Jump to content

Femi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Femi
unisex given name (en) Fassara
Bayanai
Suna a harshen gida Femi
Harshen aiki ko suna Yarbanci
Tsarin rubutu Baƙaƙen boko
Soundex (en) Fassara F500
Cologne phonetics (en) Fassara 36
Caverphone (en) Fassara FM1111

Fẹ́mi Sunan da aka bawa wani a Nijeriya ne, gama garin sunan wanda ake raɗawa namiji, na asalin Yarabawa ne, wanda ke nufin "ƙaunace ni".[1][2] Femi galibi nau'i ne na "Olufemi" wanda ke nufin "Ubangiji yana ƙaunata" ("Olu" na nufin Ubangiji ko Shugaba a yaren Yarbanci).

Ƙarin bayani

[gyara sashe | gyara masomin]

"Olufemi" na iya zama "Oluwafemi" (idan an ƙara wa tsakanin Olu...Femi. Harwayau kalmar Femi ana iya kara mata kalmomin; (Olurun, Jesu, Ni, Baba). Idan an haɗa zai bada sunaye kamar haka; Olorunfemi, Jesufemi, Nifemi, Babafemi, da sauransu.

Mutanen da ake kira Femi sun haɗa da:

Ƴan wasan kwaikwayo

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Femi Fani-Kayode (an haife shi a shekara ta 1960), ɗan siyasan Nijeriya
  • Femi Gbaja Biamila (an haife shi a shekara ta 1962), ɗan siyasan Nijeriya
  • Femi Oluwole (an haife shi a shekara ta 1990), ɗan rajin siyasa na Biritaniya
  • Femi Pedro (an haife shi a shekara ta 1955), ɗan siyasan Nijeriya
  • Femi Okurounmu, ɗan siyasan Najeriya, Sanata mai wakiltar Ogun ta Tsakiya
  • Femi Adesina, ɗan jaridar Najeriya kuma jami’in gwamnati

Yan wasanni

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Femi, sunan barkwanci na Oluwafemi Ajilore (an haife shi a shekara ta 1985), ɗan wasan ƙwallon ƙafa a yanzu yana taka leda a FC Groningen
  • Femi Babatunde(an haife shi a shekara ta 1986), ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Nijeriya da ke buga wa ƙungiyar kwallon kafa ta Kwara United FC yanzu
  • Femi Ilesanmi (an haife shi a shekara ta 1991), ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta Ingila
  • Femi Joseph (an haife shi a shekara ta 1990), yanzu ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya yana buga wa ƙungiyar ƙwararru ta Liberty FC
  • Femi Opabunmi (an haife shi a shekara ta 1985), yanzu haka yana wasa a ƙungiyar Shooting Stars FC
  • Femi Orenuga (an haife shi a shekara ta 1993), ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta Ingila a yanzu haka yana wasa ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton

Marubuta da Yan Jarida

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Femi Osofisan (an haife shi a 1946), marubucin Nijeriya
  • Femi Euba, ɗan wasan Najeriya kuma mai wasan kwaikwayo
  • Femi Oguns, ɗan wasan kwaikwayo na Burtaniya
  • Femi Oke (an haife shi a shekara ta 1966), ɗan jaridar gidan talabijin na Burtaniya, yanzu haka yana New York
  • Caleb Femi, mawaƙin Biritaniya kuma tsohon matashin da ya ci kyautar zuwa London.
  • Femi Johnson, dan jaridar gidan talabijin na Najeriya tare da Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA)
  • Femi Falana, Lauyan Najeriya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam.
  • Femi Oshagbemi, haifaffen Ba'amurke Masanin harka, Masanin Ilimin Cututtuka da Kwarewar lafiyar Jama'a
  • Femi Ojo, haifaffen Najeriya Nurse Rijista, kuma Kwararren Kiwon Lafiyar Jama'a, a California
  • Femi Otedola (an haife shi a shekara ta 1967), hamshakin ɗan kasuwar nan ɗan Nijeriya
  • Femi Kuti (an haife shi a shekara ta 1962), mawaƙin Najeriya kuma babban ɗa ne na majagaba mai suna Fela Kuti
  • Femi John Femi (an haife shi a shekara ta 1945), Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya
  • Femi Temowo, mawaƙin jazz na Burtaniya
  • La Fémis Makarantar Ilimin Hoto da Sauti ta ƙasa.
  1. Allisun Jones (2001). Exotic Names for the New Millennium. Neoteric Publications. p. 40. ISBN 9780965733847.
  2. Connie Lockhart Ellefson (1987). The Melting Pot Book of Baby Names. Pennsylvania State University. Betterway Publications. p. 132. ISBN 9780932620842.
pFad - Phonifier reborn

Pfad - The Proxy pFad of © 2024 Garber Painting. All rights reserved.

Note: This service is not intended for secure transactions such as banking, social media, email, or purchasing. Use at your own risk. We assume no liability whatsoever for broken pages.


Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy