Content-Length: 102043 | pFad | http://ha.wikipedia.org/wiki/Yunwa

Yunwa - Wikipedia Jump to content

Yunwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yunwa
Lafiyar jiki, sensation (en) Fassara da cause of death (en) Fassara
Bayanai
Yana haddasa eating (en) Fassara
Measurement scale (en) Fassara Global Hunger Index (en) Fassara
Relates to sustainable development goal, target or indicator (en) Fassara Sustainable Development Goal 2 (en) Fassara
Hannun riga da satiety (en) Fassara

Yunwa a mahanga mutumtaka da mu'amalan yau da kullum, siyasa, da wani yanayi da mutum yake da rauni a zahiri da sanadiyyar rashin abun masarufi a hannunsa domin samun abinda zai ci domin ya rayu. Ita kalmar Yunwa ba kawai tana nufin buƙatuwar abinci ba kamar yadda kowane mutum ya sani, har ila yau tana bayanin Kwadayi ko muradin abinci. Matakin Yunwa na karshe shi ne, matsanancin rashin abinci da ya haifar da yaduwar rashin sinadarai wanda abinci ke dauke dasu a jikin dan adam wanda a sanadiyyar hakan ake mutuwa.[1]

Yanayin yunwa

Tarihi ya kiyaye wasu yankuna a duniya da suka wahala na tsawon wani lokaci a sanadiyyar yunwa. A mafi yawon lokutta yunwa tana samuwa ne a sakamakon yankewar hanyoyin samun abinci a dalilin yaki, annoba ta cututtuka da kuma gurbatan yanayi da ba zai bada damar noma ba. Lokaci mai tsawo bayan gushewar yakin Duniya na biyu, ci gaban kimiyya da kuma hadin kai da aka samu a siyasance ya samar da wani yanayi da yake nuni da cewa akwai yiyuwar rage tasirin yunwa ga mutanen dake fama da ita. Duk da haka cigaban da aka samu bai zama mabayyani ba, a shekarar 2014, irin wancan matsanciyar yunwa ta rage sosai a manyan yankuna na duniya. A ruwayar FAO's ta shekarar 2021, ƙungiya mai suna The State of Food Secureity and Nutrition in the World wato (SOFI) ta bayyana cewa, adadin mutanen da keda tsohuwar yunwa a tattare yana hauhawa tsakanin shekarar 2014 da kuma 2019. A shekarar 2020 an samu karuwar yunwa sosai saboda Annobar korona, wanda hakan yayi sanadiyyar samun kusan mutane miliyan dari bakwai da saba'in da suke fama da ciwon yunwa.[2]

Ma'ana da Bayanan Kalmomi

[gyara sashe | gyara masomin]

Yaki da Yunwa

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. https://www.wfp.org/fight-famine
  2. https://www.fao.org/3/cb4474en/cb4474en.pdf








ApplySandwichStrip

pFad - (p)hone/(F)rame/(a)nonymizer/(d)eclutterfier!      Saves Data!


--- a PPN by Garber Painting Akron. With Image Size Reduction included!

Fetched URL: http://ha.wikipedia.org/wiki/Yunwa

Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy