshen lafiya gareta ba,
a cikin tana jurewa har ƙarfinta ya ƙare ta yanki jiki ta faɗi a
wurin, daga lokacin bata san ina hankalinta yake ba domin alamun suma tayi,
sai kuma kallo ya koma kan Amarya, nan da nan magana ta bazu cewa "Amarya
ta yanki jiki ta faɗi ga babu maza a gida duk taron mata ne...
Ramlat ta ce "ina kuwa lafiya Aunty Maamie, wannan ƙaramar Yarinya tana
shirin raina mun wayo..."
Hajiya Maamie ta ce "koma wacece meyasa baki ci ubanta ba sai kuma kizo
kina mun cika baki aikin banza kawai, ai indai bazaki buɗe baki kici mutuncin
mutum ba to ke da raini kuwa yanzu kuka ƙulla, wai ma wacece yarinyar?..."
Ramlat ta ce "Ummy mana kodan a gidan ubanta take ne shiyasa zata nemi
ta ci mun mutunci, har wani ƙirana take da Agola ke kuma ta ce bakya haihuwa..."
Hajiya Maamie data bugi ƙasa da ƙafarta ta wani narka uwar ashar ta
ce "buuuuro uban nan, ke kuma me kike ce mata dan durun uwarki?..."
Ramlat ta ce "ce mata nayi ai kinfi uwarta da take yawon bin hotel
tinda ke kin kama kanki kina zaune da mijinki..."
Hajiya Maamie washe baki tayi tare da faɗin "kin burge ni da
kika gaya mata haka, kinga gaba bazata sake miki gori ba tinda abun gori yana
gindin su, ai wallahi da baki tamka mata ba saina zabga miki mari sannan na kora
ki garin Kaka can ƙauye..."
Hajiya Maamie taja dogon numfashi tana hura iskar baki ta ce "ai ki bar
batun nan kawai, domin sai bokan nan yayi mun aiki tuƙuru akan Razhdeen, ko ba
yanzu ba za'ayi Auren, a duniyan nan babu wanda tsafi baya kamashi don haka ki
kwantar da hankalin ki, domin idan muka cika yin maganar tsab Razhdeen rabaki
zaiyi da duniyan nan gwara mu bi komai a hankali ba'a gaggawa da rayuwa..."
Ramlat ta ce "Ni dan Allah kibar batun Uncle Deen ɗin nan, mu koma
kan Yaya Roshan ni nafi son sa wallahi, kuma kinga shi da wuri za'a iya shawo kan
sa..."
Hajiya Maamie ta ce "Dan ubanki Roshan ɗin da aka tafi ɗauro masa
Aure shine zakiyi batun sa? ki bar komai a hannu na dole fa sai Razhdeen ya Aure
ki..."
Ramlat ta ce "wallahi ban gama warkewa da dukan da yayi mun ba, har yanzu
gaɓoɓina ciwo suke mun hakan ma ki duba yanda ya ɗaure ni a saman fanka kamar wata
lauje, Ni gaskiya bazan iya zama da Uncle Deen ba..."
Hajiya Maamie har ta buɗe baki zatayi magana suka ji kururuwa a falo,
hayaniya duk ta baza ko ina na gidan, da sauri suka fice domin gane wa idonsu,
suna fita suka tarar an fito da Baiwar ALLAH a sume, wasu sun riƙe
hannayen ta biyu wasu kuma sawaye da haka suka fito da ita,
Aunty Yolash ce tayi gudun shiga room ɗinta ta ɗauko key ɗin motar ta zata kai ta
hospital,
A ruɗe take faɗin "dan Allah ku taya ni ɗaga ta mu kai ta wurin
parking kunga ba maza a gidan sannan duk sojojin ma babu wanda aka bari..."
wata tsohuwa ce ta ce "wai ma duk meya jawo haka ne..."
Ummy tana kuka ta ce "duk ata sanadiyar waccan Agolar yarinyar ce..."
ta ƙarisa maganar tare da nuna yanda Ramlat take tsaye.
Ramlat kama kunkumi tayi ta tari yawun ta da cewa "Hmmm! Allah na gode
maka a iya Agolanci na tsaya, ke bari kiji in banda tsautsayi da kuma tsananin
soyayyar Yaya Roshan a cikin zuciyata ba mai zai sa na tsaya haɗa kishi da wannan
yarinya mai kama da farar goɗiya..."
Ramlat tayi dariya tare da tafa hannayenta biyu tana faɗin "ai kuwa
you should see what am going to do yarinya, Yaya Roshan Auren ta kawai zai yi amma
ainihin shi ɗin nawa ne..."
Pinky dake wurin ta ce "wai duk akan wancan marar asalin ake
wannan ce ce ku cen? Lallai kun haɗu da aiki..."
Pinky ta tari yawun ta da cewa "ni kuma daman can bata raina, haka
kawai nake jin tsanar ta wallahi, na rasa mai Yaya Roshan ya gani a jikin ta har ya
nace akan Auren ta..."
kallon gefen ido ya yi mata tare da faɗin "zanje ɗaurin Auren twins
ne, tinda kun fito da ita ku kaita mana..."
yana kaiwa ƙarshe ya juya zai shige motar sa Aunty Yolash tayi saurin
riƙo hannun sa tana faɗin "wai kai wani irin murɗaɗɗen mutum ne kam, ga can
yarinya rai a hannun Allah amma kai ko a jikin ka? na tabbata inda Mijin ta ne
kafin na ƙarasa magana ta zai nufi yanda take..."
Nan da wasu ƴan mintuna har sun isa hospital, a harabar hospital
ya yi parking da motar sa, lokaci guda wasu nurses sun kai biyar suka fito da
gadon tura wa,
Razhdeen da Aunty Yolash suma facility ɗin hospital suka shiga, a wasu kujeru suka
zauna domin har an shiga da Baiwar Allah emergency room,
Bayan wasu mintuna sai ga Doctor ya ce musu yana son ganin
su a office ɗin shi, hakan kuwa suka yi a office suka tarar da shi zaune yana duba
wasu files,
suma zama suka yi suna fuskantar Doctor,
numfashi Doctor ya sauƙe idon sa akan Razhdeen ya ce "Major meyasa zaku bar
yarinya ciwo ya ci jikin ta har haka? ta juma tana fama da rashin lafiya domin
zazzaɓi ne mai zafin gaske yake damun ta, rashin tarar abun da wuri ne yasa duk
jinin jikin ta tsotse wa, zata iya rasa rayuwar ta a cikin ɗan kwanakin nan in
har bata sha ledar jini biyu zuwa uku ba..."
ya ƙarasa maganar tare da miƙa musu file ɗin ta,
Razhdeen ne ya karɓa yana duba wa daga ƙarshe kuma ya ce "yanzun mai ake jira
ne?..."
Aunty Yolash murmushi tayi ganin yanda Razhdeen ya damu da rashin lafiyar
Baiwar Allah lokaci guda,
Doctor ya ce zamu duba mu gani in har zai yi mata, a take Razhdeen ya miƙa hannun
sa aka ja jinin da za'a gwada da nata,
Bayan wasu ɗan mintuna sai ga Doctor ya dawo fuska ɗauke da
murmushi ya kalli Razhdeen sannan ya kai idon sa kan Aunty Yolash ya ce "Ma sha
ALLAH! group ∅ negative zaka iya bawa kowa, amma ita ɗin matar ka ce ko wacce zaka
Aura?..."
A ranar Baiwar ALLAH sai da ta sha jini laida biyu duk daga jikin
Razhdeen aka ja,
an basu dama sun shiga duba ta amma sai dai ta tafi dogon bacci bayan ta
farfaɗo, laidar jini na biyun ma har ya kusan ƙare wa, Aunty Yolash tana zaune
akan kujerar gefen gadon shi kuma Razhdeen yana tsaye ta saitin kanta yana ƙare
ta da kallo, Doctor ne ya shigo yana faɗin "Insha ALLAHU a yau za'a sallame ku
domin ba ƙaramin duba ta muka yi ba, yanzu haka bacci ta samu yi ne zuwa an juma
kaɗan zata farka..."
Razhdeen yana tsaye gaba ɗaya ya gama gajiya da zaman hospital ɗin
nan, ga tunanin kurmiyarsa wato SARAH (Ƴar Amana)
Aunty Yolash ta ce "gaskiya ya kamata kaje ka huta kayi ƙoƙari sosai Uncle Deen,
cire laida biyu na jini a jikin mutum kuma a rana ɗaya ba wasa bane, mun gode
sosai..."
Razhdeen kawar da kai ya yi zai tafi yaji an damƙo hannun sa, a hankali
ya juya bayan sa yaga hannun Baiwar ALLAH tana riƙe da na shi,
Aunty Yolash itama tsaya kallon ta tayi cike da mamaki,
Idon ta a lumshe ta fara motsi da lips ɗinta a hankali ta soma furta
"Uncle Deen jinin jikin ka ne yake gudana a jiki na? daman ina jiran wannan ranar
ta zo na haɗakar jini, shikenam ka zamo jinin jiki nah, ina muradin ganin jinin
jikin ka a cikin jikina, ina matuƙar ƙaunar ka da son kasance tare da kai har
kullum, dan Allah ka ce wa Yaya Roshan ya yi haƙuri ya bar maka ni ..."
Jin haka yasa a zabure Aunty Yolash miƙe wa tsaye tare da faɗin
"whattttt?..."
shima Razhdeen fizgar hannun sa ya yi cike da mamaki babu bakin magana,
Baiwar ALLAH duk wannan maganganun da tayi shi ba'a cikin hayyacinta ta faɗe
su ba, domin har zuwa yanzu idonta a rufe suke, sambatu kawai take tana cigaba da
ɓare-ɓaren maganar ta...
Aunty Yolash zuwa saitin ta tayi tare da sa hannu tana ɗan bubbugan
fuskar ta tare da ambatar sunan ta,
"Dota! Dota!! ke Dota ki buɗe eyes ɗinki kin san abinda kike faɗi kuwa?..."
Muryar Abbah suka jiyo tare da wasu mutanen sun nufo ɗakin da aka
ƙwantar da Baiwar ALLAH,
Razhdeen fargaba da tsoro ne suka bayyana akan fuskar sa jin abubuwan da
Baiwar ALLAH ke faɗi kuma ga su Abba suna shirin shugo wa, domin sun ji labarin
Amarya tana kwance a gadon hospital ba lafiya,
Da sauri Razhdeen ya yi saurin fice wa kafin a tarar da shi ga
kuma bakin ta ya gagara rufuwa..."
Da ƙer Aunty Yolash ta samu ta farkar da ita, dai dai lokacin da su
Abbah suka shugo da Roshan da wasu...
*DAN ALLAH FAN'S KUYI HAƘURI 🙏 INA CIKIN BUSY NE SHIYASA BAN SAMU LOKACIN YI MUKU
UPDATE BA...*
*SANNAN INA MAI SANAR MUKU CEWA AN KUSAN KAWO ƘARSHEN FREE BOOK A CIKIN
STEP TWO ƊIN NAN*
*MY ENEMY BOOK YANZU NE WASAN FARKO DOMIN DUK WANI CHAKWAKIYAR YANA CIKIN PAID
BAZAN GUDANAR A CIKIN FREE BOOK BA...*
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*13_ TO_14*
Roshan a firgice ya yo kan Baiwar ALLAH dake kwance, zama yayi gefen gadon tare da
sa hannu yana shafar sumar kan ta, cikin sassanyar murya yake faɗin "Ammata meya
faru da ke? har da laidar jini?..."
Kallonsa tayi tare da tsiyayar da ruwan hawaye, ta kai idon ta kan Abbah
wanda yake ta ambatar sunanta yana gaishe ta da jiki, ga Aunty Yolash itama a
zaune gefe guda tana cike da mamakin kalaman Baiwar ALLAH akan Razhdeen..
A ranar aka sallame su kuma a ranar da daddare aka kai Baiwar ALLAH
ɗakin mijinta, anyi niyar yin party amma sakamakon rashin lafiyar ta yasa aka
dakatar.
Misalin ƙarfe 10 na dare kowa ya watse daga part ɗin Amarya sai iya
ita kaɗai ce ta rage a tsakiyar fantamemen gadonta na alhurma, tana rufe da mayafi
akan ta sai sharar kuka take gaba ɗaya eyes ɗinta ya yi jawur,
Tana cikin wannan halin sai taji an turo ƙofar ɗakin tare da yin
sallama, wasu irin ƙamshin turaruka ne yake dukan hancin ta kala-kala alamun ba
mutum ɗaya bane,
Abokanan Ango ne suka rako Ango ɗakin Amaryarsa a ciki har da
Razhdeen, wani daga ciki ne ya fara ƙirarin "Amarya bakya laifi ko kin daki
hancin twins ɗin Ango..."
Suka kalli Razhdeen dake tsaye a wurin bakin ƙofa su kuwa duk suka
kwashe da dariya, Roshan zama yayi a bakin gado yana bin Baiwar ALLAH da kallo
dake lulluɓe da mayafi,
Sai da Angwaye suka gama musu nasiha da shawarwari tare da musu fatan
alkhairi, kallon Razhdeen suka yi tare da faɗin "Major kai ba abinda zaka ce
ne?.."
Baiwar ALLAH jin an ambaci sunan Major yasa ta ɗan ɗago da kanta ta
cikin mayafi take binsu da kallo har eyes ɗinta suka sauƙa akan Razhdeen wanda yake
takowa a hankali ya nufo wurin Roshan tare da ajiye masa wani ƙaton laida wanda
yake ɗauke da naman chicken da su eggs har da su kayan fruit da laimuka kala-kala,
ya ɗauki hannu ya ɗora akan kafaɗar Roshan yana jijjiga shi,
Shima Roshan ɗago wa yayi yana sau masa ƙayataccen murmushi, shima Razhdeen sake
masa nasa murmushin ya yi a haka suka yi sallama,
Duk fice wa suka yi aka bar Ango da Amaryarsa, ita kuwa Baiwar ALLAH wani sabon
kuka ne ya sake kuɓuto mata,
Roshan ne ya kulle ɗaki tare da yo wa kan Amarya yana faɗin "Ammata
na an zamo Amarya yanzu kuma sauran ki zamo maman Baby.."
Ya ƙarasa maganar tare da ɗage mata mayafin kan fuskar ta,
abinda ya tarar ne ya ji sam bai ji daɗi ba ganin yanda take ta sharar kuka,
Murya ciki-ciki ya soma faɗin "Ammata what's wrong with you? please kiyi haƙuri ki
sanar mun matsalar ki, kinsan yanzu a hannu na kike duk wani matsalarki da issues
ɗinki duk suna rataye a wuya na ne,
ki taimaka ki sanar mun..."
Roshan riƙo hannun ta yayi yana shirin ɗago ta tare da faɗin "tashi
muje muyi alwala muyi sallah ko ƴar lelen mijin ta..."
Zamar da hannun ta tayi fuska a ɗaure ta ce "kaje ka fara yi
mana..."
Ya ce "Okay bari toh naje nayi tinda Allah ya haɗa ni da mata mai
alkunya..."
Baiwar Allah ko ɗagowa tayi ta kalle shi ma bata yi ba.
Shi kuwa tashi yayi ya shiga bathroom bayan wasu mintuna sai ga shi ya
fito, itama tashi tayi ta shiga ta ɗauro alwala sannan ta fito suka tsayar da
sallah a tare, bayan sun idar suka ci suka sha cikin ƙoshin lafiya ba tare da
ɓacin rai ba,
Bayan kammalawa cikin kulawa da dabara Roshan yakai hannunsa kan
hannunta yana wasa da hannun natan tare da jan ta da hirar soyayya, a hankali yake
matsawa dab da ita cikin wayancewa yake faɗin "Ammata nah ke fa ba matar Alaramma
bace ki cire wannan hijab ɗin mana..."
ya ƙarasa maganar tare da sa hannu ya zamar da hijab ɗin,
A zabure Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye fuska a ɗaure tana kallon gefe,
Shima tashi yayi tsaye tare da kamo hannun ta yana faɗin "lafiya kuwa Ammata? ya
naga kamar bakya cikin farin ciki..."
Ganin yana shirin takura mata yasa ta cewa "Please Yaya Roshan ka
ƙyale ni nikam..."
Juyar da eyes ɗinta tayi tare da faɗin "Okay zaka iya fitar mu a ɗaki
yanzu..."
Ta ce "Yes i known what am tooking about, please can you pack your
self and get out inside my room?..."
Roshan kamar zai yi kuka haka yake riƙe da hannunta ya kasa sake wa,
Sai da tayi magana sau uku akan ya sakar mata hannu amma fur ya ƙi,
Cikin zafin nama ta fizgar da hannunta tare da ɗaukar wani ɗan ƙaramin wuƙa na
yankan fruit ta ɗora a saitin maƙogaron ta ido a lumshe take faɗin "Yaya Roshan
wallahi tallahi idan ka cigaba da tsayuwa mun a ɗaki saina ja wuƙar nan ta yanke
mun wuya in yaso kowa ma ya huta da ni...."
Lokaci guda Roshan ya birkice eyes ɗin nan suka yi jawur yana kar
kaɗa mata hannu murya ta ƙi fito wa a haka yabar ɗakin a gaggauce,
Jin shuru yasa ta buɗe eyes ɗinta taga baya nan tukun ta ajiye wuƙar ta taho
da sauri ta danna key a ƙofar ɗakin,
Wani ruɗaɗɗen kuka ne ya zo mata ba shiri, haka ta doku saman gadon tana
rera kukan ta...
Bayan kwana biyu An kawo Amaryar Abbah itama cikin ƙoshin lafiya,
kowa ya watse daga matar gida sai yaran gida sai kuma Roshan dake can part ɗinsa
shima da Amaryarsa,
Pinky da Rukky sun shirya tsab zasu koma karatu ƙasar London,
Aunty Yolash ma ta koma Bauchi wurin Aikin ta, daga Ummy sai Ƴar tiny da Babbar
Auntyn su Minal, sai kuma Amaryar Abbah Ummu Salamah wacce suke ƙiranta da Ammy,
Itama Ramlat tana nan bata tafi ba tana so ta ɗan ƙara hutawa kafin ta
koma...
Ta ɓangaren Ƴar Amana kuwa a cikin daren nan ko rimtsawa batayi ba, ga
sauran yanda duk bacci ya ɗauke su gaba ɗaya an rarrage mutanen su waɗanda aka
kamo ta hanyar kashe su,
A washe garin Jumma'a ne za'a kashe Ƴar Amana da misalin ƙarfe 6:00 na asuba,
sumar kanta kuwa har yanzu bai fara tofowa ba,
A wannan lokacin har ta saddaƙar cewa babu wanda zai zo ya cecesu
daga halin da suke ciki, tayi kukan har ta gaji,
Dab da asuba ƙarfe 4 Yar Amana bata san lokacin da bacci ya ɗauke
ta a zaune ba,
Lokaci guda wani farin haske ya bayyano kan goshinta kafin ƙibtawar ido
har hasken ya ɓace kamar walƙiya, hasken bai sauƙa a ko ina ba sai a kan goshin
Razhdeen dake kwance yana ta shan baccin sa, a lokacin ne ya fara wani irin
mafarki akan Ƴar Amana,
A cikin mafarkin aka bayyana masa halin da Ƴar Amana take ciki, abu
kamar video haka yake gani a cikin mafarkin tin daga farkon al'amarin har zuwa
yanzu da kuma yanka ta da za'ayi a gobe juma'a,
Ya juma yana wannan mafarkin mai birkitar wa kafin daga bisani aka
farkar da shi,
A ruɗe ya tashi yana fitar da numfashi sama-sama kamar wanda aka ɗage masa
numfashi, gaba ɗaya ya yi jirib da gumi duk da sanyin A.C da ke cikin room ɗin,
Idanuwansa ne suka sauƙa akan Ƴar Amana dake tsaye a gabansa da
wannan kan natan da babu sumar gashi ko ɗaya yanda kasan madubi,
ta zuba masa ido babu alamar annuri a fuskar,
Zaro eyes ɗinsa shima yayi yana binta da kallo lips na motsi a hankali yake jera
Addu'o'i,
Ji yayi an dafa kafaɗarsa ana faɗin "what are you looking for?
kayi mummunar mafarki Koh?...."
Sai a lokacin idanuwansa suka fara ganin dai-dai ashe Marshall Mohandas ne ya shugo
ɗakin shi kuma sai yake kallon Ƴar Amana a madadin sa..."
Da sauri Razhdeen yakai eyes ɗinsa kan wayarsa sai yanzu ya tuna da message ɗin da
aka turo masa, a gaggauce yasa hannu ya ɗauki wayarsa ko message ɗin yana da alaƙa
da ita,
Ai kuwa cikin sa'a yana buɗe wa yaci karo da Address ɗin yanda Ƴar
Amana take can cikin daji ne, ana ƙiran dajin da suna dajin dutse, da kuma lokacin
da za'a aikata ƙiyama...
Yanda Mohandas yace haka Razhdeen ya yi, shiga toilet yayi tare da
ɗauro alwala ya fito wannan lokacin kam a gida ya yi sallar asuban sa, bai tsaya
wata-wata ba ya yi shirinsa cikin kakin soja irin na ƙasar U.S, ya fito a Major
General Razhdeen ɗinsa, ya ɗaure sumar kansa da wani jan ƙyalle mai zanen gum a
jiki, kayan sojojin nan ba ƙaramin masa kyau suka yi ba duk da a birkice yake,
Shima Mohandas yayi shirinsa na kakin soja shima na ƙasar U.S duk suka
ɗauki bindigun su already an kawo musu jirgin da zai kai su cikin dajin domin sun
shigar da bayanai sosai duk da basu tabbatar ba tukun...
Guess yana tsaye da baƙar hula a fuska daman shi koda yaushe
fuskarsa a rufe take, babu wanda yasan kamannun sa,
Yallaɓai tashi yayi ya nufi wurin da Ƴar Amana take a durƙushe, ya ɗagota
sannan ya since mata igiyoyin da aka ɗaure ta da shi, yana faɗin "Allah sarki
kurmiyar Allah yau za'a wuce ƙiyama, idan kinje kice ina gaida su mutanen mu da
kuma sabuwar Shugabar ku mace da aka kawo wato Madam Aliya wacce nayi silar
mutuwarta ta hanyar doke motar ta da trailer, da kaina nake tuƙin babbar mota
trailer nayi fushhhh na doke motar ta, domin ta maye mun gurbin shugabanci nah a
gidan marayu, Ni kuwa bazan juri ganin haka ba, ohhhh ashe dai ke baki santa ba
lokacin nasa an sace ki sorry! sorry!! sorry!!!, ki dai gaishe ta kinji ko?..."
Yana ƙarisawa ya hankaɗata gaban Guess sannan ya wulla masa wuƙa yana
faɗin "yanzun nan ba tare da ɓata lokaci ba ka yanke mata maƙogaro..."
Guess yanjo ta yayi tare da ɗora mata wuƙar akan wuya ya ɗaga mata
haɓar ta sama,
Yallaɓai wani irin murɗaɗɗen murmushi yayi ya ce "ehen gurza mata wuƙar..."
Guess dai ya kasa ai watar wa wuƙar kawai ya ɗora mata amma ya kasa gurzawa,
Yallaɓai ganin Guess bazai yanka ba yasa ya fitar da ƙaramin bindigar
sa ya saita kan Guess yana faɗin "Guess kafin na ƙirga 1 zuwa 5 ka yanke mata
maƙogaro in ba haka ba saina fasa maka kai sannan itama na kashe ta, ta tabbata
kenam kai ka barta ta gudu ko?..."
Shuru Guess ya kasa aiwatar wa, Yallaɓai ne ya fara ƙirge kamar haka
"I, 2, 3..."
Guess ganin Yallaɓai da gaske yake kuma yana matuƙar tsoron mutuwa a
hankali ya fara danna wuƙar yana shiga a hankali, nan jini ya fara zubowa sakamakon
shigarta da wuƙar ya fara yi...
Bata kula shi ba ta cigaba da aikin ta, ya ce "dan ALLAH zan iya sanin
laifi na? ki sanar mun a yanzu zan iya durƙusa miki na baki haƙuri, amma kina
azabtar dani Ammata, shin yaushe zaki bani lokaci na ne a matsayina na mijinki?..."
Juyowa tayi tana kallonsa fuska a haɗe ta ce "babu rana, bare wata
bare kuma shekara, tunda har ka Aure Ni a haka sai kuma ka cigaba da zama dani a
haka har sai ran da ka gaji da zama dani..."
tana kaiwa nan tayi ficewar ta, ta bar shi a kitchen shi kaɗai....
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*15_ TO_16*
A lokacin yasa aka ƙira masa wani Abokin sa babban Doctor yazo shi
kaɗai da kayan aiki domin an sanar masa cewa Razhdeen ne ya samu hatsari kuma ba'a
buƙatar zuwa hospital, bayan wasu mintuna sai ga Doctor ya zo da akwatin kayan
aiki a hannun sa, da sauri ya yo kan Razhdeen zai duba shi bayan ya isko shi a
bedroom.
Razhdeen yana kife akan gado babu riga a jikin sa ga kibiyoyi guda biyu
da Mohandas ya cire masa akan drower, Razhdeen ido a lumshe murya ciki-ciki ya
ce "kuje ku fara duba Yarinyar tana cikin mawuyancin hali..."
Doctor ya ce "okay ai sai ku mun bayani tin farko, insha Allahu zanyi iya
ƙoƙari na..."
Daga nan Doctor ya fara cire kayan aikin sa shi kuwa Mohandas fice wa
yayi domin ba'a son a tsaya akan majinyaci idan ana masa aiki...
Abinda Doctor ya fara yi shine ɗinke mata wuya sannan ya sanya mata bandeji
ya ɗaure wuyan, sannan ya juyar da ita ya fara ɗinke mata wurin da aka soke ta da
kibiya sai da ya gama treat ɗinta sosai sannan ya buƙaci a ɗaura mata laidar jini
domin ta zubda jini sosai..
Mohandas already ya bar wurin tin shugowar Abbah, ya gaishe da Abbah amma
sam yaƙi sauraronsa..
Abbah ya juma sosai a wurin Razhdeen kafin daga baya ya yi tafiyar sa
ya sanar masa cewa zuwa dare zai ƙara zuwa ya duba shi...
Bayan fitar Abbah ba jumawa sai ga Roshan da Baiwar ALLAH sun shugo, gaba
ɗaya hankalin Baiwar ALLAH akan Razhdeen yake, zumuɗinta tazo taga a wani hali yake
ciki domin tinda taji labarin hankalinta yaƙi kwanciya, Roshan shi kaɗai yayi
niyar zuwa ya duba twins ɗinsa amma Baiwar ALLAH ta dage akan cewa zata zo duba shi
itama, babu yanda ya iya haka ya taho da ita...
Jin haka yasa Razhdeen ɗagowa ya kalle ta sannan ya kawar da kansa gefe
tare da haɗe gira, saboda ya tuna maganganun da ta rinƙa yi a hospital wanda sam
bai ji daɗin hakan ba.
Itama kallon sa tayi gaba ɗaya kamar wanda aka ɗaure mata baki, ta kasa
cewa komai lokaci guda taga yayi mata wani irin Mungun kwarjini da kuma shakkarsa,
wani irin harara ya wurga mata ta wutsiryar ido ba tare da Roshan ya gani ba, da
sauri ta sunkuyar da kanta ƙasi kamar zata fashe da kuka...
Roshan kai tsaye upstairs ya haura room ɗin farko ya fara buɗe wa
yaga babu kowa still ya yi gaba ya buɗe room na biyu sai kawai ya tarar da
Mohandas zaune kan kujerar ɗakin yayi tagumi kansa na kallon ƙasi,
Roshan har zai yi sallama idonsa suka sauƙa akan Ƴar Amana dake kwance
saman gado, sake baki yayi yana kallon wurin, daga bisani ya ce "Marshall aina ku
ka samo yaro?..."
A ruɗe Mohandas ya ɗago yana bin Roshan da kallo ganin ya yi masa shugowar
bazata,
Ƙarasa shugowa ya yi still yana faɗin "yaron nan fa meya same shi?..."
Mohandas ya ce "samu wuri ka zauna tukun, wannan ba yaro bane
yarinya ce..."
Haɗe gira Roshan ya yi tare da faɗin "taya ya zai zamo mace bayan ga
kansa a tanɗe kamar lale kobo..."
Mohandas ya ce "bazaka fahimta bane in har ba bayani aka yi maka
ba..."
Roshan ya ce "okay ina jinka..."
Mohandas ne ya kuma cewa "mun ɓoye ta ne a cikin gidan nan ba tare da kowa
ya sani ba, kuma bama buƙatar kowa ya sani daga Ni sai kai sai kuma uban gayyar
wato Razhdeen da kuma likitan da yayi musu magani..."
Mohandas ya ce "gud! Amm daman Roshan inaso zanyi magana da kai Please..."
Roshan ya ce "about Minal ko?..."
Mohandas ya ce "of course, sannan Abbah yazo na gaishe shi amma he
didn't answer me I don't know why..."
Murmushi Roshan ya yi sannan ya ce "kafi sanin kowa dalilin da yasa ba
zai kula ka ba, amma mun kusan kawo ƙarshen wasan..."
Ita kuwa baiwar ALLAH kanta a ƙasi ba abinda take sai kuka domin ba
ƙaramin ci mata mutunci yayi ba...
Roshan da Mohandas ne suka ƙarasa shigowa cikin falon bayan sun gama
jin duk chakwakiyar da suke yi,
Roshan ne ya zaune kusa da Razhdeen tare da dafa kafaɗarsa ya ce
"haba My Man abun gwaninta fa tayi maka bai kamata kayi mata haka ba, Please am
so sorry na amshi bakin ta..."
Razhdeen kallonsa yayi fuska a haɗe ya kuma kawar da kansa gefe yana
faɗin "ka tashi ka fice mun da ita daga gida, next time idan har kasan da ita zaka
zo mun to kaima kayi zaman ka bana buƙatar ku..."
Murmushi Roshan ya yi tare da faɗin "duk mai ya yi zafi haka My
Man?..."
Tsuka Razhdeen ya yi tare da ƙoƙarin tashi zai bar wurin, kasa tashi
yayi sai da Mohandas ya tallafa masa tukun daman shine mai taimaka masa da wasu
abubuwa, suna tafiya hankali sai da suka ɗan yi nisa kaɗan sannan Razhdeen ya
waiwayo idonsa akan Roshan wanda shima miƙewa yayi zasu tafi
ya ce "Please kana zuwa kana duba mun jikin Yarinyata..."
Razhdeen bai bashi amsa ba ya juya gaban sa, Mohandas ne ya kuma cewa "kar
ka manta Yarinyar kasan a Kashmir take..."
Roshan ya ce "Okay don't worry..."
Duk sunyi wannan maganar ne saboda kar Baiwar ALLAH ta fahimci wani
abu..
Da haka suka kammala Roshan ya ja matarsa suka tafi, Razhdeen kuma kai
tsaye room ɗin da Ƴar Amana take ya nufa shi da Mohandas domin hawan upstairs zai
bashi wahala indai ba riƙe shi akayi ba ...
Baiwar ALLAH wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya daki saitin zuciyar ta jin
Razhdeen ya ambaci sunan wata da Yarinyarsa,
Da wannan tunanin a cikin zuciyarta suka isa gida....
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*17_ TO_18*
WASHE GARI
Baiwar ALLAH ne zaune akan sopar falon ta tana kallon plasman abin ta,
Daga ganin yanda take ta zuba murmushi kasan Film ɗin yayi matuƙar burge
ta, Minal ce ta shigo tana lanƙaye da handbag ɗin ta ko sallama bata samu damar
yi ba, tazo ne saboda Roshan ya riga da ya sanar wa Abbah cewa zasu fita unguwa,
Baiwar ALLAH a bazata taji Minal ta ce "ina Yaya Roshan?..."
Baiwar ALLAH ɗago wa tayi tana binta da kallo ko amsa bata ba ta ba.
Minal ta ce "Malama magana nake miki dai ko dai kin kurmance ne?..."
Baiwar ALLAH dai shuru tayi bata ce mata komai ba sai cigaba da
kallonta da ta yi, Minal tsabar ƙololuwar baƙin ciki bata san lokacin da
ta fincikota ƙasin carpet ba tare da faɗin "ba magana nake miki ba dan ubanki,
aikin banza kawai idan baya nan ki sanar mun mana..."
Roshan ya ce "Minal kin dai san mata ta ce ko? kamar yanda kike respecting
ɗina ya zama dole itama kiyi mata, idan kika raina ta toh kamar ni kika raina ne,
so be careful..."
Maganganun Roshan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, kamar zata yi kuka
ta ce "Sorry in ba dan uzuri ne ya kawo ni ba babu abinda zan zo yi ɓangaren ta
tinda ita batada mutunci..."
bata san lokacin da ta fara kuka ba tana faɗin "Yaya Roshan dan
ALLAH kayi haƙuri wallahi in har bada taimakon ka ba babu yanda zanyi na samu
Marshall, Abbah yana shirin haɗani da wani Abokinsa kaima kasan da haka, ya
hanani fita ko ina koda wurin aiki ne, sojojin gidan suna nan koda yaushe babu
halin fita ba tare da kai ba, wallahi ina son Marshall inaji a jikina bazan iya
rayuwa ba tare da shi ba, shekaru na sunata ja ina buƙatar yin Aure ga wanda nake
so, ka taimaka..."
Minal tana fita daga part ɗin Roshan kai tsaye wurin swimming pool
ta nufa tana kuka..
Tana kuka ta ce "Yaya Roshan babu wanda ya damu da damuwa ta, ina cikin
wani halin da ba kowa ne zai fahimce ni ba, kai ma da kake son taimaka mun yau kana
shirin juya mun baya saboda matar ka..."
Nan ta fashe da kuka sosai,
Riƙota yayi yana faɗin "lolz my bloody bai kamata ki yanke wannan hukunci a kanki
ba, kiyi haƙuri ina tare da ke, yanzun muje mu tafi ko..."
Rufe bakin ta tayi da hannaye biyu tana dariyar farin ciki, cikin nuna
farin ciki ta ce "Nagode sosai Yayana..."
Iya su biyu suka shiga mota ba tare da security ba Roshan shi yake
driving, sojojin bakin gate ganin Roshan ne yasa suka buɗe masa gate,
Kai tsaye wurin da za'aje a ɗaura Auren suka nufa, Mohandas kuma Roshan
ya tura masa da Address yanda suke saboda in har yaje gidan Razhdeen ɗaukar sa za'a
samu matsala sakamako sojojin da suke gidan Razhdeen zasu iya sanar wa Abbah halin
da ake ciki...
A wannan ranar kwata-kwata Roshan bai rintsa ba, kuma bai sanar
wa Abbah halin da ake ciki ba, a yayin da Minal take cikin farin ciki, tana kwance
a ɗakinta da waya a hannu alamar video call take bada kowa ba sai da mijinta
Mohandas, shima yana cikin farin ciki ta wani ɓangaren kuma yana tunanin kalar
hukuncin da Abbah zai ɗauka idan yaji wannan batun, gaba ɗaya a tsorace yake, ita
kuma Minal bata tunanin komai kuma bata jin komai a ranta, abu ɗaya ne yake damunta
shine rashin kasancewar ta tare da mijinta...
Roshan sai da yayi kwana uku yana inda-indar sanar wa Abbah, sai a
yau ya cire fargaba ya gayyato Mohandas zuwa gidan su a yau za'a sanar wa Abbah
dake yau ranar hutunsa ne babu fita aiki...
Mohandas yana zuwa Sojojin suka buɗe masa gate ya shige already
Roshan ya sanar musu cewa Mohandas zai zo ba tare da Abbah ya sani ba,
Roshan ne tsaye a wurin parking yana jiran isowar Mohandas cikin lokaci
ƙanƙani sai gashi ya iso, a tare suka nufi babban falon gidan suna shiga suka
tarar da Ummy uwar masu gida ita da Ammy da kuma Baiwar ALLAH zaune suna karatun
wani ɗan littafin hadisi, da dukkan alamun Ammy ce take koya musu wasu abubuwa a
cikin littafin, jin sallama yasa duk suka ɗago tare da amsa sallamar.
Ummy zaro ido waje tayi ganin Mohandas ɗan maƙiyin Abbah kuma shima
maƙiyin ne tinda yana neman ɗiyarsa,
Ammy kuma dake bata san Mohandas ba yasa ta fara sakin murmushi tana
faɗin "babban baƙo mukayi ne? sannu da zuwa Roshan ga wuri ku zazzauna..."
Hakan kuwa akayi duk zama suka yi, Ammy kuma tashi tayi ta shige kitchen
zata haɗo musu abin taɓawa, Uwar masu gida kuma itama tashi tayi da haura saman
upstairs da gudu zata je ta sanar wa Minal cewa ga Mohandas a gidan su, sai ya
rage iya Baiwar ALLAH a falon, idonta akan Mohandas sau ɗaya ta taɓa ganinsa ran da
suka je gidan Razhdeen nan ma bata ƙare shi da kallo ba sai yau, haka kawai take
jin tsinkar jikinta yana tashi ga wani irin bugun zuciya, ta rasa meye dalilin
faruwar wannan al'amarin, shima Mohandas ɗin kallon ta yake ya dai san itace
Amaryar Roshan amma bai gaba saninta ba sai yau shima yana jin wani abu sosai a
kanta,
Idon Baiwar ALLAH ne suka sauƙa akan wani ɗan sarƙar dake ɗaure a
hannunsa shigen irin nata, sai dai ita a wuyanta yake ɗaure kuma akwai mayafi a
kan ta balle ta sake ganin kalar natan, ƙirjinta ne yake wani irin bugawa sosai,
A lokacin ne Abbah ya fito daga part ɗinsa wayar sa a ɗore kan
kunne sai muryarsa kake ji yana ta waya,
da haka ya gama sauƙowa daga upstairs idonsa ne suka sauƙa akan Mohandas
kamar wanda aka ɗauke masa wuta haka ya tsaya cakk.
Itama Minal fitowa tayi da gudu ita da Ummy suka sauƙo falo, Ammy ce ta
jejjera musu kayan abinci akan table ɗin falo saitin gaban Mohandas,
Abbah ne ya sanar a wanda yake waya dashi cewa "Please I'll call you
back, cut the phone..."
Still idonsa akan Mohandas, shima Abbah zama yayi yana fuskantar su ba tare
da ya ce komai ba..
Mohandas kasa magana yayi sai Roshan ne ya yi ƙarfin halin cewa "Am
Abbah daman akwai maganar da muke so muyi ne..."
Abbah ya ce "nasan akan maganar Amina ne ko? wai shin dole sai ɗiyata
zai Aura ne? nace bazan taɓa haɗa jini da familyn su ba kuma babu mahalukin da ya
isa yasa na haɗi, dan haka ya tashi ya bar mun gida tin kafin na fusata..."
Abbah tashi yayi zai koma ciki Roshan ya ce "Abbah Please ka bamu
lokacin ka..."
Abbah a fusace ya juyo yana faɗin "Roshan ka maida hankalinka na gaya
maka, ka fitar mun da wannan ƙabilan a cikin gidan nan..."
Roshan gaba ɗaya jikinsa ne ya yi sanyi, bai san lokacin da ya fara zubda
hawaye ba, sai yanzu ya yi nadamar aikata hakan..."
Abbah kallon Minal yayi tare da faɗin "kin kyauta, amma ki sani cewa
bazai bar gidan nan ba tare da ya baki takardar sakin ki ba..."
Sai a wannan lokacin Mohandas ya buɗe baki shima wurin cewa "kayi haƙuri Abbah
bazan iya sakin ta ba..."
A fusace Abbah ya ce "haka kace ko? to ku jira Ni ina zuwa, yau zan nuna
muku zamani na ya ninka naku sau ba adadi..."
ABBAH yana kaiwa nan da sauri ya haura upstairs domin akwai abinda yake son
ɗauko wa (kodai gum ɗinsa zai ɗauko 🤣🤣)
Abbah da Ammy suna cikin bedroom ɗinsu sai ji sukayi an ƙarƙame su,
ga bindiga a hannun Abbah yayi ƙolon duniya akan azo a buɗe mishi ƙofa amma babu
wanda ya nufi wurin, ga wayar sa ya barta a falo balle ya ƙira sojojin gidan gaba
ɗaya Abbah ya rasa mai yake masa ciwo, ita kuwa Ammy alwalarta tayo tazo ta
tsaida sallah domin a halin yanzu Abbah ba sauraronta zai yi ba,
Baiwar ALLAH tana so taje ta buɗe musu ƙofar jin yanda Abbah yake
ta ƙiraye-ƙirayen sunayen su especially sunan Uwar masu gida yafi ƙiran ta akan
taje ta buɗe amma Ummy fur taƙi zuwa sannan tana riƙe da hannun Baiwar ALLAH taƙi
sakin ta,
Ummy tana kuka ta ce "haba Aunty Dota har yaushe za'a kawo karshen
wannan bala'in ƙiyayyar Abbah da su familyn Yaya Mohandas? Aunty Minal da Yaya
Mohandas suna matuƙar ƙaunar junan su hakan yasa bazata iya Auran kowa ba kuma
kinsan a halin da take ciki, ita fa ba ƙaramar yarinya ba ce, tanada matsalar
matsinancin sha'awa amma Abbah ya kasa ganewa, Yaya Mohandas saboda soyayyar Aunty
Minal ya musulunta fa, ai abun alfahari ne wallahi, don haka baza'a buɗe ƙofar nan
ba sai har Yaya Roshan ya dawo tukun..."
Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta rasa mai zata ce a wannan al'amarin gashi
bata san meya haɗa ƙiyayyar ba, amma itama tana mungun tausaya musu sosai...
Ganin bazata iya juran ƙiraye-ƙirayen sunayen da Abbah yake yi ba yasa
ta fice a falon gaba ɗaya, kai tsaye can part ɗinta ta nufa zuciyarta a
jagulgule...
Dab da mangariba sai ga motar da ake kai Ƴar tinny school kuma a
dawo da ita, a falo ta tsaya tare da jefar da jakar ta anan taci karo da wayar
Abbah akan kujera, ɗauka tayi tana faɗin "Yaaa wayan Abbah..."
Da gudu ta haura upstairs ta nufi room ɗin su Abbah, buga ƙofar ta soma yi
tana ƙiran sunan Abbah tare da faɗin "Abbah ganan wayay ka..."
Daga ciki Abbah ya ce "yawwa Auta duba mun akwai key a jikin ƙofar?.."
Bata ɓoye masa ba ta ce "yana ciki Abbah amma ban sani ba ko yayi
bacci..."
Da sauri ta nufi part ɗin Roshan wanda tunda aka kawo ta gidan nan bata taɓa
zuwa part ɗinsa ba, duk da bata san ina ne room ɗinsa ba amma da haka ta lalumo
ganin shima yana ƙoƙarin fitowa ne,
Jin ƙira daga Abbah ne gasa zuciyarsa bugawa da ƙarfin gaske, babu
yanda ya iya domin ya rigada ya san ya yi laifi sosai,
Yana shiga falo ya tarar da Abbah tsaye ya kasa zaune,
Abbah yana ganinsa yaje gaban Roshan ya zabga masa mari, kafin Roshan ya
ɗago Abbah ya ƙara zabga masa mari..
.
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*19_ TO_20*
A kwana a tashi sai hantsi, yau da Gobe sai ALLAH Ƴar Amana jiki
yayi sauƙi sosai, babu wani ciwo a tattare da ita sakamakon kulawar da ake bata,
Roshan shine likitan ta kullum sai ya je ya duba ta, yanzu Ma sha ALLAH!.
Abu ɗaya ne yake damun ta yanzu kuma yake hanata wargi shine rashin
sumar kanta, yanzu almost 3 weeks kenam tin lokacin da ta sanya hula a kanta bata
taɓa buɗe wa ba koda wanka zata yi saboda ji take kamar ta hallaka kanta in ta ga
ƙoƙon kanta ba gashi.
Razhdeen yayi iya dabarar sa akan ta cire hular ya gani ko gashi ya fara
tofowa amma furr taƙi yadda...
Yau ranar Sunday Razh da Rosh ne suke zaune a babban falon cikin gidan
Abbah a yayin da shima Abbah yake zaune a ɗaya daga cikin jerukan kujerun falon,
iya su uku ne da duk kan alamun akwai tattaunawar da suke yi.
Abbah ne ya kalli Razhdeen sannan ya ce "Deen wai yaushe zaka koma
wurin aiki ne?..."
Idonsa na kallon gefe ya fara motsi da lips ɗinsa murya ciki-ciki ya ce "Dadd sun
turo mun da letter akan na koma zuwa end of this month..."
Abbah ya ce "shine baka sanar mun ba sai da na tambaye ka, yanzun zuwa
lokacin zaka tafi?..."
Razhdeen ɗaga masa kai kawai yayi ba tare da ya furta komai ba..
Jinjina kai Abbah yayi sannan ya ce "Deen bana so ka bar ƙasar nan ba tare da ka
tsayar da wacce zaka Aura ba, domin in har kasa ƙafa ka tafi ban san ranar dawowar
ka ba, zaman ka a haka ba Aure kuma ba son haka nake ba..."
Razhdeen kallon Abbah yayi tare da cizar laɓɓensa na ƙasi kamar mai
nazarin wani abu..
"Whatt?..."
Abbah ne ya furta haka yana maida kallonsa kan Roshan.
Roshan ne ya kuma cewa "seriously Abbah..." ganin irin kallon da
Abbah ke masa..
Razhdeen wani irin kallo yake watsawa Roshan ganin bazai iya kame
bakinsa ba,
Da sauri Razhdeen ya rubuta text ta wayarsa ya tura wa Roshan.
Shima Roshan jin saƙo ya shugo masa waya yasa yayi saurin dubawa yaga ashe
twins ne,
Abinda ya rubuta shine:
"ka cika surutu twins, yaushe na sanar maka cewa ina son yarinyar? I just pity her
because she need help, please twins kar kasa Dad ya bincika yanda yarinyar take
banason kowa yasan ina tare da ita i beg.."
Roshan yana gama karantawa shima ya tura masa saƙo da cewa "ok
don't worry my Man..."
Razhdeen fuska a ɗaure ya ce "i don't have any lady Dad, kawai ya
sanar maka ne batare da ya sani ba shima..."
Abbah ya ce "Please Deen bana son maganar wasa fa..."
Razhdeen ya ce "seriously Dad ban taɓa cewa ina son ko wace mace ba,
ban sani ba ko sai zuwa gaba, but ina neman Alfarma a barni sai na dawo daga U.S
kafin a fara mun wannan maganar..."
Razhdeen zuciyarsa ce ta fara ƙuna kamar wanda aka zabure shi ya miƙe
yana faɗin "Dad zan tafi gidan da nake idan akwai wani damuwa a tuntuɓe ni..."
yana kaiwa nan yayi ficewar sa daga falon, shima Roshan tashi yayi
da sauri ya bi bayansa.
Shi dai Abbah zuba musu ido kawai yayi sakamakon rashin abun cewa...
Abbah yana zaune shi kaɗai a falo yana duba saƙonnin da aka turo masa
ta waya, sai ga Ammy ta shugo falon da sallama a bakin ta,
Abbah ya amsa mata cikin fara'a, durƙusa gwiwowinta ƙasin carpet tayi
fuska ɗauke da murmushi ta ce "Barka da hutawa Abban yara..."
Murmushi tayi tana faman rufe fuska da hannu ta ce "ai ba'a gajiya da
neman lada, idan ka kawo mun ƴan aiki ai shikenam nayi banƙwana da fin rabin ladan
da nake samu..."
Abbah miƙewa yayi akan zasu tafi yaga har yanzu Ammy tana nan a
durƙushe bata motsa ba, murmushi yayi domin yasan halin ta indai ba shi ya bata
umarnin ta tashi ba to sai dai ta kwana a wurin..
Gyaran murya yayi mata tare da faɗin "toh Mar'atussaliha zaki iya
tashi ko..."
Murmushi tayi sai a lokacin ta motsa itama ta miƙe tsaye suka bar
falon...
Tin shugowar su gidan suke jin ƙarar sound na kiɗa an ƙura volume
sosai,
Razhdeen kallon Roshan yayi jin ƙarar waƙa a gidan, Roshan da bakinsa ya gagara
yin shuru ya ce "waye ya kunna waƙa kuma? na farko dai Sarah kurmiya ce bata jin
sound balle....."
ya gagara ƙarisa maganar ganin Razhdeen ya wuce ya bashi wuri domin
shi ya rigada yasan ita ce...
Roshan dai shuru yayi ya bi bayansa ba tare da ya ƙarasa maganar ba,
Suna shiga falo ai kuwa sai suka tarar da Ƴar Amana sai ɗirkar rawa take
tayi ita kaɗai, har suka shugo bata san sun dawo ba, shi dai Roshan zama yayi
sai dariya yake ta mata,
Razhdeen ne ya ɗauki remote ya kashe waƙar, da sauri ta juyo tana
kallonsa gira a haɗe kamar zata fashe da kuka...
Roshan ya ce "ai da ka bar mata waƙar tinda nata so, domin idan tana
cikin nishaɗi zata rage wasu damuwar..."
Ƴar Amana cikin fushi ta wuce da gudu ta nufi part ɗinta can falo na
biyu saman upstairs ga hula tum a kai irin hular sanyin nan...
Roshan ya ce "to banda abinka ai dole zata haɗa duk biyun tinda duk ta
same su, amma na fahimci tana son kiɗe-kiɗe da rawa duk da kurmiya ce amma tana jin
komai da komai mayar wa ne kawai bazata iya ba, shawara ɗaya tinda tana son hakan
mai zai hana a shigar ta makarantar koyan rawa? kaɗa jita kuwa sai dai ta koyawa
wasu..."
Razhdeen shuru yayi na ɗan wasu lokuta daga bisani ya ce "idan na tafi
wa zai rinƙa kula mun da ita? bazan bar ta ita kaɗai a gidan nan ba..."
Roshan ya ce "to ka bayyanar da ita mana kaga saika ajiye ta a can gidan
mu..."
Girgiza kai Razhdeen yayi tare da faɗin "nop! saina dawo ko hakan zata faru, bana
so ta takura tafi son zama ba tare da mutane ba..."
Roshan ya ce "to ka kaita Bauchi wurin Aunty Yolash tinda ita kaɗai
ce..."
Nan ma Razhdeen ya ce "ba haka ba, shawara ɗaya ya yanke cewa zai kawo wata
ta taya ta zama a gidan nan, akwai security da zai rinƙa kaita school ya kuma dawo
da ita ba tare da kowa ya sani ba har ya dawo..."
Roshan ya ce "okay amma waye zaka ajiye a gidan wanda zai rinƙa kula da
ita?..."
Razhdeen ya ce "akwai wata Christal Madam Blessing zan dawo da ita gidan nan ta
cigaba da kula da Sarah har na dawo, zan rinƙa biyanta salary duk wata, sannan
kaima zaka rinƙa zuwa kana duba ta..."
Roshan ya amsa da cewa "toh shikenam Allah ya bamu ikon kula da ita yanda
ya kamata..."
Suna cikin hirar su kwatsam suka jiyo sautin jitar Ƴar Amana daga saman
ɗakin ta.
Razhdeen miƙe wa yayi ya nufi yanda ɗakinta yake domin indai yaji sautin jitar nan
gaba ɗaya hankalinsa tashi yake, zuwa yake ya zauna dab da ita yana sauraron
sautin,
A falo ya bar Roshan shi kuwa tashi yayi ya tafi domin yasan dalilin
ruɗewar twins ɗinsa...
Juya masa ƙeya tayi tana turo baki, jawota yayi tsakiyar faɗaɗɗen
ƙirjinsa yana rarrashinta, ita kuwa ƙoƙarin ɗagowa take tana tutture shi ita a
dole tayi fushi...
Ganin bazata iya ƙwacewa ba yasa ta fara kai masa duka har da su cizo a kan
dantsen sa, ko kaɗan bai ji zafin cizon ba sai cewa yake "Sarah are you mad? da
girman ki kike cizo?..."
Asan tashi tabar wurin ne hular kanta ya cire gaba ɗaya, zama
tayi ta kafa masa ido jin hular ya cire, ji tayi kamar ta haɗiyi ranta tsabar
takaicin cirewar hular domin ko zata yi wanka bata cire wa,
Razhdeen ne ya kafa nashi idon akan ta, yana so yayi magana amma ya kasa
tsabar mamakin yanda sumar kanta ya dawo kamar yanda yake, ita kuwa a tunanin ta
har yanzu kanta a gwigwiye yake, fashewa tayi da wani sabon kuka ta tashi da gudu
zata bar ɗakin yayi saurin riƙo ta tare da juyar da ita saitin gaban mirror,
Ƴar Amana zaro ido tayi waje sosai kamar zasu faɗo ganin yanda sumar
kanta ya dawo kamar ba'a Aske ba.
Hannayenta biyu tasa a kan sumar tana cakwarkwayawa taga dai gashin
ta ne da gaske, shima Razhdeen hannu yasa yana murza zirin gashin cike da
mamakin ganin ikon ALLAH.
Cikin wata uku gashi ya dawo yanda yake ba tare da kowa ya sani ba,
kanta sanye da hula amma bata san an maido mata da gashi ba..
Ƴar Amana wani irin farin ciki ne ya wanzu mata lokaci ƙanƙani a
ruɗe ta juya ta rungumi Razhdeen sosai tana tsallen farin ciki, shima kan shi
Razhdeen ɗin abun ya nishaɗartar da shi domin a halin yanzu ganin Ƴar Amana a cikin
farin ciki tamkar anyi masa bushara da gidan Aljanna ne, shima bai san lokacin da
ya tsinci kan shi acikin murmushi ba, rungumar ta yayi yana shafar sumar kanta
mai murɗi-murɗi kamar yanda yake a baya...
A wannan ranar a tare suka kasance babu wanda ya motsa ko ina a
cikinsu,
Uncle Deen ne zaune a saman gado a yayin da ita kuma Ƴar Amana ta ɗora pillow akan
cinyarsa tare da ɗora kanta akai, yana wasa da gashin kanta har bacci yayi awun
gaba da ita dake yanzu dare ne already sun ci sun sha ba tare da wata matsala ba,
yanzu misalin ƙarfe 10 ne na dare, Razhdeen sai da ya fahimci tayi nisa sosai a
baccin ta tukun ya gyara mata kwanciya ya rufe ta da mayafi daga bisani ya kashe
hasken ɗakin shima ya fice a ɗakin tare da kulle room ɗin da key ya nufi part
ɗinsa...
🌝🌝🌝
"Wallahi tallahi bazai yu ina fama da kaina ki baro gidan mijin ki kizo ki ɗora mun
wahala ba, ke wato ƴar hutu ko? to bari kiji ni ba boyi-boyin ki ba ce da har kina
kwance sai dai na dafa ki ci ba, sai dai ki bar mun gida ehen..."
Hajia Kilishi tana kuka ta ce "haba Uma Saratu ke fah ƙanwar mahaifiyata
ce, shin idan baki riƙe ni ba wazai riƙe ni, mijina ya ƙi karɓa ta ko ina naje gudu
na ake, ga a wurin aiki an kore ni..."
ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka..
Uma Saratu tana tsaye sai faman zabga mata harara take ta sau ajiyar zuciya
tare da faɗin "kin san dalilin da yasa ake ƙin ki?..."
Uma Saratu ta cigaba da cewa "dalili shine lokacin da kike gidan mijinki duk
danginki ƙin su kika yi saboda kin samu abun duniya, idan dangi suka je gidanki
sun zamo abun wulaƙantawa kenam a wurinki shiyasa yanzu kowa ya fita sabgar ki,
kuma babu mai zuwa yanda kike, kema kuma haka bakya ziyartar ƴan uwanki bare
ƴaƴanki kuma ke kike hanasu zuwa saboda bamu da kuɗi da abun more rayuwa, nasan
dai Chief mijinki yana son ƴan uwanki amma ke danginsa da danginki duk bakya
ƙaunar su, kinfi son ki zauna daga ke sai mijinki da ƴaƴanki bakya son wani ya
raɓe ku, yanzu kuma da ALLAH ya tashi jarabtarki sai kika rasa komai naki, babu
miji, babu ƴaƴanki sannan babu kuɗi kuma kin rasa aikin ki, daman mijinki ne ya
sama miki yanzu kuwa yasa an kore ki sai mu ga ta gadara, ai Allah ne ya taimake
ki dana karɓe ki da kuma naji tausayinki, aikin banza aikin wofi nasan inda
mahaifiyar ki da mahaifinki suna raye da tinin suma sun yar da ke saboda ke butulu
ce mai manta alkhairi, gashi kin jawa kanki abun kunya labari ya baza ko ina cewa
kina yawon bin hotel da Auren ki tir da halin ki wallahi, kuma gashi waɗanda kike
bin su hotel suma sun gudu sun barki babu mai sauraron ki, hatta ƴaƴan da kika
haifa a cikin ki tinda kika dawo gida babu wacce ta zo bare mijinki, ki ma fidda
rai akan Chief domin shi ya riga da yayi Auren sa, ya Auro ƙanwar matarsa ta farko
mutumiyar kirki,
Idan kin gama kukan ki ga can wanke-wanke da shara suna jiran ki..."
Uma Saratu tana kaiwa nan tayi ficewarta daga cikin ɗakin Hajia Kilishi wanda ya
kasance iya katifa ne a shimfiɗe a ƙasi ko ledar ɗaki babu bare carpet....
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*21_ TO_25*
Ya ce "Dan ALLAH..."
Jin kamar a cikin damuwa yake yasa ta buɗe masa, ganin a halin da yake
ciki ne yasa ta firgita, yana kame da cikin sa da hannu bibbiyu ko miƙe wa baya
iya yi, eyes ɗinsa duk sun kaɗa sunyi jawur, yana fitar da numfashi da ƙer, kamar
wanda aka hankaɗo shi jiki na ɓari ya shugo cikin bedroom ɗinta, wuri ya samu a
bakin gado ya zauna domin idan ya cigaba da tsayuwa zai iya faɗuwa ne...
Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta gama tsorita domin a halin da yake ciki
kamar mutuwa zai yi,
Murya na kakkarwa ta ce "mai ya faru da kai Yaya Roshan?..."
Wani abu taji ya daki zuciyarta cikin nuna fushi ta ce "Roshan please
stay away from me, kana buƙata ta amma ni sam bana ra'ayin hakan, ko ana dole ne?
shin ni kake so ko biyan buƙatar ka?..."
Haka lips ɗinsa yake kakkarwa haɗe da teeth ɗinsa kamar mai jin
sanyi ya ce "ke ke ke nake so Ammata..."
Murmushi tayi sannan ta ce "to indai har da gaske kana sona inaso ka
cire wannan batun daga bakin ka, kafin kayi Aure shin neman mata kake yi ne? nasan
baka neman mata haka kake haƙuri har tsawon shekaru, to yanzun ma inaso ka cigaba
da haƙuri ka zauna da ni a haka idan zaka iya..."
Murya cikin tsawa ta ce "saboda bana sonka Roshan, bana jin sonka a cikin
zuciyata, baka san irin raɗaɗin da nake ji a cikin zuciyata ba dana kasance inada
igiyar Auren ka,
Roshan idan nace zaka samu farin ciki daga gareni nayi maka ƙarya domin
nima an datse mun nawa farin ciki, inaso mu cigaba da zama haka cikin ƙunci nake
ga hakan zai fi..."
Roshan ji yayi kamar ana kwaɗa masa guduma a tsakiyar kansa lokaci
guda ya fara jin hawaye suna masa go slow a saman kuncin sa, girgiza kai yayi
tare da faɗin "kin zalunci kanki da baki sanar mun tin kafin a ɗaura Aure ba,
sannan kin zalunce ni da kika kasa furta mun abinda ke ranki har kika bari aka
ɗaura Aure, amma dan ALLAH inason sanin dalilin da yasa bakya sona?..."
Ta ce "Yaya Roshan kayi haƙuri da abinda zaka ji daga bakina duk da nasan zaka ji
ba daɗi amma rashin daɗin nake so kaji kamar yanda nima ba'a cikin daɗin nake ba,
tin farko zuciyata da kai ta fara aminta amma daga ƙarshe labari ta sauya zuwa kan
Razhdeen..."
Cikin rashin fahimta Roshan yake binta da kallo ya ce "bangane mai kike
nufi ba..."
Ta ce "Razhdeen ya saye mun zuciyata, shi nake so, kuma nake son
kasancewa tare da shi, har yau har gobe son sa bai ragu a cikin zuciyata ba..."
Lokaci guda taji wani irin matsanancin kuka ya yanko mata, kwantar da
kanta tayi kan cinyarsa tana kuka, shima za mo wa yayi ƙasi ya ɗago da fuskarta
suna fuskantar juna ya ce "kukan mai kike? ba nace ki kwantar da hankalin ki ba,
ina dai Razhdeen kike so? to ki yi haƙuri zaki same shi..."
Ya ƙarasa maganar tare da fashe wa da kuka shima ya rungumota jikinsa
duk kukan suke babu mai rarrashin kowa a cikin su...
Abbah ya ce "ina jinka Roshan! naga kamar kana cikin damuwa please tell me
my Son..."
Lokaci guda sai ga hawaye shaɓe-shaɓa akan fuskar sa kamar wanda yake
jira ayi masa magana, kuma daman yana maƙale da hawayen..
Abbah ya ce "Subhanallahi Roshan kuka kuma? kai ɗin? dan ALLAH ka taimaka ka sanar
mun bana so ka rinƙa jefa kan ka cikin damuwa kasan kana da matsalar heart, ka duba
kamar marar lafiyan da yayi shekara a kwance duk ka bi ka rarrame..."
A hankali Roshan yake motsa lips ɗinsa waɗanda suke ta faman kakkarwa
kamar mai jin zunzurutun sanyi, da ƙer ya iya cewa "A A A Abbbah, please help me
my heart so pain........!!!"
lokaci guda ya fashe da wani irin raunannen kuka har sai da ya za
me ƙasin carpet, ya kifar da kansa a ƙasi ba abinda yake sai kuka..
Jikin Abbah ne ya fara ɓari gaba ɗaya ya tsorita da ganin Roshan acikin
wannan hali, cike da mamaki ya nufo wurin da yake shima ya durƙusa yasa hannu yana
ƙoƙarin ɗago shi.
Abbah Ya ce "shin Daughter ce ta mutu? ko kuma tana kwance ne a gadon
asibiti? ka sanar mun mana..."
Roshan rungumar Abbah yayi jikinsa duk ya ɗau zafi murya na kakkarwa yake faɗin
"Abbah Ammata bani take so ba, gaba ɗayan mu babu mai kwanciya hankali, ni bana
cikin farin ciki itama haka, ina matuƙar ƙaunar Ammata amma ita sam ba ni ne a
gaban ta ba, tinda muka yi Aure tsawon wata uku zuwa huɗu yanzu bamu taɓa raya
sunnah ba please Abbah inaso na bar duniyan nan, am really tired of this would,
wannan duniyar cike take da ruɗani da tashin hankali Abbah, ina da abubuwan more
rayuwa amma bani da kwanciyar hankali Abbah..."
Roshan kan sa a kwance saman ƙirjin Abbah ya ce "i told you Abbah,
Ammata bani take so ba, Auren dole akayi mata..."
Roshan ya ce "yess Abbah ta sanar mun duk abinda ya ke ranta, bata sona..."
Abbah ya ce "whattt? to amma ya akayi hakan ta faru, bata sonka kuma akayi Auren?
shin waye a ranta har ta kasa karɓar soyayyarka kuma ta kasa baka haɗin kai...".
Ɗago wa yayi daga kwancen da yake akan Abbah, da rinannun eyes ɗinsa yake kallon
Abbah sannan ya ce "Razhdeen ne a cikin zuciyar ta, shi take so kuma take muradin
ya zamo mijinta uban ƴaƴanta..."
ya ƙarasa maganar yana sakin ƙayataccen murmushin baƙin ciki da kuma
farin ciki...
Abbah gaba ɗaya ya gama ruɗe wa, cike da mamaki ya ce "amma shi Razhdeen bai
taɓa sanar mun wannan maganar ba, ko a bakin wani ban taɓa jin Razhdeen da Daughter
suna soyayya ba...
Roshan tashi yayi da ƙer yana jan ƙafa da haka ya fice, shima Abbah
wayar sa ya ɗau ya danna ƙiran number Razhdeen cikin sa'a kuwa lokacin wayar tana
hannunsa ya ɗauka da sallama a bakin sa..
Razhdeen amsa masa yayi tare da faɗin "Okay..." ya katse ƙira yana mamakin ƙiran
gaggawar da akayi masa kuma da safe yaje ya gaishe da su Abbah, babu yanda ya iya
haka ya bar duk abinda yake ya ɗauki key ɗin motar sa zai fita,
A falo ya tarar da Ƴar Amana dake yau ba school ranar hutu ne, ta
zuba wa plasman ido tana kallo kai kace ba kurmiya ba ce, bata ankara ba taji an
manna mata kiss akan goshi da sauri ta ɗago tana bin sa da kallo, murmushi ya sakar
mata tare da faɗin "take care my Beb, I'll be back..."
Itama murmushi ta sau idonta akan sa, ga gashin kanta yanda ya bazu
akan gadon bayan ta...
Kaɗa mata key yayi sannan yasa hannu zai buɗe ƙofa ya fice ya ji
Madam Blessing tana faɗin "sai ka dawo Major..."
Kan ta ne yayi wani irin mungun buguwa da ƙofar get mai ƙarfin
gaske, wani irin gigitaccen ƙara tayi tare da yo wa baya zata faɗi har ta
saddaƙar kwatsam taji an riƙo ta, idonta a ƙarƙame a matuƙar tsorace ta cakume
shi sosai jikinta har wani ɓari yake tana sauƙar da numfashi da ƙer,
kallonta ya tsaya yi yana kallon kalar riƙon da yayi mata, caɗaf ya ɗaga
ta yayi mata ɗaukar jaririya wanda shima kansa bai san yayi mata irin wannan ɗaukar
ba, domin a yanda tayo baya zata faɗi inda bai yi saurin ɗaukar ta ba sai dai a
ɗauke ta sumammiya, a hankali take buɗe eyes ɗinta tana so taga a hannun wa
take, idanuwanta ne suka sauƙa akan kyakkyawan fuskar Roshan mai ɗauke da
ƙayataccen murmushi, zaro ido waje tayi ganin a hannun Roshan take, ƙoƙarin sauƙa
daga ɗaukar da yayi mata take, a hankali ya sauƙar da ita, waiwaye ta soma yi
tana duba yanda Razhdeen yake domin tasan shine a wurin.
Tayi gaba yana binta a baya da haka suka shige, a falo suka tarar da
su Abbah da Razhdeen yana zaune sai pressing phone ɗin sa yake,
Roshan ne shima ya zaune dab da Razhdeen, itama Baiwar ALLAH zama tayi a
kusa da Uwar masu gida...
Abbah ne ya soma magana yana faɗin "ba komai ne yasa duk na tara ku
ba sai dan na sama wa iyalai na Dawwamammiyar farin ciki na har abada, akwai wani
labari da naji wanda yayi matuƙar ƙona mun rai ya kuma saka ni cikin ƙunci, na
shiga tashin hankali matuƙa dana ji kalar rayuwar da ma'aurata biyu suke yi na
rashin wanzuwar farin ciki da zaman lafiya..."
Ƙirjin Baiwar ALLAH ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske jin wannan
batun tasan da su Abbah yake,
Uwar masu gida ne ta kalli Baiwar ALLAH domin ta fahimci babu zaman lafiya a
tsakaninta da Yaya Roshan kuma tasan Roshan bashi da damuwa sai dai matsalar daga
wurin ta ya fito...
Razhdeen dai yana zaune ya kasa fahimtar komai game da abinda Abbah
yake faɗi..
Abbah ne ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter Roshan ya sanar mun duk
halin da kuke ciki, ya buƙaci rabuwa da ke domin ya sama miki farin cikin da kike
nema..."
Nan Abbah ya kwashe duk maganganun da Roshan ya sanar masa ya faɗe su
yana kallon Baiwar ALLAH ya ƙarisa maganar da cewa "Shin duk maganar da ya faɗa
gaskiya ne?..."
Zaro ido Baiwar ALLAH tayi tana ƙoƙarin haɗiye ranta tsabar
tsananin fargaba da tsoro ga yanda Abbah ya fito mata da sirrin da take ɓoye wa a
gaban mutanen gidan...
Razhdeen wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci cikin zuciyar sa jin
yanda Baiwar ALLAH take wulaƙanta masa twins sannan har take furta cewa bata son
shi, jin yanda ta furta wa Roshan cewa shi take so yasa gaba ɗaya yaji ya tsani
yarinyar, sai kuma ya tuno da maganganun da take ta furtawa a gadon asibiti...
Abbah ne ya ce "bazan takura miki akan dole sai kin zauna da Roshan ba
amma ina mai sanar miki cewa duk wanda ya nuna yana sonki tsakani da ALLAH to
shine Abokin rayuwa, amma indai ke kike so kuma ba'a son ki to rayuwarki tana yawo
a tsalallakun gajumare ne,
yanzu ina so ki furta da bakin ki kina son Razhdeen..."
Da sauri ta ɗago tana kallon Abbah ido sunyi jawur tsabar kuka, ta kalli
Roshan taga shima kallon ta yake sannan ta maida idonta kan Razhdeen a yayin da
shi kuma Razhdeen idonsa suke kan Abbah jin tambayar da yake mata...
Abbah ne ya sake maimaita wa da cewa "kina son Razhdeen ne kamar
yanda kika faɗa ko kuma?..."
Girgiza kai tayi tana shaƙar numfashi da ƙer cikin kuka ta ce "zan cigaba da
zama a gidan mijina..."
Abbah ya ce "a'a Daughter kar ki cuci zuciyar ki da kuma zuciyar wanda yake miki
hallaci, nasan tinda kika furta masa cewa bakya son sa to kuwa bakya so ɗin dan
haka a yau Roshan zai baki takardar sakin ki, da zaran ki kammala iddar ki za'a
Aura miki Razhdeen, zan dakatar da tafiyar sa ƙasar U.S har sai an ɗaura muku Auren
kafin nan..."
Baiwar ALLAH ba abinda take sai kuka domin tasan zai yi wuya Razhdeen
ya amince, inda zai yadda to da kuwa tafi kowa farin ciki...
Da sauri Razhdeen ya miƙe tsaye yana huci kamar wani kuntaccen zaki, har
eyes ɗinsa sun rine yana motsi da lips ɗinsa a hankali ya ce "God forbid, that's
not comp...."
Bai ƙarasa furta kalmar da zai fito daga bakin sa ba Abbah yayi saurin daka
masa tsawa da cewa "You'll never escape for this choosing, dole ka Aure ta tinda
ta nuna kai take so, uban waye ya ce ka rufe junanku a cikin bedroom na tsawon one
week? daga kai sai ita, ita mace ce a koda yaushe kai take gani a cikin ƙwayar
idanuwanta, idan zata kwanta bacci sai ta fara tozali da fuskar ka haka nan da
zaran ta farka fuskar ka shine madubin ta, so know tell me how comes bazata kamu
da sonka ba a halin da kuka kasance a tare? wanda nasan kaima ƙarya kake kace baka
ji komai akanta ba, Razhdeen don't tell me the lie I known you too u really loving
her..."
"Father I don't love her and I'll never love her in my life forever
and ever..."
Razhdeen ne ya furta hakan tin kafin Abbah ya ƙarasa iddasa maganarsa.
wani irin kallo Razhdeen ya watsa mata mai haɗe da harara kafin ya ce
"she losses her mind that's why..."
Tinda Razhdeen yake a wayonsa bai taɓa zubda ƙwallah ba sai yau shi
kanshi Abbah sai da ya girgiza idonsa akan sa, shima Roshan miƙewa yayi tsaye
ganin hawaye kwance saman fuskar Deen,
Razhdeen ya ce "bana sonta kuma bazan taɓa sonta ba har abada balle na
Aure ta, Dad tell her bata samu mijin Aure ba indai ni zata Aura, now I hate her
and if you post me to marry her I'll hate myself too..."
Roshan shima zaro ido yayi yana kallon Abbah cike da mamaki, Uwar
masu gida itama a ruɗe ta toshe bakinta da hannayenta biyu tana kukan baƙin ciki,
bata taɓa jin haushin wani matuƙa ba sai yau daga Mahaifiyarta sai kuma Baiwar
ALLAH...
Ya ƙasara wurin da Razhdeen yake tsaye domin zama ya gagare shi, tsayawa yayi a
gaban sa tare da faɗin "zaka sake bijire wa maganata a karo na biyu ko? Ƴar uwarka
Amina ta bijire mun ta bi zaɓinta ta guje ni, kaima you can do that, now choose
your's shin zaka bi zaɓin ranka ne ko kuma zaka yi abinda nace? idan har zaɓin
ranka ka zaɓa kaje kaima na sallame ka..."
Abbah ya ce "not your Dad har sai ka zaɓi ɗaya a cikin biyun nan, shin zaɓinka ko
zaɓi na?..."
Razhdeen yana kuka ya matso dab da Abbah ya riƙe masa hannayensa biyu
yana kuka ya ce "Dad you are my life and the something happen to my life I'll even
to be leave, na amince zan Aure ta amma zaɓinka ne Abbah is not my chosen..."
Abbah ya ce "Deen are you sure are you going to get engagement with
her ?..."
Razhdeen ya ɗaga masa kai tare da faɗin "bazan taɓa bijire maka ba..."
Abbah rungumarsa yayi yana faɗin "thank you very much my son..."
Shima Razhdeen rungumar Abbah yayi,
Baiwar ALLAH ce ta ɗago da manya-manyan idanuwanta waɗanda suka canza
kamannu ta ɗora su akan Razhdeen wanda yake rungume da Abbah, lokaci guda taji
zuciyarta yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin irin kallon da Razhdeen yake
mata na tsananin tsana...
Razhdeen idonsa akan Baiwar ALLAH yake maganar zuci yana faɗin "this
is the first time that you make urself my Enemy, you are my enemy, I hate you and
I'll never love you in my life, I hate you..."
Roshan idonsa akan Razhdeen ganin yanda yake mata kallon tsana da baƙin
ciki gaba ɗaya jikinsa ba ƙaramin sanyi ba, dole yasan Baiwar ALLAH zata sha
wahala sosai a hannun Razhdeen...
Shima Roshan ba abinda yake sai kuka yana daga tsaye ya ciro wata farar takarda a
cikin aljihunsa ya nufo yanda Baiwar ALLAH take a zaune ya ce "Ammata yau burinki
zai cika, ga takardar raba Aurenki da ni..."
Tana kuka ta miƙe tsaye itama tana fuskantar sa tasa hannu ta karɓi
takardar idonta akan Roshan sai da ta dai-daici tsakiyar paper ta raba gida biyu,
haka ta yayyaga takardar tana kuka ta ce "Yaya Roshan kayi haƙuri zan cigaba da
zama da kai..."
Taje gaban Abbah ta durƙusa gwiwowinta ƙasin carpet tana kuka ta ce "Abbah
ka gafarce ni, Uncle Deen baya sona bazan iya zama da shi ba, zan cigaba da zama da
wanda yake sona har cikin zuciyarsa, zan canza hali na, zan masa biyayya yanda ya
kamata..."
Razhdeen ya buɗi baki yayi magana yana faɗin "tomorrow early morning I
will travel to U.S..."
Ya ce "Yes! zan tafi tin yanzu nayi muku sallama domin ba lallai na dawo ba, da
sassafe zan wuce airport..."
yana kaiwa nan ya juya zai tafi, Abbah ya ce "Are you Angry with your
Dad?..."
Razhdeen ya ce "no..."
a takaice
Abbah ya ce "okay zan tarar da kai a airport goben.."
Razhdeen ya ce "ok..."
daga nan ya yi tafiyar sa...
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*26_ TO_30*
Razhdeen shigar shigar motarsa yayi ya zauna yana riƙe da sitiarin motar tsabar
ƙololuwar baƙin cikin Baiwar ALLAH ne yasa ya kasa jan motar.
Baiwar ALLAH ne itama ta fito tana sharar hawaye ta nufi part ɗinta bata
ma lura da Razhdeen na wurin ba, shi kuwa idonsa akanta ganin bazai iya kyale ta
haka ba yasa shi buɗe murfin motar sa ya nufi part ɗin Roshan..
Baiwar ALLAH bayan shigar ta cikin falonta zama tayi a kujerar falon
tana sabinta kukan ta, tana cikin wannan halin ta soma jin ana knocking ƙofar
falon, da sauri ta share hawayen tayi tunanin Roshan ne bata so ta nuna masa
damuwarta saboda kar ya ƙara samun Abbah da maganar, buɗe ƙofar tayi kwatsam ta
tarar da Razhdeen a tsaye a bakin ƙofar yana mata wani irin kallo na ƙasƙanci wato
kallon up and down...
Kutsawa yayi ya shige ciki a yayin da ita kuma take ja da baya domin
ba ƙaramin ƙwarjini yake mata ba,
ma ta nuni yayi da ta zauna a kujera ba musu haka ta zauna eyes ɗinta akansa
shima jawo glass table yayi ya zauna a front ɗinta suna fuskantar juna, fuska a
haɗe ya ce "ki kalli cikin eyes ɗina kiga shin nayi kala da abokin wasan ki?..."
Shuru tayi bata bashi amsa ba sai kallonsa da take ko ƙibta idon
bata yi, cikin fushi ya cabki wuyanta ya riƙe sosai yana zazzaro mata manyan eyes
ɗinsa tare da faɗin "ke ko a ƴar aikin matata bazan ɗauke ki ba domin bakiyi kala
da wacce zata zauna a gidan da nake ba balle na haɗa jinsi da ke, kinyi kuskure
sosai da kika nuna kina sona domin ciwon haukarki ne yake rinjayarki, naso baki
janye ƙudirin ki ba wallahi tallahi nayi niyar nasa hannu na murɗe miki wuya har
sai kin bar duniyan nan, bana sonki! na tsane ki, ki janye jikinki daga gare ni
sannan ki kawar da idanuwanki daga yanda nake idan ba haka ba zan kashe ki ne har
lahira, nonsense girl ƙazama marar hankali, wawiya dabbiya..."
Razhdeen ganin yanda take riƙe da kwalar rigarsa wanda tinda yake mace
bata taɓa sa hannu da niyar riƙe gaban rigar sa ba hatta namiji balle mace a fusace
yasa bayan tafin hannunsa ya zabga mata mari rai a ɓace,
A gigice ta faɗa kan kujera tare da sakin wata ƴar ƙara, tana riƙe da
gefen fuska wani irin kuka take ta cin rai da takaici a fusace ta juyo tare da kai
hannu zata rama yayi saurin riƙo hannun ta cike da mamaki ya ce "whattttt? Ni zaki
mara? ni ne zan bari hannun mace ya sauƙa akan fuskata da niyar mari ?
impossible..."
ya ƙarisa maganar tare da wurgata kan kujera ya cabko sumar gashinta yana
murmushin takaici
ya ce "idan akwai macen da nafi tsana a rayuwata to bazai wuce ke ba, you
are my enemy..."
yana iddasa maganarsa ya juya zai tafi har ya isa bakin ƙofa yaji
ta furta wata kalma wanda ya dakatar da shi,
ƙara maimaitawa tayi ta ce "yes me too I hate you, sam baka daraja mata
especially wacce ta nuna damuwarta akan ka kafi wulakanta ta, amma ka sani duk
abunda kayi kaima sai an mata, kamar yanda ka ƙuntata mun kaima wata rana sai kayi
kuka cir da idanuwanka, wata rana saika durƙusa a gaban mace kana bata haƙuri a
yayin da ita kuma take wulaƙantaka, wallahi ina maka wannan fatan kuma ka rubuta ka
ajiye domin maganata a rubuce take, Razhdeen ko kaɗan bana jin tsoronka kaje bana
son ƙara ganin fuskar, na gama maka komai tinda na Auri ɗan uwanka..."
Wani irin haɗiyar yawu tayi sannan ta ƙara fashewa da wani irin
matsanancin kuka a haukace ta soma wurgi da filillikan kujerun falon tana kuka
tana faɗin "Nima bana sonka na tsane ka wallahi, you bastard, you are crazy and
you are my enemy, you broke my heart Razhdeen why? why? why???...."
Bin ta yake da kallo a tunaninsa rashin son zama da shi ne duk ya jawo haka,
girgiza kai yayi tare da sauƙar da nannauyar numfashi ya ce "daman nasan baki
haƙura da ƙudirinki ba Ammata, kinyi haka ne saboda ki faranta wa Abbah amma ba'a
son ranki ba, amma Insha Allahu zan kawo miki good idea wanda zaki samu
Dawwamammiyar farin ciki mai ɗorewa indai rabuwa da nine zai kawo miki farin cikin
ki kar ki damu..."
Itama Baiwar ALLAH bin kyakkyawar fuskarsa tayi da kallo, girgiza kai
tayi alamar babu matsala.
Baiwar ALLAH zuba masa ido kawai tayi tana son jin wani irin magana
zai furta mata,
Roshan ne ya cigaba da cewa "ba tare da kowa ya sani ba daga ni sai ke
zamu tsara, zakiyi haƙuri ki zauna da ni na tsawon shekara biyu ba tare da mun
kusanci juna ba duk da nasan ba amince dani zaki yi ba kamar yanda muke zaune a
haka, idan har lokacin yayi na tsawon shekara biyu aka ga bakida ciki to za'a fara
zargin ko ke bakya haihuwa ko dai ni, zan nuna cewa nine bana haihuwa kinga kuwa
Abbah zai yanke cewa na rabu da ke domin kije ki Auri wanda zaki haihu da shi, nima
zan goyi bayan haka! Abinda ba yanke kenam amma ki ƙara haƙuri da zama dani kinga
zuwa lokacin nasan Razhdeen zai dawo daga U.S tinda shima two years zai yi..."
Baiwar ALLAH jin abinda Roshan ke faɗi ne yasa ta haɗe fuska rai a
ɓace ta miƙe tsaye ta bar falo ta koma bedroom ɗinta, ita a halin yanzu bata
buƙatar jin sunan Razhdeen duk da har yanzu akwai son sa a cikin zuciyarta amma
tayi alƙawarin zata fara cire shi a ranta...
Roshan binta yayi da kallo tare da girgiza kai a fili ya furta "nasan
shekara biyu yayi miki nisa tinda a yanzu baki ƙi na rabu da ke ba, amma wannan
shine shawara mai kyau ba tare da an zargi wani abu ba..."
Ƴar Amana ce take ta fama kuka tana ƙoƙarin ƙwace wa daga riƙon da
Madam Blessing tayi mata tana son bin Razhdeen yanda zai je,
Razhdeen bai so ya tafi yabar Ƴar Amana ba domin ji yake kamar zai rasa
ta ne har abada, yana cikin kukan zuci ya shige motarsa security ya yi driving
ɗinsa suka tafi...
Ƴar Amana ganin an buɗe gate sun tafi yasa ta fizgewa da ƙarfin gaske daga
riƙon da Madam Blessing tayi mana tare da wurgar da bebin robar ta cikin fushi ta
koma cikin falo tana hawaye,
tsaya kallon da Madam Blessing tayi domin al'amarin Ƴar Amana sai Allah
shima kan shi Razhdeen ɗin a hankali yake bi da ita...
A ɓangaren ɗayan gidan kuma duk sun tafi ganawa da Razhdeen banda
Baiwar ALLAH wacce ta kasance ita kaɗai a gidan bata je ko ina ba.....
*HIP_HIP_HIP_HURRRRYY*
*DAN ALLAH MASOYA KUYI HAƘURI DA JINKIRIN DA NAKE MUKU NIMA BA'A SON RAINA BA NE,*
*EXAMINATION NAKE RUBUTAWA KUMA INA BUƘATAR NUTSUWA DOMIN KASAN ABUNDA ZAKA RUBUTA
A ƊAKIN JARABAWA, KULLUM INA CIKIN KARATU, KULLUM SAI MUN SHIGA EXAM*
*KU MUN UZURI DAN ALLAH KOMAI LOKACI NE KAMAR YANZU ZAN GAMA LITTAFIN GABA ƊAYA
NASAN A MATSE KUKA🙏🙏*
*GA SHORT PAGE*
*BANIDA LOKACI AMMA GOBE IN SHA ALLAHU ZAN SAKE YI MUKU UPDATE TINDA BA EXAM..*..
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*31_ TO_35*
Baiwar ALLAH kai a sunkuye ta ce "wallahi Ammy bana jin daɗin jiki na
ne shiyasa..."
Ammy ta ce "ayyah ban sani ba ai da zan je na duba ki, kuma naga Ummy
tana zuwa part ɗinki amma bata sanar mun ba..."
Ummy uwar masu gida tana gefen Abbah cikin zolaya ta ce "kodai kodai mun
samu ƙaruwa ne..."
Ammy ce ta fara yin dariya ganin kallon da Abbah yake yi wa Uwar masu
gida har da taguminsa jin yanda ta taƙarƙare ta zuba zance, girgiza kai yayi tare
da faɗin "Allah ya shirya mun ke Mamana..."
Rufe fuska tayi tana dariya domin sai yanzu take jin kunyar abinda ta
faɗa...
Ita kuwa Baiwar ALLAH kallon Roshan tayi ta gefen ido tana maganar zuci cewa
"taya zan samu ciki alhalin a ƙaurace muke da juna, yau tsawon shekara guda da
Auren mu amma ko a gado ɗaya bamu taɓa kwanciya ba, abun yana damu na wallahi, shi
ya ce indai bani na neme shi ba bazai taɓa nema na ba, Ni kuma kunyar hakan nake,
hmmmm! meye makomata a wurin Ubangiji na? shin laifi nake aikatawa kodai? dole zan
nema wa kaina mafita domin a halin yanzu ina matuƙar ƙaunar mijina Roshan, yafi mun
duk wani namijin da zan Aura, bazan taɓa rabuwa da kai ba Roshan..."
Shi kuwa Roshan Abbah ne yake tambayarsa cewa "ina dai babu wata damuwa a
tattare da zamantakewar ku na Aure?..."
Da murmushi akan fuskar Roshan ya ce "babu komai Abbah muna zaune cikin ƙoshin
lafiya..."
Ya ƙarasa maganar yana kallon Baiwar ALLAH wacce itama shi ɗin take kallo
domin yasan tana cikin damuwa na rashin son zama da shi wanda ba hakane a ranta ba,
Baiwar ALLAH ta kasance mace ce mai zurfin ciki sai dai abu yaita damunta a ranta
amma bazata iya sanarwa ba, ita a ranta tana son Roshan ya kasance da ita a
matsayin matarsa ta Aure, burinta shine su zauna su cigaba da soyayyarsu kamar
yanda ma'aurata suke kowa a cikin farin ciki,
Roshan ganinta a cikin damuwa hakan na nuna masa cewa haƙurin zama
da shi kawai take, especially idan ya tuno cewa twins ɗinsa take so, cije lips
ɗinsa yayi yana kukan zuci domin yana da kishi sosai wanda bazai iya cigaba da zama
da ita a haka ba, shi har yanzu baya ɗaukar kansa a matsayin mai Aure domin duk
abinda ake samu a cikin Aure har yanzu bai same shi ba...
Bayan nan Roshan ne ya tashi tare da faɗin "Abbah zan wuce wurin aiki
na sai na dawo..."
Abbah ya amsa masa cikin kulawa da cewa "Allah ya kiyaye a dawo lafiya..."
Shima Abbah tashi yayi yabar musu falon suka cigaba da hirar su, ita dai
Baiwar ALLAH a dole take iya yin magana...
____________________________________
Aunty Yolash ce take zaune a wantalelen falon ta dake garin Bauchi tana tare da
wata ƙawarta wacce ta kawo mata ziyara,
Knocking ƙofar falo aka shiga yi murya ciki-ciki Aunty Yolash ta ce "waye?"
Daga waje ne Mai gadinta ya ce "Hajiya kin yi baƙuwa ne..."
ta ce "daga ina?..."
Mai gadi ya ce "wallahi ban sani ba Hajiya..."
ta ce "ok ka ce ta shugo..."
Aunty Yolash suna zazzaune suka ji an turo ƙofa da sallama a bakin matar da
ta shugo, cike da mamaki Aunty Yolash ta miƙe tsaye baki ya gagara rufuwa ta ce
"wa nake gani kamar Hajiya Kilishi..."
Hajiya Kilishi murmushi tayi tana faɗin "wallahi Ni ce, kinyi mamakin gani na a
garin Bauchi ko?..."
Aunty Yolash ta ce "gaskiya kam saboda naga baki taɓa taka ƙafarki kinzo mun
ba, nasan yanzun ma uzurinki ne ya kawo ki..."
Aunty Yolash taɓe fuska tayi ta ce "Banga alama ba saboda tin ana tare ma baki zo
ba balle yanzu da ba'a tare..."
Hajiya Kilishi sunkuyar da kanta ƙasi tayi tana shirin zubda ƙwallah,
Ƙawar Aunty Yolash Hamdiyya ta ce "haba ke kuma Yolash ba'a haka bai
kamata ba sam, mata ta taso daga yanda take tazo wurinki ki tsaya kina gaya mata
magana ko wurin zama baki bata ba balle kayan drinks..."
Aunty Yolash kallon Hajiya Kilishi tayi sannan ta ce "ko dai kin yi
bazawari ne anan Bauchi shiyasa kika kawo masa ziyara..."
Hajiya Kilishi dai kai a sunkuye ta kasa ɗagowa balle ta haɗa ido da
Aunty Yolash,
Aunty Yolash ce ta kalli Hamdiyya ta ce "wannan ɗin dai Hajiya Kilishi
ce matar Yayana General wanda ya rabu da ita...."
Hamdiyya sake baki tayi tana kallon Kilishi cike da mamaki ta ce "wannan ɗin
Hajiya Kilishi ce? Innalillahi naga duk ta rarrame kamar mai HIV ga fuska ta
kokkoɗe tayi fiyau, ai ni bangane ta ba wallahi, duk meya faru da ita haka?..."
Aunty Yolash ta ce "Nima ina zan sani, kamata yayi yanzu muga kin
ƙara murmurewa kinyi ƙiba sakamakon ba'a takure kike ba, zaki iya fita duk san da
kika ga dama ki dawo gida duk lokacin da kike so babu mai takura miki, kinsan
General yana takura miki baya barinki kije duk yanda kike so yanzu kuwa kura ta
mutu muyi wasa, yanzu kuma naga akasin haka sosai da duk kan alamu kina cikin
tashin hankali Hajiya Kilishi,
Kinga duk taƙamarki da izzarki da girman kanki yau ke ce a gaba na
kina zubda ƙwallah?..."
Hamdiyya ce ta tashi tana faɗin "Ni zan koma gidana na bar yara su kaɗai..."
Suka yi sallama Hamdiyya ta tafi tana mamakin ganin Hajiya Kilishi a cikin
wannan halin...
Aunty Yolash ce ta ƙwalla ƙiran ƴan aikin gidanta tare da sanar musu cewa
su kawo wa baƙuwarta abinci da kayan drinks,
Bayan ƴan mintuna sai ga su da kayan abinci da su fruit da drinks sun
ajiye akan table ɗin tsakiyar falo tare da jan yo shi gaban Hajiya Kilishi, sai da
Hajiya Kilishi ta gama cin abinci da sauran kayayyaki tukun ta fuskanci Aunty
Yolash,
Itama Aunty Yolash kallonta take tana son jin mai ke tafe da ita...
Aunty Yolash ta ce "kema Allah ya rufa miki asiri sai dai kece kika tona
wa kanki asirin, abun ya ban mamaki shin wani irin taimako ne kike so nayi miki
har da durƙusawarki wanda tunda kike baki taɓa yin gigin yin haka ba..."
Hajiya Kilishi tana kuka ta ce "dan Allah kiyi haƙuri akan abubuwan da
na aikata miki, nasan ban kyauta miki ba amma ki gafarce ni..."
Aunty Yolash murmushi tayi tare da faɗin "nasan ba wai neman gafarata
kika zo yi ba, akwai abinda ke tafe dake, Ni indai nine za'a zauna lafiya ƙalau ba
tare da ɓacin rai ba don haka komai ya wuce a wuri na, shin wani taimako kike so
nayi miki indai baifi ƙarfi na ba zan taimaka miki,
Sannan ki tashi ki zauna akan kujerar bana son durƙusawarkin Nan..."
Hajiya Kilishi tana sharar hawaye ta tashi ta zauna tare da faɗin "bazai
ma fi ƙarfin ki ba, nasan kina ɗaya daga cikin waɗanda zasu faɗi magana General ya
ɗauka ko shawari haka, kina ransa sosai, yana matuƙar ji dake...."
Aunty Yolash ta katse ta da cewa "duk nasan wannan wa'azin just go ahead..."
Hajiya Kilishi ta cigaba da cewa "Auntyn yara inason komawa gidan mijina, wallahi
ina son kasancewa tareda mijina da kuma ƴaƴana, ina shan wahala sosai a gidan da
nake, ga bani da kuɗi yanzu abincin da za'a bani ma ƙyashinsa ake wani sa'in ba'a
bani, gidan mijina ya fi mun kwanciyar hankali, wallahi nayi nadamar abubuwan da
na aikata a baya, nayi kuskure wanda yanzu nake son gyarawa..."
Ajiyar zuciya Aunty Yolash ta sauƙar tare da faɗin "hakane bawa yakan
aikata kuskure daga baya yayi nadamar abinda ya aikata, amma ina so ki sani cewa
duk wanda ya tuba don wuya ba lada haka tushen hausar take amma tinda har kika gane
gaskiyar lamarin duk ba laifi, amma a gaskiya komawa gidan General zai miki wuya
domin a halin yanzu Yayana ba macen da yake jin daɗin tarayya da ita sai Amaryarsa,
zai yi wuya ya zauna da wata mace bayan ita, kuma shi daman baya son zama da mata
biyu kasancewa shi ba mazauni bane, shin a cikin maganar ki taimakon mai kike so
nayi miki?...."
Aunty Yolash ta ce "kai kai kaiiii ai duk yanda nake da General bazai taɓa yadda
da wannan batun ba hasali ma ki ja mun baƙin jini a wurin sa, ga nan abokansa kije
ki same su mana..."
Hajiya Kilishi ta ce "kab abokansa waɗanda na sani babu wurin wanda banje ba
amma ya ƙi sauraronsu akan batun, bansan wani irin zuciya ne da shi ba..."
Sauƙe numfashi Aunty Yolash tayi tare da faɗin "ke ma bakya jin magana
Hajiya Kilishi, ke kika jawa kanki komai wallahi duk abinda ya faru laifinki ne,
inda ace kin kama kanki da mutuncinki a gidan mijinki da duk hakan bata faru ba, me
zaisa kiyi abinda har Aurenki zai mutu? kin dai san General yana da matuƙar haƙuri
amma idan aka kai shi maƙura baya taɓa sauƙowa akan abu, kuma idan ya cire abu a
ransa baya taɓa maida shi, kin ƙure shi sosai, kinsan babu wanda zai iya riƙe ki
mai zai sa ki bar gidan mijinki? kowa yana rufawa kansa asiri amma ke kina ƙara
bankaɗawa kanki asiri, Ni a koda yaushe ina baki shawara bawai bana sonki bane
amma kika ɗauki ƙiyayya kika ɗora mun, gani kike babu maƙiyiyar ki kamar ni, Ni
kuma ina zaune da mutum da zuciya ɗaya ne, kuma wallahi wannan ranar nake guje miki
kuma gashi yazo shin meye amfanin haka?..."
Hajiya Kilishi babu abinda take sai kuka ta ce "bayan fitowa ta daga
gidan mijina ba ƙaramin wahala nake sha ba, kowa ya kasa riƙe ni, da farko a gidan
ƙanwar mahaifiyata nake zaune amma itama daga baya ta kore ni wai bazata iya riƙe
ni ba, sai na koma gurin baffana shima matansa sun hanani zama a gidan, duk zuriya
babu yanda ban zagaya ba amma an rasa wanda zai riƙe ni daga ƙarshe dai zaman Abuja
ya gagare ni saboda babu yanda zan shiga ga tsadar rayuwa ga bani da kuɗi, abincin
da zan saya na ci gagara ta yake, yanzu haka ina zaune a garin suleja na kama gidan
haya, to kuɗin da zan biya babu kuma watannin biyan kuɗin ya ƙare, bansan da wanne
zan ji ba, shin da kuɗin abinci yau da kullum ko kuma kuɗin hayan gidan da
nake?..."
Aunty Yolash sarkin tausayi ba ƙaramin tausaya mata tayi ba, ta ce "ke nam babu
yanda zaki je ki zauna? abincin da zaki ci gagaranki yake shin ina Alhajan
ƙawayenki matan manya-manyan masu kuɗi? shin kina nufin ki ce bakida bazawarai? to
ma ina wanda kike bin sa hotel bazai iya taimaka miki bane?..."
Hajiya Kilishi dakatar da yin kukan tayi tana faɗin "yanzu na gane su
waye masoyana da kuma maƙiyana, ƙawaye na suna hulɗa dani ne saboda kuɗina da
kuɗin mijina, basa kula talakawa idan suka fiskanci bakada komai ka tsiyace daga
nan zasu raba hanya da kai duk haka suke, suna ƙawance da wacce take da kuɗi, kuɗi
sai kuɗi to ni kuma yanzu banida komai, aikin da nake yi ake biyana maƙudan kuɗaɗe
kamfanin General ne kuma ya sallame ni, ko ba kuɗin salary General baya barina ba
kuɗi,
Bazawarai kuma su waye zasu zo mun? idan kinga mutum yazo mun to
bada niyar Aure yazo ba sai da niyar iskanci, Ni kuma na shiryu bazan iya bada
kaina ba saboda kuɗi duk da wahalar da nake sha, duk kowa ya gujeni, wasu sunyi
blocking number na wasu kuma idan na ƙira su basa picking, wai daman haka rayuwar
take?...."
Aunty Yolash ta ce "tam yanzu dai kin san masu sonki da kuma waɗanda
basa sonki..."
Hajiya Kilishi tayi saurin katse ta da cewa "indai ata ɓangaren ƙawaye
da kuma abokai babu masu Sona tsakani da ALLAH, ƴan uwana kuma daman haushi na suke
ji shiyasa suka kasa taimaka mun..."
Aunty Yolash ta ce "tam yanzu dai idan Allah yasa kika koma gidan
General babu ruwanki da wani ɗagun kai da girman kai da wulaƙanci da kuma masifa ki
kama kanki, kinga wacce take zaune yanzu babu ruwanta batada tashin hankali, idan
wani abu ya ɓullo za'a ce ke ce..."
Hajiya Kilishi ta ce "ai babu abinda zai faru Insha Allahu, zan riƙe
abokiyar zamana hannu bibbiyu..."
Aunty Yolash murmushi tayi sannan ta ce "Ni na manta ashe dai kince bakya son zama
da kishiya..."
Aunty Yolash ta ce "to shikenam gobe Insha Allahu zan shiga jirgi
naje Abuja na same shi da maganar duk yanda ake ciki zanje har yanda kike a sulejan
na sanar miki..."
Hajiya Kilishi bata san lokacin da ta washe baki ba na farin ciki ta ce
"Nagode sosai Auntyn yara Allah ya saka da ALKHAIRI..."
Hajiya Kilishi cikin nuna farin ciki ta miƙe tare da faɗin "shikenam
Auntyn yara Ni zan koma suleja..."
Hajiya Kilishi ta ce "a'ahh bani da kuɗin hawa jirgi, zanje na shiga mota..."
Aunty Yolash gani ɗaya tayi wa Hajiya Kilishi tasan bata da kuɗin motar
ma kawai tayi iya kuɗin zuwa ne,
Ta ce "shin kina da na motar ne?..."
Aunty Yolash ta haura saman upstairs yanda room ɗinta yake taje ta ɗauko
wasu maƙudan kuɗaɗe a cikin baƙar laida ta sauƙo tare da miƙawa Hajiya Kilishi tana
faɗin "ga wannan kije ki biya duk kan buƙatunki da su, ki biya kuɗin haya sannan
ki sayi kayayyakin abinci da dai sauran abubuwan da kike buƙata..."
Cikin nuna farin ciki Hajiya Kilishi ta karɓa tana godiya haɗi da cewa
"wannan ai zan daɗe ina amfana da su.."
___________________________________
A bangaren Ƴar Amana kuwa har zuwa wannan lokutan fushi take da Razhdeen saboda ya
tafi ya barta, ma sha ALLAH sai haɓaka take tayi, a shekara ɗaya ta zankaɗe tayi
tsayi ga dirin jiki kamar wacce ake hura mata iska, fatar jikinta kuwa kamar zaka
taɓa jini ya fito tsabar farin da tayi ba ƙaramin kyau tayi ba, ga gashin kanta a
baje kamar wanda ake ƙara jansa sai tsayi yake yana tafe da murɗi-murɗinsa, ta ko
ina a jikinta ya ciko hatta breast ɗinta sun fito sun cicciko, ƙugunta kuwa ba'a
magana daman kuma can Ƴar Amana ba siririya bace da ɗan dirinta balle yanzu ta haɗa
da cikar budurci, hips ɗinta irin mai shape ɗin kifi ne.
Tana zaune a falo tana kallo kwatsam taji Madam Blessing ta zauna
kusa da ita tana shirin miƙa mata wayar hannunta, da sauri Ƴar Amana ta ture wayar
tare da miƙe wa tabar falon ta koma room ɗinta domin tasan Razhdeen ne yake son yin
video call da ita, tinda Razhdeen ya tafi tsawon shekara guda Ƴar Amana bata taɓa
yadda sunyi video call ba shi kuwa kullum sai ya ƙira madam blessing akan ta haɗa
shi video da Saararsa amma fur Ƴar Amana taƙi yadda hatta photo bata taɓa yadda
tayi ba tinda Razhdeen ya tafi saboda tasan indai ta ɗauka sai madam blessing ta
tura masa, kullum sai yayi complain akan a turo masa photon Saarah amma Ƴar Amana
taƙi, har takai ta kawo yanzu indai taga waya a hannun madam blessing bata yadda
ta zauna a kusa da ita saboda kar ta ɗauke ta a photo, a tunanin ta indai yaji
zafin haka zai dawo.
Madam Blessing bayan Ƴar Amana tabar falon girgiza kai tayi ta cigaba
da magana da Razhdeen tana faɗin "Yallaɓai indai kana son ganin Saarah gwara ka
ware lokaci ɗaya kazo ka koma, nake gaya maka in kaga yanda yarinyar nan ta girma
saika kama baki, ba ƙaramin girma tayi ba amma sai dai har yanzu bata fara period
ba, amma tana dab da farawa saboda ta cika sosai, amma Yallaɓai a tunaninka zata yi
shakara nawa?..."
Daga ɓangaren Razhdeen wanda yasa computer a gaba domin da shi yake video
call ya ce "ina tunanin bazata wuce 17 years or 18 ba,
Madam!
Sarah yarinya ce ƙarama just girman jiki ne kawai..."
Madam Blessing ta ce "okay zan fara sa mata ido saboda tana dab da
farawa ai lokacin ta yayi..."
Shima Razhdeen cewa ya yi "ki kula mun da ita sosai, ki fara gwada mata yanda zata
yi kafin ta ankara da shi domin zata iya tsorita duk lokacin da abun yazo..."
Madam ta ce "okay kar ka damu tinda tana jin abinda ake ce mata mayar wa ne
bazata iya ba ai da sauƙi..."
Madam Blessing ta ce "sosai ma, wallahi nake gaya maka inda ace yarinyar nan tana
magana ba ƙaramar yarinya mai ilimi da fahimta za'ayi ba, yanzu ma tin daga kan
note ɗinta zaka gane tanada ilimi..."
Razhdeen murmushi yayi ba ƙaramin jin daɗin hakan yayi ba, ya ce "good..."
Madam Blessing ta kuma cewa "Yallaɓai zan maka rainonta yanda ya
kamata, gashi kun dace sosai, miskilancin ku ɗaya da kuma zafin rai..."
Madam Blessing zaro ido waje tayi tare da faɗin "ƴarka dai? No don't said
that, me laifin kace ƙanwarka amma ƴa ai babu Aure a tsakani kenam..."
Kafin ta ƙara cewa wani abu Razhdeen yayi saurin katse wayar,
Madam Blessing girgiza kai tayi tana murmushi domin tasan Razhdeen ba wata
budurwar da yake da shi kawai ya faɗa ne...
Washe gari da safe Ƴar Amana ta sauƙo falo cikin shirin kayan
uniform da jakarta a goye a baya, tayi gyaran gashin ta tayi rolling donut da
gashin, ga ta gaban gashin ta gyara da Gel daman su school ɗinsu ba'a saka hijab
ko hula ko kuma gyale haka nan ake barin gashi a waje, shiyasa ko wacce take
ƙoƙarin gyara gashin ta, da masu tsara kitso da kuma masu saloon su gyara gashin,
ita ƴar Amana bata kitso sai dai Madam Blessing ta kaita wurin saloon a gyara
gashin,
Style ɗin uniform ɗinsu kuma doguwar riga ne zuwa gwiwa baya sauƙa
ƙasi sai sapa da thorns mai tudu, makarantar akwai gasar fashion dake private
school ne na ƴaƴan masu kuɗi,
Ƴar Amana bayan ta gama shirinta zuwa tayi ta zauna akan dinning
table daman an haɗa mata abinci kala-kala masu kyau da gyaran jiki shiyasa take ta
haɓaka kamar yeast, madam Blessing ba ƙaramin gyara Ƴar Amana take ba kamar ƴar
cikinta haka take ji da ita, bayan ta kammala breakfast goya jakarta tayi mai
bala'in tsada sannan ta ɗauki lunch bag ɗinta wanda a ciki haɗin abinci ne masu rai
da lafiya da kayan fruits,
Madam Blessing rakata tayi har harabar gidan yanda security yake
jiran fitowar ta,
Ƴar Amana babu a wanda tayi wa alamar magana kai tsaye mota ta shige ta
zauna a back seat ta ci boom kamar wacce ba'a halicce ta da fara'a ba, haka
security ya ja mota suka fi ce...
Madam Blessing ɗaga mata hannu take tana mata fatan alkhairi amma Ƴar Amana
ko kallon yanda take bata yi ba, Razhdeen yasa tana fushi da kowa daman can ba'a
taɓa ta ba yata ƙare balle an tsokano ta....
A ranar yau ne Aunty Yolash tazo Abuja zata cika wa Hajiya Kilishi
alƙawarin da ta ɗaukar mata na cewa zata same shi...
A falon Meeting ɗin Abbah Aunty Yolash ta same shi zaune yana daddanna
computer sa, zama tayi tare da gaishe shi, ya ɗago yana murmushi ya ce "Auntyn
yara yau kece a garin Abuja?..."
Tana dariya ta ce "wallahi kuwa Yaya na shiga ciki ai Ammy take sanar mun cewa
kana nan falon ka..."
Abbah ya ce "tamm akwai problem kenam tinda har kika kasa jirana a can
public falo..."
Aunty Yolash ta ce "ai daman Yaya maganar da zamuyi yana buƙatar sirri
ne..."
Aunty Yolash har fargaban fara tuntuɓar Abbah take da maganar domin tasan ba ƙaunar
jin zance Hajiya Kilishi yake ba,
zuciyarta ne ya fara bugun uku-uku tana haɗiyar yawu ta ce "Daman!
Daman!! akan magana mai muhimmanci ne..."
Abbah shafa farin gemunsa ya fara yi yana faɗin "too gama mun wa'azi
tukun sai ki gayi abinda ya kawo ki ko..."
Aunty Yolash ta ce "Yaya shin idan mutum yayi maka laifi kuma yazo neman gafarar
ka shin zaka haƙura ko kuma ?..."
Abbah kwata-kwata bai kawo maganar Hajiya Kilishi a ransa ba, shi har ya
manta da wata Kilishi kuma bayan haka Aunty Yolash bata taɓa masa maganar ta ba
balle ya kawo haka a ransa,
Ya ce "indai yayi laifi kuma daga baya ya gano kuskurensa
ya nemi a ayafe masa da gaske har cikin ransa mai zai hana a yafe masa, ai akwai
laifukan da muke yi wa Ubangijin mu a sanin mu ko ba'a sanin mu ba mu roƙe shi kuma
ya yafe mana balle mu marasa tunani, indai akwai zuciyar musulunci zan yafe masa
mana..."
Abbah ya ce "Ni fa na tsani jan rai idan zaki faɗi magana kin rinƙa jan zance
kenam..."
Aunty Yolash ta ce "sorry Yayana daman inaso ka yafewa Hajiya Kilishi abinda
ta aikata maka, ta wakilce Ni akan nazo na baka haƙuri tayi nadama, kuma wallahi
Yaya da gaske take kaga yanda ta zama kuwa kalar tausayi, wai tasan idan tazo
yanda kake korar ta zakayi shiyasa ta turo Ni..."
Abbah yayi mamakin jin wannan magana daga bakin Aunty Yolash domin yasan
ba shiri suke yi ba,
Ya ce "aina kika haɗu da ita?..."
Jinjina kai Abbah yayi tare da faɗin "zan yi maganin wannan matar indai
bata daina bin Abokaina da ƴan uwana ba, na ce bazan dawo da ita gidana ba amma
sam ƙwaƙwalwarta na kifaye ne, Ni ban iya zama da mata biyu ba, kuma bazan fara ba
tunda da yarinta ta banyi ba balle yanzu da tsufa ta soma kamani..."
Abbah ya ce "Ni indai nine taje na yafe mata duniya da lahira tin ba yau ba,
wallahi na yafe mata, alaƙa ce dai na yanke..."
Aunty Yolash kamar zatayi kuka ta ce "Yaya ka dawo da ita kan Ƴaƴanta..."
Aunty Yolash ta ce "haba Yaya matar nan baka san irin wahalar da take
sha ba, ga babu yaranta a kusa da ita balle taji sanyi a ranta, ka rabata da komai
hatta aikinta da take yi tana samun Salaryn ta ka kore ta shin ya kake so tayi ne,
tana ta bin duk ƴan uwanka tana neman gafararsu akan abubuwan da tayi musu sannan
tana neman alfarmar a baka haƙuri ta dawo, ita ko ya ya ne zata zauna a haka, yanzu
wallahi asirinta a bankaɗe yake..."
Zaro ido Aunty Yolash tayi tana kallon Abbah wanda ya ambaci asalin
sunanta wanda tinda yake bai taɓa ƙiran sunan ba sai yau, cike da mamaki take bin
sa da kallo zuciyarta na bugun uku-uku domin ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba...
Abbah ya cigaba da cewa "Na rantse da sarkin dake busa mun numfashi idan
ban yanke alaƙata da ke ba ki canza mun suna wallahi tallahi...".
Ba Aunty Yolash ba hatta Ammy wacce shugowarta kenan tana ɗauke da try
ɗin lemuka ta kawo musu jin kalmar da Abbah ya furta ne yasa ta sakin try ɗin
drinks a ƙasin carpet tsabar firgici..
Aunty Yolash miƙe wa tsaye tayi tana faɗin "Allah ya baka haƙuri Ni na
tafi..."
Abbah ya ce "ki tafi mana, kar na sake ganin ƙafarki a gidan nan iskancin banza
kawai..."
Ammy ranta ya sosu sosai jin abinda Abbah ya ke faɗi kuma duk saboda
an kawo masa maganar Hajiya Kilishi,
Ammy ta ce "wai Abban yara shin ba'a yafiya ne? ka dawo da mata kan
ƴaƴanta mana ya zaka raba uwa da ƴaƴanta..."
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
STEP TWO
👇
*36_ TO_40*
Misalin ƙarfe 10 na dare Roshan yana kan sallaya bayan ya kammala sallar
lafilfilinsa yana jan carbi a hankali bakinsa motsi, jin knocking ɗakin da yake ne
yasa shi ɗago da kansa yana kallon bakin ƙofar, miƙewa yayi cikin farar jallabiyar
sa ba tare da ya tambaya ba ya buɗe ƙofa, ganin Baiwar ALLAH yasa shi mamaki domin
tinda take a cikin gidan nan bata taɓa zuwa ta buga masa ɗaki ba ko hanyar wurin
bata yi, cike da mamaki ya ce "Am lafiya kuwa yau na ganki a part ɗina?..."
Yamutsa fuska tayi tare da faɗin "sai wani abu ya faru tukun da na zo
ɗakin ka?..."
Ya ce "to ai naga baki taɓa zuwa bane shiyasa dole abun zai ban mamaki tsawon
shekara guda ana tare..."
Tana son sanar masa amma sai dai bazata iya ba kawai sai ta fake da
cewa "daman, daman naji motsi ne a ɗakin da nake Ni kuma ina jin tsoro..."
Haka ya riƙe hannunta suka nufi waje kai tsaye part ɗinta suka nufa, yana
zuwa ya soma Dube-dube amma bai ga alamar motsi ba.
Ita kuwa zama tayi a bakin gadonta ta wani zuwa masa ido sai sakin murmushi
take, wani irin kallon so da ƙauna take masa wanda ita kanta bata san tana masa
ba,
Juyowar da zai yi yaga ta zuba masa ido sai kallonsa take ba ƙaƙƙautawa,
kaɗa mata yatsunsa yayi a sai tin idonta, a firgice ta dawo hayyacinta tana sauƙe
nannauyar numfashi, ya ce "Are You Okay?..."
Jin tambayar da yayi mata ne yasa ta dafe goshinta tana faɗin "kai
na ciwo..."
tayi haka saboda kar ya gano ta...
Ya ce "ki sha maganin ina zuwa yanzu..." ya buɗe ƙofa ya fice da sauri
da duk kan alamu yayi mantuwa ne,
Baiwar ALLAH bin bayansa tayi da kallo tare da sakin murmushi, ta ɓaro
magani sannan ta miƙe tsaye ta nufi kan mirror ta ɗauki biro a tsakiyar magani ta
rubuta farkon harafin sunan Roshan wato ("R") har takai maganin sai tin bakin ta
kawai ta dakatar, tunowa tayi shima Razhdeen farkon sunansa kenam, yamutsa fuska
tayi tare da sa biro ta ƙara harafin O a gaban R tana nufin ROSHAN kenam tasau
murmushi ta kai maganin bakinta tare da korawa da ruwa ta haɗiye.
Roshan ne ya shugo ɗakin yana waya daga ƙarshe ya katsar idonsa akan
Baiwar ALLAH wacce itama shi ɗin take kallo, buɗar baki yayi ya ce "shikenam
yanzu babu wata matsala ko? Ni zan koma part ɗina..."
Baiwar ALLAH ji tayi zuciyarta ta buga domin bata so yayi nesa da ita, ya
juya zai tafi kenam yaji tana kuka tare da faɗin "wayyo kaina ciwo, hajijiya nake
ji..."
Juyowa yayi ya kalle ta yaga tana shirin faɗuwa ƙasi da gudu ya nufi yanda
take ya rungumota tare da faɗin "sannu ko ina kinsha maganin?..."
Itama riƙe shi tayi sosai tana faɗin "ka taimake ni zan mutu..."
Kwantar da ita yayi akan gado ya ce "ki kwantar da hankalinki babu abinda
zai same ki, kiyi bacci kinji ..."
ya rufa mata mayafi sannan ya juya zai tafi yaji ta riƙe masa hannu..
Juyowa yayi yana kallonta kamar zatayi kuka ta ce "ina jin tsoro dan ALLAH yau ka
kwana anan..."
Nan ma ƙara riƙe masa hannu tayi ta ce "can you sleep with me?..."
Kaɗa mata kai yayi ya ce "okay..." ya ajiye pillow sannan ya kwanta ata
baki-bakin gadon, ita kuma tana ta bayansa murna take yau zata kwana gado ɗaya
da Roshan...
Ta ce "Am ka manta baka kashe ligh ba kuma ni bana iya yin bacci da
haske..."
Tashi yayi yaje ya kashe ya dawo ya kwanta kamar yanda yake ya juya mata
baya...
Yana tunanin abubuwa da dama a ransa, yana jin wani abu akan Baiwar
ALLAH amma haka yake jure wa, yana maganar zuci ya ce "inasonki Ammata amma haka
zan bawa zuciyata haƙurin rashin ki, kina so ki Auri twins ɗina kuma lokaci nake
jira na rabu dake kije ki Aure shi, nayi alƙawari a kaina cewa bazan taɓa saninki
a matsayin ƴa mace ba domin inada kishin da bazan iya yin sharing ba, bazan iya
Auran mata kuma bayan na gama saninta a matsayin ƴa mace daga baya nazo na rabu da
ita ba, wani kuma daban yazo ya Aure ta i can't, Ammata indai zaki zauna dani har
ƙarshen rayuwar mu wallahi ko a yanzu kika nuna mun buƙatarki a shirye nake dana
kusance ki, amma in har ƙudirin ki yana nan na Auran twins a gaskiya ko zamuyi
shekara ɗaki a haka bazan iya kusantarki ba, bana son sharing! bana son sharing,
bana son sharing..."
Yana cikin wannan surutan a cikin zuciyarsa kwatsam sai ji yayi Baiwar
ALLAH ta rungumoshi ta baya, Shuru yayi yana jin yanda ta manno jikinta jikin na
shi,
wani irin haɗiyar yawu yayi tare da ƙarƙame idanuwansa baya so ta
tayar masa da feeling shi kuma bazai iya kusantarta ba, haka yake cikin wannan
halin yana jurewa tare da jero Addu'o'i har bacci ya yi awun gaba da shi.
Ita kuwa Baiwar ALLAH kasa bacci tayi a tunanin ta Roshan zai juyo gareta ne
sai kuma taga akasin haka ko ƙwakƙwaran motsi bai yi ba, tayi takaicin haka sosai
domin ba haka taso ba, tana rungume da shi tana ta saƙe-saƙe a ranta, jin alamun
yayi bacci yasa ta ɗan juyo da shi tana ƙarewa fuskarsa kallo can ta sumbace shi
akan goshi, ta ɗago sannan ta ƙara sumbatar sa a gefe da gefen fuskarsa, daga
ƙarshe ta ɗora lips ɗinta akan nashi tayi masa wani irin hot kiss wanda sai da ya
ɗan motsa yana shirin buɗe eyes ɗinsa, ɗagowa tayi tana kallonsa shi kuwa ya ƙara
zarce wa da yin baccin, itama kwantar da kanta tayi kan ƙirjinsa da haka har bacci
ya ɗauke ta...
Aunty Yolash ce a cikin jirgi ta miƙi ƙasar Jidder tana son samun Mai
martaba akan maganar Abbah da Hajiya Kilishi ko shi zai iya sauraronsa..
______________________________________
Aunty Yolash ce zaune a babban falon cikin gidan tana tare da INDO second ɗin Mai
martaba a yayin da ita kuma Maamie tana can part ɗinta,
Hira suke sosai suna shan dariyar su domin Aunty Yolash da Indo jinin
su ya haɗu sosai, suna cikin shan hirar su sai ga MAAMIE ta sauƙo daga upstairs
idonta akan Aunty Yolash duk tana wani binsu da harara, sauƙo wa tayi ta nemi wuri
ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana tauna ciwgim,
Aunty Yolash ce ta kalleta tare da sakin murmushi a ranta tana faɗin "mun ga
Hajiya Kilishi ma kuma daga ƙarshe abun baiyi mata kyau ba, kowa da ranar sa kema
wata rana sai kinyi kuka da idonki kinzo kina neman gafarar mutane..."
ta ƙarasa maganar idonta akan Maamie,
Maamie ce ta zaro mata idanu tana faɗin "lafiya kuwa Malama kike kallona ko dai
akwai abinda na tare miki ne..."
Maamie ta ce "ke dakata nan fa yanki nane yawwa, gidan mijina gidana
bazaki zo ki takura mun ba, ke asu wa har zakiyi magana akan banyi sallama ba..."
Aunty Yolash ta ce "hakane kamar yanda kike gadarar gidan mijinki ne haka
Nima nake gadara da gidan Yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, kuma hasali na fiki iko da
gidan domin ke ko a yanzu aka baki takardar saki dole ki bar gidan, kuma mu ƙi
maido ki in juninki rashin mutunci ne..."
Maamie ta ce "ai wallahi bari kiji ni da gidan nan Auren zobe ne ba rabuwa
sai dai mutuwa, in hassada kike mun ma gwara ki shanye abun ki..."
Suna cikin wannan cacar baki sai ga Mai martaba ya shugo da sallama a
bakinsa domin ya gama sallamar baƙin da yayi a falon masarautar,
zama yayi yana fuskantar Aunty Yolash da murmushi akan fuskarsa domin ba
ƙaramin farin ciki yayi ganin Autar ɗakinsu ba, gaisawa suka yi sannan ya ce
"Yolash mutan boko yau ɗin boko ya barki kin kawo wa ɗan uwanki ziyara kenam..."
Aunty Yolash ta ce "Yaya mai martaba inason zuwa daman amma ɗawainiya sun
mun yawa..."
Dariya tayi ta ce "wallahi a yau zan koma sai kuma idan na tashi zuwa da akwatin
zan zo nayi muku hutu sosai..."
Aunty Yolash ta gyara zama ta kwashe duk halin da ake ciki na Abbah da
Hajiya Kilishi ta sanar masa, ta cigaba da cewa "Mai martaba ko dan ƴaƴanta a
dawo da ita duk da yaran sun mallaki hankalin kansu, itama kanta Kilishi zata fi
nutsuwa, a halin da take ciki inta cigaba da zama a haka ba'a san mai zata aikata
zuwa gaba ba tinda indai wahala tayi wahala mutum zai fara neman mafita, to mafitan
ne ba'a wani iri za'a nema ba, tinda ta nemi yafiyar mutane ta gyara halayenta sai
a dawo da ita..."
Mai martaba tayi gyaran murya sannan ya ce "hakane duk naji batun ki
Insha Allahu zan je na samu Chief da maganar, sai dai matsala shine ba lallai ya
aminta ba, kar yazo yana faɗa mun maganganu ne kinga shine gaba da Ni, kuma waɗanda
suka girme shi ma bai fi maganar su ba, baffanun mu sun same shi da maganar amma
fur yaƙi to ba lallai ne Ni ɗin ma yaji ba..."
Aunty Yolash ta ce "a'a Yaya mai martaba kar ka karaya kaje ka lallame shi akan
batun dan ALLAH..."
Ya ce "toh shikenam idan kin tashi tafiya sai mu tafi tare Nima inaso na dawo a
yau saboda inada uzurirruka a gabana sosai..."
Aunty Yolash bata kulata ba domin tasan inta biye mata zasu kaure da faɗa ne
yanzu kuma bata da lokacin ta, haka suka fice Indo ta raka su har wurin parking,
suka shiga mota security ya jasu suka tafi airport.....
Mai martaba ne yake zaune a falon Abbah shima Abbah ɗin yana nan anyi
dace yau bai fita ba, bayan sun gaisa ne Mai martaba ya ce "a gaggauce nazo
domin a yau nake son komawa Jidder..."
Abbah cikin nuna farin ciki ya ce "Tinda kuwa hakane nasan kaima akwai
abinda ya kawo ka..."
Mai martaba ya ce "sosai ma kuwa shiyasa ka ganni nayi zuwan bazata ai..."
Murmushi Abbah yayi sannan ya ce "Yolash taje ƙasar da kake ko? nasan ƙarata takai
kaima kazo kayi mun maganar wancan matar da yanzu ji nake kamar na hallakata
ko ....?
Abbah ya ce "to kuwa tinda na rabu da ita har abada bazan ƙara kallon
yanda take ba balle tayi tunanin zan maido ta, kuma wallahi zanje na sameta ta fita
shirgi na, ta daina bibiya mun ƴan uwa idan ba haka ba zan yi mata abinda batayi
tunani ba, kuma da kuke cewa saboda ƴaƴanta na dawo da ita shin a tsirara kuka ga
ƴaƴanta? ko kuma barinsu nayi da yunwa? to ko su yaran su ɗauka cewa uwarsu ta mutu
domin baza su ƙara kusantar yanda take ba kada ta shafa musu baƙin hali da
dabbanci, na rantse da sarkin dake busa mun numfashi duk wanda ya ƙara mun maganar
na dawo da Kilishi wallahi sai nayi shara'a da shi domin bana son harkar
shishshigi, kuma ko kaine idan na sake jin kayi mun maganar na dawo da ita wallahi
zan yanke alaƙata da kai har abada..."
Mai martaba cike da mamaki yake kallon Abbah ya ce "Subhanallahi abun bai kai ga
haka ba, Allah ya huci zuciyarka Ni zan koma yanda na fito, na barka lafiya..."
Mai martaba fita yayi yana fita ya tarar da Ummy a tsugune sai faman kuka
take, tsugunawa yayi tare da ɗago kanta yana faɗin "Uwar masu gida ki kwantar da
hankalin ki insha Allahu mamanki zata dawo..."
Ta bayansu Abba ne ya fito yana faɗin "sai dai su haɗu a lahira domin
ita da mahaifiyarta sai a mafarki, duk photunan Kilishi nasa an fitar mun da su a
cikin gidan nan, a duniyar nan babu macen da ta sa hannu ta mareni sai ita na tsane
ta..."
Ummy cikin ɓacin rai ta taso tana kuka ta ce "wallahi Abbah banda sai
a lahira kam, mahaifiyar mu tana raye amma ka haramta mana ganinta? duk ƙiyayya ai
bazai sa ka raba mu da ita ba, idan kai baka sonta ai mu muna sonta tinda har ta
shayar damu ruwan nonon jikinta..."
Abbah a fusace yayo kanta zai dake ta Mai martaba yayi saurin riƙo shi
yana faɗin "a'a banda dukan uwar masu gida domin daga baya zakayi nadama..."
Ummy da gudu ta koma cikin babban falon gidan tana kuka, Ammy tayi rarrashin
duniyan nan amma taƙi daina wa..
Abbah a fusace ya shugo yana balbala masifa ya kalli yanda Ummy take ya
ce "ina kema kin koyi rashin kunya irin na yayunki dana uwarki ko? to kar ma ki
fara domin karya ki zanyi a cikin gidan nan, ke har nawa kike? Uwar ki ce bazaki
ƙara sakata a idonki ba na gaya miki..."
Mai martaba bayan ya fita motar Aunty Yolash ya shiga rai a ɓace, Aunty
Yolash murmushi tayi domin tasan matsalar shiyasa bata shiga ciki ba domin zata iya
yiwa Abbah rashin kunya..
Airport suka nufa anan ta sauƙe Mai martaba kafin ya shiga jirgi ya kalli
Aunty Yolash ya ce "zaku daɗe baku ganni anan Nigeria ba..."
yana kaiwa ya shige jirgi, ita kuma Aunty Yolash wuce wa tayi kai tsaye
Suleja taje daga nan ta wuce Bauchi...
★★★★★★
Bayan Aunty Yolash ta samu Hajiya Kilishi a garin Suleja zama sukayi suka tattauna
akan maganar Abbah,
Aunty Yolash kamar zatayi kuka ta ce "Hajiya Kilishi shawaran da zan baki shine ki
cire Abban yara a ranki domin bazai taɓa mai dake gidansa ba, ki duba kika irin
wulaƙanci da yayi mana Ni da mai martaba abun ba daɗi, kuma ya rantse cewa bazai
taɓa kusantar yanda kike ba to kuwa kinga babu amfanin kiyi ta bibiyansa yana
wulaƙanta ki, shi kaɗai ne namiji? ko shi ɗin ɗan gwal ne, to bari kiji inda nice
wallahi ko ɗan gwal ne bazan kalli yanda yake ba balle ya samu damar wulaƙanta Ni,
Ni mamaki ma kike bani har kina bibiyansa kina roƙonsa cab aini namiji baka isa ka
samu wannan damar ba, bazan taɓa roƙon namiji abu shi kuma ya tsaya yana mun Rashin
kunya ba.....
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*41_ TO_45*
Aunty Yolash ta cigaba da cewa "duk da nasan ke kike da laifi Amma ai yanzu kin
shiryu kuma kinyi alƙawarin bazaki ƙara maimaita kuskuren ba, ya kamata Chief ya
dubi halin da kike ciki yayi haƙuri amma tinda bashida yafiya sai ki sharar da shi,
dan Allah Kilishi ki zamo mai kamun kai, ki daina bibiyansa haka, ni duk abinda
kike so ki ƙira wayata zaki same ni zan dauke miki duk ɗawainiyar ki kar ki damu,
ki cigaba da addu'a komai mai wucewa ne, ki kwantar da hankalinki, ni yanzu zan
koma bauchi domin ayyukana na bari nazo gurin da aka wulakanta ni, na tafi saina ji
ki..."
Daga nan Aunty Yolash ta koma Bauchi, ita kuwa Hajiya Kilishi a ranar ko
rintsawa bata yi tsabar kuka, ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba, ga yanzu ba halin
ganin ƴaƴanta balle taji sanyi a ranta, idan taje yanda suke kuma Sojoji hanata
shiga ciki suke sakamakon bin umarnin Abbah, ya sanar musu cewa idan suka ƙara
barin Kilishi ta shiga masa gida duk saiya hora su...
Wata rana Ummy ta fito falo kana ganinta kasan bata da lafiya ga duk ta rame
tsabar jikinta babu ƙwari haka ta yanki jiki ta faɗi sumammiya, Ammy dake shirya
abinci akan dinning tana hangota ta tafo da gudu tana ƙiran sunanta, dai dai
lokacin da Abbah ya shugo, ganin Uwar masu gida a cikin wannan halin yasa yayo
kanta a ruɗe, haka yasa hannu ya ɗago ta yayi waje da ita sai asibiti...
Ummy Saida ta sha ledar jini da ruwa domin ba ƙaramin wahala take sha ba,
sai da suka kwana tukun ta farfaɗo tana kuka tare da faɗin "ni ku kaini wurin
mommy, nasan tana cikin mawuyancin halin, bana so na mutu ban ganta ba dan Allah,
mommy na an rabani da ita kenan? ba zan taɓa yafe wa duk wanda ya rabani da
Mahaifiyata ba wallahi...."
tana kaiwa ƙarshe ta fashe da matsanancin kuka...
Abbah yana tsaye yana jin duk maganganun da take faɗi ga kuma Ammy a zaune a gefen
gadon da take sai Baiwar ALLAH itama tazo duba ta.
Doctor ya ce "eh duk abubuwan da ya kamata ayi mata munyi yanzu komai normal..."
Abbah ya ce "good, kinga uwar masu gida tashi muje ki shirya na kai ku
wurin uwatta kun tinda kun fi sonta akan Ni..."
ya kalli Ammy ya ce "ina Auta ta?..."
Ammy ta ce "ta fita da Roshan ina tunanin gida suka nufa..."
Ya ce "Okay zan kai su amma bazan bar yarana a hannunta ba domin da mutuncin
su..."
Ammy ta ce "kenam kana nufin kace ita uwar tasun batada mutuncin
ne?..."
Ammy shuru tayi tana gudun kar ta fusata shi domin yanzun ma a dole zai
kai su ba dan yana so ba...
Haka Abbah ya riƙo hannun Ummy ya ɗago da ita duk suka tashi suka
fice,
Bayan sun koma gida duk shirya wa sukayi har ƴar tinny Ammy ta shiryata,
sai a lokacin hankalin Ummy ya dawo jikinta domin a halin yanzu tana muradin sanya
mahaifiyar ta a idonta, kuma taji labarin tana shan wahalar rayuwa kowa ya guje
ta..
★★★★★★★
Baiwar ALLAH ce a ɗakin Roshan tana gyara masa gadon kwanciyar sa, yanzu kwana
biyun nan ita take masa komai, kullum sai ta je part ɗinsa ta gyara tare da wanke
masa bathroom ta feffeshe ko ina da turare, sannan tayi girki ta shirya su akan
dinning su ci tare, a baya kuwa sai dai ta ɗauki nata ta shiga room ɗinta ta ci
acan shi kuma ya zauna a dinning ya ci shi kaɗai, yanzu kuwa zama take su ci tare,
Abun ba ƙaramin mamaki yake bashi ba, a ransa yake faɗin "shin mai
take nufi ne?..."
Itama Baiwar ALLAH kukan take jin maganganun da yake faɗa mata kuma alhalin yanzu
ba haka bane a cikin zuciyarta,
Cigaba da cewa yayi "zan roƙe ki wata alfarma shin zaki iya mun?..."
Yayi maganar yana kallonta, itama kallonsa take tare da ɗaga masa kai,
Jinjina kai yayi sannan ya ce "inaso ki daina shugo mun room, ki tsaya a
yanda kike a baya, girki ne idan kika yi zan ci idan kina so zamu zauna a dinning
muci kamar yanda muke yanzu, amma fake wa wuri ɗaya ne banaso domin nasan kaina
banida juriya, kina cuta na sosai idan naga mun fake Ni kuma bazan iya aikata komai
dake ba saboda nasan wata rana ke matar twins ɗina ne, bana so ya karɓi saura na,
nafi so ya ɓare ki sabuwa a leda zan fi jin daɗin haka sosai, inaso idan na
kusanci mace to ya zamana har ƙarshen rayuwata ita zan rinƙa kusan ta, saboda haka
kiyi nesa da abinda zai sa mu fake wuri ɗaya, zan cigaba da shan lemon tsami na har
Allah yasa mu rabu,
Da fatan dai ban ɓata miki rai ba ko?..."
Baiwar ALLAH ganin bazata iya juran kalaman Roshan ba yasa ta tashi tare da
fashewa da matsanancin kuka ta bar ɗakin da gudu, kai tsaye part ɗinta ta nufa.
Shima Roshan bai san lokacin da hawaye ya fara masa go slow ba domin ba ƙaramin
ƙaunar Baiwar ALLAH yake ba, ya kasa cire ta a ransa kodan yana ganinta koda
yaushe ne...
★★★★★★
Bayan isar su Abbah garin Suleja gidan da aka masa kwatance nan yayi parking a
ƙofar gidan, gidan ne kana gani kasan gidan haya ne amma kowa da part ɗinsa,
Har Ummy ta sauƙa daga cikin motar tayi gaba zata kutsa ciki Abbah
yayi saurin riƙo ta yana faɗin "baki da hankali ne? daga ganin gida zaki shiga
idan ba nan ne gidan kuma fa?..."
Ummy tsayawa tayi domin a halin yanzu bata da wani buri da ya wuce
taga mahaifiyarta..
Wani magidanci ne ya fito daga gidan da duk kan alamu shima a gidan yake
da iyalansa, Abbah ne yayi masa magana yana faɗin
"Dan ALLAH bawan Allah nan ne gidan da Kilishi take?..."
Mutumin ya ce "eh dake part-part ne gidan ban san a wani ƙofa take ba,
kuma akwai mata da yawa a gidan duk bansan sunayen su ba..."
Mutumin ya ce "duk matan Aure ne bazawara ɗaya ce ɓangarenta daban ita kaɗai..."
Abbah ya ce "a'ah kayi mana sallama da ita muna waje daga nan zamu wuce
ne..."
Mutumin ya ce "okay..." Sannan ya shige ciki, can ya fito ya sanar da cewa "tana
fito wa..."
Bayan wasu ƴan mintuna sai ga Hajiya Kilishi ta fito tana sanye
da hijab ɗinta sai faman leƙe leƙe take tana son ganin wanda yazo mata sam bata
lura da su Abbah ba,
Sai ji tayi an rungume ta sosai, zaro ido tayi tana kallon Ummy wacce ganin ta yasa
ta tafo da gudu ta rungume ta,
A ruɗe Hajiya Kilishi ta furta "Ummy..." cike da mamaki take binta da
kallo, Ummy tana kuka ta ce "Mommy yau gamu mun zo gare ki..." tayi maganar
cikin nuna farin ciki,
sai ga Ƴar tinny itama ta rungume ta, cikin farin ciki Hajiya Kilishi tasa
hannu ta ɗaga ƴar tinny tana hawaye tare da faɗin "Nagode muku sosai yara na,
kamar daman kun san ina cikin damuwa na rashin ganin ku a kusa da ni..."
Ummy fashewa tayi da kuka tana faɗin "Mommy ki ga duk kin rame kin zamo
ƴar ƙarama, Mommy baki da ƙashin wuya amma ki ga yanzu yayi miki sauƙa, meyasa zaki
zauna cikin wahala Mommy..."
Hajiya Kilishi tana kuka ta ce "to ya zan yi Ummy dole na zauna cikin
wahala kinga fa kowa ya guje ni, Ni kaɗai nake zaune ba mai taimaka mun, sai yanzu
da Auntyn ku Yolash take turo mun kuɗi, ita take biya mun gidan hayan da nake ciki
yanzu..."
Hajiya Kilishi sai yanzu ta lura da Abbah, kallon yanda yake tayi
tare da faɗin "kayi haƙuri ku shugo ciki mana ku ci abinci..."
Abbah cikin takaici ya ce "daman tinda kike kin taɓa cin girkin ta ne? tin
da kika zo duniya kin taɓa ganinta a kitchen?..."
Abbah ganin Ummy zata bijire masa yasa shi cewa "ok kuje ina jiran ku
yanzu..."
Abbah ya ce "kinga ba wurin ki nazo ba, na dai kawo yarana ne, amma mu shiga daman
inason miki last warning akan bibiyan yanda ƴan uwana suke..."
Ta wanke hannunta sannan ta soma basu abinci a baki duk su biyun da haka ta kammala
basu suka ci suka ƙoshi, ta basu ruwa suka sha...
Ummy ta ce "Mommy daman haka kika iya girki shine bakya mana..."
Hajiya Kilishi murmushi tayi ta ce "kuyi haƙuri nayi kuskure a gafarce
Ni yara na...".
Ummy itama murmushi tayi ta rungumi mommynta tana faɗin "kar ki damu Mommy
muna tare da ke..."
Ummy ta ce "su Aunty Pinky ai sun kusan dawowa, kwanan nan zasu yi graduation 🎓
na gama deegre..."
Jan numfashi Ummy tayi sannan ta ce "tana can tare da mijinta nasan tana
cikin ƙoshin lafiya tinda Marshall yana matuƙar ƙaunar ta..."
Hajiya Kilishi ce ta kalli Abbah ganin yanda yake ta haɗa rai yana fushi,
Abbah kuwa idonsa a gefe guda yana tunani a ransa cewa "anya kuwa wannan Kilishi
ce? gaskiya rayuwa tana bugan ta kuma ina so ta ƙara bugarta da kyau, kuma naga ta
sauya sosai kamar ba Kilishi ba..."
Daga baya ganin tunanin ba shida wani amfani yasa shi yin gyaran murya
yana kallon Kilishi ya ce "kalli Nam..."
Hajiya Kilishi kallonsa take tana son jin wani irin warning za'ayi mata,
Abbah ya ce "last warning da zan miki shine kar ki sake bibiya mun ƴan uwa da
abokaina akan maganar komar dake gidana domin bazan taɓa mayar ki ba, kin fita kin
fita kenam ba komawa, domin bazan kije ki sawa matata damuwa ba, nafi son na rinƙa
ganinta ita kaɗai a gidana tana walwala, don haka ki dakatar da wannan shirmen
nakin, idan ba haka ba wallahi tallahi kotu ce zata rabamu, a saboda ke na ɓata
da abokaina da yawa da ƴan uwana, wacce nake ji da ita a raina ƙanwata Yolash kinsa
na samu matsala da ita, a saboda ke Ɗan uwana ya taso daga wani country yazo wuri
na amma rabuwar ba daɗi muka yi duk saboda ke, meyasa kike son shiga mun rayuwata
kam? shin ana zaman Aure dole ne? nace banaso ana dole kam? Ni fa ba ƙaramin yaro
bane da za'a zo ana damu na da maganar ki, to na rantse idan kika ƙara turo mun
wani sai na ɗauki mataki na gaya miki...."
Abbah ya ce "tin tinin na goge wannan sunan domin na nema wa ƴaƴana uwa
ta gari wacce ta fi uwar su, tana can ƴar aljanna kenam, tana bawa ƴaƴana kulawar
da basu samu a wurin Uwar tasun ba..."
ya ƙarasa maganar yana hararar ta, sannan ya maida idonsa kan Ummy
yana faɗin "ku tashi mu tafi..."
Ummy ƙara narkewa tayi a jikin Hajiya Kilishi ko ɗagowa ta kalli Abbah
bata yi ba..."
Ummy ta ce "Abbah nafi son zama a wurin uwata ba'a wurin Uwar wani ba,
duk uwar da za'a kawo mun baza tafi uwata ba kuma itama uwar tawan ƴar Aljanna ce
da yardar Ubangiji..."
Ummy ta ce "Abbah wallahi bazan tafi nabar Mahaifiyata ba, idan kana so na
tafi sai dai mu tafi gaba ɗaya da ita, amma in har babu ita to Nima babu ni..."
Ƴar tinny babbar yatsar ta tasa a baki idonta akan Abbah itama ta kwanta
akan Hajiya Kilishi tana faɗin "Oh -ohhh..."
Abbah ya ce "shikenam kun kyauta, yana kaiwa nan yayi ficewar sa, a fusace ya
shige motar sa sai Abuja...."
Ummy farin ciki kamar bazata mutu ba, daman shirin ta kenam inta samu
tazo wurin mommynta ba koma wa kuma gashi shirin ta yayi kyau, Abbah yayi zuciya ya
tafi, daman haka take so..."
Itama Hajiya Kilishi tayi farin ciki sosai ganin yaranta a kusa da ita,
yau da su zata kwana...
★★★★★★★★★
Ta ƙura volume waƙa a plasman tana kokkoyan rawar da suke, kuma rawar yana mata
kyau sosai yanzu ta ƙwarai sosai domin ba rawar da bata iya ba, hatta kaɗa jita
ta ƙaro training sosai ba ƙaramin kwarai wa tayi ba,
ta ɓangaren karatu kuwa nan ma ba laifi sai dai tayi rubutu, ta iya
na Hausa sannan ta iya na Turanci sosai, ta ɓangaren islamiyya kuma dake
makarantar a haɗe take gaba ɗaya, bata iya bada hadda amma tana tattare su a cikin
kwakwalwar ta.
Tana cikin rawar sai ga Madam Blessing ta fito daga kitchen daman
tasan sana'ar ta kenam hakan yasa ko sauraronta bata yi ba, Ƴar Amana ce taje da
gudu ta kamo hannun ta tare da jawo ta gaban plasman tana mata nuni da suyi rawa,
ba yanda Madam Blessing ta iya haka ta biye mata sukai ta tiƙar rawa sai da madam
Blessing ta gaji ita kuwa Ƴar Amana kamar wacce ake ƙara mata petur, sai da waƙar
taje ƙarshe tukun ta haƙura..
Bayan sati ɗaya Madam Blessing ce ta haura saman ɗakin Ƴar Amana
zata je ta tayata shirin tafiya makaranta domin ta kammala haɗa kayan breakfast..
Shigar ɗakin ke da wuya ta tarar da Ƴar Amana kwance ƙasin carpet ɗin ɗakin
tana kame da cikinta ta tukwikwiye guri ɗaya, da gudu Madam Blessing ta ƙarasa
gurin ta tana ƙiran sunanta, ai kuwa tana ɗago ta taga bata motsi ga ido a lumshe,
ƙirjin Madam Blessing ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske sai
ambaton "Jesus, Jesus take domin bata san me zata ga ya wa Razhdeen ba, kuma
tsoron ta kar taje ta mutu, haka ta ɗagota daƙer tayi waje da ita, daƙer ta iya
sauƙar da Ƴar Amana ƙasin down stairs domin yanzu tayi cikar da mace bazata iya
ɗaukarta ba, madam Blessing niyar ta ta nufi hospital da ita, tana shirin barin
falo sai ga Roshan ya shugo falon da sallama a bakinsa, ganin madam Blessing tana
riƙe da Ƴar Amana yasa shi yowa kansu da hanzarinsa yake faɗin "me ya faru da
Sarah?..."
Cikin ƙiƙƙinar magana tsabar a ruɗe take ta ce "ban sani ba Nima, haka na
same ta a sume..."
Roshan duba ta yayi sosai ya ga jini ya ɓata farin wandon ta, girgiza kai
ya yi sannan ya ce "ba sai an kaita asibiti ba ta fara period ne..."
Yasa hannu ya karɓe ta tare da yi mata ɗaukar luɗa ya nufi ɗakinta, yana
haurawa ya kwantar da ita akan gado sannan ya sanar wa Madam Blessing cewa "ki
canza mata kaya sannan ki shirya ta, fatan dai kuna da pad?..."
Yana ƙarasa maganar sai ga ƙira ya shugo masa waya, dubawa yayi yaga Razhdeen ne
ya ɗauka yana sakin murmushi, kafin buɗe baki Razhdeen ya katsar da shi da cewa
"ka je ka dubo mun Sarah meya faru da ita..."
Roshan sake baki yayi yana jinsa yana mamakin taya yasan bata da lafiya,
Roshan ne ya ce "kai da kake can taya kasan wani abu ya faru da ita?..."
Razhdeen ya ce "haka kawai zuciyata take bugawa da kowani harafi na sunanta, gaba
ɗaya na kasa kwantar da hakalina..."
Roshan jinjina kai yayi sannan ya ce "okay don't worry the father of
lover not soldier in dis time..."
Razhdeen ne ya katse shi da cewa "who told you? kar kayi tunanin kawo
mun maganar soyayya domin she is a younger girl how comes zan yi soyayya da ita,
but ba ƙaramin raina mun wayo kayi ba twins..."
Ata ɓangaren Razhdeen kuma ganin video yasa shi miƙewa tsaye daga zaune, ganin
irin girman da Ƴar Amana tayi ta zama cikakkiyar mace, yarinyar da yake raina
shekarun ta gashi har tafi wata mai shekara 25 cikar jiki, da breast da hips haɗe
da ƙugu duk a cike, wani irin haɗiyar yawu yayi yana ƙareta da kallo kamar wanda
yake gaban ta, girman yarinyar yarinyar ba ƙaramin mamaki ta bashi ba,
yana cikin wannan tunanin yaji an masa magana ta baya, switch ɗin wayar
yayi tare da juya wa ganin Madam Parveen ce ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da
try ɗin kayan Abinci tana ƙoƙarin jera su akan dinning, cikin yaren turanci take
faɗin "M.G Razhdeen meya faru ne naga ka miƙe tsaye..."
Razhdeen ya ce "tinda har ya aiko muku letter cewar yayi Aure sannan
babu wanda zai san a yanda suke ai shikenam sai kuyi haƙuri ku jira bayyanowar su,
duk da nasan ba son ƙanwata Minal kuke ba kuma most especially ya musulunta ba tare
da sanin ku ba, duk wannan abubuwan da ya aikata ban san da su ba, ban san ya
musulunta ba sannan ban san yayi Auren sirri da Minal ba sai labarin tafiyar su
naji..."
Duk wannan maganganun Daddyn su ne ya fito daga part ɗinsa yake faɗin
haka wato
"Chief Of Defence Staff" shugaban sojojin ƙasar U.S ya ƙarasa maganar tare da
zama shima akan kujera.
Madam Parveen kallonsa tayi tare da faɗin "we are not complete, Mohandas
he's my first born bazan taɓa cire shi a raina ba ina kan son sa har gobe, sannan
my last born na rasa ta since how comes zaka ce we are completed? why? tell me your
reason..."
Rakesh ne ya shugo shima jikinsa a sanyaye jin abinda Daddynsu yake faɗi,
dawowar sa daga wurin aiki kenam gashi sanye da kakin soja a jikinsa,
Gaishe su yayi zai zauna kenam Madam Parveen ta dakatar da shi da cewa
"your welcome my Son but kaje ka rage kayan jikinka sai kazo mu je dinning..."
Ko ƙara kula Daddy bata yi ba saboda yanzu zaiyi abinda zai sa suyi
faɗa, kowa yana ji da aikin ɗamarar sa.
Razhdeen ne ya kuma yin magana yana faɗin "Dad Please i want to ask you
something..."
Razhdeen ya fara magana da cewa "meyasa kake gava da mahaifina sannan baka son
haɗa jinsi da shi amma kuma Ni ka ɗauke ni tamkar ɗan ka, ko kaɗan baka son ɓacin
raina, a koda yaushe ja na kake a jikinka kuma nasan iya Ni kaɗai kake so acikin
yaran mahaifina i don't know why...."
Madam Parveen ce ta kalli Chief domin ta daɗe tana bashi haƙuri akan
yaje su sasanta kansu ko dan saboda Razhdeen,
Razhdeen bai taɓa masa wannan tambayar ba sai yau,
Shi kuma Chief Of Defence ya ce "bazai taɓa zuwa yanda Chief Of Army's
Nigeria yake ba sai dai idan shine ya fara zuwa yanda yake domin a cewar sa ai
shine sama da shi...
Razhdeen jin a wurin aiki suka samu matsala yasa shi cewa "Rakesh ne ya
kamata ya fara neman maslaha domin Ni ne sama da shi, kuma bugu da ƙari a wurin
aikin ne ba'a ordinary place ba..."
Daddy ya ce "Good my best, to shi Abbah ku yayi laifi amma girman kai yasa
ya kasa neman sulhu tin tsawon shekaru domin tin ina Nigeria da zama yanzu shekara
23 kenam, i swear to God in har ya zo ya nemi sulhu zan yafe masa tunda a ƙasa na
yake..."
Daddy ya ce "tin a Nigeria nine Ogansa, sun fita aiki yaje ya jefar da
bindigarsa, ganin ina mutunci sosai da shi kuma a lokacin abokai muke sai dai
igiyar mu ba ɗaya ba yasa na ce sai dai yayi abu biyu na ɓatan gun a wurinsa,
zaɓi biyu ko yasa hannu a takardar Apologize letter ya bada haƙuri kenam
albarkacin ina tare da shi, inda ace wani ne daban dole sai ya biya ko kuma a kulle
shi, sannan nace ko ya biya kuɗin gun in yaso ya biya rabin kuɗin ni kuma saina
taya shi biyan rabin shin banyi masa halacci ba ? to a lokacin sai ya ɗauki
takardar bada haƙuri ya yage a gaba na sannan ya sanar mun cewa wai ina so na
tozarta shi ne yasa na bashi takardar saka hannu, sannan ya ce ba zai biya kuɗin
ba tinda wurin yaƙi yake kuma a lokacin anji masa rauni a ƙafa daƙer yake iya
tafiya a lokacin, mahaifinku ya gama mun rashin kunya sannan ya fice a office ɗina
yana ganin bazan iya koransa daga aikin soja ba amma kada ya manta nima fa inada
Oganni, bayan kwana biyu ban san ya akayi ba ashe sauran shuwagabannin sunji
labarin abinda ya faru na ɓatan gun mai bala'in tsada hakan yasa suka sa aka kamo
mahaifin ku suka kulle shi na tsawon wata uku, hakan ma Ni nayi shige da fice nasa
aka fito da shi daƙer domin tsawon zaman da zai yi a kulle tsawon shekara uku ne
amma saboda jajircewar da nayi yasa na fito da shi a cikin wata uku, a lokacin ba
ƙaramin kashe kuɗi nayi ba, dukiyata haka na ɗauka ina zubar da su duk a saboda
mahaifinku ya fito daga uƙubar da yake,
Ashe shi a tunaninsa nine nasa aka kulle shi, amma bai san Ni nayi ƙoƙari
na fito da shi ba domin hanawa nayi a sanar da shi har yau bai sani ba, kuma
wallahi Ni babu yanda za'ayi nasa a kulle shi duk girman laifin da ya mun domin tin
muna primary muke tare, muka yi Junior tare har muka yi secondary, daga nan muka
rabu na je nayi deegre da master ɗina a anan ƙasar U.S na soldier,
kuma na riga mahaifinku shiga soja bayan wasu shekaru shima ya shiga,
bayan ya fito daga maƙarƙama ya same ni anan ma ba ƙaramin matsala muka samu ba
abunda yasa na biye masa kuma shine ya ƙirani da Arnen banza kuma ina mazannin
Ogansa, daga lokacin na fusata munyi faɗa sosai daƙer aka raba mu, har an bashi
takardar barin aiki saboda yayi faɗa da Ogansa nasa aka dawo da shi wurin aikinsa,
kuma matakin da yake yanzu na chief Of Army's shine matakin da nake a lokacin,
bari na nigeria bayan an ƙara mun matsayi aka dawo dani nan ƙasar Austrolia a wani
za'a bada matsayi na a nigeria nasa aka bawa mahaifinku duk zaman gavan da muke,
amma har yau bai sani ba,
Sannan kai kuma a lokacin da za'a ɗauki sojoji anan ƙasar na
bada sunanka aka aika maka can Nigeria nasan har yau mahaifinka bai san cewa ni ne
na ɗauke ka ba, sannan na kai ka matsayin da a lokacin baka kai kaje ba, kuma sai
akayi sa'a kana aikin da ya kamata, na kuma ɗauke ka tamƙar ɗan dana haifa, nake
jan ka a jiki har muka shaƙu sosai ka kuma ɗauki nan gidan tamkar gidanku,
Kuma dake daman tin kuna yara kai da twins ɗinka Roshan kuka shiga
zuciyata, ina masifar son twins a rayuwata, ko zan yi gava da mahaifinku da kuma
sauran to ku kai da Roshan bazan taɓa ɗaukar ku a haka ba,
Daga lokacin nasan cewa Christal sun fi musulmi haƙuri da juriya da kuma
tawakkali duk da nasan a cikin musulman ba duk haka bane, to kaji dalilin samu
matsala ta da mahaifinku...."
Jinjina kai Razhdeen yayi domin a halin yanzu bashi da bakin magana
tinda kowa yasan Abbah ne bashi da gaskiya, kuma Chief Of Defence yayi musu ƙoƙari
sosai ya yi halacci ba ɗan kaɗan ba....
Duk maganganun da Chief yayi ashe Razhdeen yana yin recording domin tin kafin nan
ma yasan Abbah ne da laifi, yayi recording ne saboda akwai lokacin da zai kunna wa
Abbah ya ji irin alkhairi da Abokin gavan sa yayi musu a lokacin da yake cikin
gava da shi, domin Razhdeen ba lallai ya iya bayyanar da wannan bayani ba hakan
yasa yayi recording...
Daddy ya ce "what?..."
Ta ce "ka ce inda ace Daughter ka Amreesh tana nan da ka Aurar da ita a Razhdeen,
shin ba haka kace ba?..."
Rakesh yana zaune ya ce "ey tabbas duk muna nan har shi kan shi M.G
Razh..."
Razhdeen dai girgiza kai yayi yana ƙwaƙulo murmushi domin tin lokacin da aka haifi
Amreesh Chief yayi alƙawarin ta a Razhdeen, kuma shima Razhdeen yaso Amreesh tin
tana yarinyar ta, saboda ita kullum yake zuwa gidan su tin suna Nigeria kafin Abbah
da Daddy su samu matsala,
Amreesh ba ƙaramin shiga cikin zuciyar Razhdeen tayi ba, tin daga
lokacin yayi alƙawari a kansa cewa babu yarinyar da zai Aura in ba Amreesh ba, ya
ɗau alƙawarin zai jira ta har ta girma, yana da ƙwarin gwiwa sosai akanta domin
Daddynta shima ya sanar cewa yayi Alƙawari idan Amreesh ta girma zai sa ta
musulunta sannan ya Aura mata Razhdeen ya kuma cewa da sharaɗi ɗaya,
A lokacin kowa yana son jin wani irin sharaɗi ne wannan kuma har
Abbah mahaifin Razhdeen shima ya amince indai har zata musulunta zai amince
Razhdeen ya Aure ta.
Daddy ya sanar cewa "yana son Amreesh tayi aikin soja itama..."
Har zuwa yanzu akwai photunan Amreesh da yawa a wurin Razhdeen tin tana
yarinya ƴar shekara uku...
Jikin Razhdeen ne ya yi sanyi haka yake jin zuciyar sa tana bugawa, lokaci guda
fuskar Amreesh ya fara masa gizo lokacin da take yarinya ga kalar dariyar ta irin
na yara sai ƙyalƙyalewa take da dariya a yayinda yake lilata a lilon wasan yara,
wani irin haɗiyar yawu yayi sauran kaɗan hawaye ya gangaro masa yayi
saurin goge wa.
Kowa a wurin ya lura da damuwar da Razhdeen ya shiga lokaci guda kuma an san duk
akan Amreesh ce domin kowa yasan tsananin so da ƙaunarta da yake...
Razhdeen ya kalli Daddy sannan ya ce "har yau har gobe ina tsananin
ƙaunar Reesh, ina son Reesh nasa a raina itace matar da zan Aura kuma har kullum
ita nake kalla a matsayin nan, hakan yasa babu wata mace a gaba na, babu macen da
nasa a raina cewa zan Aura har yanzu, kullum mafarki na da tunani na shine Reesh
zata dawo gare ni ne, har yau ban daina neman ta ba, ina aiki na amma kuma ina
bincikar yanda take,
har yanzu ban yadda cewa Reesh ta mutu ba, na rantse da sarkin dake busa
mun numfashi wallahi tallahi Reesh tana nan a raye, har yanzu ɓangare guda na
zuciyata wanda na sadaukar wa Reesh tana kan bugawa hakan na nufin Reesh tana nan a
doron duniya,
zuciyata gida biyu ta kasu ɓangare guda na Reesh ce ɗayan ɓangaren
kuma...."
Lokaci guda ya tuno da Ƴar Amana videon ta daya kalla ne ya faɗo masa a
rai sai kuma yake hasasho fuskar ta,
Girgiza kai yayi cikin sassanyar murya ya ce "gaba ɗaya zuciyata ba tawa bace...."
Lokaci guda hawaye duk ya wanke masa fuska, a ruɗe ya miƙe tare da nufan
hanyar fita,
Lokaci guda itama ta kife ƙasin carpet tare da rausa uban ihu tana faɗin
"ku nemo mun Amreesh ɗin ta, tana raye wallahi, Allah yasa tana rayeee, wayyo
Amreesh ɗinta...."
Daman tana maƙale da kukan ta ganin bazata iya riƙe wa ba yasa ta fara kuka
na gaske,
Rakesh ne yayo kanta ya ɗago ta yana rarrashinta shima yana kukan,
Daddy shima a cikin damuwa ya miƙe ya koma cikin room ɗinsa, yana jin
takaicin ya kasa cika wa Razhdeen alƙawarin da ya ɗaukar masa gashi har zuwa yanzu
Allah bai ƙara basu haihuwa ba balle in ya ƙara samun mace ya ba shi......
Tin daga lokacin aka fame wa Razhdeen ciwon da ke cikin zuciyar sa,
yanzu da Amreesh yake kwana sannan ya tashi da ita a cikin zuciyar sa, ya kuma
ƙudurta a ransa cewa zai cigaba da jiran Amreesh har ta bayyana, ya furta cewa
"in har yayi Aure kafin bayyanowar Amreesh to sai dai rabin zuciyarsa ce ta daina
harbawa nan ne zai san Amreesh ta mutu....
★★★★★★★
A ɓangaren Abbah kuwa damuwa na yau daban na gobe daban ƙarfi da yaji Uwar masu
gida da Ƴar tinny sun ƙi dawowa yau tsawon wata guda, da haka har ya haƙura ya
barsu...
Suna zazzaune sai ga ƙiran wayan Abbah, yana dubawa sai yaga ƙiran su
Pinky da Rukky ne dake can ƙasar London,
Yana ɗagawa yaji muryar Pinky suka gaisa take sanar masa cewa "gobe
zasu yi graduation..."
Abbah ya nuna farin cikin sa sosai ya ce musu "Insha Allahu gobe zaku gan
mu mun zo London..."
Gashi yanda yasa wayar a speaker kowa na falon yana ji dake iya Ammy ne
da Baiwar ALLAH.
Cikin rashin fahimta Abbah ya ce "kuna nufin kun samu mijin Aure ne?..."
Pinky ta ce "a'ah Abbah Ni da Rukky ne zamu Auri juna saboda anan makarantar mu
duk haka suke yi suna Auran junan su, namiji ya Auri namiji haka itama Mace ta Auri
mace wallahi kuma fa Abbah kar kaga yanda ake dacewa da juna har party ake yi, mu
ma za'a ɗaura mana Auren ina zaku zo partyn bikin bayan graduation ɗin ?...."
Abbah jin kansa yayi ya tafi zuuuu ya rasa ganewa hajijiya ne ko kuma
mai?
Ammy da Baiwar ALLAH kallon juna suka yi cikin zaro ido waje jin abinda
Pinky ke faɗi..
Abbah ya ce "wait! wait wai kina nufin ke da Rukky zaku Auri juna? kuma haka ku ka
ga anayi?..."
Pinky ta ce "eh mana Abbah ai shiyasa nake cewa Nigeria ƙauye ne duk basu
waye ba, domin ban taɓa ganin anyi ba..."
Abbah ya ce "kenam iya Auren ku ka ga anayi? idan akayi Auren mai ake
yi?..."
Abbah yayi tambayar nan ne saboda yasan shin suna aikata mummunan aiki ne ko
kuma...
Pinky ta ce "idan akayi Auren Ni zan zama miji ita kuma Rukky mata ita zatana mana
girki da aikin gida, Ni kuma sai ina fita yawo na, bayan wasu shekaru sai mu haifi
ƴaƴan mu...."
Abbah ya ce "kamar dai miji da mata su kwana gado ɗaya har suyi sex kun
taɓa? ai dai kinsan sex kam..."
Pinky ta ce "haba Abbah wannan ai sai an ɗaura mana Aure a school ɗin kafin
nan, cab ai mun san haramun ne yin sex kafin Aure shiyasa zamu jira muyi
Auren...."
Pinky ta ce "Abbah ka taɓa jin Aure ya zama haramun? ai ko wani irin Aure halal
ne, Auren Mace da namiji halal ne haka Auren namiji da namiji shima halal ne haka
kuma Auren mace da mace shima halal ne, saboda hakane yasa na sanar maka ko kuma
zaku zo hidimar bikin..."
Pinky ta ce "Abbah ga ƙawayen mu anan har yaushe sai mun koma Nigeria
ƙauye kuma..."
Abbah ya ce "haba Balkisu baki ga Yayan ku Roshan shima a gida yayi Aure
bane, dan ALLAH ku dawo kuyi Auren nan, Ni zan ɗauki ɗawainiyar komai da komai duk
abinda kuke so, na tanadar muku da gidan da zaku zauna, in ma bazaku zauna ba zan
kai ku ƙasar waje kuje ku huta duk ƙasar da ku ka zaɓa...."
Abbah ya ce "eh gobe da sassafe ku hau jirgi ku dawo da wuri kun ji Daughter's
ɗina...."
Pinky ta ce "to shikenam Abbah zamu fara shiri tin yanzu gobe zaku gan mu a
Nigeria..."
Abbah ya amsa mata cikin kulawa amma cikin zuciyar sa tafasa yake kawai jurewa
yake....
Sai bayan sun kammala wayar ya ɗorata akan ƙirji yana sauƙe nannauyar numfashi har
zuwa yanzu ƙirjinsa bugawa take, a ransa yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi
raju'un, Allahumma ajurni fi musibati wa akhlifli khairan minha, wannan wani irin
ƙalubale nake fuskanta ne kam, duk ƴaƴa babu na gwara, ɗaya tabi saurayi sun gudu
wacce take ji da ita ta zaɓi uwarta tare da Auta ta, ga kuma sauran biyun suna son
kauce hanya wai Auren jinsi..."
haka yake ta wannan tunanin a ransa...
Baiwar ALLAH kam abun ma dariya yaso bata, kamar waɗanda basu shiga
islamiyya ba, kodan rayuwar can ta chanza su sosai, dan ma Aski yazo gaban goshi
sun kammala school ɗinsu,
*DAGA WANNAN SAI LAST PAGE SAI KUMA MU SHIGA BOOK 3 TAKUN ƘARSHE..."*
*WAƊANDA SUKA BIYA KUƊIN SU NA BOOK 3 300₦ ZAKU GA NA FARA SAKA KU A PAID GROUP,
ZUWA NEXT WEEK ZAMU FARA BOOK 3 TAKUN ƘARSHE...*
*DALILIN DA YASA NA ƊAGA SAI NEXT WEEK SABODA WAƊANDA BASU BIYA BA SU SAMU
DAMAR BIYA KAFIN ZUWA LOKACIN, SABODA A FARA A TARE...*
*TO MASOYA KAMAR YANDA NA SUBURBUƊO MUKU TYPING NIMA INASO KU SUBURBUƊO MUN
SHARHI😅😅😅*
FATAN ALKHAIRI 🙏
asmeetah writer ✍️
*MAƘIYI_NAH*
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أوال 🥳
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?
substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
STEP TWO
👇
*46_ TO_50*
*wannan shine ƙarshen littafi na biyu sai mun haɗu a littafi na uku wato takun
ƙarshe...*
Pinky zama tayi a gefen Abbah tana gaishe shi, Abbah amsa mata yayi tare da
faɗin "ji ta kamar ta Allah..."
Pinky cikin murna ta tashi tana magana a cikin ranta haɗi da cewa
"yawwa Abbah yanzu za'a tattauna akan batun party graduation da kuma engagement ɗin
mu Ni da Rukky..."
Abbah bin bayan ta yayi da kallo yana girgiza kai domin ba ƙaramin
tausayawa yaransa yake ba...
Bayan wasu mintuna sai ga Rukky sun shigo duk suka zauna akan carpet
suna sauraron abun da Abbah zai sanar musu...
Abbah ya ce "ai kun fi dabbobin ma dabbanci domin su dabbobi basa taɓa zama mutane
amma mutane sukan zama dabbobi to ku kuna daga cikin su..."
Rukky ta ce "innalillahi....."
Bata ƙarasa ba Abbah ya darara mata tsawa da cewa "ki mun shuru dallah, ke kinsan
innalillahi kuwa? Inda kun sani da baza kuyi ƙoƙarin aikata ɓarna a doron ƙasa ba,
inda ace ban saka ku a islamiyya ba sai naga laifin kaina amma yanzu na
rigada na sauƙe hakkin ku a kaina sauran abu ɗaya ya rage shine na samu na Aurar da
ku, amma saboda daƙiƙancin ku wai har kuna ƙirana a waya cewa zaku yi Auren jinsi
abu ko daɗin faɗi babu, in banda rashin ilimi da jahilci tin daga furucin sunan
zaku san cewa wannan baya daga cikin addinin Musulunci, a cikin litattafan
musulunci aina ku ka taɓa jin an sanar cewa ayi Auren jinsi?...."
Rukky ta kalli Pikky tana hararar ta cikin ranta tana faɗin "ai daman nace kar ki
sanar wa Abbah ki kayi kunnen uwar shegu..."
Pinky da Rukky gaba ɗayan su baya suka ja suna zazzaro ido waje a tsorace,
Abbah ya ce "ko ku sanar mun gaskiya ko kuma yanzu na aika ku lahira kuje
can ku cigaba da shirmen ku domin ba'a gabana zaku yi wannan ta'addanci ba..."
Abbah ya ce "ku faɗa mun gaskiya magana ɗaya shin kuna maɗigo? wallahi idan naji
ƙarya daga bakin ɗayan ku saina harbe ta..."
Itama Pinky ta ce "Abbah me zai sa mu aikata wannan abun, mun san dai sai
anyi Aure akayi..."
Suna cikin wannan halin sai ga Ammy ta shugo tana murmushi tazo har yanda suke ta
ɗago su idonta akan Abbah ta ce "kayi haƙuri Abban yara irin wannan a hankali ake
binsa, ka ciro bindiga ai tsoro ma bazai barsu su faɗi gaskiyar ba, Ni zan je da su
zamu yi magana ta fahimta sannan ayi musu nasiha a ƙara tunatar da su abubuwan da
addinin musulunci ya ƙunsa..."
Abbah cikin ɓacin rai ya kawar da kai ko sauraronsu bai yi ba, haka Ammy ta
fita da su....
Garin Suleja
Ummy da Ƴar tinny har sun murmure na ɗaukin ganin mahaifiyar su, suna zaune cikin
ƙoshin lafiya, ga Aunty Yolash kusan kullum sai tayi musu aike domin ba ƙaramin
farin ciki tayi ba jin yara biyu sun dawo wurin mahaifiyar su ko ba komai zasu
ɗauke mata kewa kuma zata rage tunanin Abbah....
Bayan wasu kwanaki Pinky da Rukky gaba ɗaya basa jin daɗin zaman
gidan domin gidan ya yi shuru kamar ba mutane ga rashin ganin ƴan uwansu ko ba
komai zasu ji daɗin zama idan suna kusa da ƴan uwan, Minal ta tafi ga Ummy da ƴar
tinny suma sun gudu wurin Maman su, ga Baiwar ALLAH basa shiri balle suje part
ɗinta, su kuma baza su iya zama da Ammy suyi hira ba hakan yasa suka yanke shawara
suma zasu gudu wurin Mamansu, gashi graduation ɗin da zasu yi ba'ayi ba Abbah ya
yaudare su a cewar su..
Kamar yanda suka tsara haka suka samu Abbah cewar zasu kai kayan su gidan wacce
take musu wanki,
Abbah ya ce "meyasa ita ɗin bazata zo tayi anan gidan ba sai an kai mata, bana so
kayan ku suna fita can wani wuri..."
Pinky ta ce "Abbah wai bata jin daɗin jikinta ne shiyasa zamu kai mata duk sanda
ta miƙe zuwa gobe ko jibi sai tayi mana sannan ta goge sai ta kawo mana..."
Already sun ciccire kayansu daga akwati sun maida su cikin babbar jaka wuri
ɗaya yanda baza'a gano su ba.
Security ne ya ɗauke a mota ya kai su har ƙofar gidan mai musu wanki, a ƙofar gidan
yayi parking da mota su kuma suka shige gidan, ba tare da matar gidan tasan da
zuwan su ba haka suka bi wata ɓoyayyar hanya dake cikin gidan suka fita ta can suka
gudu...
Security dai waran awan sa uku yana tsaye jiran fitowar su amma shuru,
ganin zaman yayi yawa yasa ya fara kwaɗa sallama dake matar tana da miji...
Matar ce ta fito tana sanye da hijab ɗinta har ƙasi ganin ɗaya
daga cikin security gidan Chief ne yasa ta durƙusawa har ƙasi tana gaishe shi, ya
amsa mata a mutunce sannan ya ce "wai waɗannan yaran sun manta dani a waje ne?..."
Security ya ce "ha'a su Pinky yaran Chief tin ɗazu na kawo su da jakar kayan
wankin su...".
Matar ta ce "ai ni basa kawo mun wanki sai dai naje har gida nayi
musu saboda tsaron da Chief yake basu, amma ya akayi yau ɗin aka barsu su kawo
wanki, kuma Ni ina gidan banji motsin kowa ba innalillahi..."
Security ya ce "na shiga uku yau sun jawo mun tashin hankali..."
Security ya ce "yanzu waran awa huɗu fa duk ina tsaye zaman jiran su..."
Suna cikin wannan halin sai ga mijinta ya dawo nan ta kwashe ta sanar
masa halin da ake ciki,
Mijin ya sanar wa security cewa "ka shigo Mu dudduba ciki ko sun ɓuya ne,
domin akwai matsala in ka koma ba tare da yaran nan ba..."
Haka suka shiga ko ina sai da suka dudduba amma ba motsin su, sai daga baya aka
gano cewa ta ƙofar baya suka fice ganin wani ɗan ƙaramin ƙofa a buɗe.
Matar ma haka take ta salati tana jero Addu'o'i domin abun ba ƙaramin bata mamaki
yayi ba, tana tunanin taya suka san da wannan ƙofa alhalin basu taɓa ganin wurin
ba...
★★★★★★
Pinky da Rukky kuwa har sun isa garin Suleja, sai da suka isa tukun suka nemi
wayar Ummy domin Mommyn su ta chanza sim, Ummy tayi farin ciki sosai jin labarin su
Pinky sun zo, haka Hajiya Kilishi ta rinƙa tunani a ranta cewa "anya da sanin
Abban su suka zo? amma kuma akwai security mai kai su ko ina zai yi wuya su tafo ba
tare da sanin kowa ba..." haka take wannan tunanin a ranta.
Bayan sun zo har suka shiga gidan da Ummy ta kotanta musu domin
yanzu tasan duk wani lungu da saƙo na unguwar yanzu a free take...
Pinky da Rukky suna shiga gidan bayan sun je part ɗin da Mommyn su take
suna ganin ta haka suka rufa da gudu suka rungume ta suna farin cikin ganin
mahaifiyar su, sunyi matuƙar kewar juna sosai haka rayuwa ta dawo musu kamar
sabuwa...
★★★★★★★
Bayan wata guda da wasu kwanaki gaba ɗaya Abbah ya fita hayyacinsa damuwa ya yi
masa yawa har sai da ya kwanta rashin lafiya hawan jininsa ya tashi, daga baya ya
samu sauƙi sai kuma ya yanke hukuncin zuwa ya gano ƴaƴansa dake garin Suleja idan
da hali yana son ɗauko su gaba ɗayansu.
Ummy uwar masu gida ta tafi ɗiban ruwa acan bakin fanfo amma a cikin
gidan yake can wani ɓangare daban,
Pinky da Rukky kuma sun tafi bakin hanya suyo kifin da zasu yi miya
da kayan vegetables, ita kuma Ƴar tinny tana cikin ɗaki tana ta shan baccin ta akan
katifar da iya ita kaɗai ne a ɗakin sai ledar tsakar ɗaki,
wurin kwanciya duk yaran ne suke haɗuwa akan katifar su kwanta dake
ƙatuwa ce katifar ita kuma Hajiya Kilishi shimfiɗi take a ƙasin ledar ɗakin ta
kwanta haka suke inganta rayuwar su ba takuri da tsangwama...
Hajiya Kilishi tana zaune ɗaga kanta da zata yi kwatsam sai suka
haɗa ido da Abbah, kamar a mafarki a gigice ta miƙe tsaye cike da fargaba da tsoro
domin tasan akan yaran yazo, ga su Pinky sun sanar mata cewa gudowa suka yi, tayi
dasu akan su koma amma fur sun ƙi da haka ta haƙura ta barsu,
Abbah cikin fushi da haɗe rai ya ce "ina kika kai mun yara?..."
Hajiya Kilishi ƙiƙƙina ta fara yi tana tunanin mai zata fara ce masa alhalin tasan
yaran basa fita ko ina acan gidan su balle a aike su,
Kafin ta iddasa maganar ya katse ta tare da darara mata tsawa yana faɗin "nace ina
yarana suke? kada ki kuskura kice mun kin aike su domin ranki zai yi mungun ɓaci a
yanzun nan, kin dai san bana aikan yaran, idan wani abu ya faru da yarana kiyi kuka
da kanki sannan idan kika kuskura aka sace mun yara wallahi sai kin ƙwammace baki
zo duniya ba..."
Hajiya Kilishi hawaye ta soma zubar wa domin tasan yaran aika suka tafi
itama ba'a son ranta ba, su suka ƙi barinta tana fita aikan da kanta..
Abbah ya buɗe baki zai yi magana sai yaji sallama ta bayansa, da sauri
ya waiwaya domin yasan ɗaya ne daga cikin su, ganin Uwar masu gida da bucket na
ruwa a kanta yasa shi zare farin glass ɗin dake kan dararan idanuwan sa, cikin
ɓacin rai ya furta "whattt?..."
Ummy ganin Abban su yasa ta wuce shi da sauri ta sauƙe bucket ɗin ruwan
taje ta rungumo Mommynsu tana rarrashinta ganin yanda take ta zubar da hawaye..
Ummy ta ce "sannu da zuwa Abbah, amma dan ALLAH kar kaga laifin Mommy domin mu
muka zaɓi mu zauna da ita ba wai ita ce ta riƙe mu ba, kar ka sa mana ita kuka tana
cikin farin ciki..."
Abbah ya ce "to meyasa ku ka zaɓi ku zauna da mahaifiyar ku akan Ni
mahaifinku wanda zanfi baku kulawa sama da ita..."
Ummy ta ce "Abbah kayi haƙuri mahaifiyar mu ita ce sama da kai a wurin mu,
domin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yana umartar mu da mu bi uwa, mu
bi uwa! mu bi uwa!! mu bi uwa!!! har sai da ya maimaita sau uku kafin nan ya ce mu
bi uba, don haka zamu fi samun farin ciki mai ɗorewa idan muna tare da mahaifiyar
mu..."
Ummy ta ce "Abbah ka sani fa inda ace kuɗi suna dawwamar da mutum cikin
farin ciki da Babbar Yayar mu bata gudu tabi mijinta ba saboda tasan duk da kuɗin
da take da shi bazai taɓa sanya ta cikin farin ciki ba, haka zalika inda kuɗi sune
kwanciyar hankalin mutum da baka kasance cikin damuwa da kaɗaici ba to haka mu ma
kuɗi bazai taɓa sanya mu cikin farin cikin ba without our mother, because our
mother she's our happiness...."
Abbah shuru yayi yana kallon Ummy ya ma rasa mezai ce mata, yana cikin
nazari sai ga Pinky da Rukky sun shugo sunata shan hirar su na school da suka baro,
idonsu ne ya sauƙa akan Abban su da gudu suka wuce shi suka je duk suka ɓuya a
bayan Mommynsu suna faɗin "Please Mom please kar ki bari ya tafi da mu please..."
Hajiya Kilishi kanta na kallon ƙasi ta kasa cewa komai domin yanzu
Ummy ta fi su baki gaba ɗayan su,
Su Pinky su kam sai dai masifa da munafurci da rashin mutunci ga kuma
tsoro, amma ita Ummy akwai ta da iya zayyano da zance wanda ko mai shekara 40
bazata nuna mata iya magana ba, domin tinin zata saye zuciyar mutum da kalamanta ko
masu daɗi ko akasin haka.....
Daga Pinky har Rukky duk kasa yin magana suka yi daga sun haɗa ido da
Abbah sai suyi saurin sunkuyar da kansu ƙasi kamar wasu marasa gaskiya,
Ummy ta ce "Abbah akwai yanda za'ayi amma mu shiga cikin ɗakin mana Abbah
kana ta tsaye tin ɗazu..."
Abbah ba yanda ya iya haka ya shiga ciki, duk suma suka shige, Ummy
ta ce "Abbah ka zauna a bakin katifar mana..."
Nan ma ya zauna yana binsu da kallo.
Ummy ta ce "tam shikenam Mommy kema zauna domin akwai maganganu masu mahimmanci
da zamu tattauna akai..."
Kowa ya nutsu yana sauraron Ummy domin ita kanta Hajiya Kilishi bata san
wani irin magana Ummy zata sanar ba..
Ummy tana zaune a ƙasin ledar ɗakin kusa da Mommyn su, suma twins suna
gefen Mommy domin duk cikinsu kowa ba son yin nesa da ita yake ba, sai Ƴar tinny
dake bayan Abbah a kwance kan katifa..
Abbah ya amsa mata cikin sassanyar murya domin har yanzu jikinsa bai gama warkewa
ba.
Ta ce "dole a cikin abu biyu ayi ɗaya ko a rasa ko kuma a samu shine kawai..."
Ummy ta cigaba da cewa "idan kanaso mu kasance da kai cikin farin ciki da
annashuwa to dole sai muna tare da mahaifiyar mu a kusa, in har zamu bika mu tafi
to dole sai da mahaifiyar mu, ƙafar ta ƙafar mu,
Idan kuma hakan bazai yu ba to zaka iya barin mu anan in yaso idan
kana son ganin mu zaka zo ka gan mu amma da sharaɗin bazaka ƙuntata wa mahaifiyar
mu ba domin ba wurinta kazo ba, wurin mu kazo, idan kuma tafiyar tayi maka nisa
ai kanada gidaje a cikin Abuja sai ka kai mu can mu zauna da mahaifiyar mu, amma
baza mu taɓa yin nesa da ita ba sai dai mutuwa...."
Abbah kawai tsaya kallon Ummy yayi tana ta zayyano da zance, daga
bisani ya ce "okay duk naji abinda kika ce an ɗauke ku har ita na maida ku gidana
domin hankali na bazai taɓa kwanciya idan bana ganin ku a kusa dani, gani nake
wani abu zai faru da ku especially idan kuna fita yawo koda yaushe dole wasu samari
zasu dakatar da ku daga lokacin da ku ka fara tsayawa da wani namiji a titi
shikenam rayuwar ku ta fara tafiya, especially Balkisu da Ruƙayyat sun fiye rawan
kai dole sai idanuwa na suna kansu, idan suka yi nesa dani hankalina bazai taɓa
kwanciya ba, dan haka na zaɓi ku koma gida yanda zaku samu tsaro na musamman..."
Pinky da Rukky farin ciki kamar zasu fidda fikafiki su fura da Mommynsu jin
da ita zasu koma gida....
Ummy murmushi tayi sannan ta ce "Abbah nayi farin cikin jin haka amma sai
dai akwai abu a ƙasa...".
Ummy ta ce "in har Mommy zata koma gidanka to a tabbatar an maida Auren ku domin
bazata taɓa komawa gidanka babu Aure ba, kayi haƙuri Abbah..."
Ummy ta ce "duk da haka Abbah domin idan ta zauna da Auren ta zata fi yin
daraja a idon mutane, bayan haka Mommy ba tsufa tayi ba balle ace tayi tsufar da
bazata yi Aure ba, idan ka barta a haka zaka cutar da ita ne, kuma sannan idan
tana gidanka babu wanda zai zo neman Auren ta kuma mu ma bason ta Auri wani muke
ba, nasan Ammy bata da matsala zata yi farin cikin kasancewa da Mommy, please
Abbah wannan shine Alfarmar da zakayi mana, sannan ka jawo mana mutunci Please..."
Abbah ya ce "shikenam idan har kasan shi zai sa kuyi farin ciki sannan ku
zauna a inuwar mahaifinku nima na amince amma saboda ku..."
Ummy tsabar murna bata san lokacin da ta tafo ta rungumi Abbanta ba,
duk sauran haka suka tafo duk suka rurrungumi Abbah..
Ummy ta hango Mommynsu tana zaune kai a sunkuyar ita kaɗai sai zabga
murmushi take..
Hajiya Kilishi ta girgiza kai tana dariya, dai dai lokacin ƴar tinny ta tashi daga
bacci, ganin Abbah yasa ta nufo wurin sa da gudu tana faɗin "Abbah nah! Abbah
nah..." ta rungume shi...
Gaba ɗaya hamdala suka yi Abbah sai da ya jira aka kammala girki sannan
suka ci su ka sha, kuma a wannan ranar Abbah zai tattare su a mota ya tafi da su
tinda ba wani shirgi ne da su ba, duk wasu kayan ɗakin Hajiya Kilishi ta sayar da
su taci abinci da kuɗin,
Kafin su tafi sai da Abbah ya biya kuɗin hayan gidan da suka zauna sannan
suka fiffito da akwatina da jakakkuna kowa ya kasance cikin shiri tsab, daga nan
suka nufi Abuja...
★★★★★★★
Baiwar ALLAH gaba ɗaya garin ya yi mata zafi, tayi kukan har ta gaji, ga yanzu duk
halin da zata shiga bata samun mai rarrashin ta, domin Roshan ko leƙa ɗakinta baya
yi sannan itama bata zuwa yanda yake, suna gida ɗaya amma sai suyi kwana biyar
basu haɗu ba...
Miƙa masa takardar hannunta tayi tare da biro tana kuka ta ce "ga shi
nan, ban ga amfanin irin wannan zaman ba, dan ALLAH yau a kawo ƙarshen zaman nan Ni
na gaji, wani sa'in har manta wa nake da inada Aure, dan ALLAH yau kam ka sallame
ni, gidan zan bari gaba ɗaya, zan fita naje na nemo iyaye na..."
Cikin ɓacin rai ta katse shi da cewa "Ni babu ruwana da wani Razhdeen ban sanshi
ba, dan Allah Yaya Roshan ka dawo hayyacin ka, ka tantance abunda nake so da kuma
abunda bana so, amma yanzu komai yazo ƙarshe, yanzu dai ka sallame ni kawai...."
Lumshe idanuwansa yayi cike da damuwa ya ce "shikenam.." yasa hannu
ya karɓi takardar da biro ya juya zai je ya rubuta mata, wani irin suka yaji
zuciyarsa tayi tare da bugawa da ƙarfin gaske a firgice yasa hannu ya dafe sai tin
zuciyarsa yana shirin kaiwa ƙasi.
Ganin yana shirin faɗuwa yasa Baiwar ALLAH shugowa ciki da gudu tayi saurin
riƙo shi tana ambatar sunansa
"Yaya Roshan! Yaya Roshan dan ALLAH ka daina Please ka tashi bana son irin wannan
wasan..."
Shi kuwa lokaci guda idanuwansa suka fara ƙaƙƙafewa yana fitar da
numfashi daƙer, ga yanda yake sama da ƙasa da ƙirjinsa alamun bugawa yake sosai,
Baiwar ALLAH fashe wa tayi da matsanancin kuka tana faɗin "dan Allah
Yaya Roshan ka tashi, wannan wani irin wasa ne haka, bana son kalar wasan nan, ni
idan baka son rabuwa da ni zan cigaba da rayuwa da kai a haka, nima ba son rabuwa
nake da kai ba, ka rufa mun asiri dan Allah..."
Tana cikin wannan halin yana kwance saman cinyar ta sai ga wani irin
jini ya burtso masa daga cikin bakin sa..
wani irin tari yake yana Amar da jini, eyes ɗinsa har sun chanza
color sun koma green, jikinsa gaba ɗaya ya koma yellow alamun babu jini a jikinsa,
yana kaiwa ƙarshen tarin sa numfashin sa ya ɗage gaba ɗaya, sai wuyansa da ya
karye..."
Hannu ta ɗora aka ta zabga wani irin gigitaccen ihu tana faɗin
"innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Yaya Roshan ɗina, wayyo nashiga uku Dan girman
Allah ka tashi, Yaya Roshan ka taimake ni ka tashi wallahi ina sonka, ina matuƙar
ƙaunar ka mijina, ina sonka mijina wallahi, bazan iya kasancewa da kowa ba inba kai
ba, wallahi idan ka mutu Nima rayuwata bata da wani amfani Yaya Roshan..."
★★★
Abbah kuwa suna isowa cikin gari basu tsaya a ko ina ba sai a babban masallacin
juma'a anan ya sanar da ɗaurin Auren sa da za'a gabatar a yau Jumma'at, ya ƙira
manya abokansa a waya, ya sanar musu cewa yana gayyatar su zuwa masallacin juma'a,
waɗanda ya gayyato basu san meye dalilin ƙiran su ba sai da suka zo tukun suke jin
labarin ɗaurin Aure, za'a mayar da Auren sa da uwar ƴaƴansa Hajiya Kilishi ba tare
da wasu daga cikin mutanen sa sun sani ba, sai iya waɗanda yake da kusanci da su,
anan ya bayar da sadaki ya wakilci wasu a mazannin wakilai ga kuma shaidu...
Hajiya Kilishi da ƴaƴanta kuwa suna cikin mota suna jiran zuwan
Abbah domin ko su basu san a yanzu za'a mayar da Auren ba..
Suna zaune sai suka hango Abbah da abokansa waɗanda ya gayyato sun nufo
motar, har an kammala ɗaurin Aure cikin ƙoshin lafiya,
Bayan isowar su Abokanan Abbah fatan alkhairi suka rinƙa musu tare da nasihohi da
wa'azi especially Hajiya Kilishi an fi ja mata kunne kafin daga baya Abbah ya ja
su suka nufi gida, amma yaso ace ammy ta sani bawai ta gani kai tsaye ba, amma babu
yanda ya iya gwara ayi abu a wuce lissafinsa...
Hajiya Kilishi ta sha mamaki sosai da taji a yanzu har aka maida
Auren ta, ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, anan ta ƙara jinjina wa ikon Allah,
Addu'ar ta yayi tasiri lokaci guda Allah ya karkato mata hankalin Chief...
Suma yaran ba ƙaramin farin ciki suka shiga ba...
Razhdeen ya ce "gaba ɗaya hankali na ya kasa kwanciya, zuciyata sai bugawa take, i
think so akwai wani mummunan abu da yake shirin faruwa a gida..."
Gaban Abbah ne ya yanke ya ce "mummunan abu kuma Razhdeen? a'a babu wani
abu da ya faru duk muna cikin ƙoshin lafiya..."
Abbah shima hankalinsa kasa kwanciya yayi jin abinda Razhdeen ya sanar masa domin
in irin haka ta faru da Razhdeen to akwai abinda ya faru ko kuma zai faru, most
especially idan abun akan Roshan zai faru...
Haka Abbah ya ƙarawa motarsa gudu yana son isa yaga shin da gaske ne
abinda Razhdeen ya sanar masa ko kuma! In har ya haɗu da Roshan cikin ƙoshin
lafiya to sai dai akan wani nashi ne abun zai faru...
Su Ummy ne suke ta tambayar sa meya faru amma Abbah ya kasa basu amsa sai
ya tabbatar da idonsa..
Abbah bai tsaya a ko ina ba sai a part ɗin Roshan ko tsaya sauƙe su
Hajiya Kilishi bai yi ba, yana sauƙa ya nufi cikin babban falon gidan, suma sauran
haka suka bi bayansa,
suka tarar falon ba kowa, Abbah ya kalli Ummy ya ce "shiga ciki ki
ƙira mun Daughter..."
Ummy ta nufi part ɗin Baiwar ALLAH, can ta dawo tana faɗin "Abbah
bata nan fa..."
Abbah ganin tsayuwar bashi da amfani yasa shi nufan room ɗin Roshan
domin yafi son yayi ido huɗu da shi,
yana zuwa ya samu ƙofar ɗakin a buɗe, ganin Baiwar ALLAH tana rungume da
Roshan a ƙasin carpet yasa shi ƙarasa shiga da sauri yana faɗin "lafiya kuwa
Daughter me ya faru da shi..."
Ɗagowa tayi da jajayen idanuwan ta waɗanda suka kaɗa sukayi jawur tsabar
kuka ga bakinta duk jini yanda ta haɗe bakinta da na Roshan tana hura masa iskar
bakinta ko numfashin zai dawo...
Abbah ganin halin da Roshan yake ciki ne yasa shi firgita yayo kansa da
gudu yana "faɗin innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ashe gaskiyar Razhdeen,
gaskiyar Razhdeen, ciwon sa ne ya tashi..."
Haka yasa hannu ya ɗago shi yana faɗin "Daughter taya ni ɗaukar sa mu fita..."
Itama Baiwar ALLAH hannu tasa suka ɗago shi, suka fice falo da shi, su
Ummy ganin halin da Roshan yake ciki ne yasa duk suka nufo su...
Gaba ɗayan su kuka suka soma yi domin a halin da Roshan yake ciki ba mai
cewa yana da rai, haka suka shige cikin gidan tamkar anyi musu mutuwa, duk a
falo suka zazzauna Hajiya Kilishi ta zabga uwar tagumi tana tunani kala-kala a
ranta, maimakon tazo ta samu kowa cikin ƙoshin lafiya sai kuma ta tarar da wani
tashin hankali,
tana cikin wannan tunanin taji Pinky tana faɗin "ai duk kece kika jefa
shi cikin wannan mun sani, wancan lokacin ma saboda ke ciwon zuciyarsa ya tashi..."
tana nuna Baiwar ALLAH cikin ɓacin rai,
Baiwar ALLAH damuwar da yake kanta ma ya ishe ta haka take zubda hawaye ba
ƙaƙƙautawa...
Hajiya Kilishi idonta akan Pinky ta ce "kina ganin halin da take ciki
amma kina gaya mata cewa ita ta jawo? mijinta ne fa taya zatayi sanadiyar mutuwar
sa, haba Balkisu ki koyi iya magana dan ALLAH...."
Pinky ta ce "to naga bata sonsa wai Uncle Deen take so shine take
son hallaka shi..."
Ummy ta ce "innalillahi wai meyasa hakane Aunty Pinky dan Allah ki bar mu da
abinda yake damun mu..."
Suna cikin wannan halin sai ga Ammy ta fito daga part ɗinta tana sanye
da hijab har ƙasi da carbi a hannunta, jin motsin mutane ne yasa ta fito domin
ganin su waye ne saboda tasan gidan shuru yake ba kowa...
Ƴar tinny ganin Ammy yasa ta rufa da gudu tana faɗin "Ammy
nahh..."
Ammy ta rungumi Ƴar tinny tana dariya, tayi matuƙar farin cikin ganin yaran
gidan sosai.
Ammy ta ce "Ayyah fatan kin samu Mommy cikin ƙoshin lafiya ko?.."
Ammy bata yi tunanin har da uwar aka dawo ba domin bata lura da ita ba,
haɗa ido suka yi Ammy tasau murmushi tare da nufan wurin tana riƙe da
hannun Ƴar tinny,
tana zuwa wurin ta durƙusa a gaban Hajiya Kilishi tana gaishe ta
Ta ce "ina wuni Aunty, fatan kin iso lafiya..."
Hajiya Kilishi fuska a sake ta ce "lafiya ƙalau Amaryar mu, nagode sosai
kin riƙe mun yara cikin mutunci..."
Pinky tana farfara ido ta ce "an maida Auren Mommy da Abbah yanzu ta
dawo gidan mijin ta..."
Ammy cikin nuna farin ciki ta ce "Masha Allah, Allah mun gode maka,
wallahi naji daɗin hakan sosai, duk da bai gaya mun ba amma nayi farin ciki..."
Hajiya Kilishi wani irin harara ta wurga wa Pinky tana faɗin "bana son
iskanci fa, abokiyar ki ce ko kuma dake take maganar ta..."
Hajiya Kilishi ta ce "ayya kar ki damu, mun zo mun tarar da wani tashin
hankali, Roshan ba lafiya yanzu haka sun nufi hospital ciwon zuciyarsa ta tashi..."
Ammy dafe ƙirji tayi tana faɗin "subhanallahi wallahi ban sani ba..."
sai yanzu ta lura da Baiwar Allah dake ta kuka fuska tayi jawur,
Ammy tayo kanta tana faɗin "Allah sarki kiyi haƙuri Daughter Insha Allahu
zai samu sauƙi..."
Wayar Ummy ce ta fara ringing tana duba wa taga Uncle Deen ne,
ɗagawa tayi tare da yin sallama,
Daga ɓangaren Razhdeen cewa yayi "wai meyasa Abbah baya picking call ɗina ne
sannan ina ƙira Roshan shima baya ɗaga wa why?..."
Ummy tana kuka ta ce "Uncle Deen su Abbah suna hospital ciwon heart ɗin
Yaya Roshan ne ya tashi, sun tafi ko motsi baya iya yi sai aman jini yake..."
Har sun miƙe zasu fita sai ga ƙiran wayan Abbah ta wayar Ummy nan ma
ɗagawa tayi tana faɗin "Abbah gamu nan zuwa..."
Baiwar ALLAH tana jin haka data fashe da wani irin marayan kuka ai kawai
ta nufi bakin ƙofa da gudu ta fice..
Duk bayanta suka bi suna faɗin "ki dawo Daughter ina zaki je kuma..."
Gudu na gaske take ta buɗe gate ɗin farko ta fice, tana zuwa
gate na biyu nan ma ta buɗe ta wuce security da gudu, bayan ta suka bi suma suna
faɗin "lafiya kuwa me yake faruwa ne..."
ai kuwa nan da nan ta iso gate na uku wato babban gate nan ne bazata iya
buɗe wa da kanta ba haka take bubbugawa tana ihu, har sauran security suka tarar
da ita, sai ga su Hajiya Kilishi da Ammy da sauran suma sun iso ta,
Sojojin dake waje jin yanda ake ta bubbuga gate yasa su buɗe wa
suna faɗin "who's here?..."
Wani soja ne ya ce mata "kiyi haƙuri ki koma ciki domin jirginsu har
ya tashi sun tafi..."
Su Hajiya Kilishi da Ammy kam tin a gate na biyu suka dakata domin ba
ƙaramin gajiya sukayi ba, daƙer su Ummy suka ƙaraso wurin gate na huɗun yanda
Baiwar Allah ta dakata suma ɗin ba ƙaramin gajiya suka sha ba..
Daƙer aka rarrashi Baiwar Allah ta haƙura suna shiga mota aka komar dasu
can cikin gidan amma ta kasa dakatar da kukan....
A haka suka wuni har zuwa dare kowa a cikin damuwa yake,
Misalin ƙarfe 9 na dare duk suna zazzaune a babban falo sai suka ji an turo ƙofar
falo da ƙarfi, a matuƙar tsorace duk suka miƙe tsaye idonsu akan bakin ƙofa ganin
mutum sangamgam gashi a kwance saman bayansa sai haki yake domin a ruɗe ya iso,
kana ganinsa kasan ba'a cikin hayyacinsa yake ba,
Ummy ce ta ƙaraso yanda yake tana faɗin "Uncle Deen..." ta ƙarasa tana
kuka...
Duk suma suka nufi yanda yake a tsaye suna ambatar sunansa, banda
Baiwar Allah dake zaune tayi tagumi ko kallon yanda suke bata yi ba...
Haka yake zarya a cikin falon yana trying number Abbah amma baya
shiga, duk wasu numbobin da yake tsammanin zai samu labarin su Abbah amma basa
tafiya, cikin ɓacin rai da takaici haka yayi wurgi da wayarsa sai tin plasman, nan
danan wayar ta fashe, hatta plasman ɗin ma ya samu rauni domin da iya ƙarfinsa ya
wurga, durƙusawa yayi da gwiwowinsa yana cakurkuɗa sumar kansa lokaci guda ya
zabga wani irin gigitaccen ihu, ai kuwa nan da nan kamar wani mahaukaci ya fara
wargaza falon yaje ya janyo plasman yayi wurgi da shi, yaje ya buga glass dinning
har sai da shima ya dagargaza shi,
Baiwar Allah ganin zai iya ji mata rauni yasa ta tashi ba shiri taje
ta ɓuya a bayan Ammy...
Hajiya Kilishi ce tayi ƙarfin halin zuwa har yanda Razhdeen yake a
durƙushe itama taje ta tsuguna tana ambatar sunansa a hankali "Razhdeen! please
ka kwantar da hankalinka Roshan zai samu sauƙi, ai cuta ba mutuwa ba ne..."
Baiwar Allah haka take cakumar Ammy ta baya tana ɓuya zuciyar ta na
harbawa da ƙarfin gaske...
Gaba ɗayan su zaro ido suka yi suna kallon Razhdeen, ganin ya fito
yana riƙe da wuƙa, yana zuwa ya ɗaga hannunsa zai caka mata wuƙar ta zabga wani
irin gigitaccen ihu, dai dai lokacin da Abbah ya shigo a ruɗe ya ambaci sunansa "
*RAZHDEEN*" ..
Hajiya Kilishi kam ja da baya tayi sauran kaɗan ta faɗi ta baya badan Pinky
tayi saurin riƙe ta ba...
Abbah a ruɗe ya shigo falon tare da nufan yanda Razhdeen yake yana
faɗin "da hankalin ka kuwa Razhdeen? shin ka haukace ne?..."
Baiwar Allah tana kuka ta tashi da gudu ta nufi yanda sauran suke a tsaye
Ammy tayi saurin rungumo ta tana rarrashinta...
Razhdeen ya ɗago yana kallon Abbah sannan ya ce "yana ina Abbah? inason
ganin twins ɗina..."
Abbah ya ce "na baro shi acan cikin kulawa, gobe zan koma Insha Allahu..."
Razhdeen ya karɓi wayar idonsa akan Roshan wanda eyes ɗinsa suke lumshe
kamar mai yin bacci, ga yanda fuskar tayi fiyau ya ƙara yin kyau sosai...
A ɓangaren Roshan kuwa jin an ambaci sunansa kamar muryar Razhdeen yasa shi buɗe
eyes ɗinsa a hankali, yana kallon screen ɗin wayar dake yana sanye da oxygen ba
halin yin magana sai ido, ga babu riga a jikinsa sai tin zuciyarsa alamun anyi aiki
a wurin...
Abba ne ya karɓi wayar yana sanar da sauran ƴan gidan akan suma su zo su
duba shi, kowa yazo ya duba shi banda Baiwar Allah dake tsaye gefe guda har yanzu
ta kasa dawo wa hayyacinta, sai da Abbah yaje har yanda take ya nuna mata Roshan
yana faɗin "Daughter kinga mijin nakin ..."
Baiwar Allah idonta akan Roshan ga yanda hawaye yake faman zirya akan
fuskarta,
Razhdeen kuwa wani irin kallo yake watsa mata na ƙiyayya da tsana....
Washe gari da safe Abba ne zai koma Ethiopia wurin Roshan har
Razhdeen ya shirya zasu tafi tare Abbah ya bashi haƙuri akan ya zauna da iyalansa
domin suma bazasu juma ba...
Razhdeen yana tsaye shima Ƴar Amana ta faɗo masa a rai domin
jiya bai samu hankalin zuwa gidan sa,
A lokacin ya shiga mota shima ya tafi..
waiwayo wa tayi ta tsaida idonta akansa, tana kallonsa ta zaro ido waje cike
da mamaki ta miƙe tsaye bata san lokacin da ta rungume shi ba, shima rungumarta
yayi sosai tare da ɗagata saman kafaɗar sa,
ta ɗago suna fuskantar juna da murmushi akan fuskarta ya ce "my
Sarah I missed you..."
Haɗe rai tayi tana shirin yin kuka lokaci guda ta fara kai masa duka
akan ƙirjinsa kuma yana ɗauke da ita yaƙi sauƙe ta, da haka ya haura da ita
upstairs, daman ita kaɗai ce a gidan madam Blessing bata nan,
Daga baya aka shigo da jakakkunan sa...
★★★★★★★
Ƙasar Jidderh.
Ramlat da Maamie yanzu zaman gava suke ta zabgawa babu mai kula kowa sannan Ramlat
ta haɗa kai da Indo Amaryar Mai martaba hatta girki tare suke yi, haka zasu zauna
su sha hirar su amma da zarar Maamie ta shigo falon sai Ramlat ta bar wurin,
Maamie tayi zaryar zuwa wurin bokan ta akan ta juyar da ƙwaƙwalwar
Ramlat akan sai abun da ta ce mata amma har yanzu ba'ayi nasara ba, domin haɗewar
da tayi da Indo yasa ta koyi yin ibada sosai, sallar dare da karatuttukan Alkur'ani
da sauran litattafan addini,
Mai martaba ya yi wa Ramlat faɗa akan ta dawo kula Yayarta amma fur
taƙi sai cewa tayi "babu abinda take ƙaruwa da shi a wurin Maamie sai jahilci don
haka yanzu ta dawo hannun Indo..."
Abinda yasa Ramlat ta koma wurin Indo shine a lokacin da sukayi faɗa
Maamie korar kare tayi wa Ramlat akan tabar gidanta tunda gidan mijinta ne...
Shine dalilin da yasa Mai martaba ya ce ta zauna a part ɗin Indo, shi ya
karɓe ta...
Dalilin faɗansu kuwa shine Maamie ta dage akan sai Ramlat ta koma
Nigeria taje tana shishshigewa Razhdeen ko hankalinsa zai karkata kanta kuma haka
bokanta ya sanar mata akan dole sai Ramlat ta koma gidan Chief da zama,
Ita kuma Ramlat ta ce "nan duniya bazata ƙara shiga shirgin Razhdeen ba
domin bazai je ya hallaka ta ba ita kuwa maamie tana gidan mijinta, hakan yasa
suka fara musayar yawu har Maamie tayi wa Ramlat dukan tsiya, saboda Ramlat taƙi
amince da Razhdeen dalilin haka yasa Maamie ta kori Ramlat shi kuma Mai martaba ya
ce ta dawo hannunsa sannan ya bayarta a Indo ....
Kuma Ramlat tana mutunta Indo sosai daman can tanada hankali zugar Maamie
ne yasa ta fita a ran kowa, Maamie ta shafa mata kashin kaji....
Ramlat tayi shuru tana sauraronsa daga baya ta ce "Abul har cikin
zuciyata ina son Yaya Roshan amma nasan shima ba sona yake ba dole zan haƙura
acikin samari na zan zaɓi ɗaya, aban lokaci zuwa nan da kwana biyu Insha Allahu
zan fitar..."
Mai martaba ya ce "Masha Allah..." kafin ya ƙara furta wata magana yaji
wayarsa tana ringing, dubawar da zai yi sai yaga number Abbah, ɗagawa yayi suka
gaisa ya kuma tambaye shi jikin Roshan duk da har yanzu basu koma Nigeria ba, daga
baya Abbah yake sanar masa cewa "mai martaba daman inason sanar maka da wani abun
mamaki ne..."
Abbah ya ce "yanzu haka muna Ethiopia gobe Insha Allahu zamu koma Nigeria jikin
Roshan yayi sauƙi sosai an sallame mu, amma ya sanar mun cewa wai zai yi Aure na
zaɓa masa matar da zai Aura..."
Abbah ya ce "wallahi ya ce haka kawai yake son ƙara Aure, amma yace duk matar da
muka zaɓa masa shi zai zauna da ita, shine nace bari na tambayeka ko ita Ramlatu
tana sonsa ne ko kuma?..."
Dariya Mai martaba yayi sannan ya ce "mai son zama da mace ɗaya yau dai an wayi
gari mata biyu gare shi...".
Ramlat har da sujjadar ta tsabar farin ciki, ta rinƙa hamdala tana gode wa
ALLAH, tare da faɗin "Allah ya amshi addu'a ta, ashe addu'a tana da rana, tabbas
na yadda cewa boka ko malami basu isa su tsara abinda Allah bai tsara ba...."
Mai martaba shima fatan alkhairi yayi mata sannan ya bata umarni da ta
tafi...
Indo ta ce "goro fari tass meya faru kamar anyi miki albishir da ƙasa mai
tsarki..."
Ramlat ta ce "Aunty Aisha Yaya Roshan zai ƙara Aure kuma Ni zai Aura,
kuma Allah yasa naga tsinannen bokan da ya isa ya raba yaga ikon Allah, tinda Allah
ne ya tsara babu mahalukin da ya isa ya raba..."
ta ƙarasa maganar tana kallon Maamie wacce take ta kumbura, ita
takaicin ta Ƙanwarta wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya yau ta gujeta ta koma hannun
kishiyar ta...
Maamie a fusace ta miƙe tare da jan wata doguwar tsuka ta haura saman
upstairs can room ɗinta ....
Ramlat ta ƙara volume da cewa "bin maganar bokaye da malamai dai rashin
imani ne da jahilci..."
Indo ta maki cinyarta tana girgiza mata kai alamar kar ta sake faɗin haka....
★★★★★★★
Bayan isar su Abbah Nigeria a babban falon Abbah suka zauna kowa sai dai yaje can
ya gaishe da Roshan domin baya son hayaniya shiyasa ya fake a part ɗin Abbah wanda
ba kowa ne yake zuwa can ba...
Baiwar ALLAH ganin yanda Roshan ya sauya mata ne yasa ranta sosuwa,
babu yanda ta iya haka ta durƙusa har ƙasi tana gaishe shi da jiki...
Amsa mata yayi cikin sassanyar murya daga ƙarshe ya miƙe tsaye dai-dai
lokacin da shima Razhdeen ya miƙe zai basu wuri.
Roshan ya kalli Razhdeen sannan ya ce "ha'a My man ya dai ka tashi? nayi tunanin
zaku ɗan fahimci juna ne...."
Bayan kwana sati da dawowar Roshan gyare-gyare aka fara yi a part ɗinsa
gaba ɗaya part ɗin an sauya kalan pantin gidan, duk kayan furniture an chanchanza
su saboda Abbah yaje har ƙasar Jidder sunyi magana sosai da mai martaba akan
bikin, sannan suka yanke cewa next week za'a ɗaura Aure, Abbah ya ce duk wasu
ɗawainiyan kayan ɗaki da sauran abubuwan duk ya ɗauke nauyinsa zai yi,
Ramlat farin ciki kamar bazata mutu ba, amma sai dai Roshan bai ƙira
wayanta ko sau ɗaya ba sannan idan ta ƙira baya ɗagawa, sai abun yake bata
mamaki....
Pinky da Rukky suma murna Yaya Roshan zai ƙara Aure kuma Ramlat zai
Aura daman ƙawarsu ce, kuma ba son Baiwar Allah daman suke ba...
Gaba ɗaya Baiwar ALLAH ta kasa kwantar da hankalinta, duk abin duniya
yabi ya ishe ta ga yanzu Roshan zai ƙara Aure, ita kaɗai tana kwance akan gadonta
sai sharar kuka take ga wani irin kishi da yake damun ta...
Tana cikin wannan halin taji ana knocking ƙofar bedroom ɗinta da sauri ta
tashi tayi tunanin Roshan ne domin tinda ya dawo ko kallonta baya son yi balle ya
saurare ta kuma tana muradin jin muryarsa...
Tana buɗe ɗakin ta gànshi yana tsaye sai ƙare ta yake da kallo, ita
kuma goge hawayen fuskarta ta soma yi tana sakin murmushi, ko kulata bai yi ba haka
ya shige ciki ya zauna a bakin gado ta, kallonta ya yi sannan ya ce "zauna
mana..." itama zama tayi a bakin gadon zuciyarta na bugun uku-uku domin tana
fargaban jin abinda zai ce mata yanda taga fuskar sa nan babu annuri....
Roshan ya ce "karɓi mana akwai ayyuka a gabana kinsan next week Aure na,
ina buƙatar yin wasu shirye-shirye..."
Baiwar Allah juyowa tayi tana kallon takardar hannun sa ga hawaye yaƙi
tsayuwa mata,
Hannu tasa ta karɓa ta ɗago tana kallonsa shima kallonta yake, idan ta
akansa haka ta saita tsakiyar takardar ta ɓe ra shi gida biyu sannan ta ƙara yaga
wa, haka ta yayyaga takardar idonta yayi jawur...
Baiwar ALLAH ta ce "Yaya Roshan kowa yasan zakayi Aure, kuma Abbah da
Uncle mai martaba sun tsayar da maganar bai kamata lokaci guda a watsa musu ƙasa a
ido ba tinda kai ka buƙaci yin Auren..."
Baiwar ALLAH ta ce "Abokiyar zama dai, baka ga Mommy da Ammy yanda suke zaman
lafiya ba, kullum Abbah a cikin farin ciki yake sun haɗe kansu..."
Roshan ya ce "shikenam amma kinsan dai kwanan nan zan koma ƙasar
Egyph da aiki shekara biyun da aka yanke mun yayi zan koma, zan tafi da ɗaya daga
cikin ku amma son samu ace ke kaɗai ce dani,
gaskiya Ammata banji daɗin ƙin sanar mun da kika yi ba, har sai da na nemi
Aure tukun zaki sanar mun abinda ke ranki why?..."
Baiwar Allah ta ce "kayi haƙuri mijina nayi laifi sannan na aikata kuskure
a yafe mun dan Allah..."
Roshan ya ce "na yafe miki Ammata nah...." ya ƙarasa tare da ja mata hanci
suka sake rungumar juna....
zuwa tayi ta buɗe bayan taji an ɗan dakata da yin knocking, tana
buɗe wa bata ga kowa ba sai wani baƙin leda da ta gani an ajiye a ƙasin ƙofar,
lelleƙa ko ina tayi bata ga kowa ba daga baya ta ɗauki ledar ta koma ciki tare da
rufe ƙofar...
Pinky da Rukky ne suka ɓuya suna leƙenta har ta koma ciki bayan
sun tabbatar ta ɗauki ledar amma ba haka suka so ba, sun so shi Roshan ne ya fito
ya ɗauka, haka suka bar part ɗin suka koma can part ɗin su ....
Baiwar Allah room ɗinta ta shiga ta zauna a bakin gado ta ciro abun
leda taga wani ƙaton gift ata baya an rubuta "from Baiwar ALLAH..."
Abun kuma sai ya ɗaure mata kai cike da mamaki take faɗin "Ni kuma?..."
tana buɗe ledar jikin gift ɗin taga wani danƙareren abaya mai sheƙin
gaske ga kuma wata takarda ta faɗo, cikin da mamaki ta ɗauka tareda buɗe takardar
ta soma karanta wa kamar haka "Amincin Allah ya tabbata a gareki gimbiyar mata,
kiyi haƙuri a bisa abubuwan da nake miki a cikin mutane nake nuna bana sonki, kema
kinsan ina matuƙar ƙaunar ki domin bazan iya ɗanɗanar zuman ki na barki haka kawai
ba, kina da zaƙin da ba ko wata mace ce take da shi ba, please haɗuwar mu a hotel
ina jiranki da yamma, tinda Roshan ya dawo dole sai a hotel zamuna haɗuwa, kar ki
bar Roshan ya sani domin ni da kaina zan zo na ɗauke ki ba tare da kowa ya sani ba,
sannan ga saƙon Abayar da kika ce na kawo miki, ki kula mun da kan ki, *DAGA
MASOYINKI RAZHDEEN TWINS ƊIN MIJINKI....* "
A zabure Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye hawaye duk ya wanke takardar domin
tinda ta fara karanta wa take zubar da hawaye tsabar takaicin sharrin da aka ƙulla
mata saboda a rabata da mijinta,
cikin kuka take furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un na shiga
uku wannan wani irin ƙalubale nake fuskanta a rayuwa ta ce, haba Razhdeen ka rasa
wani irin sharri zaka yi mun sai na zina? Ƙiyayyar da kai haka daman wayyo Allah
nahh..."
Shi kuwa Razhdeen yana zaune a falo yana jiran fitowar Ƴar Amana
zai kaita school domin yanzu tinda ya dawo yake kaita da kansa saboda tsaro, yanzu
ya ga ba ƙaramar yarinya bace tana buƙatar tsaro domin ko security yanzu bai yadda
da ya rinƙa kaita ba, ya kasa yadda shin kishinta yake ne ko kuma duk a cikin
tsaro ne....
Ƴar Amana tana can room ɗinta tana ta faman gyare-gyare da shirye-shirye
ta kammala saka uniform ɗinta tsab sai kallon mirror take domin tana so koda yaushe
ta rinƙa burge Razhdeen, domin taga duk lokacin da suke tare yana rikice wa sosai
a kanta ita kuma hakan burgeta yake domin ba ƙaramin jinsa take a ranta ba, wuni
guda idan bata gan shi ba ta rinƙa shiga damuwa kenam, yanzu ko a makaranta bata
nutsuwa tayi karatu sai fuskarsa ya rinƙa mata gizo, a koda yaushe tunaninsa take,
tunani yaƙi ƙarewa ta rasa gane kanta, tana jin wani iri sosai akan sa, ko bacci
zata yi sai ta daɗe tana kallon fuskar sa tukun ta iya komawa room ɗinta,
(Baƙuwar lovayya kenam 😁😁)
Tsayawa tayi a gaban mirror bayan ta gama shirinta tsab tana kallon
kanta amma sai dai hankalinta ba'a kanta yake ba ta shiga dogon tunani kuma tunanin
bazai wuce Razhdeen ɗin ba....
Baiwar ALLAH tsayawa tayi a bakin ƙofa tana bubbuga ƙafar falo da
ƙarfin gaske domin a cikin ɓacin rai take bugawa tana zumuɗin yazo ya buɗe ta yi
masa wankin babban bargo...
Yana zaune haka yake jin bugun ƙofa kamar za'a ɓalla ƙofar tsabar
ƙarfin bugun,
Haka shima ya tashi a fusace yayi bakin ƙofar zai buɗe domin ya ci alwashin
kowa waye zai ya zabge shi da mari indai ba Abbah ko Roshan ba.....
*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*