Jump to content

Florence Devouard

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Florence Jacqueline Sylvie Devouard, (née Nibart; an haife ta 10 ga watan Satumba shekarar alif 1968) wanda kuma injiniyan noma ce ta ƙasar Faransa wacce ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin amintattu na Gidauniyar Wikimedia tsakanin watan Oktoba, shekarar 2006 da Yuli 2008.

Devouard na da digirin injiniya a fannin aikin gona daga ENSAIA da DEA a fannin ilimin halittu da fasahar halittu daga INPL.[1]

A ranar 9 ga watan Maris na 2008, an zaɓi Devouard a matsayin memba na majalisar gunduma na Malintrat.[2]


Devouard ta shiga hukumar Gidauniyar Wikimedia a watan Yuni 2004 a matsayin shugaban kwamitin amintattu, wanda ta gaji Jimmy Wales.[3] Ta yi aiki a Hukumar Ba da Shawara ta Gidauniyar tun Yuli 2008.[4]

Ta kafa wani reshe na Wikimedia a ƙasar Faransa a cikin watan Oktoba 2004, ta kasance mataimakiyar shugabar hukumar daga 2011 har zuwa Disamba 2012.[5]

A ranar 16 ga Mayu 2008, an mai da ta jaruma a cikin tsarin Girmama na Ƙasar Faransa, wanda ma'aikatar harkokin waje ta gabatar a matsayin "shugaban wata gidauniya ta duniya".[6]

Duba Wannan

[gyara sashe | gyara masomin]
pFad - Phonifier reborn

Pfad - The Proxy pFad of © 2024 Garber Painting. All rights reserved.

Note: This service is not intended for secure transactions such as banking, social media, email, or purchasing. Use at your own risk. We assume no liability whatsoever for broken pages.


Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy